Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 114

وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّن مَّنَعَ مَسَٰجِدَ ٱللَّهِ أَن يُذۡكَرَ فِيهَا ٱسۡمُهُۥ وَسَعَىٰ فِي خَرَابِهَآۚ أُوْلَـٰٓئِكَ مَا كَانَ لَهُمۡ أَن يَدۡخُلُوهَآ إِلَّا خَآئِفِينَۚ لَهُمۡ فِي ٱلدُّنۡيَا خِزۡيٞ وَلَهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ عَذَابٌ عَظِيمٞ

Wane ne mafi zalunci kamar wanda ya hana masallatan Allah a riqa ambaton sunansa a cikinsu, ya yi ta qoqari wajen rushe su? Waxannan bai kamata su shige su ba sai a cikin halin tsoro. Za su gamu da wulaqanci a duniya a lahira kuma suna da wata azaba mai girma



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 115

وَلِلَّهِ ٱلۡمَشۡرِقُ وَٱلۡمَغۡرِبُۚ فَأَيۡنَمَا تُوَلُّواْ فَثَمَّ وَجۡهُ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ وَٰسِعٌ عَلِيمٞ

Gabas da yamma kuma na Allah ne. Duk inda aka fuskantar da ku to can ma alqiblar Allah ce. Lalle Allah Mai yalwar falala ne, kuma Mai yawan sani



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 187

أُحِلَّ لَكُمۡ لَيۡلَةَ ٱلصِّيَامِ ٱلرَّفَثُ إِلَىٰ نِسَآئِكُمۡۚ هُنَّ لِبَاسٞ لَّكُمۡ وَأَنتُمۡ لِبَاسٞ لَّهُنَّۗ عَلِمَ ٱللَّهُ أَنَّكُمۡ كُنتُمۡ تَخۡتَانُونَ أَنفُسَكُمۡ فَتَابَ عَلَيۡكُمۡ وَعَفَا عَنكُمۡۖ فَٱلۡـَٰٔنَ بَٰشِرُوهُنَّ وَٱبۡتَغُواْ مَا كَتَبَ ٱللَّهُ لَكُمۡۚ وَكُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ حَتَّىٰ يَتَبَيَّنَ لَكُمُ ٱلۡخَيۡطُ ٱلۡأَبۡيَضُ مِنَ ٱلۡخَيۡطِ ٱلۡأَسۡوَدِ مِنَ ٱلۡفَجۡرِۖ ثُمَّ أَتِمُّواْ ٱلصِّيَامَ إِلَى ٱلَّيۡلِۚ وَلَا تُبَٰشِرُوهُنَّ وَأَنتُمۡ عَٰكِفُونَ فِي ٱلۡمَسَٰجِدِۗ تِلۡكَ حُدُودُ ٱللَّهِ فَلَا تَقۡرَبُوهَاۗ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ ءَايَٰتِهِۦ لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمۡ يَتَّقُونَ

An halatta muku saduwa da matanku a daren azumi. Su sutura ne a gare ku, ku ma kuma sutura ne a gare su. Allah Ya san cewa ku lalle kun kasance kuna ha’intar kawunanku, sai Ya karvi tubanku kuma Ya yi muku afuwa; to a yanzu ku sadu da su (da daddare), kuma ku nemi abin da Allah Ya rubuta muku, kuma ku ci, kuma ku sha har farin zare ya bayyana a gare ku daga baqin zare na alfijir (wato ketowar Alfijir), sannan kuma ku cika azumi zuwa dare, kuma kar ku sadu da su alhali kuna i’itikafi a masallatai. Waxannan iyakoki ne na Allah, kada ku kusance su. Kamar haka ne Allah Yake bayyana ayoyinsa ga mutane, don su samu taqawa



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 29

قُلۡ أَمَرَ رَبِّي بِٱلۡقِسۡطِۖ وَأَقِيمُواْ وُجُوهَكُمۡ عِندَ كُلِّ مَسۡجِدٖ وَٱدۡعُوهُ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَۚ كَمَا بَدَأَكُمۡ تَعُودُونَ

Ka ce: “Ubangijina Ya yi umarni da adalci; kuma ku tsai da fuskokinku (don Allah) a kowace salla, ku kuma roqe Shi kuna masu tsantsanta addini gare Shi. Kamar yadda Ya fari halittarku, haka za ku koma (wurinsa)



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 31

۞يَٰبَنِيٓ ءَادَمَ خُذُواْ زِينَتَكُمۡ عِندَ كُلِّ مَسۡجِدٖ وَكُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ وَلَا تُسۡرِفُوٓاْۚ إِنَّهُۥ لَا يُحِبُّ ٱلۡمُسۡرِفِينَ

Ya ku ‘yan’adam, ku yi adonku a wurin kowane masallaci[1], ku ci, kuma ku sha, amma kada ku yi almubazzaranci. Lalle Shi (Allah) ba ya son masu almubazzaranci


1- Wannan ayar ta sauka ne game da mushirikai masu yin xawafi tsirara, suna cewa, wai bai dace su bauta wa Allah da tufafin da suka yi savo da su ba.


Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 17

مَا كَانَ لِلۡمُشۡرِكِينَ أَن يَعۡمُرُواْ مَسَٰجِدَ ٱللَّهِ شَٰهِدِينَ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِم بِٱلۡكُفۡرِۚ أُوْلَـٰٓئِكَ حَبِطَتۡ أَعۡمَٰلُهُمۡ وَفِي ٱلنَّارِ هُمۡ خَٰلِدُونَ

Ba zai tava yiwuwa mushrikai su raya masallatan Allah ba, alhalin kuwa suna masu iqirarin kafirci ga kawunansu. Waxannan ayyukansu sun vaci kuma a cikin wuta za su dawwama



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 18

إِنَّمَا يَعۡمُرُ مَسَٰجِدَ ٱللَّهِ مَنۡ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَأَقَامَ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَى ٱلزَّكَوٰةَ وَلَمۡ يَخۡشَ إِلَّا ٱللَّهَۖ فَعَسَىٰٓ أُوْلَـٰٓئِكَ أَن يَكُونُواْ مِنَ ٱلۡمُهۡتَدِينَ

Lalle mai raya masallatan Allah shi ne kawai wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira ya kuma tsayar da salla, kuma ya ba da zakka, bai kuma ji tsoron wani ba sai Allah. To waxannan tabbas suna cikin shiryayyu



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 19

۞أَجَعَلۡتُمۡ سِقَايَةَ ٱلۡحَآجِّ وَعِمَارَةَ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ كَمَنۡ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَجَٰهَدَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۚ لَا يَسۡتَوُۥنَ عِندَ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Yanzu kwa mayar da shayar da alhazai da raya Masallaci mai alfarma kamar wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira ya kuma yi jihadi saboda Allah? Ai ba za su zama xaya ba a wurin Allah. Allah kuma ba Ya shiryar da mutane azzalumai



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 107

وَٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ مَسۡجِدٗا ضِرَارٗا وَكُفۡرٗا وَتَفۡرِيقَۢا بَيۡنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَإِرۡصَادٗا لِّمَنۡ حَارَبَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ مِن قَبۡلُۚ وَلَيَحۡلِفُنَّ إِنۡ أَرَدۡنَآ إِلَّا ٱلۡحُسۡنَىٰۖ وَٱللَّهُ يَشۡهَدُ إِنَّهُمۡ لَكَٰذِبُونَ

Waxanda kuwa suka gina masallaci don cutarwa[1] da kafirci da rarraba kawunan muminai da kuma ba da mafaka ga wanda ya yaqi Allah da Manzonsa tun da can. Kuma lalle za su rantse da Allah cewa ba su yi nufin komai ba sai abu mafi kyau, Allah kuwa Yana ba da shaidar cewa lalle su tabbas maqaryata ne


1- Waxanda suka ware suka gina masallacinsu don cutar da Annabi () da muminai da raba kawunan Musulmi da ba wa maqiya Musulmi mafaka.


Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 108

لَا تَقُمۡ فِيهِ أَبَدٗاۚ لَّمَسۡجِدٌ أُسِّسَ عَلَى ٱلتَّقۡوَىٰ مِنۡ أَوَّلِ يَوۡمٍ أَحَقُّ أَن تَقُومَ فِيهِۚ فِيهِ رِجَالٞ يُحِبُّونَ أَن يَتَطَهَّرُواْۚ وَٱللَّهُ يُحِبُّ ٱلۡمُطَّهِّرِينَ

Kada ka yi salla a cikinsa har abada. Haqiqa masallacin da aka xora harsashinsa tun daga ranar farko a kan taqawa shi ya cancanci ka yi salla a cikinsa. A cikinsa akwai wasu mazaje da suke so su tsarkaka. Allah kuwa Yana son masu tsarkaka



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 109

أَفَمَنۡ أَسَّسَ بُنۡيَٰنَهُۥ عَلَىٰ تَقۡوَىٰ مِنَ ٱللَّهِ وَرِضۡوَٰنٍ خَيۡرٌ أَم مَّنۡ أَسَّسَ بُنۡيَٰنَهُۥ عَلَىٰ شَفَا جُرُفٍ هَارٖ فَٱنۡهَارَ بِهِۦ فِي نَارِ جَهَنَّمَۗ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Yanzu wanda ya sanya harsashin gininsa a kan taqawa ga Allah da (neman) yardarsa[1] shi ya fi ko kuwa wanda ya sanya harshashin gininsa a gefen rami mai zabtarewa, sai ya rubta da shi cikin wutar Jahannama? Allah kuwa ba Ya shiryar da mutane azzalumai


1- Shi ne masallacin Manzon Allah (). Da yawa daga cikin malaman tafsiri suna ganin shi ne masallacin Quba. Wasu kuma sun ce ana nufin duka biyun.


Capítulo: Suratul Isra’i

Verso : 1

سُبۡحَٰنَ ٱلَّذِيٓ أَسۡرَىٰ بِعَبۡدِهِۦ لَيۡلٗا مِّنَ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ إِلَى ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡأَقۡصَا ٱلَّذِي بَٰرَكۡنَا حَوۡلَهُۥ لِنُرِيَهُۥ مِنۡ ءَايَٰتِنَآۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡبَصِيرُ

Tsarki ya tabbata ga wanda Ya yi Isra’i da bawansa cikin dare daga Masallaci mai alfarma[1] zuwa Masallaci mafi nisa (na Qudus) wanda Muka albarkaci kewayensa, don Mu nuna masa wasu daga ayoyinmu. Lalle Shi Mai ji ne, Mai gani


1- Watau masallacin Ka’aba da yake Makka.


Capítulo: Suratul Isra’i

Verso : 7

إِنۡ أَحۡسَنتُمۡ أَحۡسَنتُمۡ لِأَنفُسِكُمۡۖ وَإِنۡ أَسَأۡتُمۡ فَلَهَاۚ فَإِذَا جَآءَ وَعۡدُ ٱلۡأٓخِرَةِ لِيَسُـُٔواْ وُجُوهَكُمۡ وَلِيَدۡخُلُواْ ٱلۡمَسۡجِدَ كَمَا دَخَلُوهُ أَوَّلَ مَرَّةٖ وَلِيُتَبِّرُواْ مَا عَلَوۡاْ تَتۡبِيرًا

“Idan kun kyautata to kanku kuka kyautata wa, idan kuma kuka munana to kanku kuka yi wa. To idan alqawarin (varnar) ta qarshe ya zo (sai maqiyanku su zo) don su wulaqanta ku su kuma shiga masallaci (na Baitul Maqadis) kamar yadda suka shige shi tun farko, kuma za su yi raga-raga da (duk) abin da suka biyo ta kansa



Capítulo: Suratul Hajji

Verso : 40

ٱلَّذِينَ أُخۡرِجُواْ مِن دِيَٰرِهِم بِغَيۡرِ حَقٍّ إِلَّآ أَن يَقُولُواْ رَبُّنَا ٱللَّهُۗ وَلَوۡلَا دَفۡعُ ٱللَّهِ ٱلنَّاسَ بَعۡضَهُم بِبَعۡضٖ لَّهُدِّمَتۡ صَوَٰمِعُ وَبِيَعٞ وَصَلَوَٰتٞ وَمَسَٰجِدُ يُذۡكَرُ فِيهَا ٱسۡمُ ٱللَّهِ كَثِيرٗاۗ وَلَيَنصُرَنَّ ٱللَّهُ مَن يَنصُرُهُۥٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَقَوِيٌّ عَزِيزٌ

(Su ne) waxanda aka fitar da su daga gidajensu ba da wani laifi ba, sai don kawai sun ce: “Allah ne Ubangijinmu”. Kuma ba don kariyar Allah ga wasu mutane ta hanyar wasu ba, to da lalle an rusa wuraren bauta (na Nasara da suka qaurace wa ‘yan’uwansu), da coci-coci da wuraren bautar Yahudawa da masallatai (na Musulmi) waxanda ake ambaton sunan Allah da yawa a cikinsu. Kuma tabbas Allah zai taimaki mai taimakon Sa. Lalle Allah Mai qarfi ne, Mabuwayi



Capítulo: Suratul Jinn

Verso : 18

وَأَنَّ ٱلۡمَسَٰجِدَ لِلَّهِ فَلَا تَدۡعُواْ مَعَ ٱللَّهِ أَحَدٗا

Kuma lalle masallatai na Allah ne, saboda haka kada ku bauta wa wani tare da Allah