Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 178

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ كُتِبَ عَلَيۡكُمُ ٱلۡقِصَاصُ فِي ٱلۡقَتۡلَىۖ ٱلۡحُرُّ بِٱلۡحُرِّ وَٱلۡعَبۡدُ بِٱلۡعَبۡدِ وَٱلۡأُنثَىٰ بِٱلۡأُنثَىٰۚ فَمَنۡ عُفِيَ لَهُۥ مِنۡ أَخِيهِ شَيۡءٞ فَٱتِّبَاعُۢ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَأَدَآءٌ إِلَيۡهِ بِإِحۡسَٰنٖۗ ذَٰلِكَ تَخۡفِيفٞ مِّن رَّبِّكُمۡ وَرَحۡمَةٞۗ فَمَنِ ٱعۡتَدَىٰ بَعۡدَ ذَٰلِكَ فَلَهُۥ عَذَابٌ أَلِيمٞ

Ya ku waxanda suka yi imani, an wajabta muku qisasi dangane da waxanda aka kashe; xa da xa, bawa da bawa, mace da mace[1]. To duk wanda aka yafe masa qisasin xan uwansa, to sai ya bibiye shi ta hanyar da ta dace, shi kuma ya biya diyyar ta hanyar kyautatawa. Wannan (abin da aka ambata), sauqi ne da rahama daga wajen Ubangijinku. Don haka duk wanda ya qetare iyaka bayan haka, to yana da azaba mai raxaxi


1- Haka hukuncin yake yayin da namiji xa ya kashe ‘ya mace, ko mace ta kashe xa namiji. Amma idan magadan wanda aka kashe suka yafe, to babu zancen qisasi, sai a biya diyya kawai.


Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 179

وَلَكُمۡ فِي ٱلۡقِصَاصِ حَيَوٰةٞ يَـٰٓأُوْلِي ٱلۡأَلۡبَٰبِ لَعَلَّكُمۡ تَتَّقُونَ

Kuma a cikin (hukuncin) qisasi akwai (tsare) rayuwa a gare ku, ya ku ma’abota hankula, don ku samu taqawa



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 190

وَقَٰتِلُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ ٱلَّذِينَ يُقَٰتِلُونَكُمۡ وَلَا تَعۡتَدُوٓاْۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلۡمُعۡتَدِينَ

Kuma ku yaqi waxanda suke yaqar ku don ku xaukaka kalmar Allah, kuma kada ku qetare iyaka. Lalle Allah ba Ya son masu qetare iyaka



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 191

وَٱقۡتُلُوهُمۡ حَيۡثُ ثَقِفۡتُمُوهُمۡ وَأَخۡرِجُوهُم مِّنۡ حَيۡثُ أَخۡرَجُوكُمۡۚ وَٱلۡفِتۡنَةُ أَشَدُّ مِنَ ٱلۡقَتۡلِۚ وَلَا تُقَٰتِلُوهُمۡ عِندَ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ حَتَّىٰ يُقَٰتِلُوكُمۡ فِيهِۖ فَإِن قَٰتَلُوكُمۡ فَٱقۡتُلُوهُمۡۗ كَذَٰلِكَ جَزَآءُ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Kuma ku yaqe su duk inda kuka same su, kuma ku fitar da su ta inda suka fitar da ku; kuma fitina (ta kafirci) ita ce mafi tsanani fiye da kisa, kuma kada ku yaqe su a wurin Masallaci mai alfarma, har sai idan sun yaqe ku a cikinsa, idan har suka yaqe ku, to ku ma ku yaqe su. Kamar haka ne sakamakon kafirai yake



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 192

فَإِنِ ٱنتَهَوۡاْ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Amma idan suka daina, to lalle Allah Mai yawan gafara ne, Mai jin qai



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 194

ٱلشَّهۡرُ ٱلۡحَرَامُ بِٱلشَّهۡرِ ٱلۡحَرَامِ وَٱلۡحُرُمَٰتُ قِصَاصٞۚ فَمَنِ ٱعۡتَدَىٰ عَلَيۡكُمۡ فَٱعۡتَدُواْ عَلَيۡهِ بِمِثۡلِ مَا ٱعۡتَدَىٰ عَلَيۡكُمۡۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ مَعَ ٱلۡمُتَّقِينَ

(Idan sun yaqe ku a) wata mai alfarma[1], (ku ma ku yaqe su a) wata mai alfarma, kuma a cikin abubuwa masu alfarma akwai qisasi. Don haka duk wanda ya yi muku ta’addanci, to ku ma ku rama ta’addancin gwargwadon yadda ya yi muku ta’addanci; kuma ku kiyaye dokokin Allah, kuma ku sani lalle Allah Yana tare da masu taqawa


1- Watanni masu alfarma huxu ne, su ne: Zulqi’ida, Zulhijja, Al-Muharram da Rajab.


Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 15

وَٱلَّـٰتِي يَأۡتِينَ ٱلۡفَٰحِشَةَ مِن نِّسَآئِكُمۡ فَٱسۡتَشۡهِدُواْ عَلَيۡهِنَّ أَرۡبَعَةٗ مِّنكُمۡۖ فَإِن شَهِدُواْ فَأَمۡسِكُوهُنَّ فِي ٱلۡبُيُوتِ حَتَّىٰ يَتَوَفَّىٰهُنَّ ٱلۡمَوۡتُ أَوۡ يَجۡعَلَ ٱللَّهُ لَهُنَّ سَبِيلٗا

Kuma waxannan da suke aikata zina daga cikin matanku, to ku kafa musu shaidu guda huxu daga cikinku, sannan idan sun bayar da shaida, to sai ku tsare su a cikin gidaje har sai mutuwa ta xauke su ko kuma Allah Ya sanya musu wata mafita[1]


1- Wannan hukuncin ya kasance ne gabanin a saukar da hukuncin bulala xari ga mazinatan da ba su tava yin aure ba ko jefewa ga waxanda suka tava yin aure.


Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 16

وَٱلَّذَانِ يَأۡتِيَٰنِهَا مِنكُمۡ فَـَٔاذُوهُمَاۖ فَإِن تَابَا وَأَصۡلَحَا فَأَعۡرِضُواْ عَنۡهُمَآۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ تَوَّابٗا رَّحِيمًا

Kuma maza biyu daga cikinku da za su yi zina, to ku muzguna musu; amma idan sun tuba kuma suka gyara ayyukansu, to ku kawar da kai daga gare su. Lalle Allah Ya kasance Mai yawan karvar tuba ne, Mai jin qai



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 25

وَمَن لَّمۡ يَسۡتَطِعۡ مِنكُمۡ طَوۡلًا أَن يَنكِحَ ٱلۡمُحۡصَنَٰتِ ٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ فَمِن مَّا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُكُم مِّن فَتَيَٰتِكُمُ ٱلۡمُؤۡمِنَٰتِۚ وَٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِإِيمَٰنِكُمۚ بَعۡضُكُم مِّنۢ بَعۡضٖۚ فَٱنكِحُوهُنَّ بِإِذۡنِ أَهۡلِهِنَّ وَءَاتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ بِٱلۡمَعۡرُوفِ مُحۡصَنَٰتٍ غَيۡرَ مُسَٰفِحَٰتٖ وَلَا مُتَّخِذَٰتِ أَخۡدَانٖۚ فَإِذَآ أُحۡصِنَّ فَإِنۡ أَتَيۡنَ بِفَٰحِشَةٖ فَعَلَيۡهِنَّ نِصۡفُ مَا عَلَى ٱلۡمُحۡصَنَٰتِ مِنَ ٱلۡعَذَابِۚ ذَٰلِكَ لِمَنۡ خَشِيَ ٱلۡعَنَتَ مِنكُمۡۚ وَأَن تَصۡبِرُواْ خَيۡرٞ لَّكُمۡۗ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Kuma daga cikinku wanda ba shi da yalwar dukiya da zai iya auren ‘ya’ya muminai, to ya aura daga cikin abin da kuka mallaka na kuyanginku muminai. Kuma Allah Shi ne Mafi sanin imaninku. Sashinku ‘yan’uwan sashi ne. To ku aure su da izinin iyayen gidansu. Sai ku ba su sadakinsu ta hanyar da ta dace, suna masu kame kawunansu ba mazinata ba, sannan ba waxanda suke riqar farka a voye ba. To idan sun yi aure, sannan suka yi zina, to abin da za a yi musu na azaba, shi ne rabin abin da ake yi wa ‘ya’ya. Wannan ya shafi wanda ya ji tsoron matsatsi a cikinku. Amma ku yi haquri shi ya fi muku alheri. Allah kuma Mai yawan gafara ne, Mai jin qai



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 33

إِنَّمَا جَزَـٰٓؤُاْ ٱلَّذِينَ يُحَارِبُونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَيَسۡعَوۡنَ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَسَادًا أَن يُقَتَّلُوٓاْ أَوۡ يُصَلَّبُوٓاْ أَوۡ تُقَطَّعَ أَيۡدِيهِمۡ وَأَرۡجُلُهُم مِّنۡ خِلَٰفٍ أَوۡ يُنفَوۡاْ مِنَ ٱلۡأَرۡضِۚ ذَٰلِكَ لَهُمۡ خِزۡيٞ فِي ٱلدُّنۡيَاۖ وَلَهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ عَذَابٌ عَظِيمٌ

Lalle sakamakon waxanda suke yaqar Allah da Manzonsa, kuma suke varna a bayan qasa[1], shi ne kawai a karkashe su ko kuma a giggicciye su ko kuma a yayyanke hannayensu da qafafuwansu a tarnaqe ko kuma a kore su daga qasa. Wannan qasqanci ne a gare su a nan duniya, a lahira kuma suna da azaba mai girma


1- Ana nufin duk wasu masu ta’addanci da aikata fashi da makami, wannan shi ne hukuncinsu.


Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 34

إِلَّا ٱلَّذِينَ تَابُواْ مِن قَبۡلِ أَن تَقۡدِرُواْ عَلَيۡهِمۡۖ فَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Sai dai waxanda suka tuba tun kafin ku sami damar kama su; to ku sani cewa, lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 38

وَٱلسَّارِقُ وَٱلسَّارِقَةُ فَٱقۡطَعُوٓاْ أَيۡدِيَهُمَا جَزَآءَۢ بِمَا كَسَبَا نَكَٰلٗا مِّنَ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ عَزِيزٌ حَكِيمٞ

Kuma varawo da varauniya, sai ku yanke hannayensu[1], wannan sakamako ne na abin da suka aikata, uquba ce daga Allah. Kuma Allah Mabuwayi ne, Mai hikima


1- Za a yanke hannayensu ne na dama daga tsintsiyar hannu. Sunna ta bayyana cewa ana yanke hannun varawon da ya yi satar da ta kai rubu’in dinare ko dirhami uku na azurfa ko abin da ya yi daidai da su.


Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 45

وَكَتَبۡنَا عَلَيۡهِمۡ فِيهَآ أَنَّ ٱلنَّفۡسَ بِٱلنَّفۡسِ وَٱلۡعَيۡنَ بِٱلۡعَيۡنِ وَٱلۡأَنفَ بِٱلۡأَنفِ وَٱلۡأُذُنَ بِٱلۡأُذُنِ وَٱلسِّنَّ بِٱلسِّنِّ وَٱلۡجُرُوحَ قِصَاصٞۚ فَمَن تَصَدَّقَ بِهِۦ فَهُوَ كَفَّارَةٞ لَّهُۥۚ وَمَن لَّمۡ يَحۡكُم بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّـٰلِمُونَ

Kuma Mun wajabta a kansu a cikinta (Attaura), lalle rai da rai, kuma ido da ido, kuma hanci da hanci, kuma kunne da kunne, kuma haqori da haqori, raunuka kuma a yi ramuwa. To duk wanda ya yi sadaka da shi, to wannan kaffara ce gare shi. Duk wanda bai yi hukunci da abin da Allah Ya saukar ba kuwa, to waxannan su ne azzalumai



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 85

قَالُواْ تَٱللَّهِ تَفۡتَؤُاْ تَذۡكُرُ يُوسُفَ حَتَّىٰ تَكُونَ حَرَضًا أَوۡ تَكُونَ مِنَ ٱلۡهَٰلِكِينَ

Suka ce: “Wallahi ba za ka bar tuna Yusufu ba har sai ka tasam ma mutuwa ko sai ka zamanto cikin matattu!”



Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 126

وَإِنۡ عَاقَبۡتُمۡ فَعَاقِبُواْ بِمِثۡلِ مَا عُوقِبۡتُم بِهِۦۖ وَلَئِن صَبَرۡتُمۡ لَهُوَ خَيۡرٞ لِّلصَّـٰبِرِينَ

Idan za ku yi uquba to ku yi uquba da kwatankwacin abin da aka yi muku uquba da shi. Kuma lalle idan kuka yi haquri to tabbas shi ne ya fi alheri ga masu haquri



Capítulo: Suratul Isra’i

Verso : 33

وَلَا تَقۡتُلُواْ ٱلنَّفۡسَ ٱلَّتِي حَرَّمَ ٱللَّهُ إِلَّا بِٱلۡحَقِّۗ وَمَن قُتِلَ مَظۡلُومٗا فَقَدۡ جَعَلۡنَا لِوَلِيِّهِۦ سُلۡطَٰنٗا فَلَا يُسۡرِف فِّي ٱلۡقَتۡلِۖ إِنَّهُۥ كَانَ مَنصُورٗا

Kuma kada ku kashe ran da Allah Ya haramta (kashewa) sai da haqqi. Wanda aka kashe ta hanyar zalunci, to lalle Mun bai wa magajinsa dama (ta ramuwa)[1], to (amma) kada ya wuce gona da iri wajen kisa; lalle shi ya zamanto abin dafa wa baya ne


1- Watau ta hanyar shari’a.


Capítulo: Suratul Hajji

Verso : 60

۞ذَٰلِكَۖ وَمَنۡ عَاقَبَ بِمِثۡلِ مَا عُوقِبَ بِهِۦ ثُمَّ بُغِيَ عَلَيۡهِ لَيَنصُرَنَّهُ ٱللَّهُۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَعَفُوٌّ غَفُورٞ

Wannan (abu da aka ambata haka yake), duk wanda ya yi uquba da irin abin da aka yi masa uquba da shi, sannan aka daxa yi masa ta’addanci, to lalle Allah tabbas zai taimake shi. Lalle Allah tabbas Mai afuwa ne, Mai gafara



Capítulo: Suratun Nur

Verso : 2

ٱلزَّانِيَةُ وَٱلزَّانِي فَٱجۡلِدُواْ كُلَّ وَٰحِدٖ مِّنۡهُمَا مِاْئَةَ جَلۡدَةٖۖ وَلَا تَأۡخُذۡكُم بِهِمَا رَأۡفَةٞ فِي دِينِ ٱللَّهِ إِن كُنتُمۡ تُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۖ وَلۡيَشۡهَدۡ عَذَابَهُمَا طَآئِفَةٞ مِّنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Mazinaciya da mazinaci (idan suka yi zina) sai ku yi wa kowanne xaya daga cikinsu bulala xari[1], kada kuwa wani tausayi ya kama ku game da (tabbatar da hukuncin) addinin Allah idan kun kasance kuna imani da Allah da ranar lahira; kuma lalle ne wata qungiya daga cikin muminai su halarci (wurin) yi musu haddin


1- Ga waxanda ba su yi aure ba, bayan an samu shaidun gani da ido maza huxu; ko sun yi iqirari; ko ta zo da ciki ba tare da aure ba kuma ba sa-xaka ba.


Capítulo: Suratun Nur

Verso : 4

وَٱلَّذِينَ يَرۡمُونَ ٱلۡمُحۡصَنَٰتِ ثُمَّ لَمۡ يَأۡتُواْ بِأَرۡبَعَةِ شُهَدَآءَ فَٱجۡلِدُوهُمۡ ثَمَٰنِينَ جَلۡدَةٗ وَلَا تَقۡبَلُواْ لَهُمۡ شَهَٰدَةً أَبَدٗاۚ وَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡفَٰسِقُونَ

Waxanda kuwa suke jifan mata masu kamun kai sannan ba su kawo shaidu huxu ba, sai ku yi musu bulala tamanin, kuma kada ku karvi shaidarsu har abada. Waxannan kuma su ne fasiqai



Capítulo: Suratun Nur

Verso : 5

إِلَّا ٱلَّذِينَ تَابُواْ مِنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ وَأَصۡلَحُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Sai dai waxanda suka tuba bayan wannan suka kuma gyara, to haqiqa Allah Mai gafara ne, Mai jin qai ne



Capítulo: Suratun Nur

Verso : 6

وَٱلَّذِينَ يَرۡمُونَ أَزۡوَٰجَهُمۡ وَلَمۡ يَكُن لَّهُمۡ شُهَدَآءُ إِلَّآ أَنفُسُهُمۡ فَشَهَٰدَةُ أَحَدِهِمۡ أَرۡبَعُ شَهَٰدَٰتِۭ بِٱللَّهِ إِنَّهُۥ لَمِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ

Waxanda kuma suke jifan matayensu (da zina) kuma ba su da wasu shaidu sai su kansu, to shaidar xayansu ita ce ya rantsuwa da Allah sau huxu a kan cewa shi lalle yana daga masu gaskiya



Capítulo: Suratun Nur

Verso : 7

وَٱلۡخَٰمِسَةُ أَنَّ لَعۡنَتَ ٱللَّهِ عَلَيۡهِ إِن كَانَ مِنَ ٱلۡكَٰذِبِينَ

(Rantsuwa) ta biyar kuwa kan cewa tsinuwar Allah ta hau kansa in ya kasance daga cikin maqaryata



Capítulo: Suratun Nur

Verso : 8

وَيَدۡرَؤُاْ عَنۡهَا ٱلۡعَذَابَ أَن تَشۡهَدَ أَرۡبَعَ شَهَٰدَٰتِۭ بِٱللَّهِ إِنَّهُۥ لَمِنَ ٱلۡكَٰذِبِينَ

Kuma (abin da) zai kawar mata da azabar haddi shi ne ta yi rantsuwa da Allah sau huxu kan cewa shi lalle yana daga cikin maqaryata



Capítulo: Suratun Nur

Verso : 9

وَٱلۡخَٰمِسَةَ أَنَّ غَضَبَ ٱللَّهِ عَلَيۡهَآ إِن كَانَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ

(Rantsuwa) ta biyar kuwa kan cewa lalle fushin Allah ya hau kanta idan ya kasance daga masu gaskiya



Capítulo: Suratus Shura

Verso : 40

وَجَزَـٰٓؤُاْ سَيِّئَةٖ سَيِّئَةٞ مِّثۡلُهَاۖ فَمَنۡ عَفَا وَأَصۡلَحَ فَأَجۡرُهُۥ عَلَى ٱللَّهِۚ إِنَّهُۥ لَا يُحِبُّ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Kuma sakamakon mummunan (abu) shi ne mayar da mummuna kamarsa; to wanda ya yi afuwa ya kuma kyautata, to ladansa yana wurin Allah. Lalle Shi ba Ya son azzalumai



Capítulo: Suratus Shura

Verso : 41

وَلَمَنِ ٱنتَصَرَ بَعۡدَ ظُلۡمِهِۦ فَأُوْلَـٰٓئِكَ مَا عَلَيۡهِم مِّن سَبِيلٍ

Tabbas kuma duk wanda ya rama bayan an zalunce shi, to waxannan ba wani laifi a kansu