llah ne hasken sammai da qasa . Misalin haskensa tamkar alkuki ne da fitila take a cikinsa;

Allah ne hasken sammai da qasa[1]. Misalin haskensa tamkar alkuki ne da fitila take a cikinsa; fitilar kuma tana cikin qarau; qaran kuma tamkar tauraro ne na lu’ulu’u, ana kunna ta da man bishiya mai albarka ta zaitun, ita ba daga mahudar rana take ba kuma ba daga mafaxarta ba, kuma manta kamar zai kama da kansa ko da wuta ba ta tava shi ba. Haske kan haske. Allah Yana shiryar da wanda Ya ga dama zuwa ga haskensa. Kuma Allah yana buga misalai ne ga mutane. Allah kuwa Masanin komai ne