مِن فِرۡعَوۡنَۚ إِنَّهُۥ كَانَ عَالِيٗا مِّنَ ٱلۡمُسۡرِفِينَ
Daga Fir’auna. Lalle shi ya kasance mai girman kai daga mavarnata
وَلَقَدِ ٱخۡتَرۡنَٰهُمۡ عَلَىٰ عِلۡمٍ عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ
Kuma haqiqa Mun fifita su (Banu Isra’ila) bisa saninmu a kan (sauran) talikai
وَءَاتَيۡنَٰهُم مِّنَ ٱلۡأٓيَٰتِ مَا فِيهِ بَلَـٰٓؤٞاْ مُّبِينٌ
Muka kuma ba su wasu ayoyinmu waxanda a cikinsa akwai jarrabawa mabayyaniya
إِنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ لَيَقُولُونَ
Lalle waxannan (kafiran Makka) tabbas suna cewa:
إِنۡ هِيَ إِلَّا مَوۡتَتُنَا ٱلۡأُولَىٰ وَمَا نَحۡنُ بِمُنشَرِينَ
“Babu wata mutuwa da za mu yi sai mutuwarmu ta farko, kuma mu ba za a tashe mu ba
فَأۡتُواْ بِـَٔابَآئِنَآ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
“To ku zo mana da iyayenmu idan kun kasance masu gaskiya.”
أَهُمۡ خَيۡرٌ أَمۡ قَوۡمُ تُبَّعٖ وَٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ أَهۡلَكۡنَٰهُمۡۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ مُجۡرِمِينَ
Yanzu su ne suka fi ko kuwa mutanen Tubba’u[1] da waxanda suke a gabaninsu? Duk Mun hallakar da su. Lalle sun kasance masu manyan laifuka
1- Mutanen Makka sun yarda cewa qabilun Larabawan Himyar da Saba’u waxanda ake kira mutanen Tubba’u na qasar Yaman sun fi su qarfin Mulki da jin daxin duniya.
وَمَا خَلَقۡنَا ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَيۡنَهُمَا لَٰعِبِينَ
Ba Mu kuma halicci sammai da qasa da abin da yake tsakaninsu don wasa ba
مَا خَلَقۡنَٰهُمَآ إِلَّا بِٱلۡحَقِّ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ
Ba Mu halicce su ba sai don gaskiya, sai dai kuma yawancinsu ba su san haka ba
إِنَّ يَوۡمَ ٱلۡفَصۡلِ مِيقَٰتُهُمۡ أَجۡمَعِينَ
Lalle ranar alqiyama ne lokacin da aka qayyade musu gaba xaya
يَوۡمَ لَا يُغۡنِي مَوۡلًى عَن مَّوۡلٗى شَيۡـٔٗا وَلَا هُمۡ يُنصَرُونَ
Ranar da wani masoyi ba zai amfana wa masoyinsa komai ba, su kuma ba za a taimaka musu ba
إِلَّا مَن رَّحِمَ ٱللَّهُۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
Sai fa wanda Allah Ya ji qan sa. Lalle Shi ne Mabuwayi, Mai rahama
إِنَّ شَجَرَتَ ٱلزَّقُّومِ
Lalle itaciyar Zaqqumu
طَعَامُ ٱلۡأَثِيمِ
Abincin mai babban zunubi ce
كَٱلۡمُهۡلِ يَغۡلِي فِي ٱلۡبُطُونِ
(Kuma) kamar narkakkiyar darma, tana tafarfasa a cikin ciki
كَغَلۡيِ ٱلۡحَمِيمِ
Kamar tafasar ruwan zafi
خُذُوهُ فَٱعۡتِلُوهُ إِلَىٰ سَوَآءِ ٱلۡجَحِيمِ
(Za a ce da mala’iku): “Ku kama shi sannan ku ja shi tsakiyar wutar Jahima
ثُمَّ صُبُّواْ فَوۡقَ رَأۡسِهِۦ مِنۡ عَذَابِ ٱلۡحَمِيمِ
“Sannan ku kwarara azabar ruwan zafi a tsakiyar kansa.”
ذُقۡ إِنَّكَ أَنتَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡكَرِيمُ
(Sai a ce da shi): “Xanxana, lalle kai xin nan kai babban mutum ne mai daraja[1]
1- Watau kamar yadda yake xaukar kansa a duniya. Ana faxa masa haka cikin izgili da ba’a.
إِنَّ هَٰذَا مَا كُنتُم بِهِۦ تَمۡتَرُونَ
(Za a ce da kafirai): “Lalle wannan ne abin da kuka kasance kuna shakkar sa.”
إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي مَقَامٍ أَمِينٖ
Lalle masu taqawa suna cikin wani amintaccen wuri
فِي جَنَّـٰتٖ وَعُيُونٖ
Cikin lambuna da idanuwan ruwa
يَلۡبَسُونَ مِن سُندُسٖ وَإِسۡتَبۡرَقٖ مُّتَقَٰبِلِينَ
Suna saye da tufafi na alharini mai shara-shara da mai kauri suna fuskantar juna
كَذَٰلِكَ وَزَوَّجۡنَٰهُم بِحُورٍ عِينٖ
Kamar haka ne, Muka kuma aura musu (‘yan matan) Hurul-Ini
يَدۡعُونَ فِيهَا بِكُلِّ فَٰكِهَةٍ ءَامِنِينَ
A cikinta (Aljannar) suna kiran a kawo musu duk wani kayan marmari, suna cikin aminci
لَا يَذُوقُونَ فِيهَا ٱلۡمَوۡتَ إِلَّا ٱلۡمَوۡتَةَ ٱلۡأُولَىٰۖ وَوَقَىٰهُمۡ عَذَابَ ٱلۡجَحِيمِ
Ba za su xanxani wata mutuwa a cikinta ba sai dai mutuwar farko; Ya kuma tserar da su daga azabar wutar Jahima
فَضۡلٗا مِّن رَّبِّكَۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ
(Wannan) falala ce daga Ubangijinka. Wannan shi ne babban rabo
فَإِنَّمَا يَسَّرۡنَٰهُ بِلِسَانِكَ لَعَلَّهُمۡ يَتَذَكَّرُونَ
To kawai Mun sauqaqe shi ne (wato Alqur’ani) da harshenka, don su wa’azantu
فَٱرۡتَقِبۡ إِنَّهُم مُّرۡتَقِبُونَ
To ka saurara, lalle su ma masu sauraro ne