يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱعۡبُدُواْ رَبَّكُمُ ٱلَّذِي خَلَقَكُمۡ وَٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَتَّقُونَ
Ya ku mutane, ku bauta wa Ubangijinku Wanda Ya halicce ku, da waxanda suka gabace ku, don ku samu taqawa
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ عَلَيۡكُمۡ أَنفُسَكُمۡۖ لَا يَضُرُّكُم مَّن ضَلَّ إِذَا ٱهۡتَدَيۡتُمۡۚ إِلَى ٱللَّهِ مَرۡجِعُكُمۡ جَمِيعٗا فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi ta kanku; wanda ya vata, ba zai cutar da ku ba idan har ku kun shiryu. Zuwa ga Allah ne makomarku take gaba xaya, sannan kuma zai ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa
قُلۡ أَغَيۡرَ ٱللَّهِ أَبۡغِي رَبّٗا وَهُوَ رَبُّ كُلِّ شَيۡءٖۚ وَلَا تَكۡسِبُ كُلُّ نَفۡسٍ إِلَّا عَلَيۡهَاۚ وَلَا تَزِرُ وَازِرَةٞ وِزۡرَ أُخۡرَىٰۚ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّكُم مَّرۡجِعُكُمۡ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ فِيهِ تَخۡتَلِفُونَ
Ka ce: “Yanzu wanin Allah zan riqa a matsayin ubangiji, alhalin kuwa Shi ne Ubangijin komai? Kuma ba wani rai da zai aikata wani abu face sai don kansa. Kuma ba wani rai da zai xauki laifin wani rai. Sannan kuma zuwa ga Ubangijinku ne makomarku take, sai Ya ba ku labarin abin da kuka kasance kuna savani a game da shi
يَٰبَنِيٓ ءَادَمَ لَا يَفۡتِنَنَّكُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ كَمَآ أَخۡرَجَ أَبَوَيۡكُم مِّنَ ٱلۡجَنَّةِ يَنزِعُ عَنۡهُمَا لِبَاسَهُمَا لِيُرِيَهُمَا سَوۡءَٰتِهِمَآۚ إِنَّهُۥ يَرَىٰكُمۡ هُوَ وَقَبِيلُهُۥ مِنۡ حَيۡثُ لَا تَرَوۡنَهُمۡۗ إِنَّا جَعَلۡنَا ٱلشَّيَٰطِينَ أَوۡلِيَآءَ لِلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ
Ya ku ‘yan’adam, kada Shaixan ya fitine ku kamar yadda ya fitar da iyayenku daga cikin Aljanna, yana mai cire musu tufafinsu don ya nuna musu tsiraicin junansu. Lalle shi yana ganin ku, shi da jama’arsa ta inda ku ba kwa ganin su. Lalle Mu Mun sanya shaixanu su zamo masoya ga waxanda ba sa yin imani
قُلۡ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنِّي رَسُولُ ٱللَّهِ إِلَيۡكُمۡ جَمِيعًا ٱلَّذِي لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۖ فَـَٔامِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِ ٱلنَّبِيِّ ٱلۡأُمِّيِّ ٱلَّذِي يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَكَلِمَٰتِهِۦ وَٱتَّبِعُوهُ لَعَلَّكُمۡ تَهۡتَدُونَ
Ka ce: “Ya ku mutane, lalle ni Manzon Allah ne zuwa gare ku gaba xaya, wanda Yake da mallakar sammai da qasa, babu abin bauta wa da gaskiya sai Shi; Shi ne Yake rayawa, kuma Shi Yake kashewa; don haka ku yi imani da Allah da Manzonsa Annabi Ummiyyi, wanda yake yin imani da Allah da kalmominsa, kuma ku bi shi don ku zama shiryayyu.”
ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ لَمۡ يَكُ مُغَيِّرٗا نِّعۡمَةً أَنۡعَمَهَا عَلَىٰ قَوۡمٍ حَتَّىٰ يُغَيِّرُواْ مَا بِأَنفُسِهِمۡ وَأَنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٞ
Wannan (kuwa) saboda Allah bai kasance Mai canza wata ni’ima da Ya yi wa wasu mutane ba har sai sun canja halayensu, lalle Allah kuma Mai ji ne Masani
قُلۡ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ قَدۡ جَآءَكُمُ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّكُمۡۖ فَمَنِ ٱهۡتَدَىٰ فَإِنَّمَا يَهۡتَدِي لِنَفۡسِهِۦۖ وَمَن ضَلَّ فَإِنَّمَا يَضِلُّ عَلَيۡهَاۖ وَمَآ أَنَا۠ عَلَيۡكُم بِوَكِيلٖ
Ka ce: “Ya ku mutane, haqiqa gaskiya ta zo muku daga Ubangijinku; duk wanda ya shiriya to ya shiriya ne don kansa; wanda kuma ya vace to lalle ya vace don kansa ne; ni kuwa ba wakili ne a kanku ba.”
لَهُۥ مُعَقِّبَٰتٞ مِّنۢ بَيۡنِ يَدَيۡهِ وَمِنۡ خَلۡفِهِۦ يَحۡفَظُونَهُۥ مِنۡ أَمۡرِ ٱللَّهِۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُغَيِّرُ مَا بِقَوۡمٍ حَتَّىٰ يُغَيِّرُواْ مَا بِأَنفُسِهِمۡۗ وَإِذَآ أَرَادَ ٱللَّهُ بِقَوۡمٖ سُوٓءٗا فَلَا مَرَدَّ لَهُۥۚ وَمَا لَهُم مِّن دُونِهِۦ مِن وَالٍ
(Kowanensu) yana da (mala’iku) masu take masa baya a gabansa da kuma bayansa suna kiyaye shi da umarnin Allah. Lalle Allah ba Ya canja abin da mutane suke ciki har sai sun canja halayensu. Idan kuma Allah Ya yi nufin wata azaba ga mutane, to ba mai juyar da ita, ba su kuwa da wani mai jivintar su wanda ba Shi ba
۞إِنَّ ٱللَّهَ يَأۡمُرُ بِٱلۡعَدۡلِ وَٱلۡإِحۡسَٰنِ وَإِيتَآيِٕ ذِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَيَنۡهَىٰ عَنِ ٱلۡفَحۡشَآءِ وَٱلۡمُنكَرِ وَٱلۡبَغۡيِۚ يَعِظُكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَذَكَّرُونَ
Lalle Allah Yana umarni da yin adalci da kyautatawa da kuma bai wa makusanta (taimako), Yana kuma hana alfasha da mummunan aiki da zalunci. Yana gargaxin ku don ku wa’azantu
۞وَقَضَىٰ رَبُّكَ أَلَّا تَعۡبُدُوٓاْ إِلَّآ إِيَّاهُ وَبِٱلۡوَٰلِدَيۡنِ إِحۡسَٰنًاۚ إِمَّا يَبۡلُغَنَّ عِندَكَ ٱلۡكِبَرَ أَحَدُهُمَآ أَوۡ كِلَاهُمَا فَلَا تَقُل لَّهُمَآ أُفّٖ وَلَا تَنۡهَرۡهُمَا وَقُل لَّهُمَا قَوۡلٗا كَرِيمٗا
Ubangijinka kuwa Ya hukunta cewa, kada ku bauta wa (wani) sai Shi kaxai, kuma ku kyautatawa iyaye. Ko dai ya zamanto xayansu ne ya manyanta tare da kai, ko kuma dukkansu, to kada ka nuna qosawarka da su, kada kuma ka daka musu tsawa; ka yi musu magana ta girmamawa
وَلَا تَقۡرَبُواْ مَالَ ٱلۡيَتِيمِ إِلَّا بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُ حَتَّىٰ يَبۡلُغَ أَشُدَّهُۥۚ وَأَوۡفُواْ بِٱلۡعَهۡدِۖ إِنَّ ٱلۡعَهۡدَ كَانَ مَسۡـُٔولٗا
Kuma kada ku kusanci dukiyar maraya sai dai ta (hanya) wadda take mafi kyau[1], har sai ya kawo qarfi. Kuma ku cika alqawari; lalle alqawari ya kasance abin tambaya ne (a lahira)
1- Watau ta hanyar yi masa kasuwanci da ita.
وَأَوۡفُواْ ٱلۡكَيۡلَ إِذَا كِلۡتُمۡ وَزِنُواْ بِٱلۡقِسۡطَاسِ ٱلۡمُسۡتَقِيمِۚ ذَٰلِكَ خَيۡرٞ وَأَحۡسَنُ تَأۡوِيلٗا
Kuma ku cika mudu idan kuka yi awo, kuma ku auna nauyi da ma’auni na adalci. Wannan (shi ya fi) alheri ya kuma fi kyakkyawan qarshe
وَلَا تَقۡفُ مَا لَيۡسَ لَكَ بِهِۦ عِلۡمٌۚ إِنَّ ٱلسَّمۡعَ وَٱلۡبَصَرَ وَٱلۡفُؤَادَ كُلُّ أُوْلَـٰٓئِكَ كَانَ عَنۡهُ مَسۡـُٔولٗا
Kada kuma ka dinga bibiyar abin da ba ka da ilimi a kansa. Lalle ji da gani da kuma tunani duk waxannan sun zama abin tambaya ne game da su
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱتَّقُواْ رَبَّكُمۡۚ إِنَّ زَلۡزَلَةَ ٱلسَّاعَةِ شَيۡءٌ عَظِيمٞ
Ya ku mutane, ku kiyaye dokokin Ubangijinku. Lalle girgizar (ranar) alqiyama abu ne mai girma
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱتَّقُواْ رَبَّكُمۡ وَٱخۡشَوۡاْ يَوۡمٗا لَّا يَجۡزِي وَالِدٌ عَن وَلَدِهِۦ وَلَا مَوۡلُودٌ هُوَ جَازٍ عَن وَالِدِهِۦ شَيۡـًٔاۚ إِنَّ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٞۖ فَلَا تَغُرَّنَّكُمُ ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا وَلَا يَغُرَّنَّكُم بِٱللَّهِ ٱلۡغَرُورُ
Ya ku mutane, ku kiyaye dokokin Ubangijinku, kuma ku ji tsoron ranar da mahaifi ba zai amfana wa xansa komai ba, kuma xan shi ma ba zai amfana wa mahaifinsa komai ba. Lalle alqawarin Allah gaskiya ne; to kada rayuwar duniya ta ruxe ku, kuma (Shaixan) mai ruxarwa kada ya ruxe ku game da Allah
وَلَا تَزِرُ وَازِرَةٞ وِزۡرَ أُخۡرَىٰۚ وَإِن تَدۡعُ مُثۡقَلَةٌ إِلَىٰ حِمۡلِهَا لَا يُحۡمَلۡ مِنۡهُ شَيۡءٞ وَلَوۡ كَانَ ذَا قُرۡبَىٰٓۗ إِنَّمَا تُنذِرُ ٱلَّذِينَ يَخۡشَوۡنَ رَبَّهُم بِٱلۡغَيۡبِ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَۚ وَمَن تَزَكَّىٰ فَإِنَّمَا يَتَزَكَّىٰ لِنَفۡسِهِۦۚ وَإِلَى ٱللَّهِ ٱلۡمَصِيرُ
Kuma wani mai xaukar nauyi ba ya xaukan laifin wani. Idan kuma wani mai nannauyan zunubi ya yi kira zuwa xauke nauyin nasa, ba za a xauke masa komai daga nauyin ba, ko da kuwa xan’uwa ne makusanci. Kai dai kana mai gargaxi ne kawai ga waxanda suke tsoron Ubangijinsu ba tare da ganin Sa ba, suka kuma tsai da salla. Wanda kuwa ya tsarkaka, to ya tsarkaka ne don kansa. Makoma kuma na ga Allah Shi kaxai
إِن تَكۡفُرُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَنِيٌّ عَنكُمۡۖ وَلَا يَرۡضَىٰ لِعِبَادِهِ ٱلۡكُفۡرَۖ وَإِن تَشۡكُرُواْ يَرۡضَهُ لَكُمۡۗ وَلَا تَزِرُ وَازِرَةٞ وِزۡرَ أُخۡرَىٰۚ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّكُم مَّرۡجِعُكُمۡ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَۚ إِنَّهُۥ عَلِيمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ
Idan kun kafirce, to lalle Allah Mawadaci ne ga barin ku, ba Ya kuma yarda da kafirci daga bayinsa. Idan kuwa kuka gode Zai yarda da godiyar taku. Kuma wani rai ba ya xaukar laifin wani. Sannan zuwa ga Ubangijinku ne makomarku take, sannan Ya ba ku labarin irin abubuwan da kuka kasance kuna aikatawa. Lalle Shi Masanin abubuwan da suke cikin qiraza ne
وَمَا خَلَقۡتُ ٱلۡجِنَّ وَٱلۡإِنسَ إِلَّا لِيَعۡبُدُونِ
Ban halicci aljanu da mutane ba sai don su bauta min
أَلَّا تَزِرُ وَازِرَةٞ وِزۡرَ أُخۡرَىٰ
Cewa: “Wani rai ba ya xaukar nauyin laifin wani
وَأَن لَّيۡسَ لِلۡإِنسَٰنِ إِلَّا مَا سَعَىٰ
“Kuma mutum bai mallaki wani sakamako ba sai na abin da ya aikata
وَأَنَّ سَعۡيَهُۥ سَوۡفَ يُرَىٰ
“Kuma lalle aikin nasa ba da daxewa ba za a gan shi
ثُمَّ يُجۡزَىٰهُ ٱلۡجَزَآءَ ٱلۡأَوۡفَىٰ
“Sannan a saka masa da cikakken sakamako