Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 8

وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَقُولُ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَبِٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَمَا هُم بِمُؤۡمِنِينَ

A cikin mutane kuma akwai waxanda suke cewa: “Mun yi imani da Allah kuma mun yi imani da ranar lahira,” alhalin su ba muminai ne ba



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 9

يُخَٰدِعُونَ ٱللَّهَ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَمَا يَخۡدَعُونَ إِلَّآ أَنفُسَهُمۡ وَمَا يَشۡعُرُونَ

Suna ganin suna yaudarar Allah ne da waxanda suka yi imani, amma kuwa ba kowa suke yaudara ba sai kawunansu, kuma su ba sa jin hakan



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 10

فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٞ فَزَادَهُمُ ٱللَّهُ مَرَضٗاۖ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمُۢ بِمَا كَانُواْ يَكۡذِبُونَ

Akwai wata cuta (ta munafunci) a cikin zukatansu, sai Allah Ya qara musu wata cutar, kuma suna da wata azaba mai raxaxi saboda qaryar da suke yi



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 11

وَإِذَا قِيلَ لَهُمۡ لَا تُفۡسِدُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ قَالُوٓاْ إِنَّمَا نَحۡنُ مُصۡلِحُونَ

Idan kuma aka ce musu: “Kada ku yi varna a bayan qasa”, sai su ce: “Mu fa masu gyara ne kawai.”



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 12

أَلَآ إِنَّهُمۡ هُمُ ٱلۡمُفۡسِدُونَ وَلَٰكِن لَّا يَشۡعُرُونَ

Saurara, lalle su su ne mavarnata, amma ba sa jin hakan



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 13

وَإِذَا قِيلَ لَهُمۡ ءَامِنُواْ كَمَآ ءَامَنَ ٱلنَّاسُ قَالُوٓاْ أَنُؤۡمِنُ كَمَآ ءَامَنَ ٱلسُّفَهَآءُۗ أَلَآ إِنَّهُمۡ هُمُ ٱلسُّفَهَآءُ وَلَٰكِن لَّا يَعۡلَمُونَ

Idan kuma aka ce da su: “Ku yi imani kamar yadda mutane suka yi imani”, sai su ce: “Shin za mu yi imani ne kamar yadda wawaye suka yi imani?” Saurara, lalle su ne wawayen, sai dai ba sa sanin (hakan)



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 14

وَإِذَا لَقُواْ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ قَالُوٓاْ ءَامَنَّا وَإِذَا خَلَوۡاْ إِلَىٰ شَيَٰطِينِهِمۡ قَالُوٓاْ إِنَّا مَعَكُمۡ إِنَّمَا نَحۡنُ مُسۡتَهۡزِءُونَ

Idan kuma suka haxu da waxanda suka yi imani sai su ce: “Mun yi imani.” To amma idan suka kevanta da shaixanunsu (iyayen gidansu)[1] sai su ce: “Mu fa lalle muna nan tare da ku, mu kawai izgili ne muke yi.”


1- Shexanunsu, su ne manyan kafirai da Yahudawa.


Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 15

ٱللَّهُ يَسۡتَهۡزِئُ بِهِمۡ وَيَمُدُّهُمۡ فِي طُغۡيَٰنِهِمۡ يَعۡمَهُونَ

Allah Yana yi musu izgili, kuma Yana yi musu talala cikin shisshiginsu suna masu ximuwa



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 16

أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ ٱشۡتَرَوُاْ ٱلضَّلَٰلَةَ بِٱلۡهُدَىٰ فَمَا رَبِحَت تِّجَٰرَتُهُمۡ وَمَا كَانُواْ مُهۡتَدِينَ

Waxannan su ne suka musanya shiriya da vata, don haka kasuwancinsu bai yi riba ba, kuma ba su zamo shiryayyu ba



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 204

وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يُعۡجِبُكَ قَوۡلُهُۥ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَيُشۡهِدُ ٱللَّهَ عَلَىٰ مَا فِي قَلۡبِهِۦ وَهُوَ أَلَدُّ ٱلۡخِصَامِ

Kuma daga cikin mutane akwai wanda zancensa yake burge ka a rayuwar duniya, kuma yana shaidar da Allah ga abin da yake cikin zuciyarsa, alhali kuwa shi mai tsananin husuma ne



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 205

وَإِذَا تَوَلَّىٰ سَعَىٰ فِي ٱلۡأَرۡضِ لِيُفۡسِدَ فِيهَا وَيُهۡلِكَ ٱلۡحَرۡثَ وَٱلنَّسۡلَۚ وَٱللَّهُ لَا يُحِبُّ ٱلۡفَسَادَ

Kuma idan ya juya baya, zai yi ta yawo a cikin qasa don ya yi varna a cikinta, kuma ya lalata amfanin gona da dabbobi. Allah kuwa ba Ya son varna



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 206

وَإِذَا قِيلَ لَهُ ٱتَّقِ ٱللَّهَ أَخَذَتۡهُ ٱلۡعِزَّةُ بِٱلۡإِثۡمِۚ فَحَسۡبُهُۥ جَهَنَّمُۖ وَلَبِئۡسَ ٱلۡمِهَادُ

Idan kuma aka ce masa: “Ka kiyaye dokokin Allah” sai girman kai ya kama shi saboda savo. To Jahannama ta ishe shi (makwanci), kuma lalle tir da wannan makwanci



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 167

وَلِيَعۡلَمَ ٱلَّذِينَ نَافَقُواْۚ وَقِيلَ لَهُمۡ تَعَالَوۡاْ قَٰتِلُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ أَوِ ٱدۡفَعُواْۖ قَالُواْ لَوۡ نَعۡلَمُ قِتَالٗا لَّٱتَّبَعۡنَٰكُمۡۗ هُمۡ لِلۡكُفۡرِ يَوۡمَئِذٍ أَقۡرَبُ مِنۡهُمۡ لِلۡإِيمَٰنِۚ يَقُولُونَ بِأَفۡوَٰهِهِم مَّا لَيۡسَ فِي قُلُوبِهِمۡۚ وَٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِمَا يَكۡتُمُونَ

Kuma don Ya bayyana waxanda suka yi munafunci; kuma aka riqa cewa da su: “Ku zo ku yi yaqi don Allah ko don kariya.” Sai suka ce: “Da mun san za a yi yaqi ai da lalle mun biyo ku.” Su a wannan lokacin sun fi kusanci ga kafirci fiye da imani, suna faxi da bakunansu abin da ba ya cikin zukatansu. Kuma Allah Ya san abin da suke voyewa



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 168

ٱلَّذِينَ قَالُواْ لِإِخۡوَٰنِهِمۡ وَقَعَدُواْ لَوۡ أَطَاعُونَا مَا قُتِلُواْۗ قُلۡ فَٱدۡرَءُواْ عَنۡ أَنفُسِكُمُ ٱلۡمَوۡتَ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

Su ne waxanda suka faxa wa ‘yan’uwansu, alhalin suna zaune a gida cewa: “In da sun bi (shawarar) mu da ba a kashe su ba.” Ka ce: “To ku kare kanku daga mutuwa in har kun kasance masu gaskiya.”



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 60

أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ يَزۡعُمُونَ أَنَّهُمۡ ءَامَنُواْ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ وَمَآ أُنزِلَ مِن قَبۡلِكَ يُرِيدُونَ أَن يَتَحَاكَمُوٓاْ إِلَى ٱلطَّـٰغُوتِ وَقَدۡ أُمِرُوٓاْ أَن يَكۡفُرُواْ بِهِۦۖ وَيُرِيدُ ٱلشَّيۡطَٰنُ أَن يُضِلَّهُمۡ ضَلَٰلَۢا بَعِيدٗا

Shin ba ka ganin waxannan da suke riya cewa sun yi imani da abin da aka saukar maka, da abin da aka saukar gabaninka, suna nufin su kai hukunci gaban Xagutu[1] (wanin Allah), alhalin an umarce su da su kafirce masa, Shaixan kuma yana nufin ya vatar da su vata mai nisa?


1- Xagutu, shi ne duk wani abu da bawa zai qetare iyakokin Allah a sanadiyyarsa; mutum ne ko gunki ko wata doka.


Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 61

وَإِذَا قِيلَ لَهُمۡ تَعَالَوۡاْ إِلَىٰ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ وَإِلَى ٱلرَّسُولِ رَأَيۡتَ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ يَصُدُّونَ عَنكَ صُدُودٗا

Kuma idan an ce da su: “Ku zo ga abin da Allah Ya saukar, kuma ku zo ga wannan Manzo,” sai kawai ka ga munafuqai suna bijire maka matuqar bijirewa



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 62

فَكَيۡفَ إِذَآ أَصَٰبَتۡهُم مُّصِيبَةُۢ بِمَا قَدَّمَتۡ أَيۡدِيهِمۡ ثُمَّ جَآءُوكَ يَحۡلِفُونَ بِٱللَّهِ إِنۡ أَرَدۡنَآ إِلَّآ إِحۡسَٰنٗا وَتَوۡفِيقًا

To yaya halinsu zai kasance idan wata musiba ta sauka a kansu saboda abin da hannayensu suka gabatar, sannan sai su zo maka suna rantsuwa da Allah, (suna cewa): “Ba ma nufin wani abu sai kyautatawa da kuma haxin kai.”?



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 63

أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ يَعۡلَمُ ٱللَّهُ مَا فِي قُلُوبِهِمۡ فَأَعۡرِضۡ عَنۡهُمۡ وَعِظۡهُمۡ وَقُل لَّهُمۡ فِيٓ أَنفُسِهِمۡ قَوۡلَۢا بَلِيغٗا

Waxannan su ne waxanda Allah Yake sane da abin da ke cikin zukatansu, don haka ka kawar da kai daga kansu kuma ka yi musu wa’azi kuma ka faxa musu magana a karan-kawunansu magana mai shiga zukata



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 72

وَإِنَّ مِنكُمۡ لَمَن لَّيُبَطِّئَنَّ فَإِنۡ أَصَٰبَتۡكُم مُّصِيبَةٞ قَالَ قَدۡ أَنۡعَمَ ٱللَّهُ عَلَيَّ إِذۡ لَمۡ أَكُن مَّعَهُمۡ شَهِيدٗا

Kuma lalle a cikinku akwai wanda yake daqilewa, idan wata musiba ta same ku, sai ya ce: “Haqiqa Allah Ya yi mini ni’ima da ban halarci (yaqin) tare da su ba.”



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 73

وَلَئِنۡ أَصَٰبَكُمۡ فَضۡلٞ مِّنَ ٱللَّهِ لَيَقُولَنَّ كَأَن لَّمۡ تَكُنۢ بَيۡنَكُمۡ وَبَيۡنَهُۥ مَوَدَّةٞ يَٰلَيۡتَنِي كُنتُ مَعَهُمۡ فَأَفُوزَ فَوۡزًا عَظِيمٗا

Amma idan wata falala ta same ku daga Allah, tabbas zai riqa cewa, kamar daxai ba wata soyayya tsakaninku da shi: “Ina ma na kasance tare da su, don ni ma in rabauta rabo mai girma?”[1]


1- Watau a raba ganimar da aka samo tare da shi, shi ma ya more sosai.


Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 88

۞فَمَا لَكُمۡ فِي ٱلۡمُنَٰفِقِينَ فِئَتَيۡنِ وَٱللَّهُ أَرۡكَسَهُم بِمَا كَسَبُوٓاْۚ أَتُرِيدُونَ أَن تَهۡدُواْ مَنۡ أَضَلَّ ٱللَّهُۖ وَمَن يُضۡلِلِ ٱللَّهُ فَلَن تَجِدَ لَهُۥ سَبِيلٗا

Shin me ya sa kuka kasu gida biyu dangane da lamarin munafuqai[1], alhali Allah ne Ya mayar da su baya saboda abin da suka aikata?[2] Shin kuna nufin ku shiryar da wanda Allah Ya riga Ya vatar da shi ne? Duk wanda Allah Ya vatar da shi kuwa, to ba za ka iya samar masa wata mafita ba


1- Watau wasu daga cikin muminai suna kafirta su wasu kuma ba sa kafirta su.


2- Watau na rashin biyayya da xa’a ga Allah da Manzonsa ().


Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 89

وَدُّواْ لَوۡ تَكۡفُرُونَ كَمَا كَفَرُواْ فَتَكُونُونَ سَوَآءٗۖ فَلَا تَتَّخِذُواْ مِنۡهُمۡ أَوۡلِيَآءَ حَتَّىٰ يُهَاجِرُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۚ فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَخُذُوهُمۡ وَٱقۡتُلُوهُمۡ حَيۡثُ وَجَدتُّمُوهُمۡۖ وَلَا تَتَّخِذُواْ مِنۡهُمۡ وَلِيّٗا وَلَا نَصِيرًا

Sun yi fatan ina ma za ku kafirta kamar yadda suka kafirta, sai ku zama xaya. Don haka kar ku riqi masoya a cikinsu har sai sun yi hijira don Allah. Idan kuwa suka juya baya, to ku kama su, kuma ku kashe su a duk inda kuka same su; kuma kada ku riqi wani masoyi ko mai taimako daga cikinsu



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 90

إِلَّا ٱلَّذِينَ يَصِلُونَ إِلَىٰ قَوۡمِۭ بَيۡنَكُمۡ وَبَيۡنَهُم مِّيثَٰقٌ أَوۡ جَآءُوكُمۡ حَصِرَتۡ صُدُورُهُمۡ أَن يُقَٰتِلُوكُمۡ أَوۡ يُقَٰتِلُواْ قَوۡمَهُمۡۚ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ لَسَلَّطَهُمۡ عَلَيۡكُمۡ فَلَقَٰتَلُوكُمۡۚ فَإِنِ ٱعۡتَزَلُوكُمۡ فَلَمۡ يُقَٰتِلُوكُمۡ وَأَلۡقَوۡاْ إِلَيۡكُمُ ٱلسَّلَمَ فَمَا جَعَلَ ٱللَّهُ لَكُمۡ عَلَيۡهِمۡ سَبِيلٗا

Sai dai (ban da) waxanda suke fakewa a wajen waxansu mutane da kuke da yarjejeniya ta zaman lafiya a tsakaninku (da su), ko kuma waxanda suka zo muku zukatansu sun quntata game da yaqar ku ko yaqar mutanensu. Da kuwa Allah Ya ga dama da Ya xora su a kanku, kuma tabbas da sun yaqe ku. Don haka idan suka bar ku ba su yaqe ku ba, kuma suka miqa muku saqo na sulhu, to Allah bai ba ku wata dama ta ku yaqe su ba



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 91

سَتَجِدُونَ ءَاخَرِينَ يُرِيدُونَ أَن يَأۡمَنُوكُمۡ وَيَأۡمَنُواْ قَوۡمَهُمۡ كُلَّ مَا رُدُّوٓاْ إِلَى ٱلۡفِتۡنَةِ أُرۡكِسُواْ فِيهَاۚ فَإِن لَّمۡ يَعۡتَزِلُوكُمۡ وَيُلۡقُوٓاْ إِلَيۡكُمُ ٱلسَّلَمَ وَيَكُفُّوٓاْ أَيۡدِيَهُمۡ فَخُذُوهُمۡ وَٱقۡتُلُوهُمۡ حَيۡثُ ثَقِفۡتُمُوهُمۡۚ وَأُوْلَـٰٓئِكُمۡ جَعَلۡنَا لَكُمۡ عَلَيۡهِمۡ سُلۡطَٰنٗا مُّبِينٗا

Za ku sami wasu mutanen suna qoqarin su sami amincewarku, kuma su sami amincewar mutanensu, amma duk sa’adda aka kira su zuwa kafirci sai su auka cikinsa. To idan ba su rabu da ku ba, kuma ba su neme ku da zaman lafiya ba, kuma ba su kame hannayensu ba, to ku kama su, kuma ku kashe su a duk inda kuka same su. Waxannan kuwa Mun sanya muku bayyananniyar hujja a kansu



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 138

بَشِّرِ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ بِأَنَّ لَهُمۡ عَذَابًا أَلِيمًا

Ka yi albishir ga munafuqai cewa, suna da wata azaba mai raxaxi



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 139

ٱلَّذِينَ يَتَّخِذُونَ ٱلۡكَٰفِرِينَ أَوۡلِيَآءَ مِن دُونِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَۚ أَيَبۡتَغُونَ عِندَهُمُ ٱلۡعِزَّةَ فَإِنَّ ٱلۡعِزَّةَ لِلَّهِ جَمِيعٗا

Su ne waxanda suke riqar kafirai a matsayin masoya, su qyale muminai. Shin suna neman wata xaukaka ce a wurinsu? To lalle xaukaka gaba xaya ta Allah ce[1]


1- Watau shi ne yake bayar da girma, kuma ga muminai kaxai yake ba da shi, don haka munafukai ba za su same shi ba.


Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 140

وَقَدۡ نَزَّلَ عَلَيۡكُمۡ فِي ٱلۡكِتَٰبِ أَنۡ إِذَا سَمِعۡتُمۡ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ يُكۡفَرُ بِهَا وَيُسۡتَهۡزَأُ بِهَا فَلَا تَقۡعُدُواْ مَعَهُمۡ حَتَّىٰ يَخُوضُواْ فِي حَدِيثٍ غَيۡرِهِۦٓ إِنَّكُمۡ إِذٗا مِّثۡلُهُمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ جَامِعُ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ وَٱلۡكَٰفِرِينَ فِي جَهَنَّمَ جَمِيعًا

Kuma haqiqa Ya saukar muku a cikin littafi[1] cewa, idan kuka ji ayoyin Allah ana kafirce musu, ana izgili da su, to kar ku zauna tare da su har sai sun shiga cikin wani zancen daban ba wannan ba. Lalle in har kuka zauna tare da su, to kun zama kamarsu. Lalle Allah Mai tattara munafuqai ne da kafirai cikin wutar Jahannama gaba xaya


1- Watau a cikin Alqur’ani a Suratul An’am, aya ta 68 inda Allah ya haramta wa muminai zama a inda ake yi wa shari’ar Allah izgili da rashin kunya.


Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 141

ٱلَّذِينَ يَتَرَبَّصُونَ بِكُمۡ فَإِن كَانَ لَكُمۡ فَتۡحٞ مِّنَ ٱللَّهِ قَالُوٓاْ أَلَمۡ نَكُن مَّعَكُمۡ وَإِن كَانَ لِلۡكَٰفِرِينَ نَصِيبٞ قَالُوٓاْ أَلَمۡ نَسۡتَحۡوِذۡ عَلَيۡكُمۡ وَنَمۡنَعۡكُم مِّنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَۚ فَٱللَّهُ يَحۡكُمُ بَيۡنَكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۚ وَلَن يَجۡعَلَ ٱللَّهُ لِلۡكَٰفِرِينَ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ سَبِيلًا

Su ne waxanda suke fakon ku, idan kun sami wata nasara daga Allah sai su ce: “Shin ashe ba tare da ku muke ba?” Kuma idan kafirai ne suka samu wata nasara, sai su ce: “Ashe ba mu muka sami dama a kanku ba (amma muka qyale ku), kuma muka kare ku daga muminai?” To lalle Allah zai yi hukunci a tsakaninku ranar alqiyama, kuma Allah ba zai tava ba wa kafirai wata dama ba a kan muminai[1]


1- Watau ba zai tava ba su nasara a kan muminai gaba xaya ba, sai dai ta wani wuri ban da wani wuri. Hakanan a lahira ba zai ba su hujjar da za su rinjayi muminai da ita ba.


Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 142

إِنَّ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ يُخَٰدِعُونَ ٱللَّهَ وَهُوَ خَٰدِعُهُمۡ وَإِذَا قَامُوٓاْ إِلَى ٱلصَّلَوٰةِ قَامُواْ كُسَالَىٰ يُرَآءُونَ ٱلنَّاسَ وَلَا يَذۡكُرُونَ ٱللَّهَ إِلَّا قَلِيلٗا

Lalle munafuqai suna yaudarar Allah, alhali kuwa Shi Mai mayar musu da sakamakon yaudararsu ne; kuma idan sun tashi zuwa salla, za su tashi suna masu kasala ne, suna yin aiki don mutane su gani, kuma ba su ambaton Allah sai kaxan



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 143

مُّذَبۡذَبِينَ بَيۡنَ ذَٰلِكَ لَآ إِلَىٰ هَـٰٓؤُلَآءِ وَلَآ إِلَىٰ هَـٰٓؤُلَآءِۚ وَمَن يُضۡلِلِ ٱللَّهُ فَلَن تَجِدَ لَهُۥ سَبِيلٗا

Suna ta kai-kawo tsakanin haka (kafirci da imani), su ba sa tare da waxanan, kuma ba sa tare da waxancan. Duk wanda Allah Ya vatar da shi kuwa, to babu yadda za ka iya sama masa wani tafarki na shiriya