Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 64

قُلۡ يَـٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ تَعَالَوۡاْ إِلَىٰ كَلِمَةٖ سَوَآءِۭ بَيۡنَنَا وَبَيۡنَكُمۡ أَلَّا نَعۡبُدَ إِلَّا ٱللَّهَ وَلَا نُشۡرِكَ بِهِۦ شَيۡـٔٗا وَلَا يَتَّخِذَ بَعۡضُنَا بَعۡضًا أَرۡبَابٗا مِّن دُونِ ٱللَّهِۚ فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَقُولُواْ ٱشۡهَدُواْ بِأَنَّا مُسۡلِمُونَ

Ka ce: “Ya ku Ma’abota Littafi, ku taho ga wata kalma mai daidaitawa tsakaninmu da ku cewa, kar mu bauta wa kowa sai Allah, kuma kar mu haxa Shi da wani, kuma kada wani sashi a cikinmu ya riqi wani sashi a matsayin abin bauta ba Allah ba.” Idan kuwa sun ba da baya, to ku ce: “Ku shaida cewa, lalle mu Musulmi ne.”



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 67

مَا كَانَ إِبۡرَٰهِيمُ يَهُودِيّٗا وَلَا نَصۡرَانِيّٗا وَلَٰكِن كَانَ حَنِيفٗا مُّسۡلِمٗا وَمَا كَانَ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ

Ibrahimu bai tava zama Bayahude ba, sannan bai tava zama Banasare ba, sai dai ya kasance mai barin varna ne, Musulmi, kuma bai kasance xaya daga cikin mushirikai ba



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 84

قُلۡ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَمَآ أُنزِلَ عَلَيۡنَا وَمَآ أُنزِلَ عَلَىٰٓ إِبۡرَٰهِيمَ وَإِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ وَٱلۡأَسۡبَاطِ وَمَآ أُوتِيَ مُوسَىٰ وَعِيسَىٰ وَٱلنَّبِيُّونَ مِن رَّبِّهِمۡ لَا نُفَرِّقُ بَيۡنَ أَحَدٖ مِّنۡهُمۡ وَنَحۡنُ لَهُۥ مُسۡلِمُونَ

Ka ce: “Mun yi imani da Allah da abin da aka saukar mana da kuma abin da aka saukar wa Ibrahim da Isma’ila da Ishaq da Ya’aqub da jikokin (Ya’aqub), da abin da aka ba wa Musa da Isa da abin da aka ba wa annabawa daga Ubangijinsu; ba ma nuna bambanci a kan xaya daga cikinsu, kuma mu muna masu miqa wuya gare Shi.”



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 102

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّقُواْ ٱللَّهَ حَقَّ تُقَاتِهِۦ وَلَا تَمُوتُنَّ إِلَّا وَأَنتُم مُّسۡلِمُونَ

Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi taqawa ga Allah haqiqanin taqawa, kuma lalle kada ku mutu face kuna Musulmi



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 163

لَا شَرِيكَ لَهُۥۖ وَبِذَٰلِكَ أُمِرۡتُ وَأَنَا۠ أَوَّلُ ٱلۡمُسۡلِمِينَ

“Ba Shi da abokin tarayya; kuma da hakan aka umarce ni, kuma ni ne farkon Musulmai.”



Capítulo: Suratu Hud

Verso : 14

فَإِلَّمۡ يَسۡتَجِيبُواْ لَكُمۡ فَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّمَآ أُنزِلَ بِعِلۡمِ ٱللَّهِ وَأَن لَّآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ فَهَلۡ أَنتُم مُّسۡلِمُونَ

To idan ba su amsa muku ba, to ku tabbatar cewa lalle an saukar da shi ne (Alqur’ani) da sanin Allah, kuma babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi, To shin yanzu za ku miqa wuya?



Capítulo: Suratul Hijr

Verso : 2

رُّبَمَا يَوَدُّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَوۡ كَانُواْ مُسۡلِمِينَ

Waxanda suka kafirta za su riqa burin ina ma da sun zama Musulmai[1]


1- Watau a ranar alqiyama ko kuma lokacin mutuwarsa.


Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 89

وَيَوۡمَ نَبۡعَثُ فِي كُلِّ أُمَّةٖ شَهِيدًا عَلَيۡهِم مِّنۡ أَنفُسِهِمۡۖ وَجِئۡنَا بِكَ شَهِيدًا عَلَىٰ هَـٰٓؤُلَآءِۚ وَنَزَّلۡنَا عَلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ تِبۡيَٰنٗا لِّكُلِّ شَيۡءٖ وَهُدٗى وَرَحۡمَةٗ وَبُشۡرَىٰ لِلۡمُسۡلِمِينَ

Kuma (ka tuna) ranar da za Mu tayar wa kowace al’umma da mai ba da shaida a kansu daga jinsinsu, Mu kuma zo da kai (Annabi Muhammadu) shaida a kan waxannan (wato al’ummarka). Kuma Mun saukar maka da Littafi ne (wato Alqur’ani) don bayani ga kowanne abu, kuma shiriya da rahama da bushara ga Musulmi



Capítulo: Suratul Anbiya

Verso : 108

قُلۡ إِنَّمَا يُوحَىٰٓ إِلَيَّ أَنَّمَآ إِلَٰهُكُمۡ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۖ فَهَلۡ أَنتُم مُّسۡلِمُونَ

Ka ce (da su): “Abin da kawai ake yiwo min wahayinsa (shi ne) lallai abin bautar ku Allah ne Guda Xaya; to shin ko za ku miqa wuya?”



Capítulo: Suratul Hajji

Verso : 78

وَجَٰهِدُواْ فِي ٱللَّهِ حَقَّ جِهَادِهِۦۚ هُوَ ٱجۡتَبَىٰكُمۡ وَمَا جَعَلَ عَلَيۡكُمۡ فِي ٱلدِّينِ مِنۡ حَرَجٖۚ مِّلَّةَ أَبِيكُمۡ إِبۡرَٰهِيمَۚ هُوَ سَمَّىٰكُمُ ٱلۡمُسۡلِمِينَ مِن قَبۡلُ وَفِي هَٰذَا لِيَكُونَ ٱلرَّسُولُ شَهِيدًا عَلَيۡكُمۡ وَتَكُونُواْ شُهَدَآءَ عَلَى ٱلنَّاسِۚ فَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ وَٱعۡتَصِمُواْ بِٱللَّهِ هُوَ مَوۡلَىٰكُمۡۖ فَنِعۡمَ ٱلۡمَوۡلَىٰ وَنِعۡمَ ٱلنَّصِيرُ

Kuma ku yi jihadi wajen (xaukaka addinin) Allah iyakar iyawarku. Shi ne Ya zave ku, bai kuma sanya muku wani qunci ba cikin addini. Addinin Babanku ne Ibrahimu. (Allah) Shi ne Ya kira ku Musulmi tuntuni, da kuma cikin wannan (Alqur’ani) don Manzo ya zama shaida a gare ku, ku kuma ku zama shaida ga (sauran) mutane. To sai ku tsai da salla kuma ku ba da zakka, ku kuma yi riqo da (addinin) Allah, Shi ne Majivincin al’amarinku; to madalla da Majivinci, kuma madalla da Mataimaki



Capítulo: Suratun Namli

Verso : 81

وَمَآ أَنتَ بِهَٰدِي ٱلۡعُمۡيِ عَن ضَلَٰلَتِهِمۡۖ إِن تُسۡمِعُ إِلَّا مَن يُؤۡمِنُ بِـَٔايَٰتِنَا فَهُم مُّسۡلِمُونَ

Kuma sannan kai ba za ka iya shiryar da makafi daga vatansu ba; ba wanda kake iya jiyarwa sai wanda ya yi imani da ayoyinmu, to waxannan su ne Musulmi



Capítulo: Suratun Namli

Verso : 91

إِنَّمَآ أُمِرۡتُ أَنۡ أَعۡبُدَ رَبَّ هَٰذِهِ ٱلۡبَلۡدَةِ ٱلَّذِي حَرَّمَهَا وَلَهُۥ كُلُّ شَيۡءٖۖ وَأُمِرۡتُ أَنۡ أَكُونَ مِنَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ

(Ka ce da su): “Ni dai an umarce ni ne kawai da in bauta wa Ubangijin wannan garin (Makka) wanda Ya mayar da shi mai alfarma, kuma komai nasa ne; kuma an umarce ni da in zama cikin Musulmi



Capítulo: Suratul Qasas

Verso : 52

ٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ مِن قَبۡلِهِۦ هُم بِهِۦ يُؤۡمِنُونَ

Waxanda Muka bai wa littafi a gabaninsa (Alqur’ani) (suka tsaya a kansa) su suna yin imani da shi (Alqur’ani)



Capítulo: Suratul Qasas

Verso : 53

وَإِذَا يُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ قَالُوٓاْ ءَامَنَّا بِهِۦٓ إِنَّهُ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّنَآ إِنَّا كُنَّا مِن قَبۡلِهِۦ مُسۡلِمِينَ

Idan kuma ana karanta musu (Alqur’anin) sai su ce: “Mun yi imani da shi, lalle shi gaskiya ne daga Ubangijinmu, lalle mu mun kasance Musulmi tun gabaninsa.”



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 53

وَمَآ أَنتَ بِهَٰدِ ٱلۡعُمۡيِ عَن ضَلَٰلَتِهِمۡۖ إِن تُسۡمِعُ إِلَّا مَن يُؤۡمِنُ بِـَٔايَٰتِنَا فَهُم مُّسۡلِمُونَ

Kuma kai ba mai iya shiryar da makafi (wato vatattu) ba ne daga vatansu; ba waxanda kake iya jiyarwa sai waxanda suka yi imani da ayoyinmu don haka suna masu miqa wuya



Capítulo: Suratul Ahzab

Verso : 35

إِنَّ ٱلۡمُسۡلِمِينَ وَٱلۡمُسۡلِمَٰتِ وَٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ وَٱلۡقَٰنِتِينَ وَٱلۡقَٰنِتَٰتِ وَٱلصَّـٰدِقِينَ وَٱلصَّـٰدِقَٰتِ وَٱلصَّـٰبِرِينَ وَٱلصَّـٰبِرَٰتِ وَٱلۡخَٰشِعِينَ وَٱلۡخَٰشِعَٰتِ وَٱلۡمُتَصَدِّقِينَ وَٱلۡمُتَصَدِّقَٰتِ وَٱلصَّـٰٓئِمِينَ وَٱلصَّـٰٓئِمَٰتِ وَٱلۡحَٰفِظِينَ فُرُوجَهُمۡ وَٱلۡحَٰفِظَٰتِ وَٱلذَّـٰكِرِينَ ٱللَّهَ كَثِيرٗا وَٱلذَّـٰكِرَٰتِ أَعَدَّ ٱللَّهُ لَهُم مَّغۡفِرَةٗ وَأَجۡرًا عَظِيمٗا

Lalle Musulmi maza da Musulmi mata, da muminai maza da muminai mata, da masu biyayya maza da masu biyayya mata, da masu gaskiya maza da masu gaskiya mata, da masu haquri maza da masu haquri mata, da masu qasqantar da kai maza da masu qasqantar da kai mata, da masu sadaka maza da masu sadaka mata, da masu azumi maza da masu azumi mata, da maza masu kiyaye farjinsu da mata masu kiyaye farjinsu, da maza masu ambaton Allah da yawa da mata masu ambaton Allah (da yawa, dukkaninsu) Allah ya tanadar musu gafara da lada mai girma



Capítulo: Suratuz Zumar

Verso : 11

قُلۡ إِنِّيٓ أُمِرۡتُ أَنۡ أَعۡبُدَ ٱللَّهَ مُخۡلِصٗا لَّهُ ٱلدِّينَ

Ka ce: “Lalle ni an umarce ni da in bauta wa Allah ina mai tsantsanta addini gare Shi



Capítulo: Suratuz Zumar

Verso : 12

وَأُمِرۡتُ لِأَنۡ أَكُونَ أَوَّلَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ

“An kuma umarce ni da in kasance farkon Musulmi.”



Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 33

وَمَنۡ أَحۡسَنُ قَوۡلٗا مِّمَّن دَعَآ إِلَى ٱللَّهِ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا وَقَالَ إِنَّنِي مِنَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ

Wane ne ya fi kyakkyawar magana fiye da wanda ya yi kira zuwa ga Allah ya kuma yi aiki nagari, kuma ya ce: “Lalle ni ina daga cikin Musulmi?”



Capítulo: Suratuz Zukhruf 

Verso : 68

يَٰعِبَادِ لَا خَوۡفٌ عَلَيۡكُمُ ٱلۡيَوۡمَ وَلَآ أَنتُمۡ تَحۡزَنُونَ

Ya ku bayina, babu wani tsoro gare ku a yau, kuma ba za ku yi baqin ciki ba



Capítulo: Suratuz Zukhruf 

Verso : 69

ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَكَانُواْ مُسۡلِمِينَ

(Su ne) waxanda suka yi imani da ayoyinmu, suka kuma kasance Musulmi



Capítulo: Suratul Ahqaf 

Verso : 15

وَوَصَّيۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ بِوَٰلِدَيۡهِ إِحۡسَٰنًاۖ حَمَلَتۡهُ أُمُّهُۥ كُرۡهٗا وَوَضَعَتۡهُ كُرۡهٗاۖ وَحَمۡلُهُۥ وَفِصَٰلُهُۥ ثَلَٰثُونَ شَهۡرًاۚ حَتَّىٰٓ إِذَا بَلَغَ أَشُدَّهُۥ وَبَلَغَ أَرۡبَعِينَ سَنَةٗ قَالَ رَبِّ أَوۡزِعۡنِيٓ أَنۡ أَشۡكُرَ نِعۡمَتَكَ ٱلَّتِيٓ أَنۡعَمۡتَ عَلَيَّ وَعَلَىٰ وَٰلِدَيَّ وَأَنۡ أَعۡمَلَ صَٰلِحٗا تَرۡضَىٰهُ وَأَصۡلِحۡ لِي فِي ذُرِّيَّتِيٓۖ إِنِّي تُبۡتُ إِلَيۡكَ وَإِنِّي مِنَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ

Kuma Mun yi wa mutum wasiyya da kyautata wa mahaifansa; mahaifiyarsa ta xauki cikinsa a wahalce, ta kuma haife shi a wahalce; xaukan cikinsa da yaye shi kuma wata talatin ne, har lokacin da ya cika qarfinsa ya kai shekara arba’in ya ce: “Ya Ubangijina, Ka kimsa min yadda zan gode wa ni’imarka, wadda Ka ni’imta ni da ita da kuma mahaifana, kuma (Ka ba ni iko) in yi aiki nagari wanda za Ka yarda da shi, kuma Ka kyautata min zurriyata; lalle ni na tuba a gare Ka, kuma lalle ni ina daga cikin Musulmi.”



Capítulo: Suratul Qalam

Verso : 35

أَفَنَجۡعَلُ ٱلۡمُسۡلِمِينَ كَٱلۡمُجۡرِمِينَ

Yanzu za Mu sanya Musulmi kamar kangararru?



Capítulo: Suratul Jinn

Verso : 14

وَأَنَّا مِنَّا ٱلۡمُسۡلِمُونَ وَمِنَّا ٱلۡقَٰسِطُونَۖ فَمَنۡ أَسۡلَمَ فَأُوْلَـٰٓئِكَ تَحَرَّوۡاْ رَشَدٗا

“Kuma lalle mu a cikinmu akwai Musulmi, a cikinmu kuma akwai karkatattu; saboda haka duk wanda ya musulunta, to waxannan sun nufi hanyar shiriya