Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 22

ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلۡأَرۡضَ فِرَٰشٗا وَٱلسَّمَآءَ بِنَآءٗ وَأَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَخۡرَجَ بِهِۦ مِنَ ٱلثَّمَرَٰتِ رِزۡقٗا لَّكُمۡۖ فَلَا تَجۡعَلُواْ لِلَّهِ أَندَادٗا وَأَنتُمۡ تَعۡلَمُونَ

Shi ne Wanda Ya sanya muku qasa ta zama shimfixa kuma Ya sanya muku sama ta zama gini kuma Ya saukar da ruwa daga sama Ya fitar muku da arziqi na ‘ya’yan itatuwa, don haka kada ku sanya wa Allah kishiyoyi alhalin kuna sane



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 29

هُوَ ٱلَّذِي خَلَقَ لَكُم مَّا فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗا ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰٓ إِلَى ٱلسَّمَآءِ فَسَوَّىٰهُنَّ سَبۡعَ سَمَٰوَٰتٖۚ وَهُوَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٞ

Shi ne wanda Ya halitta muku abin da yake cikin qasa gaba xaya, sannan Ya nufi sama Ya daidaita su sammai bakwai, kuma Shi Masanin komai ne



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 255

ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡحَيُّ ٱلۡقَيُّومُۚ لَا تَأۡخُذُهُۥ سِنَةٞ وَلَا نَوۡمٞۚ لَّهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ مَن ذَا ٱلَّذِي يَشۡفَعُ عِندَهُۥٓ إِلَّا بِإِذۡنِهِۦۚ يَعۡلَمُ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡۖ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَيۡءٖ مِّنۡ عِلۡمِهِۦٓ إِلَّا بِمَا شَآءَۚ وَسِعَ كُرۡسِيُّهُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَۖ وَلَا يَـُٔودُهُۥ حِفۡظُهُمَاۚ وَهُوَ ٱلۡعَلِيُّ ٱلۡعَظِيمُ

Allah, babu wani abin bauta wa da cancanta sai Shi, Rayayye, Tsayayye da Zatinsa; gyangyaxi ba ya kama shi, ballantana barci. Abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qasa nasa ne shi kaxai. Wane ne ya isa ya yi ceto a wurinsa in ba da izininsa ba? Ya san abin da yake tare da su a yanzu da kuma abin da zai biyo bayansu; kuma ba sa iya sanin wani abu cikin iliminsa sai abin da Ya ga dama. Kursiyyunsa ya yalwaci sammai da qasa, kuma kiyaye su ba zai nauyaye Shi ba, kuma Shi ne Maxaukaki Mai girma



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 75

وَكَذَٰلِكَ نُرِيٓ إِبۡرَٰهِيمَ مَلَكُوتَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَلِيَكُونَ مِنَ ٱلۡمُوقِنِينَ

Kuma kamar haka ne Muke nuna wa Ibrahimu halittun sammai da qasa, domin ya kasance cikin masu sakankancewa



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 76

فَلَمَّا جَنَّ عَلَيۡهِ ٱلَّيۡلُ رَءَا كَوۡكَبٗاۖ قَالَ هَٰذَا رَبِّيۖ فَلَمَّآ أَفَلَ قَالَ لَآ أُحِبُّ ٱلۡأٓفِلِينَ

To yayin da dare ya lulluve shi, ya ga tauraro, sai ya ce; “Wannan shi ne ubangijina;”[1] sannan yayin da ya vace, sai ya ce: “Ni fa ba na son abubuwa masu gushewa.”


1- Daga wannan ayar zuwa aya ta 79 Allah () ya koya wa Annabi Ibrahim () hanyar da zai yi wa mutanensa wa’azi cikin hikima da laluma don jan hankalinsu su fahimci abubuwan da suke bauta wa ba ababen bauta ne na gaskiya ba.


Capítulo: Suratul An’am

Verso : 77

فَلَمَّا رَءَا ٱلۡقَمَرَ بَازِغٗا قَالَ هَٰذَا رَبِّيۖ فَلَمَّآ أَفَلَ قَالَ لَئِن لَّمۡ يَهۡدِنِي رَبِّي لَأَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلضَّآلِّينَ

Sa’annan yayin da ya ga wata ya fito, sai ya ce; “Wannan shi ne ubangijina;” sannan yayin da ya gushe, sai ya ce: “Lalle idan Ubangijina bai shiryar da ni ba, haqiqa zan kasance daga cikin mutane vatattu.”



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 78

فَلَمَّا رَءَا ٱلشَّمۡسَ بَازِغَةٗ قَالَ هَٰذَا رَبِّي هَٰذَآ أَكۡبَرُۖ فَلَمَّآ أَفَلَتۡ قَالَ يَٰقَوۡمِ إِنِّي بَرِيٓءٞ مِّمَّا تُشۡرِكُونَ

Sannan yayin da ya ga rana ta hudo, sai ya ce: “Wannan shi ne ubangijina, wannan shi ya fi girma;” sannan yayin da ta vace, sai ya ce: “Ya ku mutanena, haqiqa ni ba ruwana da abin da kuke haxa Allah da shi



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 79

إِنِّي وَجَّهۡتُ وَجۡهِيَ لِلَّذِي فَطَرَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ حَنِيفٗاۖ وَمَآ أَنَا۠ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ

“Lalle ni kam na juyar da fuskata ga Wanda Ya halicci sammai da qasa, ina mai kauce wa varna kuma ni ba na cikin masu yin shirka.”



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 96

فَالِقُ ٱلۡإِصۡبَاحِ وَجَعَلَ ٱلَّيۡلَ سَكَنٗا وَٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَ حُسۡبَانٗاۚ ذَٰلِكَ تَقۡدِيرُ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡعَلِيمِ

(Shi ne) Mai keto da hasken safiya, kuma Ya sanya dare don nutsuwa; rana da wata kuma don qidayar lokatai. Wannan shiri ne na (Allah) Mabuwayi, Mai yawan sani



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 97

وَهُوَ ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلنُّجُومَ لِتَهۡتَدُواْ بِهَا فِي ظُلُمَٰتِ ٱلۡبَرِّ وَٱلۡبَحۡرِۗ قَدۡ فَصَّلۡنَا ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يَعۡلَمُونَ

Kuma Shi ne Wanda Ya sanya muku taurari domin ku gane hanya da su a cikin duffan tudu da na ruwa. Haqiqa Mun bayyana ayoyi ga mutanen da suke da sani



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 54

إِنَّ رَبَّكُمُ ٱللَّهُ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٖ ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰ عَلَى ٱلۡعَرۡشِۖ يُغۡشِي ٱلَّيۡلَ ٱلنَّهَارَ يَطۡلُبُهُۥ حَثِيثٗا وَٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَ وَٱلنُّجُومَ مُسَخَّرَٰتِۭ بِأَمۡرِهِۦٓۗ أَلَا لَهُ ٱلۡخَلۡقُ وَٱلۡأَمۡرُۗ تَبَارَكَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Lalle Ubangijinku shi ne Allah wanda Ya halicci sammai da qasa cikin kwanaki shida, sannan sai Ya daidaita a kan Al’arshi[1], Yana lulluve (duhun) dare da (hasken) yini, (kowannensu) yana neman sa (xan’uwansa) a gurguje, da rana da wata da taurari kuma abubuwan horewa ne da umarninsa. Haqiqa halitta da umarni nasa ne. Albarkatun Allah Ubangijin talikai sun yawaita


1- Allah mai girma da buwaya ya daidaita a kan Al’arshi daidaiton da ya dace da girmansa.


Capítulo: Suratu Yunus

Verso : 5

هُوَ ٱلَّذِي جَعَلَ ٱلشَّمۡسَ ضِيَآءٗ وَٱلۡقَمَرَ نُورٗا وَقَدَّرَهُۥ مَنَازِلَ لِتَعۡلَمُواْ عَدَدَ ٱلسِّنِينَ وَٱلۡحِسَابَۚ مَا خَلَقَ ٱللَّهُ ذَٰلِكَ إِلَّا بِٱلۡحَقِّۚ يُفَصِّلُ ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يَعۡلَمُونَ

Shi ne Wanda Ya sanya muku rana ta zamo mai haske da kuma wata ya zamo mai haskakawa, Ya kuma sanya shi mai masaukai don ku san adadin shekaru da kuma (sanin) lissafi (na lokuta). Allah bai halicci wannan ba sai da gaskiya. Yana bayyana ayoyi ne ga mutanen da suke da sani



Capítulo: Suratur Ra’ad

Verso : 2

ٱللَّهُ ٱلَّذِي رَفَعَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ بِغَيۡرِ عَمَدٖ تَرَوۡنَهَاۖ ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰ عَلَى ٱلۡعَرۡشِۖ وَسَخَّرَ ٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَۖ كُلّٞ يَجۡرِي لِأَجَلٖ مُّسَمّٗىۚ يُدَبِّرُ ٱلۡأَمۡرَ يُفَصِّلُ ٱلۡأٓيَٰتِ لَعَلَّكُم بِلِقَآءِ رَبِّكُمۡ تُوقِنُونَ

Allah Wanda Ya xaukaka sammai ba tare da wasu ginshiqai da kuke ganinsu ba; sannan Ya daidaita bisa Al’arshi[1]; Ya kuma hore muku rana da wata; kowannensu yana gudu zuwa wani lokaci qayyadadde. Yana shirya al’amari, Yana bayyana ayoyi don ku sakankance da haxuwarku da Ubangijinku


1- Duba Suratul A’araf aya ta 54, hashiya ta 126.


Capítulo: Suratu Ibrahim

Verso : 32

ٱللَّهُ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَأَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَخۡرَجَ بِهِۦ مِنَ ٱلثَّمَرَٰتِ رِزۡقٗا لَّكُمۡۖ وَسَخَّرَ لَكُمُ ٱلۡفُلۡكَ لِتَجۡرِيَ فِي ٱلۡبَحۡرِ بِأَمۡرِهِۦۖ وَسَخَّرَ لَكُمُ ٱلۡأَنۡهَٰرَ

Allah ne Wanda Ya halicci sammai da qasa, Ya kuma saukar da ruwa daga sama, sai Ya fitar da ‘ya’yan itace don arzuta ku; Ya kuma hore muku jiragen ruwa don ku yi tafiya a cikin kogi da umarninsa, Ya kuma hore muku qoramu



Capítulo: Suratul Hijr

Verso : 16

وَلَقَدۡ جَعَلۡنَا فِي ٱلسَّمَآءِ بُرُوجٗا وَزَيَّنَّـٰهَا لِلنَّـٰظِرِينَ

Haqiqa kuma Mun sanya taurari a sama, Muka kuma qawata ta ga masu gani



Capítulo: Suratul Hijr

Verso : 17

وَحَفِظۡنَٰهَا مِن كُلِّ شَيۡطَٰنٖ رَّجِيمٍ

Kuma Muka kiyaye ta daga duk wani shaixani la’ananne



Capítulo: Suratul Hijr

Verso : 18

إِلَّا مَنِ ٱسۡتَرَقَ ٱلسَّمۡعَ فَأَتۡبَعَهُۥ شِهَابٞ مُّبِينٞ

Sai dai wanda ya yi satar sauraro, sannan sai tauraro mai harshen wuta ya biyo shi



Capítulo: Suratul Hijr

Verso : 22

وَأَرۡسَلۡنَا ٱلرِّيَٰحَ لَوَٰقِحَ فَأَنزَلۡنَا مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَسۡقَيۡنَٰكُمُوهُ وَمَآ أَنتُمۡ لَهُۥ بِخَٰزِنِينَ

Muka kuma aiko da iska mai yin barbara (ga giza-gizai), sai Muka saukar da ruwa daga sama Muka shayar da ku da shi, ba kuma ku ne masu taskance shi ba



Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 12

وَسَخَّرَ لَكُمُ ٱلَّيۡلَ وَٱلنَّهَارَ وَٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَۖ وَٱلنُّجُومُ مُسَخَّرَٰتُۢ بِأَمۡرِهِۦٓۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَعۡقِلُونَ

Ya kuma hore muku dare da rana da kuma wata; taurari ma ababen horewa ne da umarninsa. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga mutane masu hankali



Capítulo: Suratul Isra’i

Verso : 44

تُسَبِّحُ لَهُ ٱلسَّمَٰوَٰتُ ٱلسَّبۡعُ وَٱلۡأَرۡضُ وَمَن فِيهِنَّۚ وَإِن مِّن شَيۡءٍ إِلَّا يُسَبِّحُ بِحَمۡدِهِۦ وَلَٰكِن لَّا تَفۡقَهُونَ تَسۡبِيحَهُمۡۚ إِنَّهُۥ كَانَ حَلِيمًا غَفُورٗا

Sammai bakwai da qasa da abin da yake cikinsu (duka) suna tsarkake Shi. Ba wani abu wanda ba ya tasbihi tare da gode masa, sai dai ba kwa fahimtar tasbihinsu. Lalle Shi Ya kasance Mai yawan haquri ne, Mai yawan gafara



Capítulo: Suratu Maryam

Verso : 90

تَكَادُ ٱلسَّمَٰوَٰتُ يَتَفَطَّرۡنَ مِنۡهُ وَتَنشَقُّ ٱلۡأَرۡضُ وَتَخِرُّ ٱلۡجِبَالُ هَدًّا

Sama ta kusa ta kece saboda shi (mummunan furucin), qasa kuma ta tsage, duwatsu kuma su zube su yi rugu-rugu



Capítulo: Suratul Anbiya

Verso : 30

أَوَلَمۡ يَرَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَنَّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ كَانَتَا رَتۡقٗا فَفَتَقۡنَٰهُمَاۖ وَجَعَلۡنَا مِنَ ٱلۡمَآءِ كُلَّ شَيۡءٍ حَيٍّۚ أَفَلَا يُؤۡمِنُونَ

Yanzu waxanda suka kafirta ba sa ganin cewa a da can sammai da qasa a haxe suke, sannan Muka raba su[1]; Muka kuma halicci duk wani abu mai rai daga ruwa? To me ya sa ba za su yi imani ba?


1- Watau Allah () ya fara halittar sammai da qasa a manne da juna daga bisani ya raba tsakaninsu.


Capítulo: Suratul Anbiya

Verso : 32

وَجَعَلۡنَا ٱلسَّمَآءَ سَقۡفٗا مَّحۡفُوظٗاۖ وَهُمۡ عَنۡ ءَايَٰتِهَا مُعۡرِضُونَ

Muka kuma sanya sama (ta zama) rufi tsararre; su kuwa (duk da haka) masu bijire wa ayoyinta (watau sama) ne



Capítulo: Suratul Anbiya

Verso : 33

وَهُوَ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلَّيۡلَ وَٱلنَّهَارَ وَٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَۖ كُلّٞ فِي فَلَكٖ يَسۡبَحُونَ

Shi ne kuma Wanda Ya halicci dare da rana, da kuma rana da wata; kowannensu yana ninqaya cikin falakinsa



Capítulo: Suratun Nur

Verso : 43

أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ يُزۡجِي سَحَابٗا ثُمَّ يُؤَلِّفُ بَيۡنَهُۥ ثُمَّ يَجۡعَلُهُۥ رُكَامٗا فَتَرَى ٱلۡوَدۡقَ يَخۡرُجُ مِنۡ خِلَٰلِهِۦ وَيُنَزِّلُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مِن جِبَالٖ فِيهَا مِنۢ بَرَدٖ فَيُصِيبُ بِهِۦ مَن يَشَآءُ وَيَصۡرِفُهُۥ عَن مَّن يَشَآءُۖ يَكَادُ سَنَا بَرۡقِهِۦ يَذۡهَبُ بِٱلۡأَبۡصَٰرِ

Shin ba ka gani cewa Allah Yana kora gizagizai sannan Ya harhaxa tsakaninsu sannan Ya mai da su masu hawan juna, sai ka ga ruwan sama yana fitowa ta tsakankaninsa, kuma Yana saukar da wasu kasake (na gizagizai) daga sama waxanda a cikinsu akwai qanqara, sai Ya sami wanda Ya ga dama da ita (qanqarar) Ya kuma kautar da ita daga wanda Ya ga dama. Hasken walqiyarsa yana kusa da ya fauce idanu



Capítulo: Suratul Furqan

Verso : 61

تَبَارَكَ ٱلَّذِي جَعَلَ فِي ٱلسَّمَآءِ بُرُوجٗا وَجَعَلَ فِيهَا سِرَٰجٗا وَقَمَرٗا مُّنِيرٗا

Wanda Ya sanya wuraren saukar taurari cikin sama, Ya kuma sanya mata rana mai haske da wata mai haskakawa[1], albarkatunsa sun yawaita


1- Watau rana mai xauke da haske a karan-kanta da kuma wata wanda yake samun haskensa daga hasken rana.


Capítulo: Suratur Rum

Verso : 48

ٱللَّهُ ٱلَّذِي يُرۡسِلُ ٱلرِّيَٰحَ فَتُثِيرُ سَحَابٗا فَيَبۡسُطُهُۥ فِي ٱلسَّمَآءِ كَيۡفَ يَشَآءُ وَيَجۡعَلُهُۥ كِسَفٗا فَتَرَى ٱلۡوَدۡقَ يَخۡرُجُ مِنۡ خِلَٰلِهِۦۖ فَإِذَآ أَصَابَ بِهِۦ مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦٓ إِذَا هُمۡ يَسۡتَبۡشِرُونَ

Allah (Shi ne) wanda Yake aiko da iska sai ta motsa girgije, sai Ya shimfixa shi a (sararin) sama yadda Ya ga dama, Ya kuma sanya shi yanki-yanki, sai ka ga ruwa yana fitowa ta tsakaninsa, to idan Ya saukar da shi ga waxanda Ya ga dama daga bayinsa sai ka gan su suna ta murna



Capítulo: Suratu Luqman

Verso : 10

خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ بِغَيۡرِ عَمَدٖ تَرَوۡنَهَاۖ وَأَلۡقَىٰ فِي ٱلۡأَرۡضِ رَوَٰسِيَ أَن تَمِيدَ بِكُمۡ وَبَثَّ فِيهَا مِن كُلِّ دَآبَّةٖۚ وَأَنزَلۡنَا مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَنۢبَتۡنَا فِيهَا مِن كُلِّ زَوۡجٖ كَرِيمٍ

Ya halicci sammai ba tare da wani ginshiqi da kuke ganin sa ba, Ya kuma kafa manya-manyan duwatsu a cikin qasa don kada ta riqa tangal-tangal da ku, Ya kuma yaxa kowace irin dabba a cikinta. Kuma Mun saukar da ruwa daga sama sai Muka tsirar da kowane irin dangin tsiro mai qayatarwa



Capítulo: Suratu Luqman

Verso : 29

أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ يُولِجُ ٱلَّيۡلَ فِي ٱلنَّهَارِ وَيُولِجُ ٱلنَّهَارَ فِي ٱلَّيۡلِ وَسَخَّرَ ٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَۖ كُلّٞ يَجۡرِيٓ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗى وَأَنَّ ٱللَّهَ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ

Yanzu ba ka gani cewa Allah Yana shigar da dare cikin rana, Yana kuma shigar da rana cikin dare, Ya kuma hore (muku) rana da wata, kowannensu yana tafiya zuwa ga lokaci iyakantacce, kuma lalle Allah Masanin abin da kuke aikatawa ne?



Capítulo: Suratul Ahzab

Verso : 72

إِنَّا عَرَضۡنَا ٱلۡأَمَانَةَ عَلَى ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَٱلۡجِبَالِ فَأَبَيۡنَ أَن يَحۡمِلۡنَهَا وَأَشۡفَقۡنَ مِنۡهَا وَحَمَلَهَا ٱلۡإِنسَٰنُۖ إِنَّهُۥ كَانَ ظَلُومٗا جَهُولٗا

Lalle Mun bijiro da amana[1] ga sammai da qasa da duwatsu sai suka qi xaukar ta suka ji tsoron ta, sai kuwa mutum ya xauke ta; lalle shi (mutum) ya kasance mai zaluntar kansa ne, mai jahilci


1- Amana a nan, su ne dokokin shari’a na umarni da hani.