يَٰبَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ ٱذۡكُرُواْ نِعۡمَتِيَ ٱلَّتِيٓ أَنۡعَمۡتُ عَلَيۡكُمۡ وَأَوۡفُواْ بِعَهۡدِيٓ أُوفِ بِعَهۡدِكُمۡ وَإِيَّـٰيَ فَٱرۡهَبُونِ
Ya ku ‘ya’yan Isra’ila, ku tuna ni’imata da Na yi muku, kuma ku cika alqawarina zan cika muku alkawarinku, kuma ku tsorace Ni Ni kaxai
وَءَامِنُواْ بِمَآ أَنزَلۡتُ مُصَدِّقٗا لِّمَا مَعَكُمۡ وَلَا تَكُونُوٓاْ أَوَّلَ كَافِرِۭ بِهِۦۖ وَلَا تَشۡتَرُواْ بِـَٔايَٰتِي ثَمَنٗا قَلِيلٗا وَإِيَّـٰيَ فَٱتَّقُونِ
Kuma ku yi imani da abin da Na saukar yana mai gaskata abin da yake tare da ku (na wahayi), kada kuma ku zama farkon (jinsinku) da zai kafirce masa, kuma kada ku sayar da ayoyina da xan kuxi kaxan, kuma ku kiyaye dokokina
وَلَا تَلۡبِسُواْ ٱلۡحَقَّ بِٱلۡبَٰطِلِ وَتَكۡتُمُواْ ٱلۡحَقَّ وَأَنتُمۡ تَعۡلَمُونَ
Kada kuma ku gauraya gaskiya da qarya, kuma ku voye gaskiya, alhalin kuna sane
وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ وَٱرۡكَعُواْ مَعَ ٱلرَّـٰكِعِينَ
Kuma ku tsayar da salla, ku kuma ba da zakka, kuma ku yi ruku’i tare da masu ruku’i
۞أَتَأۡمُرُونَ ٱلنَّاسَ بِٱلۡبِرِّ وَتَنسَوۡنَ أَنفُسَكُمۡ وَأَنتُمۡ تَتۡلُونَ ٱلۡكِتَٰبَۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ
Shin yanzu kwa riqa umartar mutane da ayyukan alheri ku kuma kuna mantawa da kawunanku, alhalin kuna karanta Littafi? Ashe ba za ku hankalta ba?
وَٱسۡتَعِينُواْ بِٱلصَّبۡرِ وَٱلصَّلَوٰةِۚ وَإِنَّهَا لَكَبِيرَةٌ إِلَّا عَلَى ٱلۡخَٰشِعِينَ
Kuma ku nemi agaji ta hanyar haquri da kuma salla, kuma lalle ita (salla) babban abu ne sai dai ga masu qasqantar da kai
ٱلَّذِينَ يَظُنُّونَ أَنَّهُم مُّلَٰقُواْ رَبِّهِمۡ وَأَنَّهُمۡ إِلَيۡهِ رَٰجِعُونَ
Waxanda suka tabbatar da cewa, su masu haxuwa ne da Ubangijinsu, kuma su zuwa gare Shi suke komawa
يَٰبَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ ٱذۡكُرُواْ نِعۡمَتِيَ ٱلَّتِيٓ أَنۡعَمۡتُ عَلَيۡكُمۡ وَأَنِّي فَضَّلۡتُكُمۡ عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ
Ya ku ‘ya’yan Isra’ila ku tuna ni’imata da Na yi muku, kuma Ni Na fifita ku a kan sauran mutanen duniya (na zamaninku)
وَٱتَّقُواْ يَوۡمٗا لَّا تَجۡزِي نَفۡسٌ عَن نَّفۡسٖ شَيۡـٔٗا وَلَا يُقۡبَلُ مِنۡهَا شَفَٰعَةٞ وَلَا يُؤۡخَذُ مِنۡهَا عَدۡلٞ وَلَا هُمۡ يُنصَرُونَ
Kuma ku kiyayi wata rana da babu wani (mai) rai da zai isar wa da wani (mai) rai komai a cikinta; kuma ba za a karvi wani ceto daga gare shi ba, kuma ba za a karvi wata fansa daga gare shi ba, kuma ba za a taimaka musu ba
وَإِذۡ نَجَّيۡنَٰكُم مِّنۡ ءَالِ فِرۡعَوۡنَ يَسُومُونَكُمۡ سُوٓءَ ٱلۡعَذَابِ يُذَبِّحُونَ أَبۡنَآءَكُمۡ وَيَسۡتَحۡيُونَ نِسَآءَكُمۡۚ وَفِي ذَٰلِكُم بَلَآءٞ مِّن رَّبِّكُمۡ عَظِيمٞ
Kuma ku tuna lokacin da Muka kuvutar da ku daga jama’ar Fir’auna waxanda suke xanxana muku mummunar azaba, suna yanka ‘ya’yanku maza, kuma suna qyale ‘ya’yanku mata. A cikin wannan lamari akwai babbar jarraba daga Ubangijinku
وَإِذۡ فَرَقۡنَا بِكُمُ ٱلۡبَحۡرَ فَأَنجَيۡنَٰكُمۡ وَأَغۡرَقۡنَآ ءَالَ فِرۡعَوۡنَ وَأَنتُمۡ تَنظُرُونَ
Kuma ku tuna lokacin da Muka raba muku kogi, sai Muka kuvutar da ku, kuma Muka nutsar da jama’ar Fir’auna, alhalin kuna kallo
وَإِذۡ وَٰعَدۡنَا مُوسَىٰٓ أَرۡبَعِينَ لَيۡلَةٗ ثُمَّ ٱتَّخَذۡتُمُ ٱلۡعِجۡلَ مِنۢ بَعۡدِهِۦ وَأَنتُمۡ ظَٰلِمُونَ
Kuma ku tuna lokacin da Muka yi wa Musa wa’adin (ganawa da shi) na kwana arba’in, sannan ku kuma kuka kama bautar xan maraqi a bayansa, alhalin kuna masu zaluntar kawunanku
ثُمَّ عَفَوۡنَا عَنكُم مِّنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ لَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ
Sannan sai Muka yi muku afuwa bayan haka, don ku yi godiya
وَإِذۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡفُرۡقَانَ لَعَلَّكُمۡ تَهۡتَدُونَ
Kuma ku tuna lokacin da Muka ba wa Musa Littafin (Attaura) da abin da yake rarrabewa (tsakanin gaskiya da qarya) don ku shiriya
وَإِذۡ قَالَ مُوسَىٰ لِقَوۡمِهِۦ يَٰقَوۡمِ إِنَّكُمۡ ظَلَمۡتُمۡ أَنفُسَكُم بِٱتِّخَاذِكُمُ ٱلۡعِجۡلَ فَتُوبُوٓاْ إِلَىٰ بَارِئِكُمۡ فَٱقۡتُلُوٓاْ أَنفُسَكُمۡ ذَٰلِكُمۡ خَيۡرٞ لَّكُمۡ عِندَ بَارِئِكُمۡ فَتَابَ عَلَيۡكُمۡۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلتَّوَّابُ ٱلرَّحِيمُ
Kuma ku tuna lokacin da Musa ya cewa mutanensa: “Ya ku mutanena, lalle ku kun zalunci kawunanku ta hanyar mayar da xan maraqi abin bauta, don haka ku tuba zuwa ga Mahaliccinku, kuma ku kashe kawunanku; wannan shi ne ya fi alheri a gare ku a wajen Mahaliccinku. Lalle shi Mai yawan karvar tuba ne, Mai yawan jin qai.”
وَإِذۡ قُلۡتُمۡ يَٰمُوسَىٰ لَن نُّؤۡمِنَ لَكَ حَتَّىٰ نَرَى ٱللَّهَ جَهۡرَةٗ فَأَخَذَتۡكُمُ ٱلصَّـٰعِقَةُ وَأَنتُمۡ تَنظُرُونَ
Kuma ku tuna lokacin da kuka ce: “Ya Musa ba za mu yi imani da kai ba har sai mun ga Allah a sarari”, sai tsawa ta halaka ku, alhali kuma kuna kallo
ثُمَّ بَعَثۡنَٰكُم مِّنۢ بَعۡدِ مَوۡتِكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ
Sannan sai Muka tashe ku bayan mutuwarku, don ku yi godiya
وَظَلَّلۡنَا عَلَيۡكُمُ ٱلۡغَمَامَ وَأَنزَلۡنَا عَلَيۡكُمُ ٱلۡمَنَّ وَٱلسَّلۡوَىٰۖ كُلُواْ مِن طَيِّبَٰتِ مَا رَزَقۡنَٰكُمۡۚ وَمَا ظَلَمُونَا وَلَٰكِن كَانُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ يَظۡلِمُونَ
Kuma Muka yi muku inuwa da girgije, kuma Muka saukar muku da mannu da (soyayyun) tsuntsayen salwa, ku ci daga daxaxan abin da Muka arzuta ku da shi; kuma ba su zalince Mu ba, sai dai kawunansu kaxai suke zalunta
وَإِذۡ قُلۡنَا ٱدۡخُلُواْ هَٰذِهِ ٱلۡقَرۡيَةَ فَكُلُواْ مِنۡهَا حَيۡثُ شِئۡتُمۡ رَغَدٗا وَٱدۡخُلُواْ ٱلۡبَابَ سُجَّدٗا وَقُولُواْ حِطَّةٞ نَّغۡفِرۡ لَكُمۡ خَطَٰيَٰكُمۡۚ وَسَنَزِيدُ ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Kuma ku tuna lokacin da Muka ce: “Ku shiga wannan alqaryar ku ci daga (kayan marmarinta ta) inda kuka ga dama cikin yalwa, kuma ku shiga qofar garin a duqe, kuma ku ce: “(Allah Ka) kankare mana laifuffukanmu”, za Mu gafarta muku laifuffukanku. Kuma za Mu qara wa masu kyautatawa
فَبَدَّلَ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ قَوۡلًا غَيۡرَ ٱلَّذِي قِيلَ لَهُمۡ فَأَنزَلۡنَا عَلَى ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ رِجۡزٗا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ بِمَا كَانُواْ يَفۡسُقُونَ
Sai waxanda suka yi zalunci suka canza maganar da aka faxa musu, sai Muka saukar da wata azaba daga sama a kan waxanda suka yi zalunci saboda abin da suke aikatawa na fasiqanci
۞وَإِذِ ٱسۡتَسۡقَىٰ مُوسَىٰ لِقَوۡمِهِۦ فَقُلۡنَا ٱضۡرِب بِّعَصَاكَ ٱلۡحَجَرَۖ فَٱنفَجَرَتۡ مِنۡهُ ٱثۡنَتَا عَشۡرَةَ عَيۡنٗاۖ قَدۡ عَلِمَ كُلُّ أُنَاسٖ مَّشۡرَبَهُمۡۖ كُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ مِن رِّزۡقِ ٱللَّهِ وَلَا تَعۡثَوۡاْ فِي ٱلۡأَرۡضِ مُفۡسِدِينَ
Kuma ka tuna lokacin da Musa ya roqa wa mutanensa ruwan sha, sai Muka ce: “Ka bugi dutse da sandarka”, sai idanuwan marmaron ruwa goma sha biyu suka vuvvugo daga cikinsa. Haqiqa kowaxanne mutane sun san mashayarsu. (Muka ce): “Ku ci kuma ku sha daga arzikin Allah, kuma kada ku yaxa varna a bayan qasa
وَإِذۡ قُلۡتُمۡ يَٰمُوسَىٰ لَن نَّصۡبِرَ عَلَىٰ طَعَامٖ وَٰحِدٖ فَٱدۡعُ لَنَا رَبَّكَ يُخۡرِجۡ لَنَا مِمَّا تُنۢبِتُ ٱلۡأَرۡضُ مِنۢ بَقۡلِهَا وَقِثَّآئِهَا وَفُومِهَا وَعَدَسِهَا وَبَصَلِهَاۖ قَالَ أَتَسۡتَبۡدِلُونَ ٱلَّذِي هُوَ أَدۡنَىٰ بِٱلَّذِي هُوَ خَيۡرٌۚ ٱهۡبِطُواْ مِصۡرٗا فَإِنَّ لَكُم مَّا سَأَلۡتُمۡۗ وَضُرِبَتۡ عَلَيۡهِمُ ٱلذِّلَّةُ وَٱلۡمَسۡكَنَةُ وَبَآءُو بِغَضَبٖ مِّنَ ٱللَّهِۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ كَانُواْ يَكۡفُرُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَيَقۡتُلُونَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّۚ ذَٰلِكَ بِمَا عَصَواْ وَّكَانُواْ يَعۡتَدُونَ
Kuma ku tuna lokacin da kuka ce: “Ya Musa, ba za mu iya haquri a kan abinci iri xaya ba, don haka ka roqa mana Ubangijinka Ya fitar mana (wani abincin) daga abin da qasa take tsirarwa, daga mabunqusanta da gurjinta da alkamarta da wakenta da albasarta.” Sai ya ce, “Yanzu kwa nemi musanya qasqantaccen abu da wanda yake shi ne mafifici? To ku sauka kowane gari, domin za ku samu abin da kuka roqa (a cikinsa).” Don haka sai aka sanya musu qasqanci da talauci, kuma suka koma da fushin Allah. Hakan ya faru gare su ne saboda sun kasance suna kafirce wa ayoyin Allah, kuma suna kashe annabawa ba tare da wani haqqi ba. Hakan ya faru saboda savon da suka yi da kuma ta’addancin da suka riqa yi
إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَٱلَّذِينَ هَادُواْ وَٱلنَّصَٰرَىٰ وَٱلصَّـٰبِـِٔينَ مَنۡ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا فَلَهُمۡ أَجۡرُهُمۡ عِندَ رَبِّهِمۡ وَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ
Lalle waxanda suka yi imani da Yahudawa da Nasara da Sabi’awa[1], duk wanda ya yi imani da Allah da ranar Lahira kuma ya yi aiki na qwarai, to suna da ladansu a wurin Ubangijinsu, kuma babu tsoro a tare da su, kuma ba za su yi baqin ciki ba
1- Waxanda suka yi imani, su ne al’ummar Annabi Muhammadu (). Yahudawa, ana nufin mabiya Annabi Musa () kafin a shafe addininsa, ko kafin su gurvata shi. Nasara, ana nufin mabiya Annabi Isa () kafin a shafe addininsa ko kafin su gurvata shi. Sabi’awa, wasu qungiyoyi ne, daga cikinsu akwai masu aqidar kaxaita Allah da haramta duk wata alfasha da zalunci, duk da kasancewarsu ba bisa wani addini suke ba, to amma ba sa aikata shirka.
وَإِذۡ أَخَذۡنَا مِيثَٰقَكُمۡ وَرَفَعۡنَا فَوۡقَكُمُ ٱلطُّورَ خُذُواْ مَآ ءَاتَيۡنَٰكُم بِقُوَّةٖ وَٱذۡكُرُواْ مَا فِيهِ لَعَلَّكُمۡ تَتَّقُونَ
Kuma ku tuna lokacin da Muka xauki alqawari mai qarfi daga gare ku, kuma Muka xaga dusten Xuri a kanku (Muka ce): “Ku karvi abin da Muka ba ku da qarfi (Attaura), kuma ku tuna abin da yake cikinsa, don ku yi taqawa.”
ثُمَّ تَوَلَّيۡتُم مِّنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَۖ فَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَرَحۡمَتُهُۥ لَكُنتُم مِّنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ
Sannan bayan haka sai kuka juya da baya, to ba domin falalar Allah da rahamarsa a gare ku ba, lalle da kun kasance daga cikin asararru
وَلَقَدۡ عَلِمۡتُمُ ٱلَّذِينَ ٱعۡتَدَوۡاْ مِنكُمۡ فِي ٱلسَّبۡتِ فَقُلۡنَا لَهُمۡ كُونُواْ قِرَدَةً خَٰسِـِٔينَ
Kuma haqiqa kun san waxanda suka yi shisshigi daga cikinku game da ranar Assabar, sai Muka ce da su: “Ku zama birrai kuna qasqantattu.”
فَجَعَلۡنَٰهَا نَكَٰلٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيۡهَا وَمَا خَلۡفَهَا وَمَوۡعِظَةٗ لِّلۡمُتَّقِينَ
Sai Muka sanya ta (wannan uqubar) ta zama izina ga (al’ummomin) da suke zamanin faruwarta da kuma (garuruwan) da suke daura da su, kuma don ta zama wa’azi ga masu taqawa
وَإِذۡ قَالَ مُوسَىٰ لِقَوۡمِهِۦٓ إِنَّ ٱللَّهَ يَأۡمُرُكُمۡ أَن تَذۡبَحُواْ بَقَرَةٗۖ قَالُوٓاْ أَتَتَّخِذُنَا هُزُوٗاۖ قَالَ أَعُوذُ بِٱللَّهِ أَنۡ أَكُونَ مِنَ ٱلۡجَٰهِلِينَ
Kuma ku tuna lokacin da Musa ya ce wa mutanensa: “Allah Yana umartar ku da ku yanka saniya”, sai suka ce: “Yanzu ka riqa yi mana izgili?” Sai ya ce: “Ina neman Allah Ya kiyaye ni da in zama cikin jahilai!”
قَالُواْ ٱدۡعُ لَنَا رَبَّكَ يُبَيِّن لَّنَا مَا هِيَۚ قَالَ إِنَّهُۥ يَقُولُ إِنَّهَا بَقَرَةٞ لَّا فَارِضٞ وَلَا بِكۡرٌ عَوَانُۢ بَيۡنَ ذَٰلِكَۖ فَٱفۡعَلُواْ مَا تُؤۡمَرُونَ
Sai suka ce: “Ka roqa mana Ubangijinka Ya yi mana bayanin yaya take?” Sai ya ce: “Lalle Shi Yana cewa, lalle ita saniya ce, ba tsohuwa ba kuma ba budurwa ba, tana tsakatsakin haka.” Don haka ku aikata abin da ake umartar ku
قَالُواْ ٱدۡعُ لَنَا رَبَّكَ يُبَيِّن لَّنَا مَا لَوۡنُهَاۚ قَالَ إِنَّهُۥ يَقُولُ إِنَّهَا بَقَرَةٞ صَفۡرَآءُ فَاقِعٞ لَّوۡنُهَا تَسُرُّ ٱلنَّـٰظِرِينَ
Sai suka ce: “Ka roqa mana Ubangijinka Ya bayyana mana mene ne launinta?” Sai ya ce, “Lalle Shi Yana cewa, lalle ita saniya ce mai launin fatsi-fatsi mai tsananin cizawa, tana faranta wa masu kallon ta rai.”