وَإِذۡ قُلۡنَا لِلۡمَلَـٰٓئِكَةِ ٱسۡجُدُواْ لِأٓدَمَ فَسَجَدُوٓاْ إِلَّآ إِبۡلِيسَ أَبَىٰ وَٱسۡتَكۡبَرَ وَكَانَ مِنَ ٱلۡكَٰفِرِينَ
Kuma ka tuna lokacin da Muka ce wa mala’iku: “Ku yi sujjada ga Adamu.” Sai duk suka yi sujjada[1], in ban da Iblis, sai shi ya qi, ya kuma yi girman kai, kuma ya tabbata cikin kafirai
1- Mala’iku sun yi wa Adamu () sujjada ne don biyayya ga umarnin Allah. Ba ya halatta a Musulunci wani ya yi wa wani sujjada ba Allah ba.
وَجَعَلُواْ لِلَّهِ شُرَكَآءَ ٱلۡجِنَّ وَخَلَقَهُمۡۖ وَخَرَقُواْ لَهُۥ بَنِينَ وَبَنَٰتِۭ بِغَيۡرِ عِلۡمٖۚ سُبۡحَٰنَهُۥ وَتَعَٰلَىٰ عَمَّا يَصِفُونَ
Kuma sun sanya wa Allah aljannu a matsayin abokanan tarayya, alhali kuwa Shi ya halicce su; kuma suka qago masa ‘ya’ya maza da mata, ba tare da wani ilimi ba. Tsarki ya tabbata a gare Shi, kuma Ya xaukaka daga irin abin da suke siffanta (Shi da shi)
وَكَذَٰلِكَ جَعَلۡنَا لِكُلِّ نَبِيٍّ عَدُوّٗا شَيَٰطِينَ ٱلۡإِنسِ وَٱلۡجِنِّ يُوحِي بَعۡضُهُمۡ إِلَىٰ بَعۡضٖ زُخۡرُفَ ٱلۡقَوۡلِ غُرُورٗاۚ وَلَوۡ شَآءَ رَبُّكَ مَا فَعَلُوهُۖ فَذَرۡهُمۡ وَمَا يَفۡتَرُونَ
Kuma kamar haka ne Muka sanya wa kowane annabi maqiya daga shaixanun mutane da aljannu, sashinsu yana kimsa wa wani sashi qayataccen zance, don ruxi. Kuma da Ubangijinka Ya ga dama da ba su aikata haka ba; don haka ka qyale su da irin abin da suke qagowa
وَيَوۡمَ يَحۡشُرُهُمۡ جَمِيعٗا يَٰمَعۡشَرَ ٱلۡجِنِّ قَدِ ٱسۡتَكۡثَرۡتُم مِّنَ ٱلۡإِنسِۖ وَقَالَ أَوۡلِيَآؤُهُم مِّنَ ٱلۡإِنسِ رَبَّنَا ٱسۡتَمۡتَعَ بَعۡضُنَا بِبَعۡضٖ وَبَلَغۡنَآ أَجَلَنَا ٱلَّذِيٓ أَجَّلۡتَ لَنَاۚ قَالَ ٱلنَّارُ مَثۡوَىٰكُمۡ خَٰلِدِينَ فِيهَآ إِلَّا مَا شَآءَ ٱللَّهُۚ إِنَّ رَبَّكَ حَكِيمٌ عَلِيمٞ
Kuma (ka tuna) ranar da zai tara su gaba xaya (Ya ce): “Ya ku jama’ar aljannu, haqiqa kun samu mabiya da yawa daga cikin mutane.” Sai majivinta lamarinsu cikin mutane su ce: “Ya Ubangijinmu; mun dai daxaxa wa junanmu kuma mun kawo qarshen lokacin da Ka yanka mana.” Sai Ya ce: “Wuta ita ce makomarku, za ku dawwama a cikinta, sai dai abin da Allah Ya ga dama.” Lalle Ubangijinka Mai hikima ne, Mai yawan sani
وَكَذَٰلِكَ نُوَلِّي بَعۡضَ ٱلظَّـٰلِمِينَ بَعۡضَۢا بِمَا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ
Kuma kamar haka ne Muke xora wani sashi na azzalumai a kan wani sashi, saboda abin da suka kasance suna aikatawa
يَٰمَعۡشَرَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِ أَلَمۡ يَأۡتِكُمۡ رُسُلٞ مِّنكُمۡ يَقُصُّونَ عَلَيۡكُمۡ ءَايَٰتِي وَيُنذِرُونَكُمۡ لِقَآءَ يَوۡمِكُمۡ هَٰذَاۚ قَالُواْ شَهِدۡنَا عَلَىٰٓ أَنفُسِنَاۖ وَغَرَّتۡهُمُ ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا وَشَهِدُواْ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمۡ أَنَّهُمۡ كَانُواْ كَٰفِرِينَ
Ya ku jama’ar aljannu da mutane, shin manzanni daga cikinku ba su zo muku ba, suna karanta muku ayoyina, kuma suna gargaxin ku game da saduwarku da wannan yini?” Sai su ce: “Mun ba da shaida a kan kawunanmu;” rayuwar duniya kuma ta ruxe su, kuma suka yi wa kansu shaidar cewa lalle su sun kasance kafirai
قَالَ ٱدۡخُلُواْ فِيٓ أُمَمٖ قَدۡ خَلَتۡ مِن قَبۡلِكُم مِّنَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِ فِي ٱلنَّارِۖ كُلَّمَا دَخَلَتۡ أُمَّةٞ لَّعَنَتۡ أُخۡتَهَاۖ حَتَّىٰٓ إِذَا ٱدَّارَكُواْ فِيهَا جَمِيعٗا قَالَتۡ أُخۡرَىٰهُمۡ لِأُولَىٰهُمۡ رَبَّنَا هَـٰٓؤُلَآءِ أَضَلُّونَا فَـَٔاتِهِمۡ عَذَابٗا ضِعۡفٗا مِّنَ ٱلنَّارِۖ قَالَ لِكُلّٖ ضِعۡفٞ وَلَٰكِن لَّا تَعۡلَمُونَ
Sai Ya ce: “Ku shiga cikin jerin al’ummomin da suka shuxe kafinku na aljannu da mutane a cikin wuta.” Ko da yaushe wata al’umma ta shiga (wutar) sai ta la’anci ‘yar’uwarta; har sai lokacin da suka haxu a cikinta gaba xaya, sai na qarshensu su ce wa na farkonsu: “Ya Ubangijinmu, waxannan ne suka vatar da mu, don haka Ka ninka musu azabar wuta.” Sai Ya ce: “Kowanne yana da ninki, sai dai ku ba ku sani ba ne.”
وَلَقَدۡ ذَرَأۡنَا لِجَهَنَّمَ كَثِيرٗا مِّنَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِۖ لَهُمۡ قُلُوبٞ لَّا يَفۡقَهُونَ بِهَا وَلَهُمۡ أَعۡيُنٞ لَّا يُبۡصِرُونَ بِهَا وَلَهُمۡ ءَاذَانٞ لَّا يَسۡمَعُونَ بِهَآۚ أُوْلَـٰٓئِكَ كَٱلۡأَنۡعَٰمِ بَلۡ هُمۡ أَضَلُّۚ أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡغَٰفِلُونَ
Kuma lalle haqiqa Mun halitta wa Jahannama da yawa daga cikin aljannu da mutane; ga su da zukata da ba sa hankalta da su, ga kuma idanu da ba sa kallo da su, ga kunnuwa da ba sa sauraro da su. Waxannan kamar dabbobi suke; a’a, sun ma fi (dabbobi) vacewa. Waxannan su ne gafalallu
إِلَّا مَن رَّحِمَ رَبُّكَۚ وَلِذَٰلِكَ خَلَقَهُمۡۗ وَتَمَّتۡ كَلِمَةُ رَبِّكَ لَأَمۡلَأَنَّ جَهَنَّمَ مِنَ ٱلۡجِنَّةِ وَٱلنَّاسِ أَجۡمَعِينَ
Sai wanda Ubangijinka Ya yi wa rahama. A kan haka kuwa Ya halicce su; kuma Kalmar Ubangijinka ta tabbata (cewa): Lalle zan cika Jahannama da aljannu da mutane baki xaya
وَحَفِظۡنَٰهَا مِن كُلِّ شَيۡطَٰنٖ رَّجِيمٍ
Kuma Muka kiyaye ta daga duk wani shaixani la’ananne
إِلَّا مَنِ ٱسۡتَرَقَ ٱلسَّمۡعَ فَأَتۡبَعَهُۥ شِهَابٞ مُّبِينٞ
Sai dai wanda ya yi satar sauraro, sannan sai tauraro mai harshen wuta ya biyo shi
وَٱلۡجَآنَّ خَلَقۡنَٰهُ مِن قَبۡلُ مِن نَّارِ ٱلسَّمُومِ
Aljani kuwa Mun halicce shi ne gabanin (halittar mutum) daga wuta mai tsananin zafi
قُل لَّئِنِ ٱجۡتَمَعَتِ ٱلۡإِنسُ وَٱلۡجِنُّ عَلَىٰٓ أَن يَأۡتُواْ بِمِثۡلِ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانِ لَا يَأۡتُونَ بِمِثۡلِهِۦ وَلَوۡ كَانَ بَعۡضُهُمۡ لِبَعۡضٖ ظَهِيرٗا
Ka ce da su: “Lalle da mutane da aljannu sun haxu kan su kawo irin wannan Alqur’anin, to ba za su zo da irinsa ba, ko da kuwa wasu sun zamanto suna taimaka wa wasu.”
وَإِذۡ قُلۡنَا لِلۡمَلَـٰٓئِكَةِ ٱسۡجُدُواْ لِأٓدَمَ فَسَجَدُوٓاْ إِلَّآ إِبۡلِيسَ كَانَ مِنَ ٱلۡجِنِّ فَفَسَقَ عَنۡ أَمۡرِ رَبِّهِۦٓۗ أَفَتَتَّخِذُونَهُۥ وَذُرِّيَّتَهُۥٓ أَوۡلِيَآءَ مِن دُونِي وَهُمۡ لَكُمۡ عَدُوُّۢۚ بِئۡسَ لِلظَّـٰلِمِينَ بَدَلٗا
Kuma ka tuna lokacin da Muka ce da mala’iku: “Ku yi sujjada ga Adamu”, sai suka yi sujjadar in ban da Iblis, ya kasance kuwa daga cikin aljannu, sai ya sava wa umarnin Ubangijinsa. Yanzu kwa riqe shi shi da zurriyarsa masoya ba Ni ba, alhali kuwa su maqiyanku ne? Wannan canji na azzalumai ya munana
وَمِنَ ٱلشَّيَٰطِينِ مَن يَغُوصُونَ لَهُۥ وَيَعۡمَلُونَ عَمَلٗا دُونَ ذَٰلِكَۖ وَكُنَّا لَهُمۡ حَٰفِظِينَ
Akwai kuma wasu aljannu da suke nutso don fito masa (da lu’u-lu’u) suna kuma yin wani aikin ban da wannan (kamar gine-gine); Mun zamanto kuma Masu kula da su))
وَحُشِرَ لِسُلَيۡمَٰنَ جُنُودُهُۥ مِنَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِ وَٱلطَّيۡرِ فَهُمۡ يُوزَعُونَ
Aka kuma tattara wa Sulaimanu rundunoninsa na aljannu da mutane da kuma tsuntsaye, sai aka riqa turo su sahu-sahu
قَالَ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلۡمَلَؤُاْ أَيُّكُمۡ يَأۡتِينِي بِعَرۡشِهَا قَبۡلَ أَن يَأۡتُونِي مُسۡلِمِينَ
Sai (Sulaimanu) ya ce: “Ya ku manyan fada, wane ne daga cikinku zai zo min da gadon mulkinta tun kafin su zo min suna masu miqa wuya?”
قَالَ عِفۡرِيتٞ مِّنَ ٱلۡجِنِّ أَنَا۠ ءَاتِيكَ بِهِۦ قَبۡلَ أَن تَقُومَ مِن مَّقَامِكَۖ وَإِنِّي عَلَيۡهِ لَقَوِيٌّ أَمِينٞ
Sai wani ifritu[1] daga cikin aljannu ya ce: “Ni zan zo maka da shi kafin ka tashi daga majalisarka; lalle ni kuma mai qarfi ne amintacce game da (kawo) shi.”
1- Watau wani qaqqarfan aljani.
قَالَ ٱلَّذِي عِندَهُۥ عِلۡمٞ مِّنَ ٱلۡكِتَٰبِ أَنَا۠ ءَاتِيكَ بِهِۦ قَبۡلَ أَن يَرۡتَدَّ إِلَيۡكَ طَرۡفُكَۚ فَلَمَّا رَءَاهُ مُسۡتَقِرًّا عِندَهُۥ قَالَ هَٰذَا مِن فَضۡلِ رَبِّي لِيَبۡلُوَنِيٓ ءَأَشۡكُرُ أَمۡ أَكۡفُرُۖ وَمَن شَكَرَ فَإِنَّمَا يَشۡكُرُ لِنَفۡسِهِۦۖ وَمَن كَفَرَ فَإِنَّ رَبِّي غَنِيّٞ كَرِيمٞ
Sai wani (mutum) wanda yake da ilimin Littafi (na Attaura) ya ce: “Ni zan kawo maka shi kafin ka qifta idonka!” To lokacin da (Sulaimanu) ya gan shi ga shi nan a gabansa sai ya ce: “Wannan yana daga falalar Ubangijina don Ya jarraba ni (Ya gani) shin zan gode ne ko zan butulce; to duk wanda ya gode kansa ya yi wa; wanda kuwa ya butulce, to lalle Ubangijina Mawadaci ne, Mai karamci.”
وَلِسُلَيۡمَٰنَ ٱلرِّيحَ غُدُوُّهَا شَهۡرٞ وَرَوَاحُهَا شَهۡرٞۖ وَأَسَلۡنَا لَهُۥ عَيۡنَ ٱلۡقِطۡرِۖ وَمِنَ ٱلۡجِنِّ مَن يَعۡمَلُ بَيۡنَ يَدَيۡهِ بِإِذۡنِ رَبِّهِۦۖ وَمَن يَزِغۡ مِنۡهُمۡ عَنۡ أَمۡرِنَا نُذِقۡهُ مِنۡ عَذَابِ ٱلسَّعِيرِ
Kuma (Muka hore wa) Sulaimanu iska, tafiyarta ta safe wata guda ce, ta yamma ma kuma wata guda ce; Muka kuma vuvvugo masa da narkakkiyar tagulla tana gudana. Daga aljannu kuma akwai masu aiki a wajensa da umarnin Ubangijinsa; wanda kuwa ya kauce wa umarninmu daga cikinsu, to za Mu xanxana masa azabar wutar Sa’ira
يَعۡمَلُونَ لَهُۥ مَا يَشَآءُ مِن مَّحَٰرِيبَ وَتَمَٰثِيلَ وَجِفَانٖ كَٱلۡجَوَابِ وَقُدُورٖ رَّاسِيَٰتٍۚ ٱعۡمَلُوٓاْ ءَالَ دَاوُۥدَ شُكۡرٗاۚ وَقَلِيلٞ مِّنۡ عِبَادِيَ ٱلشَّكُورُ
Suna aikata masa abubuwan da yake bukata na manya-manyan gine-gine[1] da mutum-mutumi[2] da akusa manya-manya kamar tafkuna da kafaffun tukwane. Ya ku iyalin Dawuda, ku yi aikin (xa’a) domin godiya. Masu godiya daga bayina kuwa kaxan ne
1- Watau wuraren ibada.
2- A wancan lokacin ba a haramta yin su ba. Sai bayan zuwan Annabi () ne ya haramta suranta su ko gina su.
فَلَمَّا قَضَيۡنَا عَلَيۡهِ ٱلۡمَوۡتَ مَا دَلَّهُمۡ عَلَىٰ مَوۡتِهِۦٓ إِلَّا دَآبَّةُ ٱلۡأَرۡضِ تَأۡكُلُ مِنسَأَتَهُۥۖ فَلَمَّا خَرَّ تَبَيَّنَتِ ٱلۡجِنُّ أَن لَّوۡ كَانُواْ يَعۡلَمُونَ ٱلۡغَيۡبَ مَا لَبِثُواْ فِي ٱلۡعَذَابِ ٱلۡمُهِينِ
Sannan lokacin da Muka qaddara masa mutuwa ba abin da ya nuna musu mutuwarsa sai gara da ta riqa cin sandarsa[1]; to lokacin da ya faxi sai aljannu suka gane cewa da sun san gaibu da ba su zauna cikin azabar wulaqanci ba
1- Sandarsa da yake tsaye a kanta.
قَالُواْ سُبۡحَٰنَكَ أَنتَ وَلِيُّنَا مِن دُونِهِمۖ بَلۡ كَانُواْ يَعۡبُدُونَ ٱلۡجِنَّۖ أَكۡثَرُهُم بِهِم مُّؤۡمِنُونَ
Suka ce: “Tsarki ya tabbata a gare Ka, Kai ne Majivincinmu ba su ba.” Ba haka ba ne, sun kasance suna bauta wa aljannu ne; mafiya yawansu masu yin imani da su ne
إِنَّا زَيَّنَّا ٱلسَّمَآءَ ٱلدُّنۡيَا بِزِينَةٍ ٱلۡكَوَاكِبِ
Lalle Mun qawata sama ta kusa da ado na taurari
وَحِفۡظٗا مِّن كُلِّ شَيۡطَٰنٖ مَّارِدٖ
Da kuma tsaro daga dukkan wani shaixan mai tsaurin kai
لَّا يَسَّمَّعُونَ إِلَى ٱلۡمَلَإِ ٱلۡأَعۡلَىٰ وَيُقۡذَفُونَ مِن كُلِّ جَانِبٖ
Ba kuma za su iya jiyowa ba (daga asirin) mala’iku na sama, sai a yi ta jifan su ta kowane vangare
دُحُورٗاۖ وَلَهُمۡ عَذَابٞ وَاصِبٌ
Don kora; suna kuma da wata azaba dawwamamma
إِلَّا مَنۡ خَطِفَ ٱلۡخَطۡفَةَ فَأَتۡبَعَهُۥ شِهَابٞ ثَاقِبٞ
Sai dai wanda ya yi fautowar jin, to sai wani tauraro mai haske da quna ya biyo shi
۞وَقَيَّضۡنَا لَهُمۡ قُرَنَآءَ فَزَيَّنُواْ لَهُم مَّا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡ وَحَقَّ عَلَيۡهِمُ ٱلۡقَوۡلُ فِيٓ أُمَمٖ قَدۡ خَلَتۡ مِن قَبۡلِهِم مِّنَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِۖ إِنَّهُمۡ كَانُواْ خَٰسِرِينَ
Muka kuma haxa su da abokai (shaixanu), sai suka qawata musu abin da yake gabansu (na duniya) da abin da yake bayansu (na musun alqiyama), sai kalmar (azaba) ta tabbata a kansu (na zamantowa) cikin al’ummun da suka gabace su na aljannu da mutane; lalle su, sun kasance hasararru
وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ رَبَّنَآ أَرِنَا ٱلَّذَيۡنِ أَضَلَّانَا مِنَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِ نَجۡعَلۡهُمَا تَحۡتَ أَقۡدَامِنَا لِيَكُونَا مِنَ ٱلۡأَسۡفَلِينَ
Waxanda kuma suka kafirta suka ce: “Ya Ubangijinmu, Ka nuna mana waxanda suka vatar da mu daga aljannu da mutane, mu sanya su a qarqashin dugaduganmu don su zamanto cikin na can qasan qasa.”