فَٱذۡكُرُونِيٓ أَذۡكُرۡكُمۡ وَٱشۡكُرُواْ لِي وَلَا تَكۡفُرُونِ
Don haka ku ambace Ni, Ni ma zan ambace ku, kuma ku gode Mini, kada kuma ku kafirce Mini
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ كُلُواْ مِن طَيِّبَٰتِ مَا رَزَقۡنَٰكُمۡ وَٱشۡكُرُواْ لِلَّهِ إِن كُنتُمۡ إِيَّاهُ تَعۡبُدُونَ
Ya ku waxanda suka yi imani, ku ci daga daxaxan abin da Muka arzuta ku (da shi), kuma ku yi godiya ga Allah in har kun kasance Shi kaxai kuke bauta wa
وَمَا مُحَمَّدٌ إِلَّا رَسُولٞ قَدۡ خَلَتۡ مِن قَبۡلِهِ ٱلرُّسُلُۚ أَفَإِيْن مَّاتَ أَوۡ قُتِلَ ٱنقَلَبۡتُمۡ عَلَىٰٓ أَعۡقَٰبِكُمۡۚ وَمَن يَنقَلِبۡ عَلَىٰ عَقِبَيۡهِ فَلَن يَضُرَّ ٱللَّهَ شَيۡـٔٗاۚ وَسَيَجۡزِي ٱللَّهُ ٱلشَّـٰكِرِينَ
Kuma Muhammadu ba wani ne ba face Manzo kaxai wanda manzanni haqiqa sun shuxe gabaninsa. Shin yanzu idan ya mutu ko aka kashe shi, sai ku juya baya a kan dugaduganku? Duk kuwa wanda ya juya baya a kan dugadugansa to ba zai cuci Allah da komai ba. Kuma da sannu Allah zai saka wa masu godiya
وَمَا كَانَ لِنَفۡسٍ أَن تَمُوتَ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِ كِتَٰبٗا مُّؤَجَّلٗاۗ وَمَن يُرِدۡ ثَوَابَ ٱلدُّنۡيَا نُؤۡتِهِۦ مِنۡهَا وَمَن يُرِدۡ ثَوَابَ ٱلۡأٓخِرَةِ نُؤۡتِهِۦ مِنۡهَاۚ وَسَنَجۡزِي ٱلشَّـٰكِرِينَ
Kuma babu wani rai da zai mutu sai da izinin Allah, rubutaccen abu ne qayyadajje. Kuma duk wanda yake nufin sakamakon duniya, za Mu ba shi daga gare ta, wanda kuma yake nufin sakamakon lahira, to za Mu ba shi daga gare ta. Kuma da sannu za Mu saka ma masu godiya
وَكَذَٰلِكَ فَتَنَّا بَعۡضَهُم بِبَعۡضٖ لِّيَقُولُوٓاْ أَهَـٰٓؤُلَآءِ مَنَّ ٱللَّهُ عَلَيۡهِم مِّنۢ بَيۡنِنَآۗ أَلَيۡسَ ٱللَّهُ بِأَعۡلَمَ بِٱلشَّـٰكِرِينَ
Kuma kamar haka ne Muka jarrabi sashinsu da sashi, domin su ce: “Yanzu waxannan su ne Allah Ya yi wa baiwa daga cikinmu?” Ashe Allah ba Shi ne Mafi sanin masu godiya (gare Shi) ba?
وَٱتَّبَعۡتُ مِلَّةَ ءَابَآءِيٓ إِبۡرَٰهِيمَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَۚ مَا كَانَ لَنَآ أَن نُّشۡرِكَ بِٱللَّهِ مِن شَيۡءٖۚ ذَٰلِكَ مِن فَضۡلِ ٱللَّهِ عَلَيۡنَا وَعَلَى ٱلنَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَشۡكُرُونَ
“Na kuma bi hanyar iyayena Ibrahimu da Is’haqa da kuma Yaqubu. Bai kamace mu ba a ce mu tara wani abu da Allah. Wannan yana daga falalar Allah a gare mu da kuma sauran mutane, sai dai kuma yawancin mutane ba sa godewa
وَإِذۡ تَأَذَّنَ رَبُّكُمۡ لَئِن شَكَرۡتُمۡ لَأَزِيدَنَّكُمۡۖ وَلَئِن كَفَرۡتُمۡ إِنَّ عَذَابِي لَشَدِيدٞ
“Kuma (ku tuna) lokacin da Ubangijinku ya sanar da ku: “Lalle idan kuka gode wa (ni’imata) tabbas zan qara muku; idan kuwa kuka butulce, to lalle azabata tabbas mai tsanani ce.”
فَكُلُواْ مِمَّا رَزَقَكُمُ ٱللَّهُ حَلَٰلٗا طَيِّبٗا وَٱشۡكُرُواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ إِن كُنتُمۡ إِيَّاهُ تَعۡبُدُونَ
To ku ci halal mai daxi daga abin da Allah Ya arzuta ku da shi, kuma ku gode ni’imomin Allah in kun kasance Shi kaxai kuke bauta wa
شَاكِرٗا لِّأَنۡعُمِهِۚ ٱجۡتَبَىٰهُ وَهَدَىٰهُ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ
Mai godiya ne ga ni’imarsa (wato Allah), Ya zave shi, Ya kuma shirye shi zuwa ga tafarki madaidaici
فَتَبَسَّمَ ضَاحِكٗا مِّن قَوۡلِهَا وَقَالَ رَبِّ أَوۡزِعۡنِيٓ أَنۡ أَشۡكُرَ نِعۡمَتَكَ ٱلَّتِيٓ أَنۡعَمۡتَ عَلَيَّ وَعَلَىٰ وَٰلِدَيَّ وَأَنۡ أَعۡمَلَ صَٰلِحٗا تَرۡضَىٰهُ وَأَدۡخِلۡنِي بِرَحۡمَتِكَ فِي عِبَادِكَ ٱلصَّـٰلِحِينَ
Sai ya yi murmushi yana mai dariya saboda maganarta, ya kuma ce: “Ubangijina Ka kimsa min yadda zan gode wa ni’imar da Ka yi min ni da mahaifana, da kuma yadda zan yi aiki na gari wanda za Ka yarda da shi, kuma Ka shigar da ni don rahamarka cikin bayinka na gari.”
قَالَ ٱلَّذِي عِندَهُۥ عِلۡمٞ مِّنَ ٱلۡكِتَٰبِ أَنَا۠ ءَاتِيكَ بِهِۦ قَبۡلَ أَن يَرۡتَدَّ إِلَيۡكَ طَرۡفُكَۚ فَلَمَّا رَءَاهُ مُسۡتَقِرًّا عِندَهُۥ قَالَ هَٰذَا مِن فَضۡلِ رَبِّي لِيَبۡلُوَنِيٓ ءَأَشۡكُرُ أَمۡ أَكۡفُرُۖ وَمَن شَكَرَ فَإِنَّمَا يَشۡكُرُ لِنَفۡسِهِۦۖ وَمَن كَفَرَ فَإِنَّ رَبِّي غَنِيّٞ كَرِيمٞ
Sai wani (mutum) wanda yake da ilimin Littafi (na Attaura) ya ce: “Ni zan kawo maka shi kafin ka qifta idonka!” To lokacin da (Sulaimanu) ya gan shi ga shi nan a gabansa sai ya ce: “Wannan yana daga falalar Ubangijina don Ya jarraba ni (Ya gani) shin zan gode ne ko zan butulce; to duk wanda ya gode kansa ya yi wa; wanda kuwa ya butulce, to lalle Ubangijina Mawadaci ne, Mai karamci.”
وَإِنَّ رَبَّكَ لَذُو فَضۡلٍ عَلَى ٱلنَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَشۡكُرُونَ
Kuma lalle Ubangijinka Mai falala ne ga mutane, sai dai kuma yawancinsu ba sa godewa
إِنَّمَا تَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَوۡثَٰنٗا وَتَخۡلُقُونَ إِفۡكًاۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ تَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ لَا يَمۡلِكُونَ لَكُمۡ رِزۡقٗا فَٱبۡتَغُواْ عِندَ ٱللَّهِ ٱلرِّزۡقَ وَٱعۡبُدُوهُ وَٱشۡكُرُواْ لَهُۥٓۖ إِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ
Lalle abin da kuke bauta wa ba Allah ba gumaka ne kawai, kuna kuma qirqirar qarya ne[1]. Lalle waxanda kuke bauta wa ba Allah ba, ba su mallaki wani arziki ba gare ku, sai ku nemi arziki a wurin Allah, kuma ku bauta masa, ku kuma gode masa; gare Shi ne kawai za a mayar da ku
1- Domin su ne suke sassaqa su da hannayensu suke kuma sanya musu sunaye sannan su bauta musu.
وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا لُقۡمَٰنَ ٱلۡحِكۡمَةَ أَنِ ٱشۡكُرۡ لِلَّهِۚ وَمَن يَشۡكُرۡ فَإِنَّمَا يَشۡكُرُ لِنَفۡسِهِۦۖ وَمَن كَفَرَ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَنِيٌّ حَمِيدٞ
Haqiqa kuma Mun bai wa Luqumanu[1] hikima cewa: “Ka yi godiya ga Allah. Kuma duk wanda yake godewa to yana godewa ne don kansa, wanda kuwa ya kafirta to lalle Allah Mawadaci ne, Sha-yabo.”
1- Wani salihin bawa ne da Allah ya hore masa hikima da ilimi. Wasu masana tarihi sun ce yarayu ne a zamanin Annabi Dawud ().
وَوَصَّيۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ بِوَٰلِدَيۡهِ حَمَلَتۡهُ أُمُّهُۥ وَهۡنًا عَلَىٰ وَهۡنٖ وَفِصَٰلُهُۥ فِي عَامَيۡنِ أَنِ ٱشۡكُرۡ لِي وَلِوَٰلِدَيۡكَ إِلَيَّ ٱلۡمَصِيرُ
Kuma Mun yi wa mutum wasiyya game da iyayensa, mahaifiyarsa ta xauke shi a cikinta rauni a kan rauni, yaye shi kuwa a cikin shekara biyu ne, saboda haka ka gode min da kuma iyayenka, makoma gare Ni take
ثُمَّ سَوَّىٰهُ وَنَفَخَ فِيهِ مِن رُّوحِهِۦۖ وَجَعَلَ لَكُمُ ٱلسَّمۡعَ وَٱلۡأَبۡصَٰرَ وَٱلۡأَفۡـِٔدَةَۚ قَلِيلٗا مَّا تَشۡكُرُونَ
Sannan Ya daidaita shi, Ya kuma busa masa daga ruhinsa; kuma Ya sanya muku ji da gani da zukata. Kaxan ne qwarai kuke godewa
إِن تَكۡفُرُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَنِيٌّ عَنكُمۡۖ وَلَا يَرۡضَىٰ لِعِبَادِهِ ٱلۡكُفۡرَۖ وَإِن تَشۡكُرُواْ يَرۡضَهُ لَكُمۡۗ وَلَا تَزِرُ وَازِرَةٞ وِزۡرَ أُخۡرَىٰۚ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّكُم مَّرۡجِعُكُمۡ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَۚ إِنَّهُۥ عَلِيمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ
Idan kun kafirce, to lalle Allah Mawadaci ne ga barin ku, ba Ya kuma yarda da kafirci daga bayinsa. Idan kuwa kuka gode Zai yarda da godiyar taku. Kuma wani rai ba ya xaukar laifin wani. Sannan zuwa ga Ubangijinku ne makomarku take, sannan Ya ba ku labarin irin abubuwan da kuka kasance kuna aikatawa. Lalle Shi Masanin abubuwan da suke cikin qiraza ne
بَلِ ٱللَّهَ فَٱعۡبُدۡ وَكُن مِّنَ ٱلشَّـٰكِرِينَ
A’a, Allah kaxai za ka bauta wa, ka kuma kasance daga masu godiya
ٱللَّهُ ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلَّيۡلَ لِتَسۡكُنُواْ فِيهِ وَٱلنَّهَارَ مُبۡصِرًاۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَذُو فَضۡلٍ عَلَى ٱلنَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَشۡكُرُونَ
Allah ne wanda Ya halitta muku dare don ku natsu a cikinsa, rana kuma don ku ga (yadda za ku yi harka). Lalle Allah Mai falala ne ga mutane, sai dai kuma yawancinsu ba sa godewa
وَوَصَّيۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ بِوَٰلِدَيۡهِ إِحۡسَٰنًاۖ حَمَلَتۡهُ أُمُّهُۥ كُرۡهٗا وَوَضَعَتۡهُ كُرۡهٗاۖ وَحَمۡلُهُۥ وَفِصَٰلُهُۥ ثَلَٰثُونَ شَهۡرًاۚ حَتَّىٰٓ إِذَا بَلَغَ أَشُدَّهُۥ وَبَلَغَ أَرۡبَعِينَ سَنَةٗ قَالَ رَبِّ أَوۡزِعۡنِيٓ أَنۡ أَشۡكُرَ نِعۡمَتَكَ ٱلَّتِيٓ أَنۡعَمۡتَ عَلَيَّ وَعَلَىٰ وَٰلِدَيَّ وَأَنۡ أَعۡمَلَ صَٰلِحٗا تَرۡضَىٰهُ وَأَصۡلِحۡ لِي فِي ذُرِّيَّتِيٓۖ إِنِّي تُبۡتُ إِلَيۡكَ وَإِنِّي مِنَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ
Kuma Mun yi wa mutum wasiyya da kyautata wa mahaifansa; mahaifiyarsa ta xauki cikinsa a wahalce, ta kuma haife shi a wahalce; xaukan cikinsa da yaye shi kuma wata talatin ne, har lokacin da ya cika qarfinsa ya kai shekara arba’in ya ce: “Ya Ubangijina, Ka kimsa min yadda zan gode wa ni’imarka, wadda Ka ni’imta ni da ita da kuma mahaifana, kuma (Ka ba ni iko) in yi aiki nagari wanda za Ka yarda da shi, kuma Ka kyautata min zurriyata; lalle ni na tuba a gare Ka, kuma lalle ni ina daga cikin Musulmi.”