وَٱلنَّجۡمِ إِذَا هَوَىٰ
Na rantse da tauraro yayin da ya faxi
مَا ضَلَّ صَاحِبُكُمۡ وَمَا غَوَىٰ
Mutumin naku[1] bai vata ba, kuma bai kauce hanya ba
1- Watau Annabi Muhammadu ().
وَمَا يَنطِقُ عَنِ ٱلۡهَوَىٰٓ
Kuma ba ya yin magana bisa son rai
إِنۡ هُوَ إِلَّا وَحۡيٞ يُوحَىٰ
Shi (Alqur’ani) ba wani abu ne ba in ban da wahayi da ake yiwo (masa)
عَلَّمَهُۥ شَدِيدُ ٱلۡقُوَىٰ
Mai tsananin qarfi ne (watau Jibrilu) ya koyar da shi
ذُو مِرَّةٖ فَٱسۡتَوَىٰ
Mai kyawawan halitta ne, sai ya daidaita
وَهُوَ بِٱلۡأُفُقِ ٱلۡأَعۡلَىٰ
Alhali kuwa shi yana a sassa na can sama
ثُمَّ دَنَا فَتَدَلَّىٰ
Sannan sai ya kusanto, sai ya qara matsawa[1]
1- Watau Jibrilu () ya kusanto Annabi () ya matso kusa don yi masa wahayi.
فَكَانَ قَابَ قَوۡسَيۡنِ أَوۡ أَدۡنَىٰ
Sai ya kasance kamar kusancin kamu biyu ko qasa da haka
فَأَوۡحَىٰٓ إِلَىٰ عَبۡدِهِۦ مَآ أَوۡحَىٰ
Sannan (Allah) Ya yiyo wahayin abin da Ya yi wahayi zuwa ga Bawansa (Ma’aiki)
مَا كَذَبَ ٱلۡفُؤَادُ مَا رَأَىٰٓ
Zuciyar (ta Ma’aiki) ba ta yi qaryar abin da ta gani ba
أَفَتُمَٰرُونَهُۥ عَلَىٰ مَا يَرَىٰ
Yanzu kwa riqa jayayya da shi kan abin da yake gani?
وَلَقَدۡ رَءَاهُ نَزۡلَةً أُخۡرَىٰ
Haqiqa ya gan shi (Jibrilu) a wani karon ma[1]
1- Watau lokacin Isra’i da Mi’iraji, inda ya gan shi a halittarsa ta asali.
عِندَ سِدۡرَةِ ٱلۡمُنتَهَىٰ
A wurin Magaryar tuqewa
عِندَهَا جَنَّةُ ٱلۡمَأۡوَىٰٓ
A wurinta ne Aljannar makoma take
إِذۡ يَغۡشَى ٱلسِّدۡرَةَ مَا يَغۡشَىٰ
A yayin da abin da ya lulluve Magaryar (na ban mamaki) ya lulluve ta
مَا زَاغَ ٱلۡبَصَرُ وَمَا طَغَىٰ
Ganin (nasa) bai karkace ba, kuma bai zarme ba
لَقَدۡ رَأَىٰ مِنۡ ءَايَٰتِ رَبِّهِ ٱلۡكُبۡرَىٰٓ
Haqiqa ya ga wasu ayoyin Ubangijinsa manya-manya
أَفَرَءَيۡتُمُ ٱللَّـٰتَ وَٱلۡعُزَّىٰ
Ku ba ni labarin (gumakan) Lata da Uzza
وَمَنَوٰةَ ٱلثَّالِثَةَ ٱلۡأُخۡرَىٰٓ
Da Manata cikon ta ukunsu
أَلَكُمُ ٱلذَّكَرُ وَلَهُ ٱلۡأُنثَىٰ
Yanzu xa namiji zai zama naku, Shi kuma Ya tashi da ‘ya mace?
تِلۡكَ إِذٗا قِسۡمَةٞ ضِيزَىٰٓ
Idan haka ne wannan rabon na zalunci ne[1]
1- Domin ya qunshi Fifita mahaluki a kan Mahalicci.
إِنۡ هِيَ إِلَّآ أَسۡمَآءٞ سَمَّيۡتُمُوهَآ أَنتُمۡ وَءَابَآؤُكُم مَّآ أَنزَلَ ٱللَّهُ بِهَا مِن سُلۡطَٰنٍۚ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّ وَمَا تَهۡوَى ٱلۡأَنفُسُۖ وَلَقَدۡ جَآءَهُم مِّن رَّبِّهِمُ ٱلۡهُدَىٰٓ
Su ba komai ba ne face sunaye da kuka sa musu, ku da iyayenku, Allah bai saukar muku da wata hujja ba game da su. Ba abin da suke bi sai zato da son zuciya. Haqiqa kuwa shiriya ta zo musu daga Ubangijinsu
أَمۡ لِلۡإِنسَٰنِ مَا تَمَنَّىٰ
Ko kuwa sai mutum ya sami abin da yake buri ne?
فَلِلَّهِ ٱلۡأٓخِرَةُ وَٱلۡأُولَىٰ
To lahira da duniya duka na Allah ne
۞وَكَم مِّن مَّلَكٖ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ لَا تُغۡنِي شَفَٰعَتُهُمۡ شَيۡـًٔا إِلَّا مِنۢ بَعۡدِ أَن يَأۡذَنَ ٱللَّهُ لِمَن يَشَآءُ وَيَرۡضَىٰٓ
Mala’iku nawa ne a cikin sammai cetonsu ba ya amfanar da komai sai da izinin Allah ga waxanda Ya ga dama Ya kuma yarda (da shi)?
إِنَّ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ لَيُسَمُّونَ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةَ تَسۡمِيَةَ ٱلۡأُنثَىٰ
Lalle waxanda ba sa yin imani da ranar lahira suna kiran mala’iku da sunan mata
وَمَا لَهُم بِهِۦ مِنۡ عِلۡمٍۖ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّۖ وَإِنَّ ٱلظَّنَّ لَا يُغۡنِي مِنَ ٱلۡحَقِّ شَيۡـٔٗا
Kuma ba su da wani ilimi game da haka; ba abin da suke bi sai zato; shi kuma zato, lalle ba ya wadatar da komai game da gaskiya
فَأَعۡرِضۡ عَن مَّن تَوَلَّىٰ عَن ذِكۡرِنَا وَلَمۡ يُرِدۡ إِلَّا ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا
Sai ka kau da kai daga duk wanda ya ba da baya daga ambatonmu, bai kuma yi nufin komai ba sai rayuwar duniya
ذَٰلِكَ مَبۡلَغُهُم مِّنَ ٱلۡعِلۡمِۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعۡلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِۦ وَهُوَ أَعۡلَمُ بِمَنِ ٱهۡتَدَىٰ
Wannan ne maqurar iliminsu. Lalle Ubangijinka Shi ne Ya fi sanin wanda ya vace daga hanyarsa kuma Shi Ya fi sanin wanda ya shiriya