وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَتَّخِذُ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَندَادٗا يُحِبُّونَهُمۡ كَحُبِّ ٱللَّهِۖ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَشَدُّ حُبّٗا لِّلَّهِۗ وَلَوۡ يَرَى ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓاْ إِذۡ يَرَوۡنَ ٱلۡعَذَابَ أَنَّ ٱلۡقُوَّةَ لِلَّهِ جَمِيعٗا وَأَنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعَذَابِ
Kuma akwai wasu mutane waxanda suke bauta wa wasu kishiyoyi ba Allah ba; suna son su kamar son Allah; waxanda kuwa suka yi imani sun fi son Allah (fiye da komai). Da a ce waxanda suka yi zalunci za su ga lokacin da suke ido huxu da azaba (to da sun gane) cewa, lalle duk wani qarfi na Allah ne gaba xaya, kuma lalle Allah Mai tsananin azaba ne
وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَشۡرِي نَفۡسَهُ ٱبۡتِغَآءَ مَرۡضَاتِ ٱللَّهِۚ وَٱللَّهُ رَءُوفُۢ بِٱلۡعِبَادِ
Kuma daga cikin mutane akwai wanda yake sayar da kansa don neman yardar Allah. Allah kuwa Mai yawan tausayi ne ga bayi
قُلۡ إِن كُنتُمۡ تُحِبُّونَ ٱللَّهَ فَٱتَّبِعُونِي يُحۡبِبۡكُمُ ٱللَّهُ وَيَغۡفِرۡ لَكُمۡ ذُنُوبَكُمۡۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Ka ce: “In kun kasance kuna son Allah, to ku yi mini biyayya, sai Allah Ya so ku, kuma Ya gafarta muku zunubanku. Kuma Allah Mai gafara ne, Mai jin qai.”
أَفَغَيۡرَ دِينِ ٱللَّهِ يَبۡغُونَ وَلَهُۥٓ أَسۡلَمَ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ طَوۡعٗا وَكَرۡهٗا وَإِلَيۡهِ يُرۡجَعُونَ
To shin yanzu wani addini suke nema ba na Allah ba, alhalin duk wanda yake cikin sammai da qasa gare Shi ne ya miqa wuya yana so ko yana qi, kuma zuwa gare Shi za a komar da su?
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَن يَرۡتَدَّ مِنكُمۡ عَن دِينِهِۦ فَسَوۡفَ يَأۡتِي ٱللَّهُ بِقَوۡمٖ يُحِبُّهُمۡ وَيُحِبُّونَهُۥٓ أَذِلَّةٍ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ أَعِزَّةٍ عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ يُجَٰهِدُونَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَلَا يَخَافُونَ لَوۡمَةَ لَآئِمٖۚ ذَٰلِكَ فَضۡلُ ٱللَّهِ يُؤۡتِيهِ مَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ وَٰسِعٌ عَلِيمٌ
Ya ku waxanda suka yi imani, duk wanda ya yi ridda daga cikinku, ya bar addininsa, to (ya sani) Allah zai kawo waxansu mutane da Yake son su suna son Sa, suna masu qasqantar da kai ga muminai, suna masu nuna wa kafirai isa, suna yin jihadi don xaukaka kalmar Allah, kuma ba sa jin tsoron zargin wani mai zargi. Wannan falalar Allah ce da Yake bayar da ita ga wanda Ya ga dama. Kuma Allah Mayalwaci ne, Masani
قُلۡ أَغَيۡرَ ٱللَّهِ أَبۡغِي رَبّٗا وَهُوَ رَبُّ كُلِّ شَيۡءٖۚ وَلَا تَكۡسِبُ كُلُّ نَفۡسٍ إِلَّا عَلَيۡهَاۚ وَلَا تَزِرُ وَازِرَةٞ وِزۡرَ أُخۡرَىٰۚ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّكُم مَّرۡجِعُكُمۡ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ فِيهِ تَخۡتَلِفُونَ
Ka ce: “Yanzu wanin Allah zan riqa a matsayin ubangiji, alhalin kuwa Shi ne Ubangijin komai? Kuma ba wani rai da zai aikata wani abu face sai don kansa. Kuma ba wani rai da zai xauki laifin wani rai. Sannan kuma zuwa ga Ubangijinku ne makomarku take, sai Ya ba ku labarin abin da kuka kasance kuna savani a game da shi
أَمَّنۡ هُوَ قَٰنِتٌ ءَانَآءَ ٱلَّيۡلِ سَاجِدٗا وَقَآئِمٗا يَحۡذَرُ ٱلۡأٓخِرَةَ وَيَرۡجُواْ رَحۡمَةَ رَبِّهِۦۗ قُلۡ هَلۡ يَسۡتَوِي ٱلَّذِينَ يَعۡلَمُونَ وَٱلَّذِينَ لَا يَعۡلَمُونَۗ إِنَّمَا يَتَذَكَّرُ أُوْلُواْ ٱلۡأَلۡبَٰبِ
Shin yanzu wanda yake shi mai ibada ne a cikin sa’o’in dare, yana sujjada yana kuma tsayawa, yana tsoron ranar lahira yana kuma qaunar rahamar Ubangijinsa (zai yi daidai da wanda ba haka yake ba?) Ka ce: “Yanzu waxanda suke da sani za su yi daidai da waxanda ba su da sani? Ma’abota hankula ne kawai suke wa’azantuwa
مُّحَمَّدٞ رَّسُولُ ٱللَّهِۚ وَٱلَّذِينَ مَعَهُۥٓ أَشِدَّآءُ عَلَى ٱلۡكُفَّارِ رُحَمَآءُ بَيۡنَهُمۡۖ تَرَىٰهُمۡ رُكَّعٗا سُجَّدٗا يَبۡتَغُونَ فَضۡلٗا مِّنَ ٱللَّهِ وَرِضۡوَٰنٗاۖ سِيمَاهُمۡ فِي وُجُوهِهِم مِّنۡ أَثَرِ ٱلسُّجُودِۚ ذَٰلِكَ مَثَلُهُمۡ فِي ٱلتَّوۡرَىٰةِۚ وَمَثَلُهُمۡ فِي ٱلۡإِنجِيلِ كَزَرۡعٍ أَخۡرَجَ شَطۡـَٔهُۥ فَـَٔازَرَهُۥ فَٱسۡتَغۡلَظَ فَٱسۡتَوَىٰ عَلَىٰ سُوقِهِۦ يُعۡجِبُ ٱلزُّرَّاعَ لِيَغِيظَ بِهِمُ ٱلۡكُفَّارَۗ وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ مِنۡهُم مَّغۡفِرَةٗ وَأَجۡرًا عَظِيمَۢا
Muhammadu Manzon Allah ne. Waxanda kuma suke tare da shi masu tsanani ne a kan kafirai, kuma masu tausayin junansu ne; za ka gan su suna ruku’i suna sujjada suna neman falala daga Allah da yardarsa; alamominsu na gurbin sujjada suna bayyana a fuskokinsu. Wannan shi ne misalinsu a cikin Attaura. Misalinsu kuwa a cikin Linjila kamar shuka ce da ta fitar da reshenta sai ya qarfafe ta, sannan ta yi kauri sai ta daidaita a kan tushiyarta ta riqa qayatar da manoma, don Ya cusa wa kafirai haushi. Allah Ya yi wa waxanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari daga cikinsu alqawarin gafara da lada mai girma
وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ فِيكُمۡ رَسُولَ ٱللَّهِۚ لَوۡ يُطِيعُكُمۡ فِي كَثِيرٖ مِّنَ ٱلۡأَمۡرِ لَعَنِتُّمۡ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ حَبَّبَ إِلَيۡكُمُ ٱلۡإِيمَٰنَ وَزَيَّنَهُۥ فِي قُلُوبِكُمۡ وَكَرَّهَ إِلَيۡكُمُ ٱلۡكُفۡرَ وَٱلۡفُسُوقَ وَٱلۡعِصۡيَانَۚ أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلرَّـٰشِدُونَ
Kuma ku sani cewa Manzon Allah yana cikinku. Da zai biye muku game da al’amura masu yawa, tabbas da kun wahala, sai dai kuma Allah Ya sa muku son imani Ya kuma qawata shi a cikin zukatanku, Ya kuma sa muku qin kafirci da fasiqanci da savo. Waxannan su ne shiryayyu
لَّا تَجِدُ قَوۡمٗا يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ يُوَآدُّونَ مَنۡ حَآدَّ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَلَوۡ كَانُوٓاْ ءَابَآءَهُمۡ أَوۡ أَبۡنَآءَهُمۡ أَوۡ إِخۡوَٰنَهُمۡ أَوۡ عَشِيرَتَهُمۡۚ أُوْلَـٰٓئِكَ كَتَبَ فِي قُلُوبِهِمُ ٱلۡإِيمَٰنَ وَأَيَّدَهُم بِرُوحٖ مِّنۡهُۖ وَيُدۡخِلُهُمۡ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ رَضِيَ ٱللَّهُ عَنۡهُمۡ وَرَضُواْ عَنۡهُۚ أُوْلَـٰٓئِكَ حِزۡبُ ٱللَّهِۚ أَلَآ إِنَّ حِزۡبَ ٱللَّهِ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ
Ba za ka tava samun wasu mutane da suke yin imani da Allah da ranar lahira ba, su riqa qaunar waxanda suke gaba da Allah da Manzonsa, ko da kuwa sun kasance iyayensu ne ko ‘ya’yansu ko ‘yan’uwansu ko kuma danginsu. Waxannan Allah Ya rubuta imani a cikin zukatansu, Ya kuma qarfafe su da wani ruhi daga wurinsa[1]; zai kuma shigar da su gidajen Aljanna (waxanda) qoramu suke gudana ta qarqashinsu, madawwama a cikinsu. Allah Ya yarda da su, su ma sun yarda da Shi. Waxannan ne qungiyar Allah. Ku saurara, lalle qungiyar Allah su ne masu samun babban rabo
1- Watau zai qarfafe su da wata hujja daga wurinsa da haske.
لِلۡفُقَرَآءِ ٱلۡمُهَٰجِرِينَ ٱلَّذِينَ أُخۡرِجُواْ مِن دِيَٰرِهِمۡ وَأَمۡوَٰلِهِمۡ يَبۡتَغُونَ فَضۡلٗا مِّنَ ٱللَّهِ وَرِضۡوَٰنٗا وَيَنصُرُونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓۚ أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلصَّـٰدِقُونَ
(Za a bayar da dukiyar) ga matalauta da suka yi hijira waxanda aka fitar da su daga gidajensu da dukiyoyinsu don neman falala daga Allah da yardarsa, suna kuma taimakon (addinin) Allah da Manzonsa. Waxannan su ne masu gaskiya
وَٱلَّذِينَ تَبَوَّءُو ٱلدَّارَ وَٱلۡإِيمَٰنَ مِن قَبۡلِهِمۡ يُحِبُّونَ مَنۡ هَاجَرَ إِلَيۡهِمۡ وَلَا يَجِدُونَ فِي صُدُورِهِمۡ حَاجَةٗ مِّمَّآ أُوتُواْ وَيُؤۡثِرُونَ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمۡ وَلَوۡ كَانَ بِهِمۡ خَصَاصَةٞۚ وَمَن يُوقَ شُحَّ نَفۡسِهِۦ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ
Da kuma waxanda suka tanadi gida (mutanen Madina) suka kuma (karvi) imani gabaninsu (masu hijira), suna son waxanda suka yi hijira zuwa gare su, ba sa samun wani qyashi a zukatansu game da abin da aka ba su (masu hijira), suna kuma fifita (masu hijira) a kan kawunansu, ko da kuwa suna da tsananin buqata. Duk kuwa wanda aka kiyaye shi daga son kansa, to waxannan su ne masu babban rabo