Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 165

وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَتَّخِذُ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَندَادٗا يُحِبُّونَهُمۡ كَحُبِّ ٱللَّهِۖ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَشَدُّ حُبّٗا لِّلَّهِۗ وَلَوۡ يَرَى ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓاْ إِذۡ يَرَوۡنَ ٱلۡعَذَابَ أَنَّ ٱلۡقُوَّةَ لِلَّهِ جَمِيعٗا وَأَنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعَذَابِ

Kuma akwai wasu mutane waxanda suke bauta wa wasu kishiyoyi ba Allah ba; suna son su kamar son Allah; waxanda kuwa suka yi imani sun fi son Allah (fiye da komai). Da a ce waxanda suka yi zalunci za su ga lokacin da suke ido huxu da azaba (to da sun gane) cewa, lalle duk wani qarfi na Allah ne gaba xaya, kuma lalle Allah Mai tsananin azaba ne



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 209

فَإِن زَلَلۡتُم مِّنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَتۡكُمُ ٱلۡبَيِّنَٰتُ فَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٌ

To idan kuka zame bayan hujjoji bayyanannu sun zo muku, to ku sani cewa, lalle Allah Mabuwayi ne, Mai hikima



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 4

مِن قَبۡلُ هُدٗى لِّلنَّاسِ وَأَنزَلَ ٱلۡفُرۡقَانَۗ إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ لَهُمۡ عَذَابٞ شَدِيدٞۗ وَٱللَّهُ عَزِيزٞ ذُو ٱنتِقَامٍ

Tun kafin (Alqur’ani), (don su zama) shiriya ga mutane, kuma Ya saukar da mai rarrabewa (tsakanin qarya da gaskiya). Lalle waxanda suka kafirce wa ayoyin Allah, suna da azaba mai tsanani, kuma Allah Mabuwayi ne, Ma’abocin xaukar fansa



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 139

ٱلَّذِينَ يَتَّخِذُونَ ٱلۡكَٰفِرِينَ أَوۡلِيَآءَ مِن دُونِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَۚ أَيَبۡتَغُونَ عِندَهُمُ ٱلۡعِزَّةَ فَإِنَّ ٱلۡعِزَّةَ لِلَّهِ جَمِيعٗا

Su ne waxanda suke riqar kafirai a matsayin masoya, su qyale muminai. Shin suna neman wata xaukaka ce a wurinsu? To lalle xaukaka gaba xaya ta Allah ce[1]


1- Watau shi ne yake bayar da girma, kuma ga muminai kaxai yake ba da shi, don haka munafukai ba za su same shi ba.


Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 95

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَقۡتُلُواْ ٱلصَّيۡدَ وَأَنتُمۡ حُرُمٞۚ وَمَن قَتَلَهُۥ مِنكُم مُّتَعَمِّدٗا فَجَزَآءٞ مِّثۡلُ مَا قَتَلَ مِنَ ٱلنَّعَمِ يَحۡكُمُ بِهِۦ ذَوَا عَدۡلٖ مِّنكُمۡ هَدۡيَۢا بَٰلِغَ ٱلۡكَعۡبَةِ أَوۡ كَفَّـٰرَةٞ طَعَامُ مَسَٰكِينَ أَوۡ عَدۡلُ ذَٰلِكَ صِيَامٗا لِّيَذُوقَ وَبَالَ أَمۡرِهِۦۗ عَفَا ٱللَّهُ عَمَّا سَلَفَۚ وَمَنۡ عَادَ فَيَنتَقِمُ ٱللَّهُ مِنۡهُۚ وَٱللَّهُ عَزِيزٞ ذُو ٱنتِقَامٍ

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku kashe abin farauta alhali kuna cikin Harami[1]. Duk kuwa wanda ya kashe shi daga cikinku da gangan, to sakamakonsa shi ne (ya bayar) da kwatankwacin abin da ya kashe cikin dabbobin gida; waxanda za su yi hukunci da wannan su ne mutum biyu adalai a cikinku, a matsayin hadaya wadda za ta isa Ka’aba, ko kuma ya yi kaffarar ciyar da miskinai, ko kuma ya yi azumi na kwatankwacin haka, don ya xanxani kuxar lamarinsa. Allah Ya yi afuwa dangane da abin da ya wuce. Duk kuwa wanda ya sake komawa, to Allah zai yi masa uquba. Kuma Allah Mabuwayi ne, Ma’abocin uquba


1- Watau kuna sanye da haramin hajji ko na umara.


Capítulo: Suratul An’am

Verso : 18

وَهُوَ ٱلۡقَاهِرُ فَوۡقَ عِبَادِهِۦۚ وَهُوَ ٱلۡحَكِيمُ ٱلۡخَبِيرُ

Kuma Shi ne Mai rinjaye a kan bayinsa. Kuma Shi Mai hikima ne, Masani



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 61

وَهُوَ ٱلۡقَاهِرُ فَوۡقَ عِبَادِهِۦۖ وَيُرۡسِلُ عَلَيۡكُمۡ حَفَظَةً حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءَ أَحَدَكُمُ ٱلۡمَوۡتُ تَوَفَّتۡهُ رُسُلُنَا وَهُمۡ لَا يُفَرِّطُونَ

“Kuma Shi ne wanda Yake da iko a kan bayinsa, kuma Yana aiko muku masu tsaro, har zuwa lokacin da mutuwa za ta zo wa xayanku, sai manzanninmu su karvi ransa, kuma su ba sa yin sakaci



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 49

إِذۡ يَقُولُ ٱلۡمُنَٰفِقُونَ وَٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٌ غَرَّ هَـٰٓؤُلَآءِ دِينُهُمۡۗ وَمَن يَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِ فَإِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٞ

Ka tuna lokacin da munafuqai da kuma waxanda suke da rauni a zukatansu suke cewa: “Waxannan addininsu ne ya ruxe su.” Duk wanda ya dogara ga Allah kuwa to lalle Allah Mabuwayi ne Mai hikima



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 52

كَدَأۡبِ ءَالِ فِرۡعَوۡنَ وَٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ كَفَرُواْ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ فَأَخَذَهُمُ ٱللَّهُ بِذُنُوبِهِمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ قَوِيّٞ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ

(Al’adar kafiran Makka) kamar al’adar mutanen Fir’auna ce da kuma waxanda suke gabaninsu. Sun kafirce wa ayoyin Allah, saboda haka Allah Ya kama su da zunubansu. Lalle Allah Mai qarfi ne, Mai tsananin uquba



Capítulo: Suratu Hud

Verso : 66

فَلَمَّا جَآءَ أَمۡرُنَا نَجَّيۡنَا صَٰلِحٗا وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُۥ بِرَحۡمَةٖ مِّنَّا وَمِنۡ خِزۡيِ يَوۡمِئِذٍۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ ٱلۡقَوِيُّ ٱلۡعَزِيزُ

To lokacin da umarninmu ya zo sai Muka tserar da Salihu shi da waxanda suka yi imani tare da shi saboda wata rahama daga gare mu, kuma (Muka tserar da su) daga kunyatar wannan rana. Lalle Ubangijinka Shi ne Mai qarfi Mabuwayi



Capítulo: Suratur Ra’ad

Verso : 16

قُلۡ مَن رَّبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ قُلِ ٱللَّهُۚ قُلۡ أَفَٱتَّخَذۡتُم مِّن دُونِهِۦٓ أَوۡلِيَآءَ لَا يَمۡلِكُونَ لِأَنفُسِهِمۡ نَفۡعٗا وَلَا ضَرّٗاۚ قُلۡ هَلۡ يَسۡتَوِي ٱلۡأَعۡمَىٰ وَٱلۡبَصِيرُ أَمۡ هَلۡ تَسۡتَوِي ٱلظُّلُمَٰتُ وَٱلنُّورُۗ أَمۡ جَعَلُواْ لِلَّهِ شُرَكَآءَ خَلَقُواْ كَخَلۡقِهِۦ فَتَشَٰبَهَ ٱلۡخَلۡقُ عَلَيۡهِمۡۚ قُلِ ٱللَّهُ خَٰلِقُ كُلِّ شَيۡءٖ وَهُوَ ٱلۡوَٰحِدُ ٱلۡقَهَّـٰرُ

Ka ce (da su): “Wane ne Ubangijin sammai da qasa?” Ka ce: “Allah ne”. Ka ce (da su): “Amma yaya kuka riqi wasu iyayen giji ba Shi ba su zama majivinta (gare ku), ba sa mallakar wani amfani ko cuta ga kansu?” Ka ce: “Shin makaho da mai gani za su yi daidai, ko kuwa shin duhu da haske za su yi daidai? Ko sun sanya wa Allah wasu abokan tarayya ne waxanda suka yi halitta kamar halittarsa, sai halittar ta yi musu kama da juna?” Ka ce: “Allah ne Mahaliccin komai, kuma Shi ne Makaxaici, Mai rinjaye.”



Capítulo: Suratu Ibrahim

Verso : 47

فَلَا تَحۡسَبَنَّ ٱللَّهَ مُخۡلِفَ وَعۡدِهِۦ رُسُلَهُۥٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٞ ذُو ٱنتِقَامٖ

To kada ka yi tsammanin Allah Mai sava wa manzanninsa alqawarinsa ne. Lalle Allah Mabuwayi ne Ma’abocin uquba



Capítulo: Suratul Hajji

Verso : 40

ٱلَّذِينَ أُخۡرِجُواْ مِن دِيَٰرِهِم بِغَيۡرِ حَقٍّ إِلَّآ أَن يَقُولُواْ رَبُّنَا ٱللَّهُۗ وَلَوۡلَا دَفۡعُ ٱللَّهِ ٱلنَّاسَ بَعۡضَهُم بِبَعۡضٖ لَّهُدِّمَتۡ صَوَٰمِعُ وَبِيَعٞ وَصَلَوَٰتٞ وَمَسَٰجِدُ يُذۡكَرُ فِيهَا ٱسۡمُ ٱللَّهِ كَثِيرٗاۗ وَلَيَنصُرَنَّ ٱللَّهُ مَن يَنصُرُهُۥٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَقَوِيٌّ عَزِيزٌ

(Su ne) waxanda aka fitar da su daga gidajensu ba da wani laifi ba, sai don kawai sun ce: “Allah ne Ubangijinmu”. Kuma ba don kariyar Allah ga wasu mutane ta hanyar wasu ba, to da lalle an rusa wuraren bauta (na Nasara da suka qaurace wa ‘yan’uwansu), da coci-coci da wuraren bautar Yahudawa da masallatai (na Musulmi) waxanda ake ambaton sunan Allah da yawa a cikinsu. Kuma tabbas Allah zai taimaki mai taimakon Sa. Lalle Allah Mai qarfi ne, Mabuwayi



Capítulo: Suratul Hajji

Verso : 74

مَا قَدَرُواْ ٱللَّهَ حَقَّ قَدۡرِهِۦٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَقَوِيٌّ عَزِيزٌ

Ba su girmama Allah ba kamar yadda ya kamata su girmama Shi. Lalle Allah tabbas Qaqqarfa ne, Mabuwayi



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 5

بِنَصۡرِ ٱللَّهِۚ يَنصُرُ مَن يَشَآءُۖ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ

Da samun nasar Allah (a kan Farisa). Shi Yake taimakon wanda Ya ga dama; domin kuwa Shi ne Mabuwayi, Mai rahama



Capítulo: Suratul Ahzab

Verso : 25

وَرَدَّ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِغَيۡظِهِمۡ لَمۡ يَنَالُواْ خَيۡرٗاۚ وَكَفَى ٱللَّهُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ٱلۡقِتَالَۚ وَكَانَ ٱللَّهُ قَوِيًّا عَزِيزٗا

Allah kuma Ya komar da waxanda suka kafirta da fushinsu ba su sami wani alheri ba. Allah kuma Ya xauke wa muminai yin yaqi. Domin kuwa Allah Ya kasance Mai qarfi ne, Mabuwayi



Capítulo: Suratu Faxir

Verso : 10

مَن كَانَ يُرِيدُ ٱلۡعِزَّةَ فَلِلَّهِ ٱلۡعِزَّةُ جَمِيعًاۚ إِلَيۡهِ يَصۡعَدُ ٱلۡكَلِمُ ٱلطَّيِّبُ وَٱلۡعَمَلُ ٱلصَّـٰلِحُ يَرۡفَعُهُۥۚ وَٱلَّذِينَ يَمۡكُرُونَ ٱلسَّيِّـَٔاتِ لَهُمۡ عَذَابٞ شَدِيدٞۖ وَمَكۡرُ أُوْلَـٰٓئِكَ هُوَ يَبُورُ

Wanda ya zamanto yana nufin xaukaka, to xaukaka gaba xayanta ta Allah ce. Daxaxan kalmomi[1] zuwa wurinsa suke hawa, kyakkyawan aiki kuwa shi yake xaukaka shi. Waxanda kuwa suke shirya makirci suna da (sakamakon) azaba mai tsanani, kuma makircin waxannan shi ne yake lalacewa


1- Watau kamar kalmar shahada da karatun Alqur’ani da ambaton Allah.


Capítulo: Suratu Ghafir

Verso : 16

يَوۡمَ هُم بَٰرِزُونَۖ لَا يَخۡفَىٰ عَلَى ٱللَّهِ مِنۡهُمۡ شَيۡءٞۚ لِّمَنِ ٱلۡمُلۡكُ ٱلۡيَوۡمَۖ لِلَّهِ ٱلۡوَٰحِدِ ٱلۡقَهَّارِ

Ranar da za su bayyana; babu wani abu nasu da zai vuya ga Allah. (Zai ce): “Mulki na wane ne a yau?” (Sai Ya ce): “Na Allah Makaxaici, Mai rinjaye ne.”



Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 15

فَأَمَّا عَادٞ فَٱسۡتَكۡبَرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّ وَقَالُواْ مَنۡ أَشَدُّ مِنَّا قُوَّةًۖ أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّ ٱللَّهَ ٱلَّذِي خَلَقَهُمۡ هُوَ أَشَدُّ مِنۡهُمۡ قُوَّةٗۖ وَكَانُواْ بِـَٔايَٰتِنَا يَجۡحَدُونَ

Amma Adawa sai suka yi girman kai a bayan qasa ba a kan gaskiya ba, suka kuma ce: “Wane ne ya fi mu tsananin qarfi?” Yanzu ba su ga cewa lalle Allah wanda Ya halicce su Ya fi su tsananin qarfi ba? Sun kuma kasance suna musanta ayoyinmu



Capítulo: Suratul Jasiya

Verso : 37

وَلَهُ ٱلۡكِبۡرِيَآءُ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

Girma nasa ne a cikin sammai da qasa, kuma Shi ne Mabuwayi, Mai hikima



Capítulo: Suratul Fat’h

Verso : 7

وَلِلَّهِ جُنُودُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَزِيزًا حَكِيمًا

Kuma rundunonin sammai da qasa na Allah ne. Allah kuwa Ya kasance Mabuwayi ne, Mai hikima



Capítulo: Suratuz Zariyat

Verso : 58

إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلرَّزَّاقُ ذُو ٱلۡقُوَّةِ ٱلۡمَتِينُ

Lalle Allah Shi ne Mai arzutawa, Mai tsananin qarfi



Capítulo: Suratul Qamar

Verso : 42

كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا كُلِّهَا فَأَخَذۡنَٰهُمۡ أَخۡذَ عَزِيزٖ مُّقۡتَدِرٍ

Suka qaryata ayoyinmu dukkaninsu, sai Muka kama su irin kamu na Mabuwayi, Mai iko



Capítulo: Suratul Hashr

Verso : 23

هُوَ ٱللَّهُ ٱلَّذِي لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡمَلِكُ ٱلۡقُدُّوسُ ٱلسَّلَٰمُ ٱلۡمُؤۡمِنُ ٱلۡمُهَيۡمِنُ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡجَبَّارُ ٱلۡمُتَكَبِّرُۚ سُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ عَمَّا يُشۡرِكُونَ

Shi ne Allah wanda babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi; Shi ne Sarki, Mai tsarki, Amintacce, Mai amintarwa, Mai kula da komai, Mabuwayi, Mai tsananin qarfi; Mai nuna isa. Allah Ya tsarkaka daga abin da suke tara (Shi da shi)