Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 253

۞تِلۡكَ ٱلرُّسُلُ فَضَّلۡنَا بَعۡضَهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖۘ مِّنۡهُم مَّن كَلَّمَ ٱللَّهُۖ وَرَفَعَ بَعۡضَهُمۡ دَرَجَٰتٖۚ وَءَاتَيۡنَا عِيسَى ٱبۡنَ مَرۡيَمَ ٱلۡبَيِّنَٰتِ وَأَيَّدۡنَٰهُ بِرُوحِ ٱلۡقُدُسِۗ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ مَا ٱقۡتَتَلَ ٱلَّذِينَ مِنۢ بَعۡدِهِم مِّنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَتۡهُمُ ٱلۡبَيِّنَٰتُ وَلَٰكِنِ ٱخۡتَلَفُواْ فَمِنۡهُم مَّنۡ ءَامَنَ وَمِنۡهُم مَّن كَفَرَۚ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ مَا ٱقۡتَتَلُواْ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يَفۡعَلُ مَا يُرِيدُ

Waxannan manzanni, Mun fifita sashinsu a kan sashi. Cikinsu akwai wanda Allah Ya yi magana da shi, kuma Ya xaukaka wasunsu da darajoji. Kuma Mun bai wa Isa xan Maryam hujjoji bayyanannu, kuma Mun qarfafe shi da Ruhi mai tsarki. Da kuma Allah Ya ga dama da waxanda suka zo bayansu ba su yaqi juna ba bayan hujjoji bayanannu sun zo musu, sai dai kuma sun yi savani; cikinsu akwai wanda ya yi imani, kuma cikinsu akwai wanda ya kafirce, kuma da Allah Ya ga dama da ba su yaqi juna ba, sai dai Allah Yana aikata abin da Yake nufi



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 64

وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن رَّسُولٍ إِلَّا لِيُطَاعَ بِإِذۡنِ ٱللَّهِۚ وَلَوۡ أَنَّهُمۡ إِذ ظَّلَمُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ جَآءُوكَ فَٱسۡتَغۡفَرُواْ ٱللَّهَ وَٱسۡتَغۡفَرَ لَهُمُ ٱلرَّسُولُ لَوَجَدُواْ ٱللَّهَ تَوَّابٗا رَّحِيمٗا

Kuma ba Mu tava aiko wani manzo ba, face sai don a yi masa xa’a da izinin Allah. Kuma da a ce lokacin da suka zalunci kawunansu sun zo maka, sun nemi Allah Ya gafarta musu, sannan Manzo ya roqa musu gafara, to tabbas da sun sami Allah Yana Mai yawan karvar tuba, Mai jin qai



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 163

۞إِنَّآ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ كَمَآ أَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ نُوحٖ وَٱلنَّبِيِّـۧنَ مِنۢ بَعۡدِهِۦۚ وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰٓ إِبۡرَٰهِيمَ وَإِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ وَٱلۡأَسۡبَاطِ وَعِيسَىٰ وَأَيُّوبَ وَيُونُسَ وَهَٰرُونَ وَسُلَيۡمَٰنَۚ وَءَاتَيۡنَا دَاوُۥدَ زَبُورٗا

Lalle Mun yi maka wahayi irin wahayin da Muka yi wa Nuhu da kuma annabawan da suka biyo bayansa, kuma Mun yi wahayi ga Ibrahimu da Isma’ila da Ishaqa da Ya’aqubu da kuma jikokin (Ya’aqubu) da Isa da Ayyuba da Yunusa da Haruna da Sulaimanu; kuma Muka bai wa Dawuda littafin Zabura



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 164

وَرُسُلٗا قَدۡ قَصَصۡنَٰهُمۡ عَلَيۡكَ مِن قَبۡلُ وَرُسُلٗا لَّمۡ نَقۡصُصۡهُمۡ عَلَيۡكَۚ وَكَلَّمَ ٱللَّهُ مُوسَىٰ تَكۡلِيمٗا

(Muka) kuma aiko manzanni waxanda Muka ba ka labarinsu tun da farko, da waxansu manzannin daban da ba Mu ba ka labarinsu ba; kuma Allah Ya yi magana da Musa kai-tsaye



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 165

رُّسُلٗا مُّبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ لِئَلَّا يَكُونَ لِلنَّاسِ عَلَى ٱللَّهِ حُجَّةُۢ بَعۡدَ ٱلرُّسُلِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَزِيزًا حَكِيمٗا

Manzanni ne masu albishir kuma masu gargaxi, domin kada mutane su sami wata hujja a wurin Allah bayan aiko manzannin. Kuma Allah Ya kasance Mabuwayi ne, Mai hikima



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 75

مَّا ٱلۡمَسِيحُ ٱبۡنُ مَرۡيَمَ إِلَّا رَسُولٞ قَدۡ خَلَتۡ مِن قَبۡلِهِ ٱلرُّسُلُ وَأُمُّهُۥ صِدِّيقَةٞۖ كَانَا يَأۡكُلَانِ ٱلطَّعَامَۗ ٱنظُرۡ كَيۡفَ نُبَيِّنُ لَهُمُ ٱلۡأٓيَٰتِ ثُمَّ ٱنظُرۡ أَنَّىٰ يُؤۡفَكُونَ

Shi fa Almasihu xan Maryamu bai zamo ba face Manzo, wanda haqiqa manzanni sun shuxe kafinsa. Mahaifiyarsa kuma Siddiqa ce; shi da ita sun kasance suna cin abinci. Duba ka ga yadda Muke bayyana musu ayoyi, sannan ka sake dubawa, ta yaya ake kautar da su?



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 34

وَلَقَدۡ كُذِّبَتۡ رُسُلٞ مِّن قَبۡلِكَ فَصَبَرُواْ عَلَىٰ مَا كُذِّبُواْ وَأُوذُواْ حَتَّىٰٓ أَتَىٰهُمۡ نَصۡرُنَاۚ وَلَا مُبَدِّلَ لِكَلِمَٰتِ ٱللَّهِۚ وَلَقَدۡ جَآءَكَ مِن نَّبَإِيْ ٱلۡمُرۡسَلِينَ

Kuma lalle haqiqa an qaryata waxansu manzanni a gabaninka, sai suka yi haquri a kan qaryata su da aka yi, kuma an cutar da su, har sai da taimakonmu ya zo musu. Kuma babu wanda ya isa ya musanya kalmomin Allah. Kuma lalle haqiqa wani sashi na labarin manzanni ya zo maka



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 48

وَمَا نُرۡسِلُ ٱلۡمُرۡسَلِينَ إِلَّا مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَۖ فَمَنۡ ءَامَنَ وَأَصۡلَحَ فَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ

Kuma ba ma aiko da manzanni sai suna masu bushara masu gargaxi; sannan duk wanda ya yi imani kuma ya kyautata aiki, to babu tsoro a tattare da su, kuma ba za su yi baqin ciki ba



Capítulo: Suratu Yunus

Verso : 47

وَلِكُلِّ أُمَّةٖ رَّسُولٞۖ فَإِذَا جَآءَ رَسُولُهُمۡ قُضِيَ بَيۡنَهُم بِٱلۡقِسۡطِ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ

Kowacce al’umma kuma tana da manzo. To idan manzonsu ya zo (suka qaryata shi) to sai a yi hukunci a tsakaninsu da adalci, su kuma ba za a zalunce su ba



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 109

وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ إِلَّا رِجَالٗا نُّوحِيٓ إِلَيۡهِم مِّنۡ أَهۡلِ ٱلۡقُرَىٰٓۗ أَفَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۗ وَلَدَارُ ٱلۡأٓخِرَةِ خَيۡرٞ لِّلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ

Ba Mu kuma aiko (manzanni) a gabaninka ba sai maza ‘yan birni waxanda Muke yi wa wahayi. Me ya sa (kafirai) ba za su yi tafiya ba a bayan qasa don su ga yadda qarshen waxanda suka rigaye su ya kasance? Lalle kuwa gidan lahira shi ya fi ga waxanda suke kiyaye dokokin (Allah). Shin ba za ku hankalta ba?



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 110

حَتَّىٰٓ إِذَا ٱسۡتَيۡـَٔسَ ٱلرُّسُلُ وَظَنُّوٓاْ أَنَّهُمۡ قَدۡ كُذِبُواْ جَآءَهُمۡ نَصۡرُنَا فَنُجِّيَ مَن نَّشَآءُۖ وَلَا يُرَدُّ بَأۡسُنَا عَنِ ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡمُجۡرِمِينَ

Har yayin da manzanni suka xebe qauna (da imanin mutanensu), su kuma (kafiran) suka yi zaton an faxa musu qarya ne (game da zuwan azabar Allah) sai taimakonmu ya zo musu, sai Muka tserar da wanda Muka ga dama; ba kuwa za a kawar da azabarmu daga mutane masu laifi ba



Capítulo: Suratu Ibrahim

Verso : 4

وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن رَّسُولٍ إِلَّا بِلِسَانِ قَوۡمِهِۦ لِيُبَيِّنَ لَهُمۡۖ فَيُضِلُّ ٱللَّهُ مَن يَشَآءُ وَيَهۡدِي مَن يَشَآءُۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

Ba Mu tava aiko wani manzo ba kuwa sai da harshen mutanensa don ya yi musu bayani; sannan Allah Yana vatar da wanda ya ga dama, ya kuma shiryar da wanda ya ga dama. Shi ne kuwa Mabuwayi, Mai hikima



Capítulo: Suratu Ibrahim

Verso : 11

قَالَتۡ لَهُمۡ رُسُلُهُمۡ إِن نَّحۡنُ إِلَّا بَشَرٞ مِّثۡلُكُمۡ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يَمُنُّ عَلَىٰ مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦۖ وَمَا كَانَ لَنَآ أَن نَّأۡتِيَكُم بِسُلۡطَٰنٍ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۚ وَعَلَى ٱللَّهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ

Manzanninsu suka ce: “Mu ba kowa ba ne in ban da mutane kamarku, sai dai Allah Yana yin baiwa ga wanda Ya ga dama ne daga bayinsa, kuma ba zai yiwu ba a gare mu mu zo muku da wata hujja sai dai da izinin Allah. Muminai kuwa lalle su dogara ga Allah kawai



Capítulo: Suratul Kahf 

Verso : 56

وَمَا نُرۡسِلُ ٱلۡمُرۡسَلِينَ إِلَّا مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَۚ وَيُجَٰدِلُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِٱلۡبَٰطِلِ لِيُدۡحِضُواْ بِهِ ٱلۡحَقَّۖ وَٱتَّخَذُوٓاْ ءَايَٰتِي وَمَآ أُنذِرُواْ هُزُوٗا

Ba Mu kuma aiko da manzanni ba sai don su zama masu albishir mai gargaxi. Su kuma waxanda suka kafirce sai su dinga jayayya da qarya don su kawar da gaskiya da ita; suka kuma riqi ayoyina da kuma abin da aka yi musu gargaxi da shi a matsayin abin izgili



Capítulo: Suratul Anbiya

Verso : 25

وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ مِن رَّسُولٍ إِلَّا نُوحِيٓ إِلَيۡهِ أَنَّهُۥ لَآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنَا۠ فَٱعۡبُدُونِ

Kuma ba wani manzo da Muka aiko gabaninka face sai Mun yi masa wahayi cewa, babu wani abin bauta da gaskiya sai Ni; to sai ku bauta min[1]


1- Duk manzannin da Allah ya aiko sun zo ne da saqon a bauta wa Allah shi kaxai ba tare da shirka ba.


Capítulo: Suratul Hajji

Verso : 75

ٱللَّهُ يَصۡطَفِي مِنَ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةِ رُسُلٗا وَمِنَ ٱلنَّاسِۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعُۢ بَصِيرٞ

Allah Yana zavar manzanni daga mala’iku kuma daga mutane. Lalle Allah Mai ji ne, Mai gani



Capítulo: Suratul Mu’uminun

Verso : 44

ثُمَّ أَرۡسَلۡنَا رُسُلَنَا تَتۡرَاۖ كُلَّ مَا جَآءَ أُمَّةٗ رَّسُولُهَا كَذَّبُوهُۖ فَأَتۡبَعۡنَا بَعۡضَهُم بَعۡضٗا وَجَعَلۡنَٰهُمۡ أَحَادِيثَۚ فَبُعۡدٗا لِّقَوۡمٖ لَّا يُؤۡمِنُونَ

Sannan Muka aiko manzanninmu suna biye da juna; duk sanda manzon (kowacce) al’umma ya zo musu sai su qaryata shi. Sai Muka hallaka su xaya bayan xaya, Muka kuma mai da su tarihi. To nisanta (daga rahamar Allah) ta tabbata ga mutanen da ba sa yin imani



Capítulo: Suratul Furqan

Verso : 20

وَمَآ أَرۡسَلۡنَا قَبۡلَكَ مِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ إِلَّآ إِنَّهُمۡ لَيَأۡكُلُونَ ٱلطَّعَامَ وَيَمۡشُونَ فِي ٱلۡأَسۡوَاقِۗ وَجَعَلۡنَا بَعۡضَكُمۡ لِبَعۡضٖ فِتۡنَةً أَتَصۡبِرُونَۗ وَكَانَ رَبُّكَ بَصِيرٗا

Kuma ba Mu aiko manzanni ba gabaninka sai cewa lalle suna cin abinci kuma suna tafiya cikin kasuwanni. Mun kuwa sanya wasunku su zama fitina ga wasu. Shin za ku yi haquri? Ubangijinka kuwa Ya kasance Mai gani ne



Capítulo: Suratun Namli

Verso : 10

وَأَلۡقِ عَصَاكَۚ فَلَمَّا رَءَاهَا تَهۡتَزُّ كَأَنَّهَا جَآنّٞ وَلَّىٰ مُدۡبِرٗا وَلَمۡ يُعَقِّبۡۚ يَٰمُوسَىٰ لَا تَخَفۡ إِنِّي لَا يَخَافُ لَدَيَّ ٱلۡمُرۡسَلُونَ

Kuma ka jefar da sandarka. To lokacin da ya gan ta tana jujjuyawa kamar macijiya, sai ya juya da baya a guje bai dawo ba. (Allah ya ce): Ya Musa, kada ka ji tsoro, lalle Ni manzanni ba sa jin tsoro a wurina



Capítulo: Suratu Yasin

Verso : 13

وَٱضۡرِبۡ لَهُم مَّثَلًا أَصۡحَٰبَ ٱلۡقَرۡيَةِ إِذۡ جَآءَهَا ٱلۡمُرۡسَلُونَ

Kuma ka ba su misali da mutanen wata alqarya lokacin da manzannin suka zo mata



Capítulo: Suratu Yasin

Verso : 14

إِذۡ أَرۡسَلۡنَآ إِلَيۡهِمُ ٱثۡنَيۡنِ فَكَذَّبُوهُمَا فَعَزَّزۡنَا بِثَالِثٖ فَقَالُوٓاْ إِنَّآ إِلَيۡكُم مُّرۡسَلُونَ

A yayin da Muka aika musu (manzanni) biyu sai suka qaryata su, sannan Muka qarfafe su da na uku, sai suka ce: “Lalle mu manzanni ne zuwa gare ku.”



Capítulo: Suratu Yasin

Verso : 15

قَالُواْ مَآ أَنتُمۡ إِلَّا بَشَرٞ مِّثۡلُنَا وَمَآ أَنزَلَ ٱلرَّحۡمَٰنُ مِن شَيۡءٍ إِنۡ أَنتُمۡ إِلَّا تَكۡذِبُونَ

Suka ce: “Ku ai ba kowa ba ne face mutane kamarmu, kuma (Allah) Mai rahama bai saukar da komai ba, ku dai ba abin da kuke yi sai qarya.”



Capítulo: Suratu Yasin

Verso : 16

قَالُواْ رَبُّنَا يَعۡلَمُ إِنَّآ إِلَيۡكُمۡ لَمُرۡسَلُونَ

Suka ce: “Ubangijinmu Yana sane da cewa mu lalle tabbas manzanni ne zuwa gare ku



Capítulo: Suratu Yasin

Verso : 17

وَمَا عَلَيۡنَآ إِلَّا ٱلۡبَلَٰغُ ٱلۡمُبِينُ

“Kuma babu wani abu a kanmu sai isar da aike bayyananne.”



Capítulo: Suratu Yasin

Verso : 20

وَجَآءَ مِنۡ أَقۡصَا ٱلۡمَدِينَةِ رَجُلٞ يَسۡعَىٰ قَالَ يَٰقَوۡمِ ٱتَّبِعُواْ ٱلۡمُرۡسَلِينَ

Wani mutum kuma ya zo daga can qarshen gari yana sauri ya ce: “Ya ku mutanena, ku bi waxannan manzannin



Capítulo: Suratu Yasin

Verso : 21

ٱتَّبِعُواْ مَن لَّا يَسۡـَٔلُكُمۡ أَجۡرٗا وَهُم مُّهۡتَدُونَ

“Ku bi waxanda ba sa tambayar ku wani lada, ga su kuma shiryayyu



Capítulo: Suratu Ghafir

Verso : 78

وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا رُسُلٗا مِّن قَبۡلِكَ مِنۡهُم مَّن قَصَصۡنَا عَلَيۡكَ وَمِنۡهُم مَّن لَّمۡ نَقۡصُصۡ عَلَيۡكَۗ وَمَا كَانَ لِرَسُولٍ أَن يَأۡتِيَ بِـَٔايَةٍ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۚ فَإِذَا جَآءَ أَمۡرُ ٱللَّهِ قُضِيَ بِٱلۡحَقِّ وَخَسِرَ هُنَالِكَ ٱلۡمُبۡطِلُونَ

Haqiqa Mun aiko manzanni a gabaninka, daga cikinsu akwai waxanda Muka labarta maka akwai kuma daga cikinsu waxanda ba Mu labarta maka ba. Ba zai yiwu ba ga wani manzo ya zo da wata aya sai da izinin Allah. Sannan idan al’amarin Allah ya zo, to sai a yi hukunci da gaskiya, kuma a nan ne mavarnata za su yi asara



Capítulo: Suratul Hashr

Verso : 6

وَمَآ أَفَآءَ ٱللَّهُ عَلَىٰ رَسُولِهِۦ مِنۡهُمۡ فَمَآ أَوۡجَفۡتُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ خَيۡلٖ وَلَا رِكَابٖ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يُسَلِّطُ رُسُلَهُۥ عَلَىٰ مَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Kuma duk abin da Allah Ya bai wa Manzonsa na wata dukiya tasu (don falalarsa), to ba wani hari kuka kai na dawaki ko raquma[1] ba saboda shi, sai dai kuma Allah Shi ne Yake xora manzanninsa a kan wanda Ya ga dama. Allah kuwa Mai iko ne a kan komai


1- Watau ku sami dukiya ba tare da yaqi ba.