Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 143

وَكَذَٰلِكَ جَعَلۡنَٰكُمۡ أُمَّةٗ وَسَطٗا لِّتَكُونُواْ شُهَدَآءَ عَلَى ٱلنَّاسِ وَيَكُونَ ٱلرَّسُولُ عَلَيۡكُمۡ شَهِيدٗاۗ وَمَا جَعَلۡنَا ٱلۡقِبۡلَةَ ٱلَّتِي كُنتَ عَلَيۡهَآ إِلَّا لِنَعۡلَمَ مَن يَتَّبِعُ ٱلرَّسُولَ مِمَّن يَنقَلِبُ عَلَىٰ عَقِبَيۡهِۚ وَإِن كَانَتۡ لَكَبِيرَةً إِلَّا عَلَى ٱلَّذِينَ هَدَى ٱللَّهُۗ وَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيُضِيعَ إِيمَٰنَكُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ بِٱلنَّاسِ لَرَءُوفٞ رَّحِيمٞ

Kamar haka ne Muka sanya ku al’umma tsaka-tsaki (zavavvu) don ku zamo masu shaida ga mutane, kuma Manzo ya zamo mai shaida a gare ku. Kuma ba Mu sanya alqiblar da ka kasance a kanta ba sai don Mu bayyana wanda yake biyayya ga Manzo da wanda zai ja da baya (ya bijire). Kuma lalle wannan babban lamari ne sai dai ga waxanda Allah Ya shiryar. Kuma Allah ba zai tava tozarta imaninku ba. Lalle Allah Mai tausayi ne, Mai jin qai ga mutane



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 20

فَإِنۡ حَآجُّوكَ فَقُلۡ أَسۡلَمۡتُ وَجۡهِيَ لِلَّهِ وَمَنِ ٱتَّبَعَنِۗ وَقُل لِّلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡأُمِّيِّـۧنَ ءَأَسۡلَمۡتُمۡۚ فَإِنۡ أَسۡلَمُواْ فَقَدِ ٱهۡتَدَواْۖ وَّإِن تَوَلَّوۡاْ فَإِنَّمَا عَلَيۡكَ ٱلۡبَلَٰغُۗ وَٱللَّهُ بَصِيرُۢ بِٱلۡعِبَادِ

To idan sun yi jayayya da kai, sai ka ce: “Ni na miqa wuyana ne ga Allah, haka ma wanda ya bi ni.” Kuma ka faxa wa waxanda aka bai wa Littafi da Ummiyyai (Larabawa): “Shin kun miqa wuya?” To idan sun miqa wuya, haqiqa sun shiryu; idan kuwa suka juya baya, to babu abin da yake a kanka sai isar da saqo. Kuma Allah Mai ganin bayinsa ne



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 164

لَقَدۡ مَنَّ ٱللَّهُ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ إِذۡ بَعَثَ فِيهِمۡ رَسُولٗا مِّنۡ أَنفُسِهِمۡ يَتۡلُواْ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتِهِۦ وَيُزَكِّيهِمۡ وَيُعَلِّمُهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَإِن كَانُواْ مِن قَبۡلُ لَفِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٍ

Lalle haqiqa Allah Ya yi baiwa ga muminai yayin da Ya aiko musu Manzo daga cikinsu, wanda yake karanta musu ayoyinsa, kuma yake tsarkake su, kuma yake koyar da su Littafi da Hikima, lalle kuma sun kasance kafin (zuwansa) tabbas suna cikin vata mabayyani



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 67

۞يَـٰٓأَيُّهَا ٱلرَّسُولُ بَلِّغۡ مَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَۖ وَإِن لَّمۡ تَفۡعَلۡ فَمَا بَلَّغۡتَ رِسَالَتَهُۥۚ وَٱللَّهُ يَعۡصِمُكَ مِنَ ٱلنَّاسِۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Ya kai wannan Manzo, ka isar da abin da aka saukar maka daga Ubangijinka; idan kuwa ba ka yi ba, to ba ka isar da saqonsa ba. Allah kuwa Shi ne Yake kare ka daga (sharrin) mutane. Lalle Allah ba Ya shiryar da mutanen da suke kafirai



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 92

وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَ وَٱحۡذَرُواْۚ فَإِن تَوَلَّيۡتُمۡ فَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّمَا عَلَىٰ رَسُولِنَا ٱلۡبَلَٰغُ ٱلۡمُبِينُ

Kuma ku bi Allah, kuma ku bi wannan Manzon, kuma ku yi hattara. Idan kuka juya baya, to ku sani abin da kawai yake kan Manzonmu shi ne isar da saqo filla-filla



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 99

مَّا عَلَى ٱلرَّسُولِ إِلَّا ٱلۡبَلَٰغُۗ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ مَا تُبۡدُونَ وَمَا تَكۡتُمُونَ

Babu abin da yake kan Manzo sai isarwa. Kuma Allah Yana sane da abin da kuke bayyanawa da abin da kuke voyewa



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 14

قُلۡ أَغَيۡرَ ٱللَّهِ أَتَّخِذُ وَلِيّٗا فَاطِرِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَهُوَ يُطۡعِمُ وَلَا يُطۡعَمُۗ قُلۡ إِنِّيٓ أُمِرۡتُ أَنۡ أَكُونَ أَوَّلَ مَنۡ أَسۡلَمَۖ وَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ

Ka ce: “Shin yanzu wanin Allah ne zan riqa a matsayin majivinci, alhalin Shi ne Ya halicci sammai da qasa, kuma Shi Yake ciyarwa, ba a ciyar da Shi?” Ka ce: “Lalle ni an umarce ni da in zamo farkon mai miqa wuya; kuma lalle kada ka kasance daga masu shirka.”



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 51

وَأَنذِرۡ بِهِ ٱلَّذِينَ يَخَافُونَ أَن يُحۡشَرُوٓاْ إِلَىٰ رَبِّهِمۡ لَيۡسَ لَهُم مِّن دُونِهِۦ وَلِيّٞ وَلَا شَفِيعٞ لَّعَلَّهُمۡ يَتَّقُونَ

Kuma ka yi gargaxi da shi (Alqur’ani) ga waxanda suke jin tsoron a tattara su a gaban Ubangijinsu, ba su da wani majivincin lamari in ba Shi ba, kuma ba su da wani mai ceto, don su kiyaye dokokin Allah



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 52

وَلَا تَطۡرُدِ ٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ رَبَّهُم بِٱلۡغَدَوٰةِ وَٱلۡعَشِيِّ يُرِيدُونَ وَجۡهَهُۥۖ مَا عَلَيۡكَ مِنۡ حِسَابِهِم مِّن شَيۡءٖ وَمَا مِنۡ حِسَابِكَ عَلَيۡهِم مِّن شَيۡءٖ فَتَطۡرُدَهُمۡ فَتَكُونَ مِنَ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Kuma kada ka kori waxannan da suke bauta wa Ubangijinsu safe da yamma, suna nufin Fuskarsa (watau suna yi don Shi kaxai); ba wani abu na haqqinsu a kanka, kuma babu wani abu na haqqinka a kansu, balle ka kore su, sai ka kasance cikin azzalumai.[1]


1- Daga nan zuwa aya ta 54 suna magana ne game da mushirikan Larabawa da suka nuna wa Manzon Allah () cewa za su musulunta amma da sharaxin zai kori Musulmi talakawa daga majalisarsa don kada su riqa yi musu rashin kunya. Sai Allah () ya hana shi aikata hakan.


Capítulo: Suratul An’am

Verso : 106

ٱتَّبِعۡ مَآ أُوحِيَ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَۖ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ وَأَعۡرِضۡ عَنِ ٱلۡمُشۡرِكِينَ

Ka bi abin da aka yi maka wahayi daga Ubangijinka; ba abin bautawa da gaskiya sai Shi; kuma ka kawar da kai daga mushrikai



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 107

وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ مَآ أَشۡرَكُواْۗ وَمَا جَعَلۡنَٰكَ عَلَيۡهِمۡ حَفِيظٗاۖ وَمَآ أَنتَ عَلَيۡهِم بِوَكِيلٖ

Kuma da Allah Ya ga dama, da ba su yi shirka ba. Ba Mu kuma sanya ka mai tsaro a kansu ba; kuma kai ba wakili ne a gare su ba



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 157

ٱلَّذِينَ يَتَّبِعُونَ ٱلرَّسُولَ ٱلنَّبِيَّ ٱلۡأُمِّيَّ ٱلَّذِي يَجِدُونَهُۥ مَكۡتُوبًا عِندَهُمۡ فِي ٱلتَّوۡرَىٰةِ وَٱلۡإِنجِيلِ يَأۡمُرُهُم بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَيَنۡهَىٰهُمۡ عَنِ ٱلۡمُنكَرِ وَيُحِلُّ لَهُمُ ٱلطَّيِّبَٰتِ وَيُحَرِّمُ عَلَيۡهِمُ ٱلۡخَبَـٰٓئِثَ وَيَضَعُ عَنۡهُمۡ إِصۡرَهُمۡ وَٱلۡأَغۡلَٰلَ ٱلَّتِي كَانَتۡ عَلَيۡهِمۡۚ فَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِهِۦ وَعَزَّرُوهُ وَنَصَرُوهُ وَٱتَّبَعُواْ ٱلنُّورَ ٱلَّذِيٓ أُنزِلَ مَعَهُۥٓ أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ

“(Su ne) waxanda suke bin Manzo Annabi Ummiyyi, wanda suke samun sa a rubuce a wurinsu a cikin Attaura da Linjila, yana umartar su da kyakkyawan abu, kuma yana hana su mummuna, kuma yana halatta musu daxaxan abubuwa, yana kuma haramta musu qazantattu, kuma yana sauke musu nauyaye-nauyayensu da ququmce-ququmcen da suka kasance a kansu[1]. Don haka waxanda suka yi imani da shi, kuma suka qarfafe shi, suka kuma taimake shi, suka bi hasken da aka saukar tare da shi, waxannan su ne masu rabauta.”


1- Nauyaye-nauyayensu su ne abubuwa masu wuya da aka wajabta musu aiki da su a littafin Attaura. Ququmce-ququmcensu kuwa su ne abubuwan da aka tsananta musu haramcinsu masu kama da ququmi.


Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 184

أَوَلَمۡ يَتَفَكَّرُواْۗ مَا بِصَاحِبِهِم مِّن جِنَّةٍۚ إِنۡ هُوَ إِلَّا نَذِيرٞ مُّبِينٌ

Shin ba za su yi tunani ba. Lalle abokin nasu fa babu hauka a tattare da shi. Ba kowa ne shi ba, face mai gargaxi, mai bayyanarwa?



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 65

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ حَرِّضِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ عَلَى ٱلۡقِتَالِۚ إِن يَكُن مِّنكُمۡ عِشۡرُونَ صَٰبِرُونَ يَغۡلِبُواْ مِاْئَتَيۡنِۚ وَإِن يَكُن مِّنكُم مِّاْئَةٞ يَغۡلِبُوٓاْ أَلۡفٗا مِّنَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِأَنَّهُمۡ قَوۡمٞ لَّا يَفۡقَهُونَ

Ya kai wannan Annabi, ka zaburar da muminai a kan yaqi. Idan daga cikinku akwai (mutum) ashirin masu haquri to za su rinjayi (mutum) xari biyu (kafirai). Idan kuma daga cikinku akwai (mutum) xari to za su rinjayi (mutum) dubu daga waxanda suka kafirta, saboda su mutane ne da ba sa ganewa



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 73

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ جَٰهِدِ ٱلۡكُفَّارَ وَٱلۡمُنَٰفِقِينَ وَٱغۡلُظۡ عَلَيۡهِمۡۚ وَمَأۡوَىٰهُمۡ جَهَنَّمُۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ

Ya kai wannan Annabi, ka yaqi kafirai da munafukai ka kuma tsananta musu. Jahannama ce kuma makomarsu. Makoma kuwa ta munana



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 103

خُذۡ مِنۡ أَمۡوَٰلِهِمۡ صَدَقَةٗ تُطَهِّرُهُمۡ وَتُزَكِّيهِم بِهَا وَصَلِّ عَلَيۡهِمۡۖ إِنَّ صَلَوٰتَكَ سَكَنٞ لَّهُمۡۗ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ

Ka karvi sadaka daga dukiyoyinsu da za ka tsarkake su kuma ka gyara musu halaye da ita, ka kuma yi musu addu’a. Lalle addu’arka nutsuwa ce a gare su. Allah kuwa Mai ji ne, Masani



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 113

مَا كَانَ لِلنَّبِيِّ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَن يَسۡتَغۡفِرُواْ لِلۡمُشۡرِكِينَ وَلَوۡ كَانُوٓاْ أُوْلِي قُرۡبَىٰ مِنۢ بَعۡدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمۡ أَنَّهُمۡ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَحِيمِ

Bai kamata ba ga Annabi da waxanda suka yi imani su nema wa mushrikai gafara, ko da kuwa sun kasance dangi ne na kusa, bayan kuwa ya riga ya bayyana gare su cewa lalle su ‘yan wuta ne



Capítulo: Suratu Yunus

Verso : 104

قُلۡ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِن كُنتُمۡ فِي شَكّٖ مِّن دِينِي فَلَآ أَعۡبُدُ ٱلَّذِينَ تَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلَٰكِنۡ أَعۡبُدُ ٱللَّهَ ٱلَّذِي يَتَوَفَّىٰكُمۡۖ وَأُمِرۡتُ أَنۡ أَكُونَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Ka ce: “Ya ku mutane, idan kun kasance cikin kokwanto game da addinina, to ba zan bauta wa waxanda kuke bauta wa ba Allah ba, sai dai ni zan bauta wa Allah ne wanda Yake karvar rayukanku, an kuma umarce ni da in zama cikin muminai



Capítulo: Suratu Yunus

Verso : 105

وَأَنۡ أَقِمۡ وَجۡهَكَ لِلدِّينِ حَنِيفٗا وَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ

“Kuma (an umarce ni) da cewa: ‘Ka tsai da fuskarka ga addinin Allah wanda ya karkace wa varna, kada kuma ka kasance cikin mushirikai



Capítulo: Suratu Yunus

Verso : 106

وَلَا تَدۡعُ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَنفَعُكَ وَلَا يَضُرُّكَۖ فَإِن فَعَلۡتَ فَإِنَّكَ إِذٗا مِّنَ ٱلظَّـٰلِمِينَ

“Kada kuma ka bauta wa wani ba Allah ba, abin da ba zai amfane ka ba, ba kuma zai cuce ka ba; to idan kuwa ka aikata haka to lalle daga sannan ka zama cikin azzalumai.’”



Capítulo: Suratu Yunus

Verso : 109

وَٱتَّبِعۡ مَا يُوحَىٰٓ إِلَيۡكَ وَٱصۡبِرۡ حَتَّىٰ يَحۡكُمَ ٱللَّهُۚ وَهُوَ خَيۡرُ ٱلۡحَٰكِمِينَ

Kuma ka bi abin da aka yi maka wahayinsa, ka kuma yi haquri har sai Allah Ya yi hukunci. Shi ne kuwa Fiyayyen masu hukunci



Capítulo: Suratu Hud

Verso : 2

أَلَّا تَعۡبُدُوٓاْ إِلَّا ٱللَّهَۚ إِنَّنِي لَكُم مِّنۡهُ نَذِيرٞ وَبَشِيرٞ

Da cewa kada ku bauta wa kowa sai Allah. (Ka ce): “Lalle ni mai yi muku gargaxi ne mai albishir daga gare Shi (Allah)



Capítulo: Suratu Hud

Verso : 112

فَٱسۡتَقِمۡ كَمَآ أُمِرۡتَ وَمَن تَابَ مَعَكَ وَلَا تَطۡغَوۡاْۚ إِنَّهُۥ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ

Don haka sai ka tsaya totar kamar yadda aka umarce ka kai da waxanda suka tuba tare da kai, kada kuwa ku wuce iyaka. Lalle Shi (Allah) Mai ganin abin da kuke aikatawa ne



Capítulo: Suratu Hud

Verso : 113

وَلَا تَرۡكَنُوٓاْ إِلَى ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ فَتَمَسَّكُمُ ٱلنَّارُ وَمَا لَكُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ مِنۡ أَوۡلِيَآءَ ثُمَّ لَا تُنصَرُونَ

Kuma kada ku karkata zuwa ga waxanda suka yi zalunci, sai wuta ta shafe ku, ba ku kuwa da wasu majivinta lamura ba Allah ba, sannan ba za a taimake ku ba



Capítulo: Suratu Hud

Verso : 114

وَأَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ طَرَفَيِ ٱلنَّهَارِ وَزُلَفٗا مِّنَ ٱلَّيۡلِۚ إِنَّ ٱلۡحَسَنَٰتِ يُذۡهِبۡنَ ٱلسَّيِّـَٔاتِۚ ذَٰلِكَ ذِكۡرَىٰ لِلذَّـٰكِرِينَ

Ka kuma tsai da salla farkon rana da qarshenta da kuma farkon dare. Lalle kyawawan (ayyuka) suna shafe munana. Wannan tunasarwa ne ga masu tunawa



Capítulo: Suratu Hud

Verso : 115

وَٱصۡبِرۡ فَإِنَّ ٱللَّهَ لَا يُضِيعُ أَجۡرَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Kuma ka yi haquri, domin lalle Allah ba Ya tozarta ladan masu kyautatawa



Capítulo: Suratur Ra’ad

Verso : 40

وَإِن مَّا نُرِيَنَّكَ بَعۡضَ ٱلَّذِي نَعِدُهُمۡ أَوۡ نَتَوَفَّيَنَّكَ فَإِنَّمَا عَلَيۡكَ ٱلۡبَلَٰغُ وَعَلَيۡنَا ٱلۡحِسَابُ

Ko dai Mu nuna maka irin sashin abin da Muke yi musu gargaxi da aukuwarsa, ko kuma Mu karvi ranka (kafin lokacin), abin da yake kanka kawai shi ne isar da aike, Mu kuma hisabi yana a kanmu



Capítulo: Suratul Hijr

Verso : 89

وَقُلۡ إِنِّيٓ أَنَا ٱلنَّذِيرُ ٱلۡمُبِينُ

Ka kuma ce: “Lalle ni, ni ne mai gargaxi mabayyani»



Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 82

فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَإِنَّمَا عَلَيۡكَ ٱلۡبَلَٰغُ ٱلۡمُبِينُ

To idan suka ba da baya, to kai isar da aike a fili ne kawai a kanka



Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 125

ٱدۡعُ إِلَىٰ سَبِيلِ رَبِّكَ بِٱلۡحِكۡمَةِ وَٱلۡمَوۡعِظَةِ ٱلۡحَسَنَةِۖ وَجَٰدِلۡهُم بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعۡلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِۦ وَهُوَ أَعۡلَمُ بِٱلۡمُهۡتَدِينَ

Ka yi kira zuwa ga tafarkin Ubangiijnka cikin hikima da kyakkyawan wa’azi, ka kuma yi jayayya da su ta hanyar da ta fi kyau. Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sanin wanda ya vace daga hanyarsa, kuma Shi ne Mafi sanin shiryayyu