يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَقُولُواْ رَٰعِنَا وَقُولُواْ ٱنظُرۡنَا وَٱسۡمَعُواْۗ وَلِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابٌ أَلِيمٞ
Ya ku waxanda suka yi imani kada ku ce, ra’ina, (watau kula da mu), sai dai ku ce, dakata mana[1], kuma ku saurara. Kafirai kuma suna da wata azaba mai raxaxi
1- Sahabban Annabi () sun kasance idan yana biya musu karatu sukan nemi ya xan dakata musu kaxan domin su fahimta sosai, to sai sukan yi amfani da kalmar ‘ra’ina’. A harshen Yahudawa kuma kalmar tana kusa da wata kalma da take da ma’anar ‘daqiqi’, to sai su ma suka riqa fakewa da wannan kalmar suna zagin Annabi (). Sai Allah ya hana sahabbai amfani da kalmar, a maimakonta ya ce su yi amfani da kalmar ‘unzurna’ wadda take nufin ‘dakata mana’.
قُلۡ إِن كُنتُمۡ تُحِبُّونَ ٱللَّهَ فَٱتَّبِعُونِي يُحۡبِبۡكُمُ ٱللَّهُ وَيَغۡفِرۡ لَكُمۡ ذُنُوبَكُمۡۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Ka ce: “In kun kasance kuna son Allah, to ku yi mini biyayya, sai Allah Ya so ku, kuma Ya gafarta muku zunubanku. Kuma Allah Mai gafara ne, Mai jin qai.”
قُلۡ أَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَٱلرَّسُولَۖ فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَإِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلۡكَٰفِرِينَ
Ka ce: “Ku yi xa’a ga Allah da Manzo; to in kuwa kuka juya baya, to lalle Allah ba Ya son kafirai.”
وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَٱلرَّسُولَ لَعَلَّكُمۡ تُرۡحَمُونَ
Kuma ku bi Allah da Manzo don a ji qan ku (a ranar tashin alqiyama)
تِلۡكَ حُدُودُ ٱللَّهِۚ وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ يُدۡخِلۡهُ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ وَذَٰلِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ
Waxannan iyakoki ne na Allah. Wanda duk yake bin Allah da Manzonsa, to zai shigar da shi gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, suna masu dawwama a cikinsu. Kuma wannan shi ne rabo mai girma
وَمَن يَعۡصِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَيَتَعَدَّ حُدُودَهُۥ يُدۡخِلۡهُ نَارًا خَٰلِدٗا فِيهَا وَلَهُۥ عَذَابٞ مُّهِينٞ
Wanda kuma yake sava wa Allah da Manzonsa, yake kuma qetare iyakokinsa, to zai shigar da shi wuta, yana mai dawwama a cikinta, kuma yana da wata azaba mai wulaqantarwa
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَ وَأُوْلِي ٱلۡأَمۡرِ مِنكُمۡۖ فَإِن تَنَٰزَعۡتُمۡ فِي شَيۡءٖ فَرُدُّوهُ إِلَى ٱللَّهِ وَٱلرَّسُولِ إِن كُنتُمۡ تُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۚ ذَٰلِكَ خَيۡرٞ وَأَحۡسَنُ تَأۡوِيلًا
Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi xa’a ga Allah, kuma ku yi xa’a ga Manzo da kuma majivinta lamarinku. Idan kun yi jayayya a kan wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da Manzonsa in kun kasance kun yi imani da Allah da ranar qarshe. Wannan shi ne mafi alheri, kuma mafi kyan makoma
وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن رَّسُولٍ إِلَّا لِيُطَاعَ بِإِذۡنِ ٱللَّهِۚ وَلَوۡ أَنَّهُمۡ إِذ ظَّلَمُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ جَآءُوكَ فَٱسۡتَغۡفَرُواْ ٱللَّهَ وَٱسۡتَغۡفَرَ لَهُمُ ٱلرَّسُولُ لَوَجَدُواْ ٱللَّهَ تَوَّابٗا رَّحِيمٗا
Kuma ba Mu tava aiko wani manzo ba, face sai don a yi masa xa’a da izinin Allah. Kuma da a ce lokacin da suka zalunci kawunansu sun zo maka, sun nemi Allah Ya gafarta musu, sannan Manzo ya roqa musu gafara, to tabbas da sun sami Allah Yana Mai yawan karvar tuba, Mai jin qai
فَلَا وَرَبِّكَ لَا يُؤۡمِنُونَ حَتَّىٰ يُحَكِّمُوكَ فِيمَا شَجَرَ بَيۡنَهُمۡ ثُمَّ لَا يَجِدُواْ فِيٓ أَنفُسِهِمۡ حَرَجٗا مِّمَّا قَضَيۡتَ وَيُسَلِّمُواْ تَسۡلِيمٗا
To ina rantsuwa da Ubangijinka, ba za su yi imani ba har sai sun kai hukunci a gabanka game da duk abin da ya faru na savani a tsakaninsu, sannan ba su ji wani qunci a cikin zukatansu ba game da abin da ka zartar na hukunci, kuma su miqa wuya miqawa gaba xaya
وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَٱلرَّسُولَ فَأُوْلَـٰٓئِكَ مَعَ ٱلَّذِينَ أَنۡعَمَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِم مِّنَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ وَٱلصِّدِّيقِينَ وَٱلشُّهَدَآءِ وَٱلصَّـٰلِحِينَۚ وَحَسُنَ أُوْلَـٰٓئِكَ رَفِيقٗا
Kuma duk waxanda suka yi wa Allah xa’a da wannan Manzon, to waxannan suna tare da waxanda Allah Ya yi musu ni’ima, su ne annabawa da siddiqai da shahidai da salihan bayi. Kuma madalla da waxannan abokai
مَّن يُطِعِ ٱلرَّسُولَ فَقَدۡ أَطَاعَ ٱللَّهَۖ وَمَن تَوَلَّىٰ فَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ عَلَيۡهِمۡ حَفِيظٗا
Duk wanda ya yi wa wannan Manzo xa’a, to haqiqa ya yi wa Allah xa’a ne; wanda kuwa ya bijire, to ba Mu aiko ka a matsayin mai tsaron su ba
وَمَن يُشَاقِقِ ٱلرَّسُولَ مِنۢ بَعۡدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُ ٱلۡهُدَىٰ وَيَتَّبِعۡ غَيۡرَ سَبِيلِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ نُوَلِّهِۦ مَا تَوَلَّىٰ وَنُصۡلِهِۦ جَهَنَّمَۖ وَسَآءَتۡ مَصِيرًا
Kuma duk wanda yake sava wa wannan Manzo bayan shiriya ta bayyana a gare shi, yake kuma bin tafarkin da ba na muminai ba, to za Mu bar shi da abin da ya xaukar wa kansa, sannan Mu shigar da shi wutar Jahannama; makoma kuwa ta munana
وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَ وَٱحۡذَرُواْۚ فَإِن تَوَلَّيۡتُمۡ فَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّمَا عَلَىٰ رَسُولِنَا ٱلۡبَلَٰغُ ٱلۡمُبِينُ
Kuma ku bi Allah, kuma ku bi wannan Manzon, kuma ku yi hattara. Idan kuka juya baya, to ku sani abin da kawai yake kan Manzonmu shi ne isar da saqo filla-filla
ٱلَّذِينَ يَتَّبِعُونَ ٱلرَّسُولَ ٱلنَّبِيَّ ٱلۡأُمِّيَّ ٱلَّذِي يَجِدُونَهُۥ مَكۡتُوبًا عِندَهُمۡ فِي ٱلتَّوۡرَىٰةِ وَٱلۡإِنجِيلِ يَأۡمُرُهُم بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَيَنۡهَىٰهُمۡ عَنِ ٱلۡمُنكَرِ وَيُحِلُّ لَهُمُ ٱلطَّيِّبَٰتِ وَيُحَرِّمُ عَلَيۡهِمُ ٱلۡخَبَـٰٓئِثَ وَيَضَعُ عَنۡهُمۡ إِصۡرَهُمۡ وَٱلۡأَغۡلَٰلَ ٱلَّتِي كَانَتۡ عَلَيۡهِمۡۚ فَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِهِۦ وَعَزَّرُوهُ وَنَصَرُوهُ وَٱتَّبَعُواْ ٱلنُّورَ ٱلَّذِيٓ أُنزِلَ مَعَهُۥٓ أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ
“(Su ne) waxanda suke bin Manzo Annabi Ummiyyi, wanda suke samun sa a rubuce a wurinsu a cikin Attaura da Linjila, yana umartar su da kyakkyawan abu, kuma yana hana su mummuna, kuma yana halatta musu daxaxan abubuwa, yana kuma haramta musu qazantattu, kuma yana sauke musu nauyaye-nauyayensu da ququmce-ququmcen da suka kasance a kansu[1]. Don haka waxanda suka yi imani da shi, kuma suka qarfafe shi, suka kuma taimake shi, suka bi hasken da aka saukar tare da shi, waxannan su ne masu rabauta.”
1- Nauyaye-nauyayensu su ne abubuwa masu wuya da aka wajabta musu aiki da su a littafin Attaura. Ququmce-ququmcensu kuwa su ne abubuwan da aka tsananta musu haramcinsu masu kama da ququmi.
يَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡأَنفَالِۖ قُلِ ٱلۡأَنفَالُ لِلَّهِ وَٱلرَّسُولِۖ فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَصۡلِحُواْ ذَاتَ بَيۡنِكُمۡۖ وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ
Suna tambayar ka game da ganimomi[1]; ka ce (da su): “Ganimomi na Allah ne da kuma Manzo; saboda haka ku kiyaye dokokin Allah, ku kuma gyara tsakaninku, kuma ku bi Allah da Manzonsa, idan kun kasance muminai.”
1- Watau tambayar da sahabbai suka yi wa Annabi () game da hukuncin ganimar yaqin Badar.
ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ شَآقُّواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥۚ وَمَن يُشَاقِقِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ فَإِنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ
Wannan kuwa saboda sun sava wa Allah da Manzonsa. Duk wanda kuwa ya sava wa Allah da Manzonsa to lalle Allah Mai tsananin uquba ne
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَلَا تَوَلَّوۡاْ عَنۡهُ وَأَنتُمۡ تَسۡمَعُونَ
Ya ku waxanda suka yi imani, ku bi Allah da Manzonsa kada kuma ku ba shi baya alhali kuwa kuna ji
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱسۡتَجِيبُواْ لِلَّهِ وَلِلرَّسُولِ إِذَا دَعَاكُمۡ لِمَا يُحۡيِيكُمۡۖ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ يَحُولُ بَيۡنَ ٱلۡمَرۡءِ وَقَلۡبِهِۦ وَأَنَّهُۥٓ إِلَيۡهِ تُحۡشَرُونَ
Ya ku waxanda suka yi imani, ku amsa kiran Allah da na Manzo idan ya yi kiran ku ga abin da zai raya ku; kuma ku sani cewa, lalle Allah Yana kange tsakanin mutum da zuciyarsa, kuma lalle wurinsa ne za a tattara ku
وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَلَا تَنَٰزَعُواْ فَتَفۡشَلُواْ وَتَذۡهَبَ رِيحُكُمۡۖ وَٱصۡبِرُوٓاْۚ إِنَّ ٱللَّهَ مَعَ ٱلصَّـٰبِرِينَ
Kuma ku bi Allah da Manzonsa, kada ku rarrabu sai ku zama matsorata kuma qarfinku ya tafi; ku kuma yi haquri. Lalle Allah Yana tare da masu haquri
قُلۡ إِن كَانَ ءَابَآؤُكُمۡ وَأَبۡنَآؤُكُمۡ وَإِخۡوَٰنُكُمۡ وَأَزۡوَٰجُكُمۡ وَعَشِيرَتُكُمۡ وَأَمۡوَٰلٌ ٱقۡتَرَفۡتُمُوهَا وَتِجَٰرَةٞ تَخۡشَوۡنَ كَسَادَهَا وَمَسَٰكِنُ تَرۡضَوۡنَهَآ أَحَبَّ إِلَيۡكُم مِّنَ ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَجِهَادٖ فِي سَبِيلِهِۦ فَتَرَبَّصُواْ حَتَّىٰ يَأۡتِيَ ٱللَّهُ بِأَمۡرِهِۦۗ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡفَٰسِقِينَ
Ka ce: “Idan iyayenku da ‘ya’yanku da matanku da danginku da dukiyoyin da kuka tara da kasuwanci da kuke tsoron gurguncewarsa da kuma gidajen da kuke sha’awa; idan har su kuka fi so fiye da Allah da Manzonsa da kuma jihadi saboda Shi, to sai ku saurara har Allah Ya zo da al’amarinsa. Allah kuwa ba Ya shiryar da mutane fasiqai.”
يَحۡلِفُونَ بِٱللَّهِ لَكُمۡ لِيُرۡضُوكُمۡ وَٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥٓ أَحَقُّ أَن يُرۡضُوهُ إِن كَانُواْ مُؤۡمِنِينَ
Suna rantse muku da Allah don su samu yardarku, Allah da Manzonsa kuwa su suka fi cancanta su yardar da su in sun kasance muminai
أَلَمۡ يَعۡلَمُوٓاْ أَنَّهُۥ مَن يُحَادِدِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ فَأَنَّ لَهُۥ نَارَ جَهَنَّمَ خَٰلِدٗا فِيهَاۚ ذَٰلِكَ ٱلۡخِزۡيُ ٱلۡعَظِيمُ
Yanzu ba su sani ba cewa, wanda yake jayayya da Allah da Manzonsa, to lalle yana da wutar Jahannama da zai dawwama a cikinta? Wannan kuwa kunyata ce mai girma
وَٱلۡمُؤۡمِنُونَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتُ بَعۡضُهُمۡ أَوۡلِيَآءُ بَعۡضٖۚ يَأۡمُرُونَ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَيَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلۡمُنكَرِ وَيُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُؤۡتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَيُطِيعُونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓۚ أُوْلَـٰٓئِكَ سَيَرۡحَمُهُمُ ٱللَّهُۗ إِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٞ
Muminai maza da muninai mata kuwa masoyan juna ne: Suna yin umurni da kyakkyawan abu suna kuma hana mummunan, suna kuma tsai da salla suna ba da zakka suna kuma bin Allah da Manzonsa. Waxannan Allah zai yi musu rahama. Lalle Allah kuwa Mabuwayi ne Mai hikima
وَقُلِ ٱعۡمَلُواْ فَسَيَرَى ٱللَّهُ عَمَلَكُمۡ وَرَسُولُهُۥ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَۖ وَسَتُرَدُّونَ إِلَىٰ عَٰلِمِ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Ka kuma ce: “Ku yi aiki, Allah ne zai ga aikinku shi da Manzonsa da kuma muminai, kuma za a mayar da ku zuwa ga Masanin abin da yake voye da na sarari, sannan Ya ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa
مَا كَانَ لِأَهۡلِ ٱلۡمَدِينَةِ وَمَنۡ حَوۡلَهُم مِّنَ ٱلۡأَعۡرَابِ أَن يَتَخَلَّفُواْ عَن رَّسُولِ ٱللَّهِ وَلَا يَرۡغَبُواْ بِأَنفُسِهِمۡ عَن نَّفۡسِهِۦۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ لَا يُصِيبُهُمۡ ظَمَأٞ وَلَا نَصَبٞ وَلَا مَخۡمَصَةٞ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَلَا يَطَـُٔونَ مَوۡطِئٗا يَغِيظُ ٱلۡكُفَّارَ وَلَا يَنَالُونَ مِنۡ عَدُوّٖ نَّيۡلًا إِلَّا كُتِبَ لَهُم بِهِۦ عَمَلٞ صَٰلِحٌۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُضِيعُ أَجۡرَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Bai kamata ba ga mutanen Madina da waxanda suke kewaye da su daga mazauna qauye su noqe su qi bin Manzon Allah, ko kuma su zavi kansu fiye da shi. Wannan kuwa saboda ba wata qishirwa ko wahala ko yunwa da za ta same su a kan hanyar Allah, kuma ba za su taka wani wuri ba da zai vata wa kafirai rai, kuma ba za su tafka wa abokan gaba wata hasara ba sai an rubuta musu lada saboda shi (wato kowane xaya daga abubuwan da aka zana). Lalle Allah ba Ya tozarta ladan masu kyautatawa
وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَيَخۡشَ ٱللَّهَ وَيَتَّقۡهِ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡفَآئِزُونَ
Duk kuwa wanda ya bi Allah da Manzonsa kuma yake tsoron Allah kuma yake kiyaye dokokinsa, to waxannan su ne masu rabauta
قُلۡ أَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَۖ فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَإِنَّمَا عَلَيۡهِ مَا حُمِّلَ وَعَلَيۡكُم مَّا حُمِّلۡتُمۡۖ وَإِن تُطِيعُوهُ تَهۡتَدُواْۚ وَمَا عَلَى ٱلرَّسُولِ إِلَّا ٱلۡبَلَٰغُ ٱلۡمُبِينُ
Ka ce (da su): “Ku bi Allah kuma ku bi Manzo; sannan idan kuka ba da baya, to lalle nauyin abin da aka xora masa ne kawai a kansa; kuma nauyin da aka xora muku yana kanku, idan kuwa kuka bi shi za ku shiriya. Ba kuwa abin da yake kan Manzo sai isar da aike mabayyani
وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَ لَعَلَّكُمۡ تُرۡحَمُونَ
Kuma ku tsai da salla ku kuma ba da zakka kuma ku bi Manzo don a ji qan ku
لَّا تَجۡعَلُواْ دُعَآءَ ٱلرَّسُولِ بَيۡنَكُمۡ كَدُعَآءِ بَعۡضِكُم بَعۡضٗاۚ قَدۡ يَعۡلَمُ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ يَتَسَلَّلُونَ مِنكُمۡ لِوَاذٗاۚ فَلۡيَحۡذَرِ ٱلَّذِينَ يُخَالِفُونَ عَنۡ أَمۡرِهِۦٓ أَن تُصِيبَهُمۡ فِتۡنَةٌ أَوۡ يُصِيبَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Kada ku mayar da kiran Manzo a tsakaninku kamar kiran junanku ga juna[1]. Haqiqa Allah Yana sane da waxanda suke zare jiki daga cikinku a voye. To lalle waxanda suke sava wa umarninsa su ji tsoron kada wata fitina ta shafe su ko kuma wata azaba mai raxaxi ta same su
1- Watau xayansu ya riqa cewa: “Ya Muhammadu” ko “Ya Muhammadu xan Abdullahi” ko “Ya xan Abdullahi”. Sai dai su ce: “Ya Manzon Allah” ko “Ya Annabin Allah”.
وَمَا كَانَ لِمُؤۡمِنٖ وَلَا مُؤۡمِنَةٍ إِذَا قَضَى ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥٓ أَمۡرًا أَن يَكُونَ لَهُمُ ٱلۡخِيَرَةُ مِنۡ أَمۡرِهِمۡۗ وَمَن يَعۡصِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ فَقَدۡ ضَلَّ ضَلَٰلٗا مُّبِينٗا
Bai kamata ga wani mumini ko wata mumina ba, idan Allah da Manzonsa suka yi hukunci a kan wani al’amari su zama suna da wani zavi game da al’amarinsu. Wanda kuwa ya sava wa Allah da Manzonsa, to haqiqa ya vata, bayyanannen vata