Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 61

وَإِذۡ قُلۡتُمۡ يَٰمُوسَىٰ لَن نَّصۡبِرَ عَلَىٰ طَعَامٖ وَٰحِدٖ فَٱدۡعُ لَنَا رَبَّكَ يُخۡرِجۡ لَنَا مِمَّا تُنۢبِتُ ٱلۡأَرۡضُ مِنۢ بَقۡلِهَا وَقِثَّآئِهَا وَفُومِهَا وَعَدَسِهَا وَبَصَلِهَاۖ قَالَ أَتَسۡتَبۡدِلُونَ ٱلَّذِي هُوَ أَدۡنَىٰ بِٱلَّذِي هُوَ خَيۡرٌۚ ٱهۡبِطُواْ مِصۡرٗا فَإِنَّ لَكُم مَّا سَأَلۡتُمۡۗ وَضُرِبَتۡ عَلَيۡهِمُ ٱلذِّلَّةُ وَٱلۡمَسۡكَنَةُ وَبَآءُو بِغَضَبٖ مِّنَ ٱللَّهِۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ كَانُواْ يَكۡفُرُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَيَقۡتُلُونَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّۚ ذَٰلِكَ بِمَا عَصَواْ وَّكَانُواْ يَعۡتَدُونَ

Kuma ku tuna lokacin da kuka ce: “Ya Musa, ba za mu iya haquri a kan abinci iri xaya ba, don haka ka roqa mana Ubangijinka Ya fitar mana (wani abincin) daga abin da qasa take tsirarwa, daga mabunqusanta da gurjinta da alkamarta da wakenta da albasarta.” Sai ya ce, “Yanzu kwa nemi musanya qasqantaccen abu da wanda yake shi ne mafifici? To ku sauka kowane gari, domin za ku samu abin da kuka roqa (a cikinsa).” Don haka sai aka sanya musu qasqanci da talauci, kuma suka koma da fushin Allah. Hakan ya faru gare su ne saboda sun kasance suna kafirce wa ayoyin Allah, kuma suna kashe annabawa ba tare da wani haqqi ba. Hakan ya faru saboda savon da suka yi da kuma ta’addancin da suka riqa yi



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 178

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ كُتِبَ عَلَيۡكُمُ ٱلۡقِصَاصُ فِي ٱلۡقَتۡلَىۖ ٱلۡحُرُّ بِٱلۡحُرِّ وَٱلۡعَبۡدُ بِٱلۡعَبۡدِ وَٱلۡأُنثَىٰ بِٱلۡأُنثَىٰۚ فَمَنۡ عُفِيَ لَهُۥ مِنۡ أَخِيهِ شَيۡءٞ فَٱتِّبَاعُۢ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَأَدَآءٌ إِلَيۡهِ بِإِحۡسَٰنٖۗ ذَٰلِكَ تَخۡفِيفٞ مِّن رَّبِّكُمۡ وَرَحۡمَةٞۗ فَمَنِ ٱعۡتَدَىٰ بَعۡدَ ذَٰلِكَ فَلَهُۥ عَذَابٌ أَلِيمٞ

Ya ku waxanda suka yi imani, an wajabta muku qisasi dangane da waxanda aka kashe; xa da xa, bawa da bawa, mace da mace[1]. To duk wanda aka yafe masa qisasin xan uwansa, to sai ya bibiye shi ta hanyar da ta dace, shi kuma ya biya diyyar ta hanyar kyautatawa. Wannan (abin da aka ambata), sauqi ne da rahama daga wajen Ubangijinku. Don haka duk wanda ya qetare iyaka bayan haka, to yana da azaba mai raxaxi


1- Haka hukuncin yake yayin da namiji xa ya kashe ‘ya mace, ko mace ta kashe xa namiji. Amma idan magadan wanda aka kashe suka yafe, to babu zancen qisasi, sai a biya diyya kawai.


Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 191

وَٱقۡتُلُوهُمۡ حَيۡثُ ثَقِفۡتُمُوهُمۡ وَأَخۡرِجُوهُم مِّنۡ حَيۡثُ أَخۡرَجُوكُمۡۚ وَٱلۡفِتۡنَةُ أَشَدُّ مِنَ ٱلۡقَتۡلِۚ وَلَا تُقَٰتِلُوهُمۡ عِندَ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ حَتَّىٰ يُقَٰتِلُوكُمۡ فِيهِۖ فَإِن قَٰتَلُوكُمۡ فَٱقۡتُلُوهُمۡۗ كَذَٰلِكَ جَزَآءُ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Kuma ku yaqe su duk inda kuka same su, kuma ku fitar da su ta inda suka fitar da ku; kuma fitina (ta kafirci) ita ce mafi tsanani fiye da kisa, kuma kada ku yaqe su a wurin Masallaci mai alfarma, har sai idan sun yaqe ku a cikinsa, idan har suka yaqe ku, to ku ma ku yaqe su. Kamar haka ne sakamakon kafirai yake



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 217

يَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلشَّهۡرِ ٱلۡحَرَامِ قِتَالٖ فِيهِۖ قُلۡ قِتَالٞ فِيهِ كَبِيرٞۚ وَصَدٌّ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ وَكُفۡرُۢ بِهِۦ وَٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ وَإِخۡرَاجُ أَهۡلِهِۦ مِنۡهُ أَكۡبَرُ عِندَ ٱللَّهِۚ وَٱلۡفِتۡنَةُ أَكۡبَرُ مِنَ ٱلۡقَتۡلِۗ وَلَا يَزَالُونَ يُقَٰتِلُونَكُمۡ حَتَّىٰ يَرُدُّوكُمۡ عَن دِينِكُمۡ إِنِ ٱسۡتَطَٰعُواْۚ وَمَن يَرۡتَدِدۡ مِنكُمۡ عَن دِينِهِۦ فَيَمُتۡ وَهُوَ كَافِرٞ فَأُوْلَـٰٓئِكَ حَبِطَتۡ أَعۡمَٰلُهُمۡ فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِۖ وَأُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ

Suna tambayar ka game da wata mai alfarma, yin yaqi a cikinsa. Ka ce: “Yaqi a cikinsa, babban laifi ne, amma hana (mutane) bin tafarkin Allah da kafirce masa da kuma (hana mutane shiga) Masallaci mai alfarma da fitar da mutanensa daga gare shi, su ne mafi girman laifi a wajen Allah. Kuma (laifin) fitina ya fi na kisa girma.”[1] Kuma (kafirai) ba za su gushe ba suna yaqar ku, har sai sun raba ku da addininku, idan da za su sami dama. Kuma duk wanda ya yi ridda daga cikinku, ya bar addininsa, kuma ya mutu yana kafiri, to waxannan ayyukansu sun lalace a duniya da lahira, kuma waxannan su ne ma’abota wuta, suna masu dawwama a cikinta


1- Wannan ayar ta sauka ne bayan da wata runduna ta Musulmi suka kashe wani kafiri mai suna Ibnul Hadhrami a watan Rajab ba su sani ba. Sai kafirai suka riqa aibata su da haka, sai Allah ya saukar da wannan ayar.


Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 21

إِنَّ ٱلَّذِينَ يَكۡفُرُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَيَقۡتُلُونَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ بِغَيۡرِ حَقّٖ وَيَقۡتُلُونَ ٱلَّذِينَ يَأۡمُرُونَ بِٱلۡقِسۡطِ مِنَ ٱلنَّاسِ فَبَشِّرۡهُم بِعَذَابٍ أَلِيمٍ

Lalle waxanda suke kafirce wa ayoyin Allah, kuma suke kashe annabawa ba tare da wani haqqi ba, kuma suke kashe waxanda suke yin umarni da adalci cikin mutane, to ka yi musu albishir da wata azaba mai raxaxi



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 29

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَأۡكُلُوٓاْ أَمۡوَٰلَكُم بَيۡنَكُم بِٱلۡبَٰطِلِ إِلَّآ أَن تَكُونَ تِجَٰرَةً عَن تَرَاضٖ مِّنكُمۡۚ وَلَا تَقۡتُلُوٓاْ أَنفُسَكُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِكُمۡ رَحِيمٗا

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku ci dukiyoyinku a tsakaninku ta hanyar rashin gaskiya, sai dai in ya kasance kasuwanci ne bisa yarjejeniya a tsakaninku. Kuma kada ku kashe kawunanku. Lalle Allah Ya kasance Mai tausaya muku ne



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 92

وَمَا كَانَ لِمُؤۡمِنٍ أَن يَقۡتُلَ مُؤۡمِنًا إِلَّا خَطَـٔٗاۚ وَمَن قَتَلَ مُؤۡمِنًا خَطَـٔٗا فَتَحۡرِيرُ رَقَبَةٖ مُّؤۡمِنَةٖ وَدِيَةٞ مُّسَلَّمَةٌ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِۦٓ إِلَّآ أَن يَصَّدَّقُواْۚ فَإِن كَانَ مِن قَوۡمٍ عَدُوّٖ لَّكُمۡ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَتَحۡرِيرُ رَقَبَةٖ مُّؤۡمِنَةٖۖ وَإِن كَانَ مِن قَوۡمِۭ بَيۡنَكُمۡ وَبَيۡنَهُم مِّيثَٰقٞ فَدِيَةٞ مُّسَلَّمَةٌ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِۦ وَتَحۡرِيرُ رَقَبَةٖ مُّؤۡمِنَةٖۖ فَمَن لَّمۡ يَجِدۡ فَصِيَامُ شَهۡرَيۡنِ مُتَتَابِعَيۡنِ تَوۡبَةٗ مِّنَ ٱللَّهِۗ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمٗا

Kuma bai dace ga mumini ya kashe wani mumini ba, sai bisa kuskure. Wanda ya kashe mumini bisa ga kuskure, to zai ‘yanta bawa ko baiwa mumina da kuma diyya wadda za a miqa wa iyalinsa, sai fa idan sun yafe. Amma idan wanda aka kashe yana cikin mutanen da suke maqiyanku, alhalin kuma shi mumini ne, to za ku ‘yanta bawa ko baiwa mumina; idan kuwa ya kasance yana cikin mutanen da kuke da yarjejeniyar zaman lafiya da su, to za a bayar da diyya wadda za a miqa wa iyalinsa, sannan za ku ‘yanta bawa ko baiwa mumina; wanda kuwa bai sami ikon haka ba, to sai ya yi azumin wata biyu a jere[1] don tuba zuwa ga Allah. Allah kuwa Ya kasance Mai yawan sani ne, Mai hikima


1- Watau sai dai idan akwai wani uzuri na rashin lafiya, ko na shari’a kamar shigowar Ramadana ko a ranar salla.


Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 27

۞وَٱتۡلُ عَلَيۡهِمۡ نَبَأَ ٱبۡنَيۡ ءَادَمَ بِٱلۡحَقِّ إِذۡ قَرَّبَا قُرۡبَانٗا فَتُقُبِّلَ مِنۡ أَحَدِهِمَا وَلَمۡ يُتَقَبَّلۡ مِنَ ٱلۡأٓخَرِ قَالَ لَأَقۡتُلَنَّكَۖ قَالَ إِنَّمَا يَتَقَبَّلُ ٱللَّهُ مِنَ ٱلۡمُتَّقِينَ

Kuma ka karanta musu labarin gaskiya na ‘ya’yan Adamu su biyu, yayin da suka gabatar da wani abin neman lada, sai aka karvi na xaya daga cikinsu, xayan kuma ba a karvi nasa ba, sai ya ce: “Wallahi, sai na kashe ka!” Sai ya ce: “Allah Yana karvar aiki ne kawai daga masu taqawa



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 28

لَئِنۢ بَسَطتَ إِلَيَّ يَدَكَ لِتَقۡتُلَنِي مَآ أَنَا۠ بِبَاسِطٖ يَدِيَ إِلَيۡكَ لِأَقۡتُلَكَۖ إِنِّيٓ أَخَافُ ٱللَّهَ رَبَّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

“Wallahi, idan har ka miqa hannunka gare ni domin ka kashe ni, ni kam ba zan miqa hannuna gare ka don in kashe ka ba; lalle ni ina jin tsoron Allah Ubangijin talikai



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 29

إِنِّيٓ أُرِيدُ أَن تَبُوٓأَ بِإِثۡمِي وَإِثۡمِكَ فَتَكُونَ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلنَّارِۚ وَذَٰلِكَ جَزَـٰٓؤُاْ ٱلظَّـٰلِمِينَ

“Lalle ni ina son ka xauki zunubina da zunubinka, sai ka kasance daga cikin ‘yan wuta. Kuma wannan shi ne sakamakon azzalumai.”



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 30

فَطَوَّعَتۡ لَهُۥ نَفۡسُهُۥ قَتۡلَ أَخِيهِ فَقَتَلَهُۥ فَأَصۡبَحَ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ

Sai zuciyarsa ta qawata masa ya kashe xan’uwansa, sai ya kashe shi, sai ya zama cikin hasararru[1]


1- Wannan shi ne xan’adam na farko da ya fara kisan kai a duniya, don haka yana da kamasho a cikin kowane jini da za a zubar har zuwa tashin alqiyam..


Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 31

فَبَعَثَ ٱللَّهُ غُرَابٗا يَبۡحَثُ فِي ٱلۡأَرۡضِ لِيُرِيَهُۥ كَيۡفَ يُوَٰرِي سَوۡءَةَ أَخِيهِۚ قَالَ يَٰوَيۡلَتَىٰٓ أَعَجَزۡتُ أَنۡ أَكُونَ مِثۡلَ هَٰذَا ٱلۡغُرَابِ فَأُوَٰرِيَ سَوۡءَةَ أَخِيۖ فَأَصۡبَحَ مِنَ ٱلنَّـٰدِمِينَ

Sai Allah Ya aiko da wani hankaka ya riqa tona qasa don ya nuna masa yadda zai binne gawar xan’uwansa. Sai ya ce: “Kaicona! Yanzu na kasa zama kamar wannan hankakan, in je in binne gawar xan’uwana?” Sai ya wayi gari cikin masu nadama



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 32

مِنۡ أَجۡلِ ذَٰلِكَ كَتَبۡنَا عَلَىٰ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ أَنَّهُۥ مَن قَتَلَ نَفۡسَۢا بِغَيۡرِ نَفۡسٍ أَوۡ فَسَادٖ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَكَأَنَّمَا قَتَلَ ٱلنَّاسَ جَمِيعٗا وَمَنۡ أَحۡيَاهَا فَكَأَنَّمَآ أَحۡيَا ٱلنَّاسَ جَمِيعٗاۚ وَلَقَدۡ جَآءَتۡهُمۡ رُسُلُنَا بِٱلۡبَيِّنَٰتِ ثُمَّ إِنَّ كَثِيرٗا مِّنۡهُم بَعۡدَ ذَٰلِكَ فِي ٱلۡأَرۡضِ لَمُسۡرِفُونَ

Saboda wannan ne muka wajabta wa Banu-Isra’ila cewa, duk wanda ya kashe wani rai ba tare da (laifin kisan) kai ba, ko kuma wata varna a bayan qasa, to kamar ya kashe mutane ne gaba xaya, wanda kuwa ya raya shi, to kamar ya raya mutane ne gaba xaya. Kuma lalle haqiqa manzanninmu sun zo musu da (hujjoji) mabayyana, amma sai ga shi da yawa daga cikinsu bayan hakan, lalle masu varna ne a bayan qasa



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 33

إِنَّمَا جَزَـٰٓؤُاْ ٱلَّذِينَ يُحَارِبُونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَيَسۡعَوۡنَ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَسَادًا أَن يُقَتَّلُوٓاْ أَوۡ يُصَلَّبُوٓاْ أَوۡ تُقَطَّعَ أَيۡدِيهِمۡ وَأَرۡجُلُهُم مِّنۡ خِلَٰفٍ أَوۡ يُنفَوۡاْ مِنَ ٱلۡأَرۡضِۚ ذَٰلِكَ لَهُمۡ خِزۡيٞ فِي ٱلدُّنۡيَاۖ وَلَهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ عَذَابٌ عَظِيمٌ

Lalle sakamakon waxanda suke yaqar Allah da Manzonsa, kuma suke varna a bayan qasa[1], shi ne kawai a karkashe su ko kuma a giggicciye su ko kuma a yayyanke hannayensu da qafafuwansu a tarnaqe ko kuma a kore su daga qasa. Wannan qasqanci ne a gare su a nan duniya, a lahira kuma suna da azaba mai girma


1- Ana nufin duk wasu masu ta’addanci da aikata fashi da makami, wannan shi ne hukuncinsu.


Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 34

إِلَّا ٱلَّذِينَ تَابُواْ مِن قَبۡلِ أَن تَقۡدِرُواْ عَلَيۡهِمۡۖ فَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Sai dai waxanda suka tuba tun kafin ku sami damar kama su; to ku sani cewa, lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 151

۞قُلۡ تَعَالَوۡاْ أَتۡلُ مَا حَرَّمَ رَبُّكُمۡ عَلَيۡكُمۡۖ أَلَّا تُشۡرِكُواْ بِهِۦ شَيۡـٔٗاۖ وَبِٱلۡوَٰلِدَيۡنِ إِحۡسَٰنٗاۖ وَلَا تَقۡتُلُوٓاْ أَوۡلَٰدَكُم مِّنۡ إِمۡلَٰقٖ نَّحۡنُ نَرۡزُقُكُمۡ وَإِيَّاهُمۡۖ وَلَا تَقۡرَبُواْ ٱلۡفَوَٰحِشَ مَا ظَهَرَ مِنۡهَا وَمَا بَطَنَۖ وَلَا تَقۡتُلُواْ ٱلنَّفۡسَ ٱلَّتِي حَرَّمَ ٱللَّهُ إِلَّا بِٱلۡحَقِّۚ ذَٰلِكُمۡ وَصَّىٰكُم بِهِۦ لَعَلَّكُمۡ تَعۡقِلُونَ

Ka ce: “Ku taho in karanta muku abin da Ubangijinku Ya haramta muku; kada ku haxa Shi da wani; kuma ku kyautata wa mahaifa; kuma kar ku kashe ‘ya’yanku saboda talauci; Mu ne za Mu arzuta ku har da su; kuma kada ku kusanci munanan (ayyuka) na sarari da na voye; kuma kada ku kashe ran da Allah Ya haramta (a kashe shi), sai idan da wani hakki. Wannan shi ne abin da (Allah) Ya yi muku wasiyya da shi, don ku zamo masu hankali



Capítulo: Suratul Isra’i

Verso : 31

وَلَا تَقۡتُلُوٓاْ أَوۡلَٰدَكُمۡ خَشۡيَةَ إِمۡلَٰقٖۖ نَّحۡنُ نَرۡزُقُهُمۡ وَإِيَّاكُمۡۚ إِنَّ قَتۡلَهُمۡ كَانَ خِطۡـٔٗا كَبِيرٗا

Kada kuma ku kashe ‘ya’yayenku don tsoron talauci: Mu ne Muke arzuta su har ma da ku. Lalle kashe su kuskure ne babba



Capítulo: Suratul Isra’i

Verso : 33

وَلَا تَقۡتُلُواْ ٱلنَّفۡسَ ٱلَّتِي حَرَّمَ ٱللَّهُ إِلَّا بِٱلۡحَقِّۗ وَمَن قُتِلَ مَظۡلُومٗا فَقَدۡ جَعَلۡنَا لِوَلِيِّهِۦ سُلۡطَٰنٗا فَلَا يُسۡرِف فِّي ٱلۡقَتۡلِۖ إِنَّهُۥ كَانَ مَنصُورٗا

Kuma kada ku kashe ran da Allah Ya haramta (kashewa) sai da haqqi. Wanda aka kashe ta hanyar zalunci, to lalle Mun bai wa magajinsa dama (ta ramuwa)[1], to (amma) kada ya wuce gona da iri wajen kisa; lalle shi ya zamanto abin dafa wa baya ne


1- Watau ta hanyar shari’a.


Capítulo: Suratu Ghafir

Verso : 28

وَقَالَ رَجُلٞ مُّؤۡمِنٞ مِّنۡ ءَالِ فِرۡعَوۡنَ يَكۡتُمُ إِيمَٰنَهُۥٓ أَتَقۡتُلُونَ رَجُلًا أَن يَقُولَ رَبِّيَ ٱللَّهُ وَقَدۡ جَآءَكُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ مِن رَّبِّكُمۡۖ وَإِن يَكُ كَٰذِبٗا فَعَلَيۡهِ كَذِبُهُۥۖ وَإِن يَكُ صَادِقٗا يُصِبۡكُم بَعۡضُ ٱلَّذِي يَعِدُكُمۡۖ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي مَنۡ هُوَ مُسۡرِفٞ كَذَّابٞ

Kuma wani mutum mumini daga dangin Fir’auna wanda yake voye imaninsa ya ce: “Yanzu kwa kashe mutum don ya ce ‘Allah ne Ubangijina’, kuma alhalin ya zo muku da hujjoji bayyanannu daga Ubangijinku? Idan ya zama maqaryaci ne to laifin qaryarsa yana kansa; idan kuwa ya zama mai gaskiya, to wani abu daga abin da yake yi muku gargaxinsa zai same ku. Lalle Allah ba Ya shiryar da wanda yake shi mai yawan varna ne, maqaryaci



Capítulo: Suratul Mumtahana

Verso : 12

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ إِذَا جَآءَكَ ٱلۡمُؤۡمِنَٰتُ يُبَايِعۡنَكَ عَلَىٰٓ أَن لَّا يُشۡرِكۡنَ بِٱللَّهِ شَيۡـٔٗا وَلَا يَسۡرِقۡنَ وَلَا يَزۡنِينَ وَلَا يَقۡتُلۡنَ أَوۡلَٰدَهُنَّ وَلَا يَأۡتِينَ بِبُهۡتَٰنٖ يَفۡتَرِينَهُۥ بَيۡنَ أَيۡدِيهِنَّ وَأَرۡجُلِهِنَّ وَلَا يَعۡصِينَكَ فِي مَعۡرُوفٖ فَبَايِعۡهُنَّ وَٱسۡتَغۡفِرۡ لَهُنَّ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Ya kai wannan Annabi, idan muminai mata suka zo maka suna yi maka mubaya’a a kan ba za su yi shirka da Allah ba, kuma ba za su yi sata ba, ba kuma za su yi zina ba, kuma ba za su kashe ‘ya’yansu ba, kuma ba za su zo da wani qage ba wanda za su qirqira (game da xan da suka haifa) a tsakanin hannayensu da qafafuwansu[1], kuma ba za su sava maka ba game da wani aiki na kirki, to sai ka yi musu mubaya’a, ka kuma nema musu gafarar Allah. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai


1- Kamar yadda suke yi a jahiliyya idan mace ta yi zina da mazaje da yawa sai ta zavi xaya ta danganta masa xan da ta haifa.