Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 28

كَيۡفَ تَكۡفُرُونَ بِٱللَّهِ وَكُنتُمۡ أَمۡوَٰتٗا فَأَحۡيَٰكُمۡۖ ثُمَّ يُمِيتُكُمۡ ثُمَّ يُحۡيِيكُمۡ ثُمَّ إِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ

Ta yaya kuke kafirce wa Allah alhalin a da kun kasance matattu, sannan Ya raya ku, sannan zai kuma mayar da ku matattu sannan Ya raya ku (a karo na biyu) sannan zuwa gare Shi ake mayar da ku?



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 156

ٱلَّذِينَ إِذَآ أَصَٰبَتۡهُم مُّصِيبَةٞ قَالُوٓاْ إِنَّا لِلَّهِ وَإِنَّآ إِلَيۡهِ رَٰجِعُونَ

(Su ne) waxanda idan wata musiba ta same su sai su ce: “Lalle mu na Allah ne, kuma lalle mu gare Shi muke komawa.”



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 245

مَّن ذَا ٱلَّذِي يُقۡرِضُ ٱللَّهَ قَرۡضًا حَسَنٗا فَيُضَٰعِفَهُۥ لَهُۥٓ أَضۡعَافٗا كَثِيرَةٗۚ وَٱللَّهُ يَقۡبِضُ وَيَبۡصُۜطُ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ

Wane ne zai ba wa Allah kyakkyawan rance, sai Ya ninka masa shi ninki mai yawa? Kuma Allah ne Yake kame (dukiya), Yake kuma shimfixa ta, kuma zuwa gare Shi za a mayar da ku



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 281

وَٱتَّقُواْ يَوۡمٗا تُرۡجَعُونَ فِيهِ إِلَى ٱللَّهِۖ ثُمَّ تُوَفَّىٰ كُلُّ نَفۡسٖ مَّا كَسَبَتۡ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ

Kuma ku kiyayi wani yini da za a mayar da ku zuwa ga Allah a cikinsa, sannan kowane rai za a cika masa abin da ya aiwatar na aiki, kuma su ba za a zalunce su ba



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 105

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ عَلَيۡكُمۡ أَنفُسَكُمۡۖ لَا يَضُرُّكُم مَّن ضَلَّ إِذَا ٱهۡتَدَيۡتُمۡۚ إِلَى ٱللَّهِ مَرۡجِعُكُمۡ جَمِيعٗا فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi ta kanku; wanda ya vata, ba zai cutar da ku ba idan har ku kun shiryu. Zuwa ga Allah ne makomarku take gaba xaya, sannan kuma zai ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 36

۞إِنَّمَا يَسۡتَجِيبُ ٱلَّذِينَ يَسۡمَعُونَۘ وَٱلۡمَوۡتَىٰ يَبۡعَثُهُمُ ٱللَّهُ ثُمَّ إِلَيۡهِ يُرۡجَعُونَ

Lalle masu ji su ne kawai suke amsa (kiranka). Matattu kuwa Allah zai tashe su (ranar alqiyama), sannan zuwa gare Shi za a mayar da su



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 60

وَهُوَ ٱلَّذِي يَتَوَفَّىٰكُم بِٱلَّيۡلِ وَيَعۡلَمُ مَا جَرَحۡتُم بِٱلنَّهَارِ ثُمَّ يَبۡعَثُكُمۡ فِيهِ لِيُقۡضَىٰٓ أَجَلٞ مُّسَمّٗىۖ ثُمَّ إِلَيۡهِ مَرۡجِعُكُمۡ ثُمَّ يُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

“Kuma Shi ne Yake karvar rayukanku da daddare[1], kuma Ya san abin da kuka aikata da rana, sannan Ya tayar da ku a cikinta (ranar), har zuwa lokacin da zai zartar da wani ajali sananne, sannan zuwa gare Shi ne makomarku take, sannan zai ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa


1- Watau lokacin barcinku; ya riqe ran da ya hukunta masa mutuwa, ya sako wanda lokacin mutuwarsa bai zo ba. duba Suratuz Zumar aya ta 42.


Capítulo: Suratul An’am

Verso : 61

وَهُوَ ٱلۡقَاهِرُ فَوۡقَ عِبَادِهِۦۖ وَيُرۡسِلُ عَلَيۡكُمۡ حَفَظَةً حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءَ أَحَدَكُمُ ٱلۡمَوۡتُ تَوَفَّتۡهُ رُسُلُنَا وَهُمۡ لَا يُفَرِّطُونَ

“Kuma Shi ne wanda Yake da iko a kan bayinsa, kuma Yana aiko muku masu tsaro, har zuwa lokacin da mutuwa za ta zo wa xayanku, sai manzanninmu su karvi ransa, kuma su ba sa yin sakaci



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 62

ثُمَّ رُدُّوٓاْ إِلَى ٱللَّهِ مَوۡلَىٰهُمُ ٱلۡحَقِّۚ أَلَا لَهُ ٱلۡحُكۡمُ وَهُوَ أَسۡرَعُ ٱلۡحَٰسِبِينَ

“Sannan sai a mayar da su zuwa ga Allah Majivincin lamarinsu na gaskiya. Ku saurara, dukkan hukunci nasa ne, kuma Shi ne Mafi gaggawar masu hisabi.”



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 108

وَلَا تَسُبُّواْ ٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ فَيَسُبُّواْ ٱللَّهَ عَدۡوَۢا بِغَيۡرِ عِلۡمٖۗ كَذَٰلِكَ زَيَّنَّا لِكُلِّ أُمَّةٍ عَمَلَهُمۡ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّهِم مَّرۡجِعُهُمۡ فَيُنَبِّئُهُم بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Kuma kada ku zagi waxanda suke bauta wa ba Allah ba, sai su zagi Allah saboda zalunci, ba tare da sanin (girmansa) ba. Kamar haka ne Muka qawata wa kowace al’umma ayyukansu (nagari da munana), sannan zuwa ga Ubangijinsu ne makomarsu take, sai Ya ba su labarin abin da suka kasance suna aikatawa



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 94

يَعۡتَذِرُونَ إِلَيۡكُمۡ إِذَا رَجَعۡتُمۡ إِلَيۡهِمۡۚ قُل لَّا تَعۡتَذِرُواْ لَن نُّؤۡمِنَ لَكُمۡ قَدۡ نَبَّأَنَا ٱللَّهُ مِنۡ أَخۡبَارِكُمۡۚ وَسَيَرَى ٱللَّهُ عَمَلَكُمۡ وَرَسُولُهُۥ ثُمَّ تُرَدُّونَ إِلَىٰ عَٰلِمِ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

Za su kawo muku uzurinsu idan kuka dawo musu. Ka ce: “Kada ku kawo wani uziri, mu ba za mu gaskata ku ba har abada, haqiqa Allah Ya faxa mana labarinku. Allah kuwa zai ga ayyukanku Shi da Manzonsa, sannan a komar da ku zuwa ga Masanin abin da yake voye da na sarari, sai Ya ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa.”



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 105

وَقُلِ ٱعۡمَلُواْ فَسَيَرَى ٱللَّهُ عَمَلَكُمۡ وَرَسُولُهُۥ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَۖ وَسَتُرَدُّونَ إِلَىٰ عَٰلِمِ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

Ka kuma ce: “Ku yi aiki, Allah ne zai ga aikinku shi da Manzonsa da kuma muminai, kuma za a mayar da ku zuwa ga Masanin abin da yake voye da na sarari, sannan Ya ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa



Capítulo: Suratu Yunus

Verso : 4

إِلَيۡهِ مَرۡجِعُكُمۡ جَمِيعٗاۖ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقًّاۚ إِنَّهُۥ يَبۡدَؤُاْ ٱلۡخَلۡقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥ لِيَجۡزِيَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ بِٱلۡقِسۡطِۚ وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَهُمۡ شَرَابٞ مِّنۡ حَمِيمٖ وَعَذَابٌ أَلِيمُۢ بِمَا كَانُواْ يَكۡفُرُونَ

Zuwa gare Shi ne makomarku take gaba xaya; alqawarin Allah ne da gaske. Lalle Shi ne Yake farar da halitta sannan Ya maido da ita (bayan mutuwa) don Ya saka wa waxanda suka yi imani suka kuma yi aiki nagari da adalci. Waxanda suka kafirce kuwa suna da abin sha mai tsananin quna da kuma azaba mai raxaxi saboda kafircewa da suke yi



Capítulo: Suratu Yunus

Verso : 23

فَلَمَّآ أَنجَىٰهُمۡ إِذَا هُمۡ يَبۡغُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّۗ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنَّمَا بَغۡيُكُمۡ عَلَىٰٓ أَنفُسِكُمۖ مَّتَٰعَ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ ثُمَّ إِلَيۡنَا مَرۡجِعُكُمۡ فَنُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

To lokacin da Ya tserar da su sai ga su suna varna a bayan qasa ba da gaskiya ba. Ya ku mutane, haqiqa (sakamakon) varnarku a kanku kawai yake; ku xan ji daxin rayuwar duniya; sannan (daga qarshe) zuwa gare Mu ne makomarku take, sannan mu ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa



Capítulo: Suratu Yunus

Verso : 30

هُنَالِكَ تَبۡلُواْ كُلُّ نَفۡسٖ مَّآ أَسۡلَفَتۡۚ وَرُدُّوٓاْ إِلَى ٱللَّهِ مَوۡلَىٰهُمُ ٱلۡحَقِّۖ وَضَلَّ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَفۡتَرُونَ

A can ne kowane rai zai samu sakamakon abin da ya gabatar (a duniya). An kuma mayar da su zuwa ga Allah Majivincinsu na gaskiya; abin da kuma suka kasance suna qirqira ya vace musu



Capítulo: Suratu Yunus

Verso : 45

وَيَوۡمَ يَحۡشُرُهُمۡ كَأَن لَّمۡ يَلۡبَثُوٓاْ إِلَّا سَاعَةٗ مِّنَ ٱلنَّهَارِ يَتَعَارَفُونَ بَيۡنَهُمۡۚ قَدۡ خَسِرَ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِلِقَآءِ ٱللَّهِ وَمَا كَانُواْ مُهۡتَدِينَ

Ranar da zai tattara su kuwa (za su ga) kamar ba su zauna ba sai wani xan lokaci na rana da suke gane junansu (a cikinsa). Haqiqa waxanda suka qaryata gamuwa da Allah sun tave, ba su kuma zamanto shiryayyu ba



Capítulo: Suratu Yunus

Verso : 46

وَإِمَّا نُرِيَنَّكَ بَعۡضَ ٱلَّذِي نَعِدُهُمۡ أَوۡ نَتَوَفَّيَنَّكَ فَإِلَيۡنَا مَرۡجِعُهُمۡ ثُمَّ ٱللَّهُ شَهِيدٌ عَلَىٰ مَا يَفۡعَلُونَ

Ko dai Mu nuna maka sashin abin da Muke musu alkawarinsa ko kuma Mu karvi ranka, to makomarsu dai gare Mu take, sannan Allah Yana sane da abin da suke aikatawa



Capítulo: Suratu Yunus

Verso : 56

هُوَ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ

Shi ne Yake rayawa Yake kuma kashewa, kuma wurinsa za a mai da ku



Capítulo: Suratu Hud

Verso : 4

إِلَى ٱللَّهِ مَرۡجِعُكُمۡۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ

“Zuwa ga Allah ne makomarku; Shi kuwa Mai iko ne a kan komai.”



Capítulo: Suratul Kahf 

Verso : 87

قَالَ أَمَّا مَن ظَلَمَ فَسَوۡفَ نُعَذِّبُهُۥ ثُمَّ يُرَدُّ إِلَىٰ رَبِّهِۦ فَيُعَذِّبُهُۥ عَذَابٗا نُّكۡرٗا

(Zulqarnaini) ya ce: “Amma wanda ya yi zalunci to za mu azabtar da shi, sannan a mayar da shi zuwa ga Ubangijinsa (shi ma) Ya yi masa mummunar azaba



Capítulo: Suratul Anbiya

Verso : 93

وَتَقَطَّعُوٓاْ أَمۡرَهُم بَيۡنَهُمۡۖ كُلٌّ إِلَيۡنَا رَٰجِعُونَ

Sannan sai suka rarraba al’amarinsu (na addini) a tsakaninsu; dukkaninsu dai masu komowa ne zuwa gare Mu



Capítulo: Suratul Qasas

Verso : 70

وَهُوَ ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ لَهُ ٱلۡحَمۡدُ فِي ٱلۡأُولَىٰ وَٱلۡأٓخِرَةِۖ وَلَهُ ٱلۡحُكۡمُ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ

Kuma Shi ne Allah, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi; yabo ya tabbata a gare Shi a duniya da lahira; hukunci kuma nasa ne, kuma zuwa gare Shi ne kawai za a mayar da ku



Capítulo: Suratul Qasas

Verso : 88

وَلَا تَدۡعُ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَۘ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۚ كُلُّ شَيۡءٍ هَالِكٌ إِلَّا وَجۡهَهُۥۚ لَهُ ٱلۡحُكۡمُ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ

Kuma kada ka bauta wa wani abin bauta daban tare da Allah. Babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi. Kowane abu mai halaka ne sai Fuskarsa kawai. Hukunci (duk) nasa ne, zuwa gare Shi kuma za a mayar da ku



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 8

وَوَصَّيۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ بِوَٰلِدَيۡهِ حُسۡنٗاۖ وَإِن جَٰهَدَاكَ لِتُشۡرِكَ بِي مَا لَيۡسَ لَكَ بِهِۦ عِلۡمٞ فَلَا تُطِعۡهُمَآۚ إِلَيَّ مَرۡجِعُكُمۡ فَأُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

Kuma Mun yi wa mutum wasiyya da kyautata wa iyayensa; idan kuma suka yaqe ka kan ka yi shirka da Ni game da abin da ba ka da sani a kansa, to kada ka bi su. Wurina ne makomarku take kawai, sannan zan ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 17

إِنَّمَا تَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَوۡثَٰنٗا وَتَخۡلُقُونَ إِفۡكًاۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ تَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ لَا يَمۡلِكُونَ لَكُمۡ رِزۡقٗا فَٱبۡتَغُواْ عِندَ ٱللَّهِ ٱلرِّزۡقَ وَٱعۡبُدُوهُ وَٱشۡكُرُواْ لَهُۥٓۖ إِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ

Lalle abin da kuke bauta wa ba Allah ba gumaka ne kawai, kuna kuma qirqirar qarya ne[1]. Lalle waxanda kuke bauta wa ba Allah ba, ba su mallaki wani arziki ba gare ku, sai ku nemi arziki a wurin Allah, kuma ku bauta masa, ku kuma gode masa; gare Shi ne kawai za a mayar da ku


1- Domin su ne suke sassaqa su da hannayensu suke kuma sanya musu sunaye sannan su bauta musu.


Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 58

وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ لَنُبَوِّئَنَّهُم مِّنَ ٱلۡجَنَّةِ غُرَفٗا تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ نِعۡمَ أَجۡرُ ٱلۡعَٰمِلِينَ

Waxanda kuma suka yi imani suka kuma yi aiki nagari, lallai za Mu zaunar da su cikin manya-manyan gidaje a Aljanna (waxanda) qoramu za su riqa gudana ta qarqashinsu suna madawwama a cikinsu. Madalla da ladan masu aiki (nagari)



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 11

ٱللَّهُ يَبۡدَؤُاْ ٱلۡخَلۡقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥ ثُمَّ إِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ

Allah ne Yake farar halitta sannan Ya dawo da ita (bayan mutuwa), sannan kuma gare Shi za a komar da ku



Capítulo: Suratu Luqman

Verso : 15

وَإِن جَٰهَدَاكَ عَلَىٰٓ أَن تُشۡرِكَ بِي مَا لَيۡسَ لَكَ بِهِۦ عِلۡمٞ فَلَا تُطِعۡهُمَاۖ وَصَاحِبۡهُمَا فِي ٱلدُّنۡيَا مَعۡرُوفٗاۖ وَٱتَّبِعۡ سَبِيلَ مَنۡ أَنَابَ إِلَيَّۚ ثُمَّ إِلَيَّ مَرۡجِعُكُمۡ فَأُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

Idan kuma suka matsa maka kan ka yi tarayya da Ni game da abin da ba ka da wani sani a kansa, to kada ka bi su; kuma ka yi zaman duniya da su ta kyakkyawar hanya; ka kuma bi hanyar wanda ya mayar da al’amarinsa gare Ni. Sannan kuma zuwa gare Ni ne kawai makomarku, sai in ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa



Capítulo: Suratus Sajda

Verso : 11

۞قُلۡ يَتَوَفَّىٰكُم مَّلَكُ ٱلۡمَوۡتِ ٱلَّذِي وُكِّلَ بِكُمۡ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّكُمۡ تُرۡجَعُونَ

Ka ce (da su): “Mala’ikan mutuwa ne wanda aka wakilta muku zai karvi ranku sannan kuma ga Ubangijinku za a komar da ku



Capítulo: Suratu Yasin

Verso : 83

فَسُبۡحَٰنَ ٱلَّذِي بِيَدِهِۦ مَلَكُوتُ كُلِّ شَيۡءٖ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ

To tsarki ya tabbata ga wanda mulkin kowane abu yake a hannunsa, kuma wurinsa ne kawai za a komar da ku