Capítulo: Suratus Shu’ara

Verso : 213

فَلَا تَدۡعُ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ فَتَكُونَ مِنَ ٱلۡمُعَذَّبِينَ

To kada ka bauta wa wani tare da Allah, sai ka zamanto daga waxanda za a yi wa azaba



Capítulo: Suratun Namli

Verso : 62

أَمَّن يُجِيبُ ٱلۡمُضۡطَرَّ إِذَا دَعَاهُ وَيَكۡشِفُ ٱلسُّوٓءَ وَيَجۡعَلُكُمۡ خُلَفَآءَ ٱلۡأَرۡضِۗ أَءِلَٰهٞ مَّعَ ٱللَّهِۚ قَلِيلٗا مَّا تَذَكَّرُونَ

Ko kuwa wane ne yake amsa wa wanda yake cikin matsuwa lokacin da ya roqe shi, yake kuma yaye duk wani bala’i, yake kuma sanya ku halifofi a bayan qasa[1]? Shin akwai wani abin bauta da gaskiya tare da Allah? Kaxan ne qwarai kuke wa’azantuwa


1- Wasu su shuxe wasu su zo su gaje su, tsareku bayan tsareku.


Capítulo: Suratul Qasas

Verso : 64

وَقِيلَ ٱدۡعُواْ شُرَكَآءَكُمۡ فَدَعَوۡهُمۡ فَلَمۡ يَسۡتَجِيبُواْ لَهُمۡ وَرَأَوُاْ ٱلۡعَذَابَۚ لَوۡ أَنَّهُمۡ كَانُواْ يَهۡتَدُونَ

Kuma aka ce: “Ku kirawo abokan tarayyar naku”, sannan suka kirawo su, sai ba su amsa musu ba, suka kuma ga azaba. (Suka riqa burin) ina ma sun kasance shiryayyu!



Capítulo: Suratul Qasas

Verso : 87

وَلَا يَصُدُّنَّكَ عَنۡ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ بَعۡدَ إِذۡ أُنزِلَتۡ إِلَيۡكَۖ وَٱدۡعُ إِلَىٰ رَبِّكَۖ وَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ

Kuma lallai kada su hana ka (isar da) ayoyin Allah bayan an riga an saukar maka da su; kuma ka yi kira zuwa ga Ubangijinka; kuma lallai kada ka zamanto daga mushrikai



Capítulo: Suratul Qasas

Verso : 88

وَلَا تَدۡعُ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَۘ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۚ كُلُّ شَيۡءٍ هَالِكٌ إِلَّا وَجۡهَهُۥۚ لَهُ ٱلۡحُكۡمُ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ

Kuma kada ka bauta wa wani abin bauta daban tare da Allah. Babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi. Kowane abu mai halaka ne sai Fuskarsa kawai. Hukunci (duk) nasa ne, zuwa gare Shi kuma za a mayar da ku



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 65

فَإِذَا رَكِبُواْ فِي ٱلۡفُلۡكِ دَعَوُاْ ٱللَّهَ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ فَلَمَّا نَجَّىٰهُمۡ إِلَى ٱلۡبَرِّ إِذَا هُمۡ يُشۡرِكُونَ

To idan suka hau jiragen ruwa sukan roqi Allah suna masu tsantsanta addini a gare Shi; to lokacin da Ya tserar da su zuwa tudu sai ga su suna yin shirka



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 33

وَإِذَا مَسَّ ٱلنَّاسَ ضُرّٞ دَعَوۡاْ رَبَّهُم مُّنِيبِينَ إِلَيۡهِ ثُمَّ إِذَآ أَذَاقَهُم مِّنۡهُ رَحۡمَةً إِذَا فَرِيقٞ مِّنۡهُم بِرَبِّهِمۡ يُشۡرِكُونَ

Idan kuma wani matsi ya sami mutane sai su roqi Ubangijinsu suna masu komawa gare Shi, sannan kuma idan Ya xanxana musu rahama daga gare Shi sai ka ga wata qungiyar daga cikinsu suna tarayya da Ubangijinsu



Capítulo: Suratu Luqman

Verso : 32

وَإِذَا غَشِيَهُم مَّوۡجٞ كَٱلظُّلَلِ دَعَوُاْ ٱللَّهَ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ فَلَمَّا نَجَّىٰهُمۡ إِلَى ٱلۡبَرِّ فَمِنۡهُم مُّقۡتَصِدٞۚ وَمَا يَجۡحَدُ بِـَٔايَٰتِنَآ إِلَّا كُلُّ خَتَّارٖ كَفُورٖ

Idan kuwa wata igiyar ruwa kamar duwatsu ta kere su, sai su roqi Allah suna tsantsanta addini a gare Shi, to kuma idan Ya tserar da su zuwa gaci, to akan sami tsaka-tsaki daga cikinsu. Kuma babu mai yin jayayya da ayoyinmu sai duk wani mayaudari, mai butulci



Capítulo: Suratus Sajda

Verso : 16

تَتَجَافَىٰ جُنُوبُهُمۡ عَنِ ٱلۡمَضَاجِعِ يَدۡعُونَ رَبَّهُمۡ خَوۡفٗا وَطَمَعٗا وَمِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ يُنفِقُونَ

Kuyavunsu suna nesantar wuraren kwanciya[1], suna bauta wa Ubangijinsu cikin halin tsoro da kuma kwaxayi, kuma suna ciyarwa daga abin da Muka arzuta su


1- Watau suna qaurace wa wuraren barci, suna tsayawa cikin dare suna sallolin nafilfilu suna roqon Allah ().


Capítulo: Suratu Saba’i

Verso : 22

قُلِ ٱدۡعُواْ ٱلَّذِينَ زَعَمۡتُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ لَا يَمۡلِكُونَ مِثۡقَالَ ذَرَّةٖ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَلَا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَا لَهُمۡ فِيهِمَا مِن شِرۡكٖ وَمَا لَهُۥ مِنۡهُم مِّن ظَهِيرٖ

Ka ce: “Ku kirawo waxanda kuka riya (cewa su ne iyayen giji) ba Allah ba;” ba sa mallakar wani abu daidai da qwayar zarra a cikin sammai ko a cikin qasa, ba kuma su da wata tarayya a cikinsu, ba Shi kuma da wani mataimaki daga cikinsu



Capítulo: Suratuz Zumar

Verso : 8

۞وَإِذَا مَسَّ ٱلۡإِنسَٰنَ ضُرّٞ دَعَا رَبَّهُۥ مُنِيبًا إِلَيۡهِ ثُمَّ إِذَا خَوَّلَهُۥ نِعۡمَةٗ مِّنۡهُ نَسِيَ مَا كَانَ يَدۡعُوٓاْ إِلَيۡهِ مِن قَبۡلُ وَجَعَلَ لِلَّهِ أَندَادٗا لِّيُضِلَّ عَن سَبِيلِهِۦۚ قُلۡ تَمَتَّعۡ بِكُفۡرِكَ قَلِيلًا إِنَّكَ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلنَّارِ

Idan kuma wata cuta ta sami mutum sai ya roqi Ubangijinsa yana mai komawa gare Shi, sannan idan Ya ba shi wata ni’ima daga gare Shi, sai ya manta abin da ya kasance yana roqon Sa a da, ya kuma sanya abokan tarayya ga Allah don ya vatar (da mutane) daga hanyarsa (Allah). Ka ce: “Ka ji daxi xan kaxan da kafircinka; lalle kai kam kana daga cikin ‘yan wuta.”



Capítulo: Suratuz Zumar

Verso : 49

فَإِذَا مَسَّ ٱلۡإِنسَٰنَ ضُرّٞ دَعَانَا ثُمَّ إِذَا خَوَّلۡنَٰهُ نِعۡمَةٗ مِّنَّا قَالَ إِنَّمَآ أُوتِيتُهُۥ عَلَىٰ عِلۡمِۭۚ بَلۡ هِيَ فِتۡنَةٞ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ

To idan wata cuta ta samu mutum sai ya roqe Mu, sannan idan Mun ba shi wata ni’ima daga gare Mu sai ya ce: “Ai an ba ni ita ne kawai don sanin (cancantata)”. Ba haka ba ne, ita wata jarrabawa ce kawai, sai dai yawancinsu ba sa sanin (haka)



Capítulo: Suratu Ghafir

Verso : 14

فَٱدۡعُواْ ٱللَّهَ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡكَٰفِرُونَ

Sai ku bauta wa Allah kuna masu tsantsanta addini gare Shi, ko da kuwa kafirai ba sa so



Capítulo: Suratu Ghafir

Verso : 43

لَا جَرَمَ أَنَّمَا تَدۡعُونَنِيٓ إِلَيۡهِ لَيۡسَ لَهُۥ دَعۡوَةٞ فِي ٱلدُّنۡيَا وَلَا فِي ٱلۡأٓخِرَةِ وَأَنَّ مَرَدَّنَآ إِلَى ٱللَّهِ وَأَنَّ ٱلۡمُسۡرِفِينَ هُمۡ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِ

“Ba shakka abin da kuke kira na zuwa gare shi ba shi da wani kira karvavve a duniya ko a lahira, kuma lalle makomarmu zuwa ga Allah ne, mavarnata kuma tabbas su ne ‘yan wuta



Capítulo: Suratu Ghafir

Verso : 49

وَقَالَ ٱلَّذِينَ فِي ٱلنَّارِ لِخَزَنَةِ جَهَنَّمَ ٱدۡعُواْ رَبَّكُمۡ يُخَفِّفۡ عَنَّا يَوۡمٗا مِّنَ ٱلۡعَذَابِ

Kuma waxanda suke cikin wuta suka ce da masu tsaron Jahannama: “Ku roqa mana Ubangijinku mana Ya sauqaqe mana azaba ta wuni (xaya).”



Capítulo: Suratu Ghafir

Verso : 50

قَالُوٓاْ أَوَلَمۡ تَكُ تَأۡتِيكُمۡ رُسُلُكُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِۖ قَالُواْ بَلَىٰۚ قَالُواْ فَٱدۡعُواْۗ وَمَا دُعَـٰٓؤُاْ ٱلۡكَٰفِرِينَ إِلَّا فِي ضَلَٰلٍ

Suka ce: “Yanzu manzanninku ba su kasance suna zo muku da (ayoyi) bayyanannu ba?” Suka ce: “Haka ne (sun zo)”. Sai su ce: “To sai ku yi ta roqon. Roqon kafirai kuwa bai zamo ba sai a tave.”



Capítulo: Suratu Ghafir

Verso : 60

وَقَالَ رَبُّكُمُ ٱدۡعُونِيٓ أَسۡتَجِبۡ لَكُمۡۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ يَسۡتَكۡبِرُونَ عَنۡ عِبَادَتِي سَيَدۡخُلُونَ جَهَنَّمَ دَاخِرِينَ

Ubangijinku kuma Ya ce: “Ku roqe Ni zan amsa muku. Lalle waxanda suke yin girman kai game da bauta min, ba da daxewa ba za su shiga Jahannama a wulaqance.”



Capítulo: Suratu Ghafir

Verso : 65

هُوَ ٱلۡحَيُّ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ فَٱدۡعُوهُ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَۗ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Shi Rayayye ne, babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi, sai ku roqe Shi kuna masu tsantsanta addini a gare Shi. Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai



Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 49

لَّا يَسۡـَٔمُ ٱلۡإِنسَٰنُ مِن دُعَآءِ ٱلۡخَيۡرِ وَإِن مَّسَّهُ ٱلشَّرُّ فَيَـُٔوسٞ قَنُوطٞ

Mutum ba ya qosawa wajen roqon alheri, idan kuwa wani sharri ya same shi, to sai ya zama mai tsananin xebe qauna



Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 51

وَإِذَآ أَنۡعَمۡنَا عَلَى ٱلۡإِنسَٰنِ أَعۡرَضَ وَنَـَٔا بِجَانِبِهِۦ وَإِذَا مَسَّهُ ٱلشَّرُّ فَذُو دُعَآءٍ عَرِيضٖ

Idan kuma Muka yi wa mutum ni’ima sai ya bijire ya ja jikinsa nesa (daga tuna Allah), kuma idan sharri ya same shi, sai ya zama mai faffaxar addu’a



Capítulo: Suratul Ahqaf 

Verso : 5

وَمَنۡ أَضَلُّ مِمَّن يَدۡعُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَن لَّا يَسۡتَجِيبُ لَهُۥٓ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَهُمۡ عَن دُعَآئِهِمۡ غَٰفِلُونَ

Wane ne ya fi vata fiye da wanda yake bauta wa wani ba Allah ba, wanda ba zai amsa masa ba har zuwa ranar alqiyama, kuma su (ababen bautar) rafkanannu ne game da bautar da suke yi musu?



Capítulo: Suratul Ahqaf 

Verso : 15

وَوَصَّيۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ بِوَٰلِدَيۡهِ إِحۡسَٰنًاۖ حَمَلَتۡهُ أُمُّهُۥ كُرۡهٗا وَوَضَعَتۡهُ كُرۡهٗاۖ وَحَمۡلُهُۥ وَفِصَٰلُهُۥ ثَلَٰثُونَ شَهۡرًاۚ حَتَّىٰٓ إِذَا بَلَغَ أَشُدَّهُۥ وَبَلَغَ أَرۡبَعِينَ سَنَةٗ قَالَ رَبِّ أَوۡزِعۡنِيٓ أَنۡ أَشۡكُرَ نِعۡمَتَكَ ٱلَّتِيٓ أَنۡعَمۡتَ عَلَيَّ وَعَلَىٰ وَٰلِدَيَّ وَأَنۡ أَعۡمَلَ صَٰلِحٗا تَرۡضَىٰهُ وَأَصۡلِحۡ لِي فِي ذُرِّيَّتِيٓۖ إِنِّي تُبۡتُ إِلَيۡكَ وَإِنِّي مِنَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ

Kuma Mun yi wa mutum wasiyya da kyautata wa mahaifansa; mahaifiyarsa ta xauki cikinsa a wahalce, ta kuma haife shi a wahalce; xaukan cikinsa da yaye shi kuma wata talatin ne, har lokacin da ya cika qarfinsa ya kai shekara arba’in ya ce: “Ya Ubangijina, Ka kimsa min yadda zan gode wa ni’imarka, wadda Ka ni’imta ni da ita da kuma mahaifana, kuma (Ka ba ni iko) in yi aiki nagari wanda za Ka yarda da shi, kuma Ka kyautata min zurriyata; lalle ni na tuba a gare Ka, kuma lalle ni ina daga cikin Musulmi.”



Capítulo: Suratux Xur

Verso : 28

إِنَّا كُنَّا مِن قَبۡلُ نَدۡعُوهُۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡبَرُّ ٱلرَّحِيمُ

“Lalle mu mun kasance a da can muna bauta masa; lalle shi Mai kyautatawa ne, Mai jin qai.”



Capítulo: Suratul Jinn

Verso : 18

وَأَنَّ ٱلۡمَسَٰجِدَ لِلَّهِ فَلَا تَدۡعُواْ مَعَ ٱللَّهِ أَحَدٗا

Kuma lalle masallatai na Allah ne, saboda haka kada ku bauta wa wani tare da Allah



Capítulo: Suratul Jinn

Verso : 20

قُلۡ إِنَّمَآ أَدۡعُواْ رَبِّي وَلَآ أُشۡرِكُ بِهِۦٓ أَحَدٗا

Ka ce: “Lalle ina bauta wa Ubangijina ne kawai, ba kuwa na tara wani da Shi.”