ٱهۡدِنَا ٱلصِّرَٰطَ ٱلۡمُسۡتَقِيمَ
Ka shiryar da mu tafarkin nan madaidaici
صِرَٰطَ ٱلَّذِينَ أَنۡعَمۡتَ عَلَيۡهِمۡ غَيۡرِ ٱلۡمَغۡضُوبِ عَلَيۡهِمۡ وَلَا ٱلضَّآلِّينَ
Tafarkin waxanda Ka yi wa ni’ima[1], ba waxanda aka yi fushi da su ba[2], ba kuma vatattu ba[3]
1- Su ne waxanda aka ambata a aya ta 69 a Suratun Nisa’i.
2- Watau waxanda suka san gaskiya suka take, kamar Yahudawa.
3- Watau waxanda suke bautar Allah da jahilci, kamar Nasara.
ذَٰلِكَ ٱلۡكِتَٰبُ لَا رَيۡبَۛ فِيهِۛ هُدٗى لِّلۡمُتَّقِينَ
Wannan littafin babu wani kokwanto a cikinsa; shiriya ne ga masu taqawa[1]
1- Taqawa tana nufin aikata abin Allah ya wajabta da nisantar abin da ya haramta.
ٱلَّذِينَ يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡغَيۡبِ وَيُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَمِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ يُنفِقُونَ
Waxanda suke yin imani da gaibi kuma suke tsayar da salla kuma suke ciyarwa daga abin da Muka arzuta su da shi
وَٱلَّذِينَ يُؤۡمِنُونَ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ وَمَآ أُنزِلَ مِن قَبۡلِكَ وَبِٱلۡأٓخِرَةِ هُمۡ يُوقِنُونَ
Waxanda suke yin imani da abin da aka saukar maka da abin da aka saukar a gabaninka, kuma suke sakankancewa da ranar lahira
أُوْلَـٰٓئِكَ عَلَىٰ هُدٗى مِّن رَّبِّهِمۡۖ وَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ
Waxannan suna kan (babbar) shiriya daga Ubangijinsu, kuma waxannan su ne masu samun babban rabo
قُلۡنَا ٱهۡبِطُواْ مِنۡهَا جَمِيعٗاۖ فَإِمَّا يَأۡتِيَنَّكُم مِّنِّي هُدٗى فَمَن تَبِعَ هُدَايَ فَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ
Muka ce: “Dukkanku ku sauko daga cikinta, sannan idan wata shiriyata ta zo muku, to waxanda suka bi shiriyata, babu wani tsoro a tare da su, kuma ba za su yi baqin ciki ba
وَلَن تَرۡضَىٰ عَنكَ ٱلۡيَهُودُ وَلَا ٱلنَّصَٰرَىٰ حَتَّىٰ تَتَّبِعَ مِلَّتَهُمۡۗ قُلۡ إِنَّ هُدَى ٱللَّهِ هُوَ ٱلۡهُدَىٰۗ وَلَئِنِ ٱتَّبَعۡتَ أَهۡوَآءَهُم بَعۡدَ ٱلَّذِي جَآءَكَ مِنَ ٱلۡعِلۡمِ مَا لَكَ مِنَ ٱللَّهِ مِن وَلِيّٖ وَلَا نَصِيرٍ
Yahudawa da Nasara ba za su tava yarda da kai ba har sai ka bi addininsu. Ka ce: “Shiriyar Allah lalle ita ce shiriya”. Idan har ka bi son zuciyarsu bayan abin da ya zo maka na gaskiya, to ba ka da wani majivinci ko mai taimakonka wajen Allah
قُولُوٓاْ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيۡنَا وَمَآ أُنزِلَ إِلَىٰٓ إِبۡرَٰهِـۧمَ وَإِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ وَٱلۡأَسۡبَاطِ وَمَآ أُوتِيَ مُوسَىٰ وَعِيسَىٰ وَمَآ أُوتِيَ ٱلنَّبِيُّونَ مِن رَّبِّهِمۡ لَا نُفَرِّقُ بَيۡنَ أَحَدٖ مِّنۡهُمۡ وَنَحۡنُ لَهُۥ مُسۡلِمُونَ
Ku ce: “Mun yi imani da Allah da abin da aka saukar mana, da abin da aka saukar wa Ibrahimu da Isma’ila da Ishaqa da Ya’aqubu da jikoki da abin da aka ba wa Musa da Isa da abin da aka ba annabawa duka daga Ubangijinsu, kuma ba ma nuna bambanci tsakanin wani daga cikinsu, kuma mu gare Shi muke miqa wuya.”
فَإِنۡ ءَامَنُواْ بِمِثۡلِ مَآ ءَامَنتُم بِهِۦ فَقَدِ ٱهۡتَدَواْۖ وَّإِن تَوَلَّوۡاْ فَإِنَّمَا هُمۡ فِي شِقَاقٖۖ فَسَيَكۡفِيكَهُمُ ٱللَّهُۚ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ
Don haka idan sun yi imani da irin abin da kuka yi imani da shi, to haqiqa sun shiriya, idan kuwa suka juya da baya, to haqiqa su suna cikin savani. To da sannu Allah zai isar maka da su, kuma Shi Mai ji ne, Mai gani
صِبۡغَةَ ٱللَّهِ وَمَنۡ أَحۡسَنُ مِنَ ٱللَّهِ صِبۡغَةٗۖ وَنَحۡنُ لَهُۥ عَٰبِدُونَ
Rinin Allah, wane ne kuwa ya fi Allah kyan rini? Kuma mu masu bauta ne a gare Shi
وَإِذَا سَأَلَكَ عِبَادِي عَنِّي فَإِنِّي قَرِيبٌۖ أُجِيبُ دَعۡوَةَ ٱلدَّاعِ إِذَا دَعَانِۖ فَلۡيَسۡتَجِيبُواْ لِي وَلۡيُؤۡمِنُواْ بِي لَعَلَّهُمۡ يَرۡشُدُونَ
Kuma idan bayina sun tambaye ka game da Ni, to Ni kusa Nake (da su), Ina amsa kiran mai kira idan ya kiraye Ni; to su amsa Mini nawa kiran, kuma su yi imani da Ni, don su shiryu
كَانَ ٱلنَّاسُ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ فَبَعَثَ ٱللَّهُ ٱلنَّبِيِّـۧنَ مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ وَأَنزَلَ مَعَهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ لِيَحۡكُمَ بَيۡنَ ٱلنَّاسِ فِيمَا ٱخۡتَلَفُواْ فِيهِۚ وَمَا ٱخۡتَلَفَ فِيهِ إِلَّا ٱلَّذِينَ أُوتُوهُ مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَتۡهُمُ ٱلۡبَيِّنَٰتُ بَغۡيَۢا بَيۡنَهُمۡۖ فَهَدَى ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لِمَا ٱخۡتَلَفُواْ فِيهِ مِنَ ٱلۡحَقِّ بِإِذۡنِهِۦۗ وَٱللَّهُ يَهۡدِي مَن يَشَآءُ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٍ
Mutane sun kasance al’umma guda xaya, sai Allah Ya aiko da annabawa, suna masu albishir, kuma masu gargaxi, kuma Ya saukar da littafi tare da su da gaskiya, don ya yi hukunci tsakanin mutane cikin abin da suka yi savani a kansa. Kuma ba wasu ne suka yi savani a kansa ba sai waxanda aka ba wa shi, bayan hujjoji bayyanannu sun zo musu, don zalunci a tsakaninsu; sai Allah Ya shiryar da waxanda suka yi imani ga abin da (mutane) suka yi savani cikinsa na gaskiya da izininsa. Kuma Allah Yana shiryar da wanda Ya ga dama zuwa ga tafarki madaidaici
۞لَّيۡسَ عَلَيۡكَ هُدَىٰهُمۡ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يَهۡدِي مَن يَشَآءُۗ وَمَا تُنفِقُواْ مِنۡ خَيۡرٖ فَلِأَنفُسِكُمۡۚ وَمَا تُنفِقُونَ إِلَّا ٱبۡتِغَآءَ وَجۡهِ ٱللَّهِۚ وَمَا تُنفِقُواْ مِنۡ خَيۡرٖ يُوَفَّ إِلَيۡكُمۡ وَأَنتُمۡ لَا تُظۡلَمُونَ
Shiryar da su ba a kanka yake ba, sai dai Allah ne Yake shiryar da wanda Ya ga dama, kuma duk abin da kuka ciyar na alheri, to domin kawunanku ne, kuma ba za ku ciyar ba sai don neman yardar Allah; kuma duk abin da kuka ciyar na alheri, za a cika muku ladansa, alhali kuma ba za a zalunce ku ba
فَإِنۡ حَآجُّوكَ فَقُلۡ أَسۡلَمۡتُ وَجۡهِيَ لِلَّهِ وَمَنِ ٱتَّبَعَنِۗ وَقُل لِّلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡأُمِّيِّـۧنَ ءَأَسۡلَمۡتُمۡۚ فَإِنۡ أَسۡلَمُواْ فَقَدِ ٱهۡتَدَواْۖ وَّإِن تَوَلَّوۡاْ فَإِنَّمَا عَلَيۡكَ ٱلۡبَلَٰغُۗ وَٱللَّهُ بَصِيرُۢ بِٱلۡعِبَادِ
To idan sun yi jayayya da kai, sai ka ce: “Ni na miqa wuyana ne ga Allah, haka ma wanda ya bi ni.” Kuma ka faxa wa waxanda aka bai wa Littafi da Ummiyyai (Larabawa): “Shin kun miqa wuya?” To idan sun miqa wuya, haqiqa sun shiryu; idan kuwa suka juya baya, to babu abin da yake a kanka sai isar da saqo. Kuma Allah Mai ganin bayinsa ne
وَلَا تُؤۡمِنُوٓاْ إِلَّا لِمَن تَبِعَ دِينَكُمۡ قُلۡ إِنَّ ٱلۡهُدَىٰ هُدَى ٱللَّهِ أَن يُؤۡتَىٰٓ أَحَدٞ مِّثۡلَ مَآ أُوتِيتُمۡ أَوۡ يُحَآجُّوكُمۡ عِندَ رَبِّكُمۡۗ قُلۡ إِنَّ ٱلۡفَضۡلَ بِيَدِ ٱللَّهِ يُؤۡتِيهِ مَن يَشَآءُۗ وَٱللَّهُ وَٰسِعٌ عَلِيمٞ
“Kuma kada ku amince da kowa sai wanda ya bi addininku.” Ka ce: “Lalle shiriya ita ce shiriyar Allah, domin kar (ku yarda a ce) an ba wani mutum irin abin da aka ba ku, ko kuma ku ba su dama su yi jayayya da ku a wajen Ubangijinku.” Ka ce: “Lalle falala a hannun Allah take, Yana bayar da ita ga wanda Ya ga dama. Kuma Allah Mai yalwa ne, Mai yawan sani
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ قَدۡ جَآءَكُم بُرۡهَٰنٞ مِّن رَّبِّكُمۡ وَأَنزَلۡنَآ إِلَيۡكُمۡ نُورٗا مُّبِينٗا
Ya ku mutane, haqiqa hujja ta zo muku daga Ubangijinku, kuma Mun saukar muku wani haske mabayyani[1]
1- Watau Alqur’ani mai girma.
فَأَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱللَّهِ وَٱعۡتَصَمُواْ بِهِۦ فَسَيُدۡخِلُهُمۡ فِي رَحۡمَةٖ مِّنۡهُ وَفَضۡلٖ وَيَهۡدِيهِمۡ إِلَيۡهِ صِرَٰطٗا مُّسۡتَقِيمٗا
To amma waxanda suka yi imani da Allah kuma suka yi garkuwa da Shi, to zai shigar da su cikin wata rahama tasa da kuma wata falala, kuma Ya shiryar da su tafarki madaidaici zuwa gare Shi
يَـٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ قَدۡ جَآءَكُمۡ رَسُولُنَا يُبَيِّنُ لَكُمۡ كَثِيرٗا مِّمَّا كُنتُمۡ تُخۡفُونَ مِنَ ٱلۡكِتَٰبِ وَيَعۡفُواْ عَن كَثِيرٖۚ قَدۡ جَآءَكُم مِّنَ ٱللَّهِ نُورٞ وَكِتَٰبٞ مُّبِينٞ
Ya ku waxanda aka bai wa Littafi, haqiqa Manzonmu ya zo muku, yana bayyana muku da yawa daga cikin abin da kuke voyewa daga Littafin, yana kuma yin afuwa ga abubuwa da dama daga ciki. Haqiqa haske ya zo muku daga Allah, da kuma Littafi mai bayyanawa
يَهۡدِي بِهِ ٱللَّهُ مَنِ ٱتَّبَعَ رِضۡوَٰنَهُۥ سُبُلَ ٱلسَّلَٰمِ وَيُخۡرِجُهُم مِّنَ ٱلظُّلُمَٰتِ إِلَى ٱلنُّورِ بِإِذۡنِهِۦ وَيَهۡدِيهِمۡ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ
Da shi ne Allah Yake shiryar da wanda ya bi yardarsa hanyoyi na aminci, kuma Yake fitar da su daga duffai zuwa ga haske da izininsa, kuma Yana shiryar da su zuwa ga tafarki madaidaici
قُلۡ أَنَدۡعُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَنفَعُنَا وَلَا يَضُرُّنَا وَنُرَدُّ عَلَىٰٓ أَعۡقَابِنَا بَعۡدَ إِذۡ هَدَىٰنَا ٱللَّهُ كَٱلَّذِي ٱسۡتَهۡوَتۡهُ ٱلشَّيَٰطِينُ فِي ٱلۡأَرۡضِ حَيۡرَانَ لَهُۥٓ أَصۡحَٰبٞ يَدۡعُونَهُۥٓ إِلَى ٱلۡهُدَى ٱئۡتِنَاۗ قُلۡ إِنَّ هُدَى ٱللَّهِ هُوَ ٱلۡهُدَىٰۖ وَأُمِرۡنَا لِنُسۡلِمَ لِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Ka ce: “Shin yanzu ma riqa bauta wa wani wanda ba Allah ba, abin da ba zai amfane mu ba, kuma ba zai cutar da mu ba, mu koma gidan jiya (kafirai) bayan kuwa Allah Ya shiryar da mu, (mu koma) kamar wanda shaixanu suka vatar da shi yana ta ximuwa a bayan qasa, ga shi da wasu abokai suna kiran sa zuwa ga shiriya, (suna cewa): “Ka zo (mu bi tafarkin shiriya)[1].” Ka ce: “Lalle shiriyar Allah fa ita kaxai ce shiriya; kuma mu an umarce mu da mu miqa wuya ne kaxai ga Ubangijin talikai
1- Misali ne na wanda ya saki Musulunci ya kama shirka ko vata, ya zama kamar mutumin da aljanu suka xauke shi suka tafi da shi suka jefar da shi a qurgurmin daji. Don haka ya yi nisan da ba zai ji kira ba, balle ya gane hanyar dawowa.
ذَٰلِكَ هُدَى ٱللَّهِ يَهۡدِي بِهِۦ مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦۚ وَلَوۡ أَشۡرَكُواْ لَحَبِطَ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Wannan ita ce shiriyar Allah wadda da ita ne Yake shiryar da wanda Ya ga dama cikin bayinsa. Kuma da a ce sun yi shirka, to lalle da duk abin da suka kasance suna aikatawa ya rushe
أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحُكۡمَ وَٱلنُّبُوَّةَۚ فَإِن يَكۡفُرۡ بِهَا هَـٰٓؤُلَآءِ فَقَدۡ وَكَّلۡنَا بِهَا قَوۡمٗا لَّيۡسُواْ بِهَا بِكَٰفِرِينَ
Waxannan su ne waxanda Muka bai wa littattafai da hukunci da annabta. To idan waxancan (mutanen Makka) suka kafirce mata (shiriya), to haqiqa Mun shirya musu waxansu mutane waxanda ba za su kafirce mata ba
أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ هَدَى ٱللَّهُۖ فَبِهُدَىٰهُمُ ٱقۡتَدِهۡۗ قُل لَّآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ أَجۡرًاۖ إِنۡ هُوَ إِلَّا ذِكۡرَىٰ لِلۡعَٰلَمِينَ
Waxannan su ne waxanda Allah Ya shiryar; don haka ka yi koyi da irin shiriyarsu. Ka ce: “Ba na roqon ku wani lada game da shi (Alqur’ani); shi ba komai ba ne face tunatarwa ga talikai.”
فَمَن يُرِدِ ٱللَّهُ أَن يَهۡدِيَهُۥ يَشۡرَحۡ صَدۡرَهُۥ لِلۡإِسۡلَٰمِۖ وَمَن يُرِدۡ أَن يُضِلَّهُۥ يَجۡعَلۡ صَدۡرَهُۥ ضَيِّقًا حَرَجٗا كَأَنَّمَا يَصَّعَّدُ فِي ٱلسَّمَآءِۚ كَذَٰلِكَ يَجۡعَلُ ٱللَّهُ ٱلرِّجۡسَ عَلَى ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ
Sannan duk wanda Allah Ya yi nufin shiryar da shi, sai Ya yalwata qirjinsa ga karvar Musulunci. Duk wanda kuwa Ya yi nufin Ya vatar da shi, sai Ya sanya qirjinsa a quntace ainun kamar wanda yake yunqurin hawa sama. Kamar haka ne Allah Yake sanya vata a kan waxanda ba sa yin imani
قُلۡ فَلِلَّهِ ٱلۡحُجَّةُ ٱلۡبَٰلِغَةُۖ فَلَوۡ شَآءَ لَهَدَىٰكُمۡ أَجۡمَعِينَ
Ka ce: “To a wurin Allah ne cikakkiyar hujja take; kuma da Ya ga dama, tabbas da Ya shiryar da ku gaba xaya.”
وَلَقَدۡ جِئۡنَٰهُم بِكِتَٰبٖ فَصَّلۡنَٰهُ عَلَىٰ عِلۡمٍ هُدٗى وَرَحۡمَةٗ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ
Lalle haqiqa kuma Mun zo musu da littafin[1] da Muka bayyana shi filla-filla bisa ilimi da shiriya da rahama ga mutanen da suke yin imani
1- Watau Alqur’ani mai girma.
وَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيُضِلَّ قَوۡمَۢا بَعۡدَ إِذۡ هَدَىٰهُمۡ حَتَّىٰ يُبَيِّنَ لَهُم مَّا يَتَّقُونَۚ إِنَّ ٱللَّهَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٌ
Allah kuwa ba zai tava vatar da wasu mutane ba bayan Ya riga Ya shiryar da su, har sai Ya bayyana musu abin da za su kiyaye. Lalle Allah Masanin komai ne
وَٱللَّهُ يَدۡعُوٓاْ إِلَىٰ دَارِ ٱلسَّلَٰمِ وَيَهۡدِي مَن يَشَآءُ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ
Allah kuwa Yana kira ne zuwa gidan aminci (wato Aljanna), Yana kuma shiryar da wanda Ya ga dama zuwa tafarki madaidaici
قُلۡ هَلۡ مِن شُرَكَآئِكُم مَّن يَهۡدِيٓ إِلَى ٱلۡحَقِّۚ قُلِ ٱللَّهُ يَهۡدِي لِلۡحَقِّۗ أَفَمَن يَهۡدِيٓ إِلَى ٱلۡحَقِّ أَحَقُّ أَن يُتَّبَعَ أَمَّن لَّا يَهِدِّيٓ إِلَّآ أَن يُهۡدَىٰۖ فَمَا لَكُمۡ كَيۡفَ تَحۡكُمُونَ
Ka ce: “Shin daga abokan tarayyarku ko akwai wanda yake shiryarwa zuwa gaskiya?” Ka ce: “Allah Shi ne Yake shiryarwa zuwa ga gaskiya. To yanzu wanda yake shiryarwa zuwa gaskiya shi ya fi cancanta a bi, ko kuwa wanda ba ya shiryarwa sai dai a shiryar da shi? To me ya same ku ne? Yaya kuke wannan hukuncin?