يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَدۡخُلُواْ بُيُوتَ ٱلنَّبِيِّ إِلَّآ أَن يُؤۡذَنَ لَكُمۡ إِلَىٰ طَعَامٍ غَيۡرَ نَٰظِرِينَ إِنَىٰهُ وَلَٰكِنۡ إِذَا دُعِيتُمۡ فَٱدۡخُلُواْ فَإِذَا طَعِمۡتُمۡ فَٱنتَشِرُواْ وَلَا مُسۡتَـٔۡنِسِينَ لِحَدِيثٍۚ إِنَّ ذَٰلِكُمۡ كَانَ يُؤۡذِي ٱلنَّبِيَّ فَيَسۡتَحۡيِۦ مِنكُمۡۖ وَٱللَّهُ لَا يَسۡتَحۡيِۦ مِنَ ٱلۡحَقِّۚ وَإِذَا سَأَلۡتُمُوهُنَّ مَتَٰعٗا فَسۡـَٔلُوهُنَّ مِن وَرَآءِ حِجَابٖۚ ذَٰلِكُمۡ أَطۡهَرُ لِقُلُوبِكُمۡ وَقُلُوبِهِنَّۚ وَمَا كَانَ لَكُمۡ أَن تُؤۡذُواْ رَسُولَ ٱللَّهِ وَلَآ أَن تَنكِحُوٓاْ أَزۡوَٰجَهُۥ مِنۢ بَعۡدِهِۦٓ أَبَدًاۚ إِنَّ ذَٰلِكُمۡ كَانَ عِندَ ٱللَّهِ عَظِيمًا
Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku shiga gidajen Annabi sai idan an yi muku izini zuwa (cin) abinci, alhali ba tare da kuna jiran dahuwarsa ba, sai dai kuma idan aka kira ku, to ku shiga, sannan idan kuka ci sai ku fice, ba tare da yin wata hira ta xebe kewa ba. Lalle wannan ya kasance yana cutar Annabi, sai yakan ji kunyar ku; Allah kuwa ba Ya jin kunyar (faxar) gaskiya. Idan kuma za ku tambaye su (wato matan Annabi) wani abu na amfani, sai ku tambaye su ta bayan shamaki. Yin wannan shi ya fi tsarki ga zukatanku da kuma zukatansu. Kuma bai kamace ku ba ku cuci Manzon Allah ko kuma ku auri matansa a bayansa har abada. Lalle (yin) wannan ya kasance abu mai girma a wurin Allah
إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَـٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِيِّۚ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ صَلُّواْ عَلَيۡهِ وَسَلِّمُواْ تَسۡلِيمًا
Lalle Allah da mala’ikunsa suna yin salati ga Annabi. Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama mai yawa
إِنَّ ٱلَّذِينَ يُؤۡذُونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ لَعَنَهُمُ ٱللَّهُ فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِ وَأَعَدَّ لَهُمۡ عَذَابٗا مُّهِينٗا
Lalle waxanda suke cutar Allah da Manzonsa, to Allah Ya la’ance su a duniya da lahira, Ya kuma tanadar musu azaba mai wulaqantarwa
يَوۡمَ تُقَلَّبُ وُجُوهُهُمۡ فِي ٱلنَّارِ يَقُولُونَ يَٰلَيۡتَنَآ أَطَعۡنَا ٱللَّهَ وَأَطَعۡنَا ٱلرَّسُولَا۠
A ranar da za a riqa jujjuya fuskokinsu cikin wuta, suna cewa: “Kaiconmu, ina ma da mun bi Allah mun bi Manzo!”
يُصۡلِحۡ لَكُمۡ أَعۡمَٰلَكُمۡ وَيَغۡفِرۡ لَكُمۡ ذُنُوبَكُمۡۗ وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ فَقَدۡ فَازَ فَوۡزًا عَظِيمًا
Zai kyautata muku ayyukanku, Ya kuma gafarta muku zunubanku. Duk kuwa wanda ya bi Allah da Manzonsa, to haqiqa ya rabauta rabauta mai girma
۞يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَ وَلَا تُبۡطِلُوٓاْ أَعۡمَٰلَكُمۡ
Ya ku waxanda suka yi imani, ku bi Allah, kuma ku bi Manzonsa, kada kuma ku vata ayyukanku[1]
1- Watau ta hanyar aikata kafirci ko munafurci ko riya.
إِنَّآ أَرۡسَلۡنَٰكَ شَٰهِدٗا وَمُبَشِّرٗا وَنَذِيرٗا
Lalle Mu Muka aiko ka don ka zama sheda kuma mai albishir mai gargaxi
لِّتُؤۡمِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَتُعَزِّرُوهُ وَتُوَقِّرُوهُۚ وَتُسَبِّحُوهُ بُكۡرَةٗ وَأَصِيلًا
Don (ku mutane) ku yi imani da Allah da Manzonsa ku kuma taimake shi (wato Annabinsa), kuma ku girmama shi, ku kuma tsarkake Shi (wato Allah) safe da yamma
إِنَّ ٱلَّذِينَ يُبَايِعُونَكَ إِنَّمَا يُبَايِعُونَ ٱللَّهَ يَدُ ٱللَّهِ فَوۡقَ أَيۡدِيهِمۡۚ فَمَن نَّكَثَ فَإِنَّمَا يَنكُثُ عَلَىٰ نَفۡسِهِۦۖ وَمَنۡ أَوۡفَىٰ بِمَا عَٰهَدَ عَلَيۡهُ ٱللَّهَ فَسَيُؤۡتِيهِ أَجۡرًا عَظِيمٗا
Lalle waxanda suka yi maka mubaya’a[1] Allah kawai suke yi wa mubaya’a, Hannun Allah yana saman hannayensu. To duk wanda ya warware, to kansa kawai ya warware wa, wanda kuwa ya cika abin da ya yi wa Allah alqawarinsa, to ba da daxewa ba za Mu ba shi lada mai girma
1- Su ne sahabbai dubu da xari huxu da suka yi wa Annabi () mubaya’ar yaqi a Hudaibiyya, watau Bai’atur Ridhwan.
لَّيۡسَ عَلَى ٱلۡأَعۡمَىٰ حَرَجٞ وَلَا عَلَى ٱلۡأَعۡرَجِ حَرَجٞ وَلَا عَلَى ٱلۡمَرِيضِ حَرَجٞۗ وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ يُدۡخِلۡهُ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۖ وَمَن يَتَوَلَّ يُعَذِّبۡهُ عَذَابًا أَلِيمٗا
Babu wani laifi a kan makaho, babu kuma wani laifi a kan gurgu, kuma babu wani laifi a kan marar lafiya (game da rashin fita yaqi). Wanda kuwa ya bi Allah da Manzonsa to zai shigar da shi gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, wanda kuma ya ba da baya to zai azabtar da shi azaba mai raxaxi
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تُقَدِّمُواْ بَيۡنَ يَدَيِ ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٞ
Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku wuce gaban Allah da Manzonsa[1], kuma ku kiyaye dokokin Allah. Lalle Allah Mai ji ne, Masani
1- Watau wajen aikata wani aiki ko faxar wata magana kafin su saurari abin da Allah da Manzonsa () za su faxa.
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَرۡفَعُوٓاْ أَصۡوَٰتَكُمۡ فَوۡقَ صَوۡتِ ٱلنَّبِيِّ وَلَا تَجۡهَرُواْ لَهُۥ بِٱلۡقَوۡلِ كَجَهۡرِ بَعۡضِكُمۡ لِبَعۡضٍ أَن تَحۡبَطَ أَعۡمَٰلُكُمۡ وَأَنتُمۡ لَا تَشۡعُرُونَ
Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku xaga muryoyinku sama da muryar Annabi, kada kuma ku xaga masa murya wajen yin magana kamar yadda shashinku yake xaga wa shashi, don kada ayyukanku su lalace alhali kuwa ku ba ku sani ba
إِنَّ ٱلَّذِينَ يَغُضُّونَ أَصۡوَٰتَهُمۡ عِندَ رَسُولِ ٱللَّهِ أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ ٱمۡتَحَنَ ٱللَّهُ قُلُوبَهُمۡ لِلتَّقۡوَىٰۚ لَهُم مَّغۡفِرَةٞ وَأَجۡرٌ عَظِيمٌ
Lalle waxanda suke yin qasa-qasa da muryoyinsu a wurin Manzon Allah, waxannan su ne waxanda Allah Ya jarrabi zukatansu da imani. Suna da (sakamakon) gafara da lada mai girma
إِنَّ ٱلَّذِينَ يُنَادُونَكَ مِن وَرَآءِ ٱلۡحُجُرَٰتِ أَكۡثَرُهُمۡ لَا يَعۡقِلُونَ
Lalle waxanda suke kiran ka ta bayan xakuna[1] yawancinsu ba su da hankali
1- Watau xakunan matan Annabi (). Ana nufin mutanen qauye masu zuwa Madina wurin Annabi () don wata buqata.
وَلَوۡ أَنَّهُمۡ صَبَرُواْ حَتَّىٰ تَخۡرُجَ إِلَيۡهِمۡ لَكَانَ خَيۡرٗا لَّهُمۡۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Da za su yi haquri har sai ka fito wurinsu da ya fiye musu alheri. Allah kuma Mai gafara ne, Mai jin qai
۞قَالَتِ ٱلۡأَعۡرَابُ ءَامَنَّاۖ قُل لَّمۡ تُؤۡمِنُواْ وَلَٰكِن قُولُوٓاْ أَسۡلَمۡنَا وَلَمَّا يَدۡخُلِ ٱلۡإِيمَٰنُ فِي قُلُوبِكُمۡۖ وَإِن تُطِيعُواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ لَا يَلِتۡكُم مِّنۡ أَعۡمَٰلِكُمۡ شَيۡـًٔاۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٌ
(Larabawa) qauyawa suka ce: “Mun yi imani.” Ka ce: “Ba ku yi imani ba, sai dai ku ce ‘mun musulunta’, don kuwa imani bai riga ya shiga zukatanku ba; idan kuwa kuka bi Allah da Manzonsa, to ba zai tauye muku wani abu daga (ladan) ayyukanku ba. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai rahama.”
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا تَنَٰجَيۡتُمۡ فَلَا تَتَنَٰجَوۡاْ بِٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡعُدۡوَٰنِ وَمَعۡصِيَتِ ٱلرَّسُولِ وَتَنَٰجَوۡاْ بِٱلۡبِرِّ وَٱلتَّقۡوَىٰۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ ٱلَّذِيٓ إِلَيۡهِ تُحۡشَرُونَ
Ya ku waxanda suka yi imani, idan za ku gana to kada ku yi ganawar savo da ta’addanci da kuma sava wa Manzo. (A maimakon haka) ku gana a kan ayyukan alheri da taqawa; kuma ku kiyaye dokokin Allah wanda zuwa gare Shi ne za a tattaro ku
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا نَٰجَيۡتُمُ ٱلرَّسُولَ فَقَدِّمُواْ بَيۡنَ يَدَيۡ نَجۡوَىٰكُمۡ صَدَقَةٗۚ ذَٰلِكَ خَيۡرٞ لَّكُمۡ وَأَطۡهَرُۚ فَإِن لَّمۡ تَجِدُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٌ
Ya ku waxanda suka yi imani, idan za ku gana da Manzo, to sai ku gabatar da wata sadaka kafin ganawar taku. Wannan shi ya fi muku alheri da tsarkaka. Sannan idan ba ku samu ba, to lalle Allah Mai gafara ne, Mai rahama
ءَأَشۡفَقۡتُمۡ أَن تُقَدِّمُواْ بَيۡنَ يَدَيۡ نَجۡوَىٰكُمۡ صَدَقَٰتٖۚ فَإِذۡ لَمۡ تَفۡعَلُواْ وَتَابَ ٱللَّهُ عَلَيۡكُمۡ فَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥۚ وَٱللَّهُ خَبِيرُۢ بِمَا تَعۡمَلُونَ
Yanzu kun samu damuwa ne ta gabatar da sadaka kafin ganawarku? To idan ba ku aikata haka ba Allah kuma ya karvi tubarku, to sai ku tsayar da salla, ku ba da zakka, ku kuma bi Allah da Manzonsa. Allah kuma Masanin abin da kuke aikatawa ne
إِنَّ ٱلَّذِينَ يُحَآدُّونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓ أُوْلَـٰٓئِكَ فِي ٱلۡأَذَلِّينَ
Lalle waxanda suke sava wa Allah da Manzonsa waxannan suna cikin mafiya qasqanci
مَّآ أَفَآءَ ٱللَّهُ عَلَىٰ رَسُولِهِۦ مِنۡ أَهۡلِ ٱلۡقُرَىٰ فَلِلَّهِ وَلِلرَّسُولِ وَلِذِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينِ وَٱبۡنِ ٱلسَّبِيلِ كَيۡ لَا يَكُونَ دُولَةَۢ بَيۡنَ ٱلۡأَغۡنِيَآءِ مِنكُمۡۚ وَمَآ ءَاتَىٰكُمُ ٱلرَّسُولُ فَخُذُوهُ وَمَا نَهَىٰكُمۡ عَنۡهُ فَٱنتَهُواْۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۖ إِنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ
Abin da Allah ya bai wa Manzonsa na wata dukiya daga mutanen alqaryu, to na Allah ne da Manzonsa da kuma danginsa na kusa[1] da marayu da miskinai da matafiyin (da guzuri ya yanke wa), don kada ya zama mai juyawa tsakanin mawadata daga cikinku. Kuma abin da Manzo ya ba ku sai ku karve shi, abin kuma da ya hana ku sai ku hanu. Ku kuma kiyaye dokokin Allah; lalle Allah Mai tsananin uquba ne
1- Watau Banu Hashim da Banul Muxxalib, waxanda aka haramta musu karvar sadaka ko zakka.
لِلۡفُقَرَآءِ ٱلۡمُهَٰجِرِينَ ٱلَّذِينَ أُخۡرِجُواْ مِن دِيَٰرِهِمۡ وَأَمۡوَٰلِهِمۡ يَبۡتَغُونَ فَضۡلٗا مِّنَ ٱللَّهِ وَرِضۡوَٰنٗا وَيَنصُرُونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓۚ أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلصَّـٰدِقُونَ
(Za a bayar da dukiyar) ga matalauta da suka yi hijira waxanda aka fitar da su daga gidajensu da dukiyoyinsu don neman falala daga Allah da yardarsa, suna kuma taimakon (addinin) Allah da Manzonsa. Waxannan su ne masu gaskiya
وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَۚ فَإِن تَوَلَّيۡتُمۡ فَإِنَّمَا عَلَىٰ رَسُولِنَا ٱلۡبَلَٰغُ ٱلۡمُبِينُ
Ku bi Allah kuma ku bi Manzon. To idan kuka ba da baya to abin da yake kan Manzonmu kawai shi ne isar da aike
إِلَّا بَلَٰغٗا مِّنَ ٱللَّهِ وَرِسَٰلَٰتِهِۦۚ وَمَن يَعۡصِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ فَإِنَّ لَهُۥ نَارَ جَهَنَّمَ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدًا
“Sai dai isar da aike daga Allah da kuma saqwanninsa. Duk kuwa waxanda suka sava wa Allah da Manzonsa, to lalle suna da wutar Jahannama, suna madawwama a cikinta har abada.”