ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡحَيُّ ٱلۡقَيُّومُۚ لَا تَأۡخُذُهُۥ سِنَةٞ وَلَا نَوۡمٞۚ لَّهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ مَن ذَا ٱلَّذِي يَشۡفَعُ عِندَهُۥٓ إِلَّا بِإِذۡنِهِۦۚ يَعۡلَمُ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡۖ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَيۡءٖ مِّنۡ عِلۡمِهِۦٓ إِلَّا بِمَا شَآءَۚ وَسِعَ كُرۡسِيُّهُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَۖ وَلَا يَـُٔودُهُۥ حِفۡظُهُمَاۚ وَهُوَ ٱلۡعَلِيُّ ٱلۡعَظِيمُ
Allah, babu wani abin bauta wa da cancanta sai Shi, Rayayye, Tsayayye da Zatinsa; gyangyaxi ba ya kama shi, ballantana barci. Abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qasa nasa ne shi kaxai. Wane ne ya isa ya yi ceto a wurinsa in ba da izininsa ba? Ya san abin da yake tare da su a yanzu da kuma abin da zai biyo bayansu; kuma ba sa iya sanin wani abu cikin iliminsa sai abin da Ya ga dama. Kursiyyunsa ya yalwaci sammai da qasa, kuma kiyaye su ba zai nauyaye Shi ba, kuma Shi ne Maxaukaki Mai girma
مَّن يَشۡفَعۡ شَفَٰعَةً حَسَنَةٗ يَكُن لَّهُۥ نَصِيبٞ مِّنۡهَاۖ وَمَن يَشۡفَعۡ شَفَٰعَةٗ سَيِّئَةٗ يَكُن لَّهُۥ كِفۡلٞ مِّنۡهَاۗ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ مُّقِيتٗا
Duk wanda ya yi (ma wani) kyakkyawar alfarma, zai samu rabonsa na lada daga gare ta; kuma duk wanda ya yi wa wani mummunar alfarma, zai samu rabonsa na zunubi daga gare ta. Kuma Allah Ya kasance Mai kiyaye komai ne[1]
1- Watau zai yi wa kowa sakamako gwargwadon aikinsa mai kyau ko mummuna.
وَأَنذِرۡ بِهِ ٱلَّذِينَ يَخَافُونَ أَن يُحۡشَرُوٓاْ إِلَىٰ رَبِّهِمۡ لَيۡسَ لَهُم مِّن دُونِهِۦ وَلِيّٞ وَلَا شَفِيعٞ لَّعَلَّهُمۡ يَتَّقُونَ
Kuma ka yi gargaxi da shi (Alqur’ani) ga waxanda suke jin tsoron a tattara su a gaban Ubangijinsu, ba su da wani majivincin lamari in ba Shi ba, kuma ba su da wani mai ceto, don su kiyaye dokokin Allah
وَذَرِ ٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ دِينَهُمۡ لَعِبٗا وَلَهۡوٗا وَغَرَّتۡهُمُ ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَاۚ وَذَكِّرۡ بِهِۦٓ أَن تُبۡسَلَ نَفۡسُۢ بِمَا كَسَبَتۡ لَيۡسَ لَهَا مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلِيّٞ وَلَا شَفِيعٞ وَإِن تَعۡدِلۡ كُلَّ عَدۡلٖ لَّا يُؤۡخَذۡ مِنۡهَآۗ أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ أُبۡسِلُواْ بِمَا كَسَبُواْۖ لَهُمۡ شَرَابٞ مِّنۡ حَمِيمٖ وَعَذَابٌ أَلِيمُۢ بِمَا كَانُواْ يَكۡفُرُونَ
Ka rabu da waxanda suka xauki addininsu wasa da sharholiya, rayuwarsu ta duniya kuma ta ruxe su. Ka kuma yi gargaxi da shi (Alqur’ani), saboda kada a jarrabi rai da abin da ya aikata wanda ba ya da wani mataimaki ko mai ceto ban da Allah, ko da kuwa (ran) ya ba da kowace irin fansa ba za a karva ba daga gare shi. Waxancan su ne waxanda aka kange (don yi musu azaba) saboda abin da suka aikata; suna da abin sha na tafasasshen ruwa da kuma azaba mai raxaxi saboda abin da suka zamanto suna kafircewa (da shi)
إِنَّ رَبَّكُمُ ٱللَّهُ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٖ ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰ عَلَى ٱلۡعَرۡشِۖ يُدَبِّرُ ٱلۡأَمۡرَۖ مَا مِن شَفِيعٍ إِلَّا مِنۢ بَعۡدِ إِذۡنِهِۦۚ ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمۡ فَٱعۡبُدُوهُۚ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ
Lalle Ubangijinku Shi ne Allah wanda Ya halicci sammai da qasa cikin kwana shida, sannan Ya daidaita a kan Al’arshi[1]; Yana tsara al’amari (yadda Ya ga dama). Babu wani mai ceto sai da izininsa. Wannan Shi ne Allah Ubangijinku. To sai ku bauta masa. Ashe ba za ku wa’azantu ba?
1- Duba Suratul A’araf aya ta 54. hashiya ta 126.
يَعۡلَمُ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡ وَلَا يَشۡفَعُونَ إِلَّا لِمَنِ ٱرۡتَضَىٰ وَهُم مِّنۡ خَشۡيَتِهِۦ مُشۡفِقُونَ
Yana sane da ayyukansu da suka gabatar da na nan gaba, ba kuma za su yi ceto ba sai ga wanda Ya yarda (daga bayinsa), suna kuwa masu kaffa-kaffa don tsoron Sa
ٱللَّهُ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَيۡنَهُمَا فِي سِتَّةِ أَيَّامٖ ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰ عَلَى ٱلۡعَرۡشِۖ مَا لَكُم مِّن دُونِهِۦ مِن وَلِيّٖ وَلَا شَفِيعٍۚ أَفَلَا تَتَذَكَّرُونَ
Allah ne Wanda Ya halicci sammai da qasa da abin da yake tsakaninsu cikin kwana shida sannan Ya daidaita bisa Al’arshi; ba ku da wani majivincin al’amari ko mai ceto bayansa. Yanzu me ya sa ba kwa wa’azantuwa?
ءَأَتَّخِذُ مِن دُونِهِۦٓ ءَالِهَةً إِن يُرِدۡنِ ٱلرَّحۡمَٰنُ بِضُرّٖ لَّا تُغۡنِ عَنِّي شَفَٰعَتُهُمۡ شَيۡـٔٗا وَلَا يُنقِذُونِ
“Yanzu na riqi wasu ababen bauta ba Shi ba, alhali kuwa idan (Allah) Mai rahama Ya nufe ni da wata cuta, cetonsu ba zai amfana min komai ba, kuma ba za su iya tsamo ni ba?
أَمِ ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ شُفَعَآءَۚ قُلۡ أَوَلَوۡ كَانُواْ لَا يَمۡلِكُونَ شَيۡـٔٗا وَلَا يَعۡقِلُونَ
Tabbas sun dai riqi wasu masu ceto ne ba Allah ba. Ka ce: “Yanzu (kwa yi haka) ko da kuwa sun kasance ba sa mallakin komai, kuma ba sa hankalta?”
قُل لِّلَّهِ ٱلشَّفَٰعَةُ جَمِيعٗاۖ لَّهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ ثُمَّ إِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ
Ka ce: “Ceto gaba xaya na Allah ne; mulkin sammai da qasa nasa ne Shi kaxai; sannan kuma wurinsa ne kawai za a komar da ku.”
وَلَا يَمۡلِكُ ٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ مِن دُونِهِ ٱلشَّفَٰعَةَ إِلَّا مَن شَهِدَ بِٱلۡحَقِّ وَهُمۡ يَعۡلَمُونَ
Waxanda kuwa suke bauta wa wani abu ba Shi ba, ba sa mallakar ceto, sai dai waxanda suka yi Kalmar Shahada ta gaskiya, alhalin suna sane (da ma’anarta)
۞وَكَم مِّن مَّلَكٖ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ لَا تُغۡنِي شَفَٰعَتُهُمۡ شَيۡـًٔا إِلَّا مِنۢ بَعۡدِ أَن يَأۡذَنَ ٱللَّهُ لِمَن يَشَآءُ وَيَرۡضَىٰٓ
Mala’iku nawa ne a cikin sammai cetonsu ba ya amfanar da komai sai da izinin Allah ga waxanda Ya ga dama Ya kuma yarda (da shi)?
فَمَا تَنفَعُهُمۡ شَفَٰعَةُ ٱلشَّـٰفِعِينَ
Saboda haka ceton masu ceto ba zai amfane su ba