مَٰلِكِ يَوۡمِ ٱلدِّينِ
Mamallakin ranar sakamako
أَلَمۡ تَعۡلَمۡ أَنَّ ٱللَّهَ لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۗ وَمَا لَكُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ مِن وَلِيّٖ وَلَا نَصِيرٍ
Kuma ba ka sani ba cewa, lalle mulkin sammai da qasa na Allah ne, kuma ba ku da wani majivinci ko wani mai taimako ba Allah ba?
قُلِ ٱللَّهُمَّ مَٰلِكَ ٱلۡمُلۡكِ تُؤۡتِي ٱلۡمُلۡكَ مَن تَشَآءُ وَتَنزِعُ ٱلۡمُلۡكَ مِمَّن تَشَآءُ وَتُعِزُّ مَن تَشَآءُ وَتُذِلُّ مَن تَشَآءُۖ بِيَدِكَ ٱلۡخَيۡرُۖ إِنَّكَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ
Ka ce: “Ya Allah, Kai ne Mamallakin mulki, Kana bayar da mulki ga wanda Ka ga dama, kuma Kana qwace mulki daga wanda Ka ga dama, kuma Kana xaukaka wanda Ka ga dama, kuma Kana qasqantar da wanda Ka ga dama; duk alheri yana hannuka, lalle Kai Mai iko ne a kan komai
وَلَا يَحۡسَبَنَّ ٱلَّذِينَ يَبۡخَلُونَ بِمَآ ءَاتَىٰهُمُ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦ هُوَ خَيۡرٗا لَّهُمۖ بَلۡ هُوَ شَرّٞ لَّهُمۡۖ سَيُطَوَّقُونَ مَا بَخِلُواْ بِهِۦ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۗ وَلِلَّهِ مِيرَٰثُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۗ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ
Kuma waxanda suke yin rowar abin da Allah Ya ba su na falalarsa kar su yi tsammanin hakan alheri ne a gare su; a’a, hakan sharri ne a gare su; da sannu za a yi musu saqandami da abin da suka yi rowa da shi a ranar alqiyama. Kuma Allah Shi ne Mai gadon sammai da qasa. Kuma Allah Mai cikakken sanin abin da kuke aikatawa ne
وَلِلَّهِ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۗ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ
Kuma ga Allah ne mulkin sammai da qasa yake. Kuma Allah Mai iko ne a kan komai
لَّقَدۡ كَفَرَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓاْ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡمَسِيحُ ٱبۡنُ مَرۡيَمَۚ قُلۡ فَمَن يَمۡلِكُ مِنَ ٱللَّهِ شَيۡـًٔا إِنۡ أَرَادَ أَن يُهۡلِكَ ٱلۡمَسِيحَ ٱبۡنَ مَرۡيَمَ وَأُمَّهُۥ وَمَن فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗاۗ وَلِلَّهِ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَاۚ يَخۡلُقُ مَا يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ
Lalle haqiqa, waxannan da suka ce: “Lalle Allah Shi ne Almasihu xan Maryamu” sun kafirta. Ka ce: “To wane ne ya isa ya hana Allah, idan Ya yi nufin Ya hallaka Almasihu xan Maryamu da mahaifiyarsa da duk wanda yake ban qasa gaba xaya? Allah kuwa Shi Yake mallakar abin da yake cikin sammai da qasa da kuma abin da yake tsakaninsu. Yana halittar abin da Ya ga dama. Kuma Allah Mai cikakken iko ne a kan komai.”
وَقَالَتِ ٱلۡيَهُودُ وَٱلنَّصَٰرَىٰ نَحۡنُ أَبۡنَـٰٓؤُاْ ٱللَّهِ وَأَحِبَّـٰٓؤُهُۥۚ قُلۡ فَلِمَ يُعَذِّبُكُم بِذُنُوبِكُمۖ بَلۡ أَنتُم بَشَرٞ مِّمَّنۡ خَلَقَۚ يَغۡفِرُ لِمَن يَشَآءُ وَيُعَذِّبُ مَن يَشَآءُۚ وَلِلَّهِ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَاۖ وَإِلَيۡهِ ٱلۡمَصِيرُ
Kuma Yahudawa da Nasara suka ce: “Mu ‘ya’yan Allah ne, kuma masoyansa.” Ka ce: “To don me Yake muku azaba a sanadiyyar zunubanku? Ba haka ne ba, ku mutane ne daga cikin waxanda Ya halitta. Yana yin gafara ga wanda Ya ga dama, kuma Yana yin azaba ga wanda Ya ga dama. Kuma mulkin sammai da qasa da abin da yake tsakaninsu na Allah ne, kuma zuwa gare Shi ne makoma take.”
لِلَّهِ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا فِيهِنَّۚ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرُۢ
Mulkin sammai da qasa da abin da yake cikinsu na Allah ne. Kuma Shi Mai iko ne a kan komai
وَهُوَ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ بِٱلۡحَقِّۖ وَيَوۡمَ يَقُولُ كُن فَيَكُونُۚ قَوۡلُهُ ٱلۡحَقُّۚ وَلَهُ ٱلۡمُلۡكُ يَوۡمَ يُنفَخُ فِي ٱلصُّورِۚ عَٰلِمُ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِۚ وَهُوَ ٱلۡحَكِيمُ ٱلۡخَبِيرُ
“Kuma Shi ne Wanda ya halicci sammai da qasa da gaskiya; kuma (ku tuna) ranar da zai ce da abu: ‘Kasance!’ Nan take sai ya kasance. Maganarsa gaskiya ce. Kuma Shi ne Yake da cikakken mulki a ranar da za a busa qaho Masanin gaibu da sarari, kuma Shi ne Mai hikima, Mai cikakken sani.”
قُلۡ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنِّي رَسُولُ ٱللَّهِ إِلَيۡكُمۡ جَمِيعًا ٱلَّذِي لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۖ فَـَٔامِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِ ٱلنَّبِيِّ ٱلۡأُمِّيِّ ٱلَّذِي يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَكَلِمَٰتِهِۦ وَٱتَّبِعُوهُ لَعَلَّكُمۡ تَهۡتَدُونَ
Ka ce: “Ya ku mutane, lalle ni Manzon Allah ne zuwa gare ku gaba xaya, wanda Yake da mallakar sammai da qasa, babu abin bauta wa da gaskiya sai Shi; Shi ne Yake rayawa, kuma Shi Yake kashewa; don haka ku yi imani da Allah da Manzonsa Annabi Ummiyyi, wanda yake yin imani da Allah da kalmominsa, kuma ku bi shi don ku zama shiryayyu.”
إِنَّ ٱللَّهَ لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۚ وَمَا لَكُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ مِن وَلِيّٖ وَلَا نَصِيرٖ
Lalle Allah Shi ne Mai mulkin sammai da qasa, Yana rayawa kuma Yana kashewa. Ba ku da wani majivincin lamarinku in ban da Allah, ba ku kuma da wani mai taimako
وَقُلِ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِي لَمۡ يَتَّخِذۡ وَلَدٗا وَلَمۡ يَكُن لَّهُۥ شَرِيكٞ فِي ٱلۡمُلۡكِ وَلَمۡ يَكُن لَّهُۥ وَلِيّٞ مِّنَ ٱلذُّلِّۖ وَكَبِّرۡهُ تَكۡبِيرَۢا
Kuma ka ce, “Yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda bai riqi xa ba, kuma ba Shi da wani abokin tarayya a cikin mulki, kuma ba Shi da wani mataimaki don kare masa qasqanci.” Kuma ka girmama shi girmamawa ta sosai
فَتَعَٰلَى ٱللَّهُ ٱلۡمَلِكُ ٱلۡحَقُّۗ وَلَا تَعۡجَلۡ بِٱلۡقُرۡءَانِ مِن قَبۡلِ أَن يُقۡضَىٰٓ إِلَيۡكَ وَحۡيُهُۥۖ وَقُل رَّبِّ زِدۡنِي عِلۡمٗا
Kuma fa Allah Sarki na gaskiya Ya xaukaka (daga maganganun kafirai). Kada kuma ka yi garaje da (karatun) Alqur’ani tun kafin a gama yi maka wahayinsa, kuma ka ce: “Ubangiji Ka qara min ilimi.”
ٱلۡمُلۡكُ يَوۡمَئِذٖ لِّلَّهِ يَحۡكُمُ بَيۡنَهُمۡۚ فَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ فِي جَنَّـٰتِ ٱلنَّعِيمِ
Mulki a wannan ranar na Allah ne, zai yi hukunci a tsakaninsu. To waxanda suka yi imani suka kuma yi kyawawan ayyuka, suna cikin gidajen Aljanna na ni’ima
فَتَعَٰلَى ٱللَّهُ ٱلۡمَلِكُ ٱلۡحَقُّۖ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ رَبُّ ٱلۡعَرۡشِ ٱلۡكَرِيمِ
To Allah Sarki na gaskiya Ya xaukaka; babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi, (Shi ne) Ubangijin Al’arshi mai girma
وَلِلَّهِ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ وَإِلَى ٱللَّهِ ٱلۡمَصِيرُ
Kuma mulkin sammai da qasa na Allah ne; makoma kuma zuwa ga Allah take
ٱلَّذِي لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَلَمۡ يَتَّخِذۡ وَلَدٗا وَلَمۡ يَكُن لَّهُۥ شَرِيكٞ فِي ٱلۡمُلۡكِ وَخَلَقَ كُلَّ شَيۡءٖ فَقَدَّرَهُۥ تَقۡدِيرٗا
(Shi ne) Wanda mulkin sammai da qasa nasa ne, kuma bai riqi wani xa ba, ba kuma Shi da wani abokin tarayya a cikin mulkin, Ya kuma halicci kowanne abu, sannan Ya ajiye shi a irin gwargwadon da ya dace da shi
ٱلۡمُلۡكُ يَوۡمَئِذٍ ٱلۡحَقُّ لِلرَّحۡمَٰنِۚ وَكَانَ يَوۡمًا عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ عَسِيرٗا
Mulki tabbatacce a wannan ranar na (Allah) Mai rahama ne. Kuma ta kasance rana ce mawuyaciya ga kafurai
يُولِجُ ٱلَّيۡلَ فِي ٱلنَّهَارِ وَيُولِجُ ٱلنَّهَارَ فِي ٱلَّيۡلِ وَسَخَّرَ ٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَۖ كُلّٞ يَجۡرِي لِأَجَلٖ مُّسَمّٗىۚ ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمۡ لَهُ ٱلۡمُلۡكُۚ وَٱلَّذِينَ تَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦ مَا يَمۡلِكُونَ مِن قِطۡمِيرٍ
Yana shigar da dare cikin yini, Yana kuma shigar da yini cikin dare, Ya kuma hore rana da wata kowannensu yana tafiya zuwa ga ajali iyakantacce. (Mai yin wannan kuwa) Shi ne Allah Ubangijinku, mulki (kuwa) nasa ne. Waxanda kuwa kuke bauta wa ba Shi ba, ba su mallaki ko da rigar qwallon dabino ba
فَسُبۡحَٰنَ ٱلَّذِي بِيَدِهِۦ مَلَكُوتُ كُلِّ شَيۡءٖ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ
To tsarki ya tabbata ga wanda mulkin kowane abu yake a hannunsa, kuma wurinsa ne kawai za a komar da ku
خَلَقَكُم مِّن نَّفۡسٖ وَٰحِدَةٖ ثُمَّ جَعَلَ مِنۡهَا زَوۡجَهَا وَأَنزَلَ لَكُم مِّنَ ٱلۡأَنۡعَٰمِ ثَمَٰنِيَةَ أَزۡوَٰجٖۚ يَخۡلُقُكُمۡ فِي بُطُونِ أُمَّهَٰتِكُمۡ خَلۡقٗا مِّنۢ بَعۡدِ خَلۡقٖ فِي ظُلُمَٰتٖ ثَلَٰثٖۚ ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمۡ لَهُ ٱلۡمُلۡكُۖ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ فَأَنَّىٰ تُصۡرَفُونَ
Ya halicce ku daga rai guda (shi ne Adamu), sannan Ya halicci matarsa daga gare shi, Ya kuma halitta muku dangogi guda takwas na dabbobin ni’ima. Yana (shirya) halittarku a cikin cikkunan iyayenku mata, matakin halitta bayan wani matakin, cikin duffai guda uku[1]. Wannan kuwa Shi ne Allah Ubangijinku; Wanda mulki nasa ne; babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi. To ta ina ne ake juyar da ku?
1- Watau duhun ciki da duhun mahaifa da kuma duhun mabiyiya.
قُل لِّلَّهِ ٱلشَّفَٰعَةُ جَمِيعٗاۖ لَّهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ ثُمَّ إِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ
Ka ce: “Ceto gaba xaya na Allah ne; mulkin sammai da qasa nasa ne Shi kaxai; sannan kuma wurinsa ne kawai za a komar da ku.”
يَوۡمَ هُم بَٰرِزُونَۖ لَا يَخۡفَىٰ عَلَى ٱللَّهِ مِنۡهُمۡ شَيۡءٞۚ لِّمَنِ ٱلۡمُلۡكُ ٱلۡيَوۡمَۖ لِلَّهِ ٱلۡوَٰحِدِ ٱلۡقَهَّارِ
Ranar da za su bayyana; babu wani abu nasu da zai vuya ga Allah. (Zai ce): “Mulki na wane ne a yau?” (Sai Ya ce): “Na Allah Makaxaici, Mai rinjaye ne.”
لِّلَّهِ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ يَخۡلُقُ مَا يَشَآءُۚ يَهَبُ لِمَن يَشَآءُ إِنَٰثٗا وَيَهَبُ لِمَن يَشَآءُ ٱلذُّكُورَ
Mulkin sammai da qasa na Allah ne. Yana halittar abin da Ya ga dama. Yana ba da `ya`ya mata ga wanda Ya ga dama, Yana kuma ba da `ya`ya maza ga wanda Ya ga dama
وَتَبَارَكَ ٱلَّذِي لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَا وَعِندَهُۥ عِلۡمُ ٱلسَّاعَةِ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ
Kuma wanda Yake da mulkin sammai da qasa da abin da yake tsakaninsu alhairansa sun yi yawa, kuma a wurinsa sanin (ranar) alqiyama yake, wurinsa kuma za a komar da ku
وَلِلَّهِ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَيَوۡمَ تَقُومُ ٱلسَّاعَةُ يَوۡمَئِذٖ يَخۡسَرُ ٱلۡمُبۡطِلُونَ
Mulkin sammai da qasa kuma na Allah ne. Kuma ranar da alqiyama za ta tashi, a wannan ranar mavarnata za su yi asara
وَلِلَّهِ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ يَغۡفِرُ لِمَن يَشَآءُ وَيُعَذِّبُ مَن يَشَآءُۚ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمٗا
Kuma mulkin sammai da qasa na Allah ne. Yana yin gafara ga wanda Ya ga dama, Yana kuma azabtar da wanda Ya ga dama. Allah kuwa Ya kasance Mai gafara ne, Mai rahama
لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ
Mulkin sammai da qasa nasa ne; Yana rayawa, Yana kuma kashewa; kuma Shi Mai iko ne a kan komai
لَّهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَإِلَى ٱللَّهِ تُرۡجَعُ ٱلۡأُمُورُ
Mulkin sammai da qasa nasa ne. Kuma ga Allah ake mayar da al’amura
وَمَا لَكُمۡ أَلَّا تُنفِقُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَلِلَّهِ مِيرَٰثُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ لَا يَسۡتَوِي مِنكُم مَّنۡ أَنفَقَ مِن قَبۡلِ ٱلۡفَتۡحِ وَقَٰتَلَۚ أُوْلَـٰٓئِكَ أَعۡظَمُ دَرَجَةٗ مِّنَ ٱلَّذِينَ أَنفَقُواْ مِنۢ بَعۡدُ وَقَٰتَلُواْۚ وَكُلّٗا وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلۡحُسۡنَىٰۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ
Kuma me ya same ku ne da ba za ku ciyar saboda Allah ba, alhali kuwa gadon sammai da qasa na Allah ne? Wanda ya ciyar daga cikinku tun kafin buxe (Makka)[1] ya kuma yi yaqi, ba zai zama daidai (da wanda bai yi) ba. Waxannan su suka fi girman daraja a kan waxanda suka ciyar daga bisani, suka kuma yi yaqi. Amma kuma kowannensu Allah Ya yi masa alqawarin Aljanna. Allah kuma Masanin abin da kuke aikatawa ne
1- Wasu daga cikin malamai sun fassara Fat’hu a wannan ayar da cewa ana nufin Sulhul Hudaibiyya.