ٱتَّخَذُوٓاْ أَيۡمَٰنَهُمۡ جُنَّةٗ فَصَدُّواْ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ فَلَهُمۡ عَذَابٞ مُّهِينٞ
Sun xauki rantse-rantsensu su zama garkuwa, sai suka kange hanyar Allah, saboda haka suna da (sakamakon) azaba mai wulaqantarwa
لَّن تُغۡنِيَ عَنۡهُمۡ أَمۡوَٰلُهُمۡ وَلَآ أَوۡلَٰدُهُم مِّنَ ٱللَّهِ شَيۡـًٔاۚ أُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ
Dukiyoyinsu da ‘ya’yansu ba za su amfanar musu komai ba a wurin Allah. Waxannan su ne ‘yan wuta; su madawwama ne a cikinta
يَوۡمَ يَبۡعَثُهُمُ ٱللَّهُ جَمِيعٗا فَيَحۡلِفُونَ لَهُۥ كَمَا يَحۡلِفُونَ لَكُمۡ وَيَحۡسَبُونَ أَنَّهُمۡ عَلَىٰ شَيۡءٍۚ أَلَآ إِنَّهُمۡ هُمُ ٱلۡكَٰذِبُونَ
A ranar da Allah zai tashe su baki xaya sai su rantse Masa kamar yadda suke rantse muku, su kuma riqa tsammanin su sun yi wani abu (mai amfani). Ku saurara, lalle kam su ne maqaryata
ٱسۡتَحۡوَذَ عَلَيۡهِمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ فَأَنسَىٰهُمۡ ذِكۡرَ ٱللَّهِۚ أُوْلَـٰٓئِكَ حِزۡبُ ٱلشَّيۡطَٰنِۚ أَلَآ إِنَّ حِزۡبَ ٱلشَّيۡطَٰنِ هُمُ ٱلۡخَٰسِرُونَ
Shaixan ya ci qarfinsu, sai ya mantar da su ambaton Allah. Waxannan su ne qungiyar Shaixan. Ku saurara, lalle qungiyar Shaixan su ne tavavvu
۞أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ نَافَقُواْ يَقُولُونَ لِإِخۡوَٰنِهِمُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ لَئِنۡ أُخۡرِجۡتُمۡ لَنَخۡرُجَنَّ مَعَكُمۡ وَلَا نُطِيعُ فِيكُمۡ أَحَدًا أَبَدٗا وَإِن قُوتِلۡتُمۡ لَنَنصُرَنَّكُمۡ وَٱللَّهُ يَشۡهَدُ إِنَّهُمۡ لَكَٰذِبُونَ
Ba ka ga waxanda suka yi munafunci suna ce wa ‘yan’uwansu waxanda suka kafirta daga ma’abota littafi: “Tabbas idan aka fitar da ku, lalle za mu fita tare da ku, ba kuma za mu bi wani mutum game da ku ba har adaba, kuma idan aka yaqe ku tabbas za mu taimake ku.” Allah kuma Ya san tabbas qarya suke yi
لَئِنۡ أُخۡرِجُواْ لَا يَخۡرُجُونَ مَعَهُمۡ وَلَئِن قُوتِلُواْ لَا يَنصُرُونَهُمۡ وَلَئِن نَّصَرُوهُمۡ لَيُوَلُّنَّ ٱلۡأَدۡبَٰرَ ثُمَّ لَا يُنصَرُونَ
Tabbas idan aka fitar da su ba za su fita tare da su ba, kuma tabbas idan aka yaqe su ba za su taimake su ba, tabbas kuwa idan ma sun taimake su xin, lalle za su gudu su ba da baya, sannan kuma ba za a ba su nasara ba
كَبُرَ مَقۡتًا عِندَ ٱللَّهِ أَن تَقُولُواْ مَا لَا تَفۡعَلُونَ
Ya isa babban abin qi a wurin Allah, ku riqa faxin abin da ba kwa aikatawa
إِذَا جَآءَكَ ٱلۡمُنَٰفِقُونَ قَالُواْ نَشۡهَدُ إِنَّكَ لَرَسُولُ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ إِنَّكَ لَرَسُولُهُۥ وَٱللَّهُ يَشۡهَدُ إِنَّ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ لَكَٰذِبُونَ
Idan munafukai suka zo maka sai suka ce: “Muna shaidawa cewa lalle kai Manzon Allah ne.” Allah kuma Yana sane da cewa kai tabbas Manzonsa ne, kuma Allah Yana shaidawa cewa munafukai tabbas qarya suke yi
ٱتَّخَذُوٓاْ أَيۡمَٰنَهُمۡ جُنَّةٗ فَصَدُّواْ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِۚ إِنَّهُمۡ سَآءَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Sun xauki rantse-rantsensu garkuwa, saboda haka suka kange (mutane) daga hanyar Allah. Lalle su abin da suka kasance suna aikatawa ya munana
ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ ءَامَنُواْ ثُمَّ كَفَرُواْ فَطُبِعَ عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ فَهُمۡ لَا يَفۡقَهُونَ
Wannan kuwa saboda cewa sun yi imani sannan suka kafirta, sai aka rufe zukatansu, saboda haka su ba sa fahimta
۞وَإِذَا رَأَيۡتَهُمۡ تُعۡجِبُكَ أَجۡسَامُهُمۡۖ وَإِن يَقُولُواْ تَسۡمَعۡ لِقَوۡلِهِمۡۖ كَأَنَّهُمۡ خُشُبٞ مُّسَنَّدَةٞۖ يَحۡسَبُونَ كُلَّ صَيۡحَةٍ عَلَيۡهِمۡۚ هُمُ ٱلۡعَدُوُّ فَٱحۡذَرۡهُمۡۚ قَٰتَلَهُمُ ٱللَّهُۖ أَنَّىٰ يُؤۡفَكُونَ
Idan ka gan su sai jikkunansu su qayatar da kai; idan kuma suka yi magana za ka saurari maganarsu; kai ka ce su wasu gumaguman itatuwa ne a jingine[1]; suna tsammanin kowace irin kururuwa saboda su ne. Su ne maqiya, saboda haka ka yi hattara da su. Allah kuma Ya la’ance su; ta ina ne ake karkatar da su?
1- Watau dai wannan cika fuskar duka fankanfayau ne, ba sa fahimtar komai daga bayanan da Annabi () yake yi.
وَإِذَا قِيلَ لَهُمۡ تَعَالَوۡاْ يَسۡتَغۡفِرۡ لَكُمۡ رَسُولُ ٱللَّهِ لَوَّوۡاْ رُءُوسَهُمۡ وَرَأَيۡتَهُمۡ يَصُدُّونَ وَهُم مُّسۡتَكۡبِرُونَ
Idan kuma aka ce da su: “Ku zo Manzon Allah ya nema muku gafara,” sai su kau da kansu, sai ka gan su suna bijirewa, alhalin suna masu girman kai
سَوَآءٌ عَلَيۡهِمۡ أَسۡتَغۡفَرۡتَ لَهُمۡ أَمۡ لَمۡ تَسۡتَغۡفِرۡ لَهُمۡ لَن يَغۡفِرَ ٱللَّهُ لَهُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡفَٰسِقِينَ
Duk xaya ne game da su, ka nema musu gafara, ko ba ka nema musu gafara ba, Allah ba zai gafarta musu ba har abada. Lalle Allah ba Ya shiryar da mutane fasiqai
هُمُ ٱلَّذِينَ يَقُولُونَ لَا تُنفِقُواْ عَلَىٰ مَنۡ عِندَ رَسُولِ ٱللَّهِ حَتَّىٰ يَنفَضُّواْۗ وَلِلَّهِ خَزَآئِنُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَلَٰكِنَّ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ لَا يَفۡقَهُونَ
Su ne waxanda suke cewa: “Kada ku ciyar da waxanda suke wurin Manzon Allah har sai sun dare[1]”. Alhali kuwa taskokin sammai da qasa na Allah ne, sai dai kuma munafukai ba sa ganewa
1- Watau su daina taimaka wa sahabbai faqirai da suke tare da Manzon Allah () har sai sun waste sun bar shi.
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ جَٰهِدِ ٱلۡكُفَّارَ وَٱلۡمُنَٰفِقِينَ وَٱغۡلُظۡ عَلَيۡهِمۡۚ وَمَأۡوَىٰهُمۡ جَهَنَّمُۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ
Ya kai wannan Annabi, ka yaqi kafirai da munafukai, ka kuma tsananta musu. Makomarsu kuma Jahannama ce; makoma kuwa ta munana