وَٱذۡكُرۡ فِي ٱلۡكِتَٰبِ إِدۡرِيسَۚ إِنَّهُۥ كَانَ صِدِّيقٗا نَّبِيّٗا
Kuma ka ambaci (labarin) Idrisu a cikin (wannan) Littafi (Alqur’ani). Lalle shi ya kasance mai yawan gaskiya ne, Annabi
Compartir :
وَرَفَعۡنَٰهُ مَكَانًا عَلِيًّا
Muka kuma xaukaka shi daraja maxaukakiya[1]
1- A Mi’iraji da Annabi () ya yi ya haxu da shi a sama ta huxu.
وَإِسۡمَٰعِيلَ وَإِدۡرِيسَ وَذَا ٱلۡكِفۡلِۖ كُلّٞ مِّنَ ٱلصَّـٰبِرِينَ
(Ka tuna) kuma Isma’ila da Idrisa da kuma Zulkifli; dukkansu suna cikin masu haquri