وَإِذَا سَأَلَكَ عِبَادِي عَنِّي فَإِنِّي قَرِيبٌۖ أُجِيبُ دَعۡوَةَ ٱلدَّاعِ إِذَا دَعَانِۖ فَلۡيَسۡتَجِيبُواْ لِي وَلۡيُؤۡمِنُواْ بِي لَعَلَّهُمۡ يَرۡشُدُونَ
Kuma idan bayina sun tambaye ka game da Ni, to Ni kusa Nake (da su), Ina amsa kiran mai kira idan ya kiraye Ni; to su amsa Mini nawa kiran, kuma su yi imani da Ni, don su shiryu
بَلۡ إِيَّاهُ تَدۡعُونَ فَيَكۡشِفُ مَا تَدۡعُونَ إِلَيۡهِ إِن شَآءَ وَتَنسَوۡنَ مَا تُشۡرِكُونَ
Ba haka ba ne, (Allah) Shi kaxai za ku kira, sai Ya yaye abin da kuke roqonsa a kai idan Ya ga dama, kuma za ku manta abin da kuke haxa Allah da shi wajen bauta
قُلۡ مَن يُنَجِّيكُم مِّن ظُلُمَٰتِ ٱلۡبَرِّ وَٱلۡبَحۡرِ تَدۡعُونَهُۥ تَضَرُّعٗا وَخُفۡيَةٗ لَّئِنۡ أَنجَىٰنَا مِنۡ هَٰذِهِۦ لَنَكُونَنَّ مِنَ ٱلشَّـٰكِرِينَ
Ka ce: “Wane ne yake tserar da ku daga cikin duffai na tudu da na kogi, kuna roqon sa a fili da a voye (cewa): “Tabbas, in da zai tserar da mu daga wannan, to lalle za mu kasance cikin masu godiya.”
قُلۡ أَمَرَ رَبِّي بِٱلۡقِسۡطِۖ وَأَقِيمُواْ وُجُوهَكُمۡ عِندَ كُلِّ مَسۡجِدٖ وَٱدۡعُوهُ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَۚ كَمَا بَدَأَكُمۡ تَعُودُونَ
Ka ce: “Ubangijina Ya yi umarni da adalci; kuma ku tsai da fuskokinku (don Allah) a kowace salla, ku kuma roqe Shi kuna masu tsantsanta addini gare Shi. Kamar yadda Ya fari halittarku, haka za ku koma (wurinsa)
ٱدۡعُواْ رَبَّكُمۡ تَضَرُّعٗا وَخُفۡيَةًۚ إِنَّهُۥ لَا يُحِبُّ ٱلۡمُعۡتَدِينَ
Ku roqi Ubangijinku kuna masu qasqantar da kai, kuma a voye. Lalle Shi ba ya son masu qetare iyaka
وَلَا تُفۡسِدُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ بَعۡدَ إِصۡلَٰحِهَا وَٱدۡعُوهُ خَوۡفٗا وَطَمَعًاۚ إِنَّ رَحۡمَتَ ٱللَّهِ قَرِيبٞ مِّنَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Kuma kada ku yi varna a bayan qasa bayan gyara ta, kuma ku bauta masa kuna masu tsoro da kwaxayi. Lalle rahamar Allah a kusa take da masu kyautatawa
وَلِلَّهِ ٱلۡأَسۡمَآءُ ٱلۡحُسۡنَىٰ فَٱدۡعُوهُ بِهَاۖ وَذَرُواْ ٱلَّذِينَ يُلۡحِدُونَ فِيٓ أَسۡمَـٰٓئِهِۦۚ سَيُجۡزَوۡنَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Allah kuma Yana da sunaye mafiya kyau, don haka ku roqe Shi da su; kuma ku rabu da waxanda suke fanxarewa game da sunayensa; da sannu za a yi musu sakamakon abin da suka kasance suna aikatawa
۞هُوَ ٱلَّذِي خَلَقَكُم مِّن نَّفۡسٖ وَٰحِدَةٖ وَجَعَلَ مِنۡهَا زَوۡجَهَا لِيَسۡكُنَ إِلَيۡهَاۖ فَلَمَّا تَغَشَّىٰهَا حَمَلَتۡ حَمۡلًا خَفِيفٗا فَمَرَّتۡ بِهِۦۖ فَلَمَّآ أَثۡقَلَت دَّعَوَا ٱللَّهَ رَبَّهُمَا لَئِنۡ ءَاتَيۡتَنَا صَٰلِحٗا لَّنَكُونَنَّ مِنَ ٱلشَّـٰكِرِينَ
Shi ne Wanda Ya halicce ku daga rai guda xaya, kuma Ya halicci matarsa daga gare shi, don ya sami nutsuwa tare da ita; to yayin da ya kusance ta, sai ta xauki yaron ciki, sai ta ci gaba (da harkokinta) da shi, to yayin da (cikin) ya yi nauyi, sai suka roqi Allah Ubangijinsu cewa: “Lalle idan Ka ba mu xa lafiyayye[1], lalle za mu kasance masu godiya.”
1- Watau lafiyayye kuma nagari.
إِنَّ ٱلَّذِينَ تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ عِبَادٌ أَمۡثَالُكُمۡۖ فَٱدۡعُوهُمۡ فَلۡيَسۡتَجِيبُواْ لَكُمۡ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Lalle waxanda kuke kira ba Allah ba bayi ne kamarku, to ku kirawo su mana, sai su kuma su amsa muku idan kun kasance masu gaskiya ne
وَإِذَا مَسَّ ٱلۡإِنسَٰنَ ٱلضُّرُّ دَعَانَا لِجَنۢبِهِۦٓ أَوۡ قَاعِدًا أَوۡ قَآئِمٗا فَلَمَّا كَشَفۡنَا عَنۡهُ ضُرَّهُۥ مَرَّ كَأَن لَّمۡ يَدۡعُنَآ إِلَىٰ ضُرّٖ مَّسَّهُۥۚ كَذَٰلِكَ زُيِّنَ لِلۡمُسۡرِفِينَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Idan kuma wata cuta ta sami mutum, sai ya roqe Mu, a kishingixe ne ko a zaune ko kuwa a tsaye. To lokacin da Muka yaye masa cutarsa sai ya ci gaba (da halinsa) kamar bai tava roqon Mu game da wata cuta da ta shafe shi ba. Kamar haka ne aka qawata wa mavarnata abin da suka kasance suna aikatawa
هُوَ ٱلَّذِي يُسَيِّرُكُمۡ فِي ٱلۡبَرِّ وَٱلۡبَحۡرِۖ حَتَّىٰٓ إِذَا كُنتُمۡ فِي ٱلۡفُلۡكِ وَجَرَيۡنَ بِهِم بِرِيحٖ طَيِّبَةٖ وَفَرِحُواْ بِهَا جَآءَتۡهَا رِيحٌ عَاصِفٞ وَجَآءَهُمُ ٱلۡمَوۡجُ مِن كُلِّ مَكَانٖ وَظَنُّوٓاْ أَنَّهُمۡ أُحِيطَ بِهِمۡ دَعَوُاْ ٱللَّهَ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ لَئِنۡ أَنجَيۡتَنَا مِنۡ هَٰذِهِۦ لَنَكُونَنَّ مِنَ ٱلشَّـٰكِرِينَ
Shi ne Wanda Yake tafiyar da ku a tudu da cikin ruwa, har lokacin da kuka shiga cikin jiragen ruwa, (jiragen) kuwa suka yi gudu da su tare da iska mai daxi, suka kuma yi farin ciki da su (jiragen) sai kuma wata iska mai qarfi ta zo musu; raqumin ruwa kuma ya zo musu ta kowane wuri, suka kuma tabbatar cewa dai su kam an rutsa da su, sai kuma suka roqi Allah suna masu tsarkake addini gare Shi (suna cewa): “Tabbas idan Ka tserar da mu daga wannan, lalle haqiqa za mu zamo cikin masu godiya.”
وَلَا تَدۡعُ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَنفَعُكَ وَلَا يَضُرُّكَۖ فَإِن فَعَلۡتَ فَإِنَّكَ إِذٗا مِّنَ ٱلظَّـٰلِمِينَ
“Kada kuma ka bauta wa wani ba Allah ba, abin da ba zai amfane ka ba, ba kuma zai cuce ka ba; to idan kuwa ka aikata haka to lalle daga sannan ka zama cikin azzalumai.’”
لَهُۥ دَعۡوَةُ ٱلۡحَقِّۚ وَٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦ لَا يَسۡتَجِيبُونَ لَهُم بِشَيۡءٍ إِلَّا كَبَٰسِطِ كَفَّيۡهِ إِلَى ٱلۡمَآءِ لِيَبۡلُغَ فَاهُ وَمَا هُوَ بِبَٰلِغِهِۦۚ وَمَا دُعَآءُ ٱلۡكَٰفِرِينَ إِلَّا فِي ضَلَٰلٖ
Gare Shi (Shi kaxai) kira na gaske yake; waxanda kuwa suke bauta wa wasu ba Shi ba, to ba sa amsa musu da komai illa tamkar wanda ya shimfixa tafukansa ga ruwa don ya isa bakinsa, ba kuwa zai isa gare shi ba[1]. Addu’ar kafirai kuma ba a komai take ba illa a cikin vata
1- Watau kamar mai shimfixa hannunsa a kan ruwa yana jiran ya taso ya shiga bakinsa yake yin aikin wofi, hakanan mai bautar wanin Allah shi ma yake yin bautar banza da wofi.
وَيَدۡعُ ٱلۡإِنسَٰنُ بِٱلشَّرِّ دُعَآءَهُۥ بِٱلۡخَيۡرِۖ وَكَانَ ٱلۡإِنسَٰنُ عَجُولٗا
Kuma mutum yakan roqi sharri[1] kamar yadda yake roqon alheri; mutum kuwa ya zamanto mai gaggawa ne
1- Watau idan ya yi fushi yakan yi wa kansa ko ‘ya’yansa ko dukiyarsa mummunar addu’a.
قُلِ ٱدۡعُواْ ٱلَّذِينَ زَعَمۡتُم مِّن دُونِهِۦ فَلَا يَمۡلِكُونَ كَشۡفَ ٱلضُّرِّ عَنكُمۡ وَلَا تَحۡوِيلًا
Ka ce (da su): “Ku kirawo waxanda kuka riya (cewa su ne iyayen gijinku) ba Shi ba, to ba su da ikon yaye muku cuta ko juyar da ita.”
أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ يَبۡتَغُونَ إِلَىٰ رَبِّهِمُ ٱلۡوَسِيلَةَ أَيُّهُمۡ أَقۡرَبُ وَيَرۡجُونَ رَحۡمَتَهُۥ وَيَخَافُونَ عَذَابَهُۥٓۚ إِنَّ عَذَابَ رَبِّكَ كَانَ مَحۡذُورٗا
Waxancan da suke bauta wa[1], su ma suna neman hanya ne zuwa ga Ubangijinsu, a cikinsu wa zai fi kusanci? Suna kuma qaunar rahamarsa, kuma suna tsoron azabarsa. Lalle azabar Ubangijinka ta kasance abar tsoro ce
1- Watau kamar mala’iku ko annabawa ko salihan bayi.
قُلِ ٱدۡعُواْ ٱللَّهَ أَوِ ٱدۡعُواْ ٱلرَّحۡمَٰنَۖ أَيّٗا مَّا تَدۡعُواْ فَلَهُ ٱلۡأَسۡمَآءُ ٱلۡحُسۡنَىٰۚ وَلَا تَجۡهَرۡ بِصَلَاتِكَ وَلَا تُخَافِتۡ بِهَا وَٱبۡتَغِ بَيۡنَ ذَٰلِكَ سَبِيلٗا
Ka ce: “Ku kira (sunan) Allah ko ku kira (sunan) Arrahaman; kowanne kuka kira to shi Yana da sunaye ne mafiya kyau.” Kada kuma ka xaga muryarka da (karatun) sallarka, kada kuma ka yi shi a voye, ka nemi tsaka-tsakin wannan
وَرَبَطۡنَا عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ إِذۡ قَامُواْ فَقَالُواْ رَبُّنَا رَبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ لَن نَّدۡعُوَاْ مِن دُونِهِۦٓ إِلَٰهٗاۖ لَّقَدۡ قُلۡنَآ إِذٗا شَطَطًا
Muka kuma xaure zukatansu lokacin da suka tsaya suka ce: “Ubangijinmu Shi ne Ubangijin sammai da qasa; ba za mu bauta wa wani abin bauta ba in ban da Shi; idan muka yi haka kuwa to haqiqa mun faxi qarya
وَيَوۡمَ يَقُولُ نَادُواْ شُرَكَآءِيَ ٱلَّذِينَ زَعَمۡتُمۡ فَدَعَوۡهُمۡ فَلَمۡ يَسۡتَجِيبُواْ لَهُمۡ وَجَعَلۡنَا بَيۡنَهُم مَّوۡبِقٗا
Kuma (ka tuna) ranar da (Allah) zai ce (da kafirai): “Ku kirawo abokan tarayyar nawa waxanda kuka riya (cewa su ne iyayen gijinku)”, to sai suka kirawo su, sai ba su amsa musu ba, Muka kuma sanya mahallaka a tsakaninsu
قَالَ رَبِّ إِنِّي وَهَنَ ٱلۡعَظۡمُ مِنِّي وَٱشۡتَعَلَ ٱلرَّأۡسُ شَيۡبٗا وَلَمۡ أَكُنۢ بِدُعَآئِكَ رَبِّ شَقِيّٗا
Ya ce: “Ya Ubangiji lalle qasusuwana sun yi rauni, kaina kuma ya yi fari fat da furfura, Ubangijina ban kuma zama mai tavewa ba game da roqon Ka
وَأَعۡتَزِلُكُمۡ وَمَا تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَأَدۡعُواْ رَبِّي عَسَىٰٓ أَلَّآ أَكُونَ بِدُعَآءِ رَبِّي شَقِيّٗا
“Zan kuwa qaurace muku ku da abin da kuke bauta wa wanda ba Allah ba, in kuma roqi Ubangijina, na kuma sa tsammanin cewa ba zan zama tavavve ba game da roqon Ubangijina.”
فَٱسۡتَجَبۡنَا لَهُۥ وَوَهَبۡنَا لَهُۥ يَحۡيَىٰ وَأَصۡلَحۡنَا لَهُۥ زَوۡجَهُۥٓۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ يُسَٰرِعُونَ فِي ٱلۡخَيۡرَٰتِ وَيَدۡعُونَنَا رَغَبٗا وَرَهَبٗاۖ وَكَانُواْ لَنَا خَٰشِعِينَ
Sai Muka amsa masa Muka ba shi Yahya, Muka kuma gyara masa (mahaifar) matarsa. Lallai su sun kasance suna gaggawa wajen yin alherai, suna kuma roqon Mu suna masu kwaxayin (rahamarmu) masu kuma tsoron (azabarmu), sun kuma zamanto masu qasqantar da kai gare Mu
يَدۡعُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَضُرُّهُۥ وَمَا لَا يَنفَعُهُۥۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلضَّلَٰلُ ٱلۡبَعِيدُ
Yana bauta wa wanin Allah, abin da ba zai cuce shi ba kuma ba zai amfane shi ba. Wannan kuwa shi ne vata mai nisa
يَدۡعُواْ لَمَن ضَرُّهُۥٓ أَقۡرَبُ مِن نَّفۡعِهِۦۚ لَبِئۡسَ ٱلۡمَوۡلَىٰ وَلَبِئۡسَ ٱلۡعَشِيرُ
Yana bauta wa abin da cutarsa ta fi kusa fiye da amfaninsa. Tabbas mataimaki ya munana, kuma tabbas aboki ya munana
لِّكُلِّ أُمَّةٖ جَعَلۡنَا مَنسَكًا هُمۡ نَاسِكُوهُۖ فَلَا يُنَٰزِعُنَّكَ فِي ٱلۡأَمۡرِۚ وَٱدۡعُ إِلَىٰ رَبِّكَۖ إِنَّكَ لَعَلَىٰ هُدٗى مُّسۡتَقِيمٖ
Kowacce al’umma Mun sanya mata hanyar (shari’a) da za su yi aiki da ita; to lalle kada su yi jayayya da kai game da lamarin (addini). Kuma ka yi kira zuwa ga (addinin) Ubangijinka; lalle kai tabbas kana bisa shiriya madaidaiciya
وَقُل رَّبِّ ٱغۡفِرۡ وَٱرۡحَمۡ وَأَنتَ خَيۡرُ ٱلرَّـٰحِمِينَ
Kuma ka ce: “Ya Ubangijina Ka gafarta (mana) kuma Ka ji qan mu, Kai ne kuwa Fiyayyen masu jin qai.”
وَٱلَّذِينَ يَقُولُونَ رَبَّنَا ٱصۡرِفۡ عَنَّا عَذَابَ جَهَنَّمَۖ إِنَّ عَذَابَهَا كَانَ غَرَامًا
(Su ne) kuma waxanda suke cewa: “Ya Ubangijinmu, Ka kawar mana da azabar Jahannama; lalle azabarta ta kasance halaka ce mai xorewa
إِنَّهَا سَآءَتۡ مُسۡتَقَرّٗا وَمُقَامٗا
“Lalle ita (Jahannama) ta kasance mummunar matabbata kuma mazauna (ga kafirai).”
وَٱلَّذِينَ يَقُولُونَ رَبَّنَا هَبۡ لَنَا مِنۡ أَزۡوَٰجِنَا وَذُرِّيَّـٰتِنَا قُرَّةَ أَعۡيُنٖ وَٱجۡعَلۡنَا لِلۡمُتَّقِينَ إِمَامًا
(Su ne) kuma waxanda suke cewa: “Ya Ubangijinmu, Ka ba mu masu sanyaya mana zukata daga matayenmu da zuri’armu, kuma Ka sanya mu abin koyi ga masu taqawa
قُلۡ مَا يَعۡبَؤُاْ بِكُمۡ رَبِّي لَوۡلَا دُعَآؤُكُمۡۖ فَقَدۡ كَذَّبۡتُمۡ فَسَوۡفَ يَكُونُ لِزَامَۢا
Ka ce: “Ba ruwan Ubangijina da ku in ba don ibadarku ba; to ga shi kun qaryata, to wannan (sakamakonsa) zai zama azaba ce mai xorewa[1].”
1- Watau ba domin bayinsa na gari waxanda suke bauta masa kuma suna roqon sa ba, da ba ruwansa da su domin sun qaryata Manzon Allah ().