Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 20

يَكَادُ ٱلۡبَرۡقُ يَخۡطَفُ أَبۡصَٰرَهُمۡۖ كُلَّمَآ أَضَآءَ لَهُم مَّشَوۡاْ فِيهِ وَإِذَآ أَظۡلَمَ عَلَيۡهِمۡ قَامُواْۚ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ لَذَهَبَ بِسَمۡعِهِمۡ وَأَبۡصَٰرِهِمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Walqiyar ta kusa ta fauce idanuwansu. Duk sa›adda ta haska musu sai su ci gaba da tafiya cikin (haskenta); idan kuma ta rufe su da duhu sai su tsaya cak. Da kuwa Allah Ya ga dama da sai Ya tafiyar da jinsu da ganinsu. Lalle Allah Mai iko ne a kan komai



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 148

وَلِكُلّٖ وِجۡهَةٌ هُوَ مُوَلِّيهَاۖ فَٱسۡتَبِقُواْ ٱلۡخَيۡرَٰتِۚ أَيۡنَ مَا تَكُونُواْ يَأۡتِ بِكُمُ ٱللَّهُ جَمِيعًاۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Kuma kowane vangare yana da inda ya sa gaba, don haka sai ku yi gaggawar cim ma alheri. A duk inda kuke Allah zai zo da ku gaba xaya. Lalle Allah Mai iko ne a kan komai



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 26

قُلِ ٱللَّهُمَّ مَٰلِكَ ٱلۡمُلۡكِ تُؤۡتِي ٱلۡمُلۡكَ مَن تَشَآءُ وَتَنزِعُ ٱلۡمُلۡكَ مِمَّن تَشَآءُ وَتُعِزُّ مَن تَشَآءُ وَتُذِلُّ مَن تَشَآءُۖ بِيَدِكَ ٱلۡخَيۡرُۖ إِنَّكَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Ka ce: “Ya Allah, Kai ne Mamallakin mulki, Kana bayar da mulki ga wanda Ka ga dama, kuma Kana qwace mulki daga wanda Ka ga dama, kuma Kana xaukaka wanda Ka ga dama, kuma Kana qasqantar da wanda Ka ga dama; duk alheri yana hannuka, lalle Kai Mai iko ne a kan komai



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 27

تُولِجُ ٱلَّيۡلَ فِي ٱلنَّهَارِ وَتُولِجُ ٱلنَّهَارَ فِي ٱلَّيۡلِۖ وَتُخۡرِجُ ٱلۡحَيَّ مِنَ ٱلۡمَيِّتِ وَتُخۡرِجُ ٱلۡمَيِّتَ مِنَ ٱلۡحَيِّۖ وَتَرۡزُقُ مَن تَشَآءُ بِغَيۡرِ حِسَابٖ

“Kana shigar da dare a cikin yini, kuma Kana shigar da yini a cikin dare, kuma Kana fitar da mai rai daga cikin matacce, kuma Kana fitar da matacce daga cikin mai rai; kuma Kana arzurta wanda Ka ga dama ba tare da lissafi ba.”



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 133

إِن يَشَأۡ يُذۡهِبۡكُمۡ أَيُّهَا ٱلنَّاسُ وَيَأۡتِ بِـَٔاخَرِينَۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلَىٰ ذَٰلِكَ قَدِيرٗا

Idan Ya ga dama sai Ya tafiyar da ku, ya ku mutane, kuma Ya kawo waxansu daban. Allah kuwa Ya kasance Mai iko ne a kan hakan



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 40

أَلَمۡ تَعۡلَمۡ أَنَّ ٱللَّهَ لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ يُعَذِّبُ مَن يَشَآءُ وَيَغۡفِرُ لِمَن يَشَآءُۗ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Shin ba ka da masaniyar cewa, lalle Allah Shi ne Yake mallakar abin da yake cikin sammai da kuma qasa, Yana yin azaba ga wanda Ya ga dama, kuma Yana gafarta wa wanda Ya ga dama. Kuma Allah Mai iko ne a kan komai?



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 37

وَقَالُواْ لَوۡلَا نُزِّلَ عَلَيۡهِ ءَايَةٞ مِّن رَّبِّهِۦۚ قُلۡ إِنَّ ٱللَّهَ قَادِرٌ عَلَىٰٓ أَن يُنَزِّلَ ءَايَةٗ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ

Kuma suka ce: “Ina ma da an saukar masa da wata aya daga Ubangijinsa ?” Ka ce: “Lalle Allah Mai iko ne a kan Ya saukar da kowace irin aya, sai dai yawancinsu ba sa sanin (haka).”



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 65

قُلۡ هُوَ ٱلۡقَادِرُ عَلَىٰٓ أَن يَبۡعَثَ عَلَيۡكُمۡ عَذَابٗا مِّن فَوۡقِكُمۡ أَوۡ مِن تَحۡتِ أَرۡجُلِكُمۡ أَوۡ يَلۡبِسَكُمۡ شِيَعٗا وَيُذِيقَ بَعۡضَكُم بَأۡسَ بَعۡضٍۗ ٱنظُرۡ كَيۡفَ نُصَرِّفُ ٱلۡأٓيَٰتِ لَعَلَّهُمۡ يَفۡقَهُونَ

Ka ce: “Shi ne Mai cikakken ikon Ya aiko muku da azaba ta samanku ko ta qarqashin qafafuwanku ko Ya mayar da ku qungiyoyi daban-daban, kuma Ya xanxana wa sashinku azabar sashi.” Duba ka ga yadda Muke bayyana ayoyi, don su fahimta



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 73

وَهُوَ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ بِٱلۡحَقِّۖ وَيَوۡمَ يَقُولُ كُن فَيَكُونُۚ قَوۡلُهُ ٱلۡحَقُّۚ وَلَهُ ٱلۡمُلۡكُ يَوۡمَ يُنفَخُ فِي ٱلصُّورِۚ عَٰلِمُ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِۚ وَهُوَ ٱلۡحَكِيمُ ٱلۡخَبِيرُ

“Kuma Shi ne Wanda ya halicci sammai da qasa da gaskiya; kuma (ku tuna) ranar da zai ce da abu: ‘Kasance!’ Nan take sai ya kasance. Maganarsa gaskiya ce. Kuma Shi ne Yake da cikakken mulki a ranar da za a busa qaho Masanin gaibu da sarari, kuma Shi ne Mai hikima, Mai cikakken sani.”



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 39

إِلَّا تَنفِرُواْ يُعَذِّبۡكُمۡ عَذَابًا أَلِيمٗا وَيَسۡتَبۡدِلۡ قَوۡمًا غَيۡرَكُمۡ وَلَا تَضُرُّوهُ شَيۡـٔٗاۗ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ

Idan ba za ku fita (yaqi ba to (Allah) zai azabtar da ku da azaba mai raxaxi, Ya kuma canja wasu mutanen daban, ba kuwa za ku cutar da Shi da komai ba. Allah kuwa Mai iko ne a kan komai



Capítulo: Suratul Kahf 

Verso : 45

وَٱضۡرِبۡ لَهُم مَّثَلَ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا كَمَآءٍ أَنزَلۡنَٰهُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ فَٱخۡتَلَطَ بِهِۦ نَبَاتُ ٱلۡأَرۡضِ فَأَصۡبَحَ هَشِيمٗا تَذۡرُوهُ ٱلرِّيَٰحُۗ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ مُّقۡتَدِرًا

Kuma ka ba su misalin rayuwar duniya (wadda take) kamar ruwa ne da Muka saukar da shi daga sama, sai tsirran qasa suka cakuxa da shi, sannan ya zama busasshe, iska tana xaixaita shi. Allah kuwa Ya kasance Mai iko ne a kan komai



Capítulo: Suratul Hajji

Verso : 39

أُذِنَ لِلَّذِينَ يُقَٰتَلُونَ بِأَنَّهُمۡ ظُلِمُواْۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ نَصۡرِهِمۡ لَقَدِيرٌ

An yi izini (na yin yaqi) ga waxanda ake yaqa[1] don ko lalle an zalunce su. Lalle kuma Allah Mai iko ne bisa taimakon su


1- Watau sahabban Annabi () waxanda kafirai a lokacin suke yaqar su.


Capítulo: Suratul Mu’uminun

Verso : 18

وَأَنزَلۡنَا مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءَۢ بِقَدَرٖ فَأَسۡكَنَّـٰهُ فِي ٱلۡأَرۡضِۖ وَإِنَّا عَلَىٰ ذَهَابِۭ بِهِۦ لَقَٰدِرُونَ

Muka kuma saukar da ruwa daga sama daidai gwargwado, sai Muka zaunar da shi a cikin qasa, kuma lalle Mu Masu iko ne a kan kawar da shi



Capítulo: Suratul Mu’uminun

Verso : 95

وَإِنَّا عَلَىٰٓ أَن نُّرِيَكَ مَا نَعِدُهُمۡ لَقَٰدِرُونَ

Mu kuma lalle Masu iko ne a kan Mu nuna maka abin da Muke musu alkawari



Capítulo: Suratun Namli

Verso : 60

أَمَّنۡ خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَأَنزَلَ لَكُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَنۢبَتۡنَا بِهِۦ حَدَآئِقَ ذَاتَ بَهۡجَةٖ مَّا كَانَ لَكُمۡ أَن تُنۢبِتُواْ شَجَرَهَآۗ أَءِلَٰهٞ مَّعَ ٱللَّهِۚ بَلۡ هُمۡ قَوۡمٞ يَعۡدِلُونَ

Ko kuwa wane ne ya halicci sammai da qasa, ya kuma saukar muku da ruwa daga sama, sannan Muka tsirar da (shukokin) gonaki masu qayatarwa, ba kuwa za ku iya tsirar da bishiyoyinsu ba? Shin akwai wani abin bauta na gaskiya tare da Allah? A’a, su dai mutane ne da suke kauce wa gaskiya



Capítulo: Suratun Namli

Verso : 61

أَمَّن جَعَلَ ٱلۡأَرۡضَ قَرَارٗا وَجَعَلَ خِلَٰلَهَآ أَنۡهَٰرٗا وَجَعَلَ لَهَا رَوَٰسِيَ وَجَعَلَ بَيۡنَ ٱلۡبَحۡرَيۡنِ حَاجِزًاۗ أَءِلَٰهٞ مَّعَ ٱللَّهِۚ بَلۡ أَكۡثَرُهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ

Ko kuwa wane ne ya sanya qasa wurin zama, ya kuma sanya qoramu a tsattsakinta, kuma ya sanya mata turaku, kana kuma ya sanya shamaki tsakanin kogunan nan biyu (na ruwan daxi da na ruwan zartsi)? Shin akwai wani abin bauta da gaskiya tare da Allah? A’a, yawancinsu dai ba sa ganewa



Capítulo: Suratun Namli

Verso : 62

أَمَّن يُجِيبُ ٱلۡمُضۡطَرَّ إِذَا دَعَاهُ وَيَكۡشِفُ ٱلسُّوٓءَ وَيَجۡعَلُكُمۡ خُلَفَآءَ ٱلۡأَرۡضِۗ أَءِلَٰهٞ مَّعَ ٱللَّهِۚ قَلِيلٗا مَّا تَذَكَّرُونَ

Ko kuwa wane ne yake amsa wa wanda yake cikin matsuwa lokacin da ya roqe shi, yake kuma yaye duk wani bala’i, yake kuma sanya ku halifofi a bayan qasa[1]? Shin akwai wani abin bauta da gaskiya tare da Allah? Kaxan ne qwarai kuke wa’azantuwa


1- Wasu su shuxe wasu su zo su gaje su, tsareku bayan tsareku.


Capítulo: Suratun Namli

Verso : 63

أَمَّن يَهۡدِيكُمۡ فِي ظُلُمَٰتِ ٱلۡبَرِّ وَٱلۡبَحۡرِ وَمَن يُرۡسِلُ ٱلرِّيَٰحَ بُشۡرَۢا بَيۡنَ يَدَيۡ رَحۡمَتِهِۦٓۗ أَءِلَٰهٞ مَّعَ ٱللَّهِۚ تَعَٰلَى ٱللَّهُ عَمَّا يُشۡرِكُونَ

Ko kuwa wane ne yake shiryar da ku a cikin duffan tudu da na kogi, kuma wane ne yake sako iska tana mai bushara gabanin (saukar) rahamarsa? Shin akwai wani abin bauta da gaskiya tare da Allah? Allah Ya xaukaka daga abin da suke tara (Shi da shi)



Capítulo: Suratun Namli

Verso : 64

أَمَّن يَبۡدَؤُاْ ٱلۡخَلۡقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥ وَمَن يَرۡزُقُكُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِۗ أَءِلَٰهٞ مَّعَ ٱللَّهِۚ قُلۡ هَاتُواْ بُرۡهَٰنَكُمۡ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

Ko kuwa wane ne yake qagar halitta sannan ya dawo da ita (bayan mutuwa), kuma wane ne yake arzuta ku ta sama da qasa? Shin akwai wani abin bauta da gaskiya tare da Allah?” Ka ce (da su): “Ku kawo dalilinku idan kun kasance masu gaskiya.”



Capítulo: Suratun Namli

Verso : 88

وَتَرَى ٱلۡجِبَالَ تَحۡسَبُهَا جَامِدَةٗ وَهِيَ تَمُرُّ مَرَّ ٱلسَّحَابِۚ صُنۡعَ ٱللَّهِ ٱلَّذِيٓ أَتۡقَنَ كُلَّ شَيۡءٍۚ إِنَّهُۥ خَبِيرُۢ بِمَا تَفۡعَلُونَ

Kuma za ka ga duwatsu ka zaci a tsaye suke cak, alhali kuwa su suna tafiya ne irin tafiyar gizagizai. Aikin Allah kenan wanda Ya kyautata halittar kowane irin abu. Lalle Shi Masanin abin da kuke aikatawa ne



Capítulo: Suratu Faxir

Verso : 44

أَوَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ وَكَانُوٓاْ أَشَدَّ مِنۡهُمۡ قُوَّةٗۚ وَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيُعۡجِزَهُۥ مِن شَيۡءٖ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَلَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ إِنَّهُۥ كَانَ عَلِيمٗا قَدِيرٗا

Shin ba su yi tafiya ba ne a cikin qasa, sai su ga yaya qarshen waxanda suke gabaninsu ya kasance, alhali kuwa sun zamanto qarfafa fiye da su? Ba kuwa wani abu da zai gagari Allah a cikin sammai ko a cikin qasa. Lalle Shi Ya kasance Masani ne, Mai iko



Capítulo: Suratuz Zukhruf 

Verso : 42

أَوۡ نُرِيَنَّكَ ٱلَّذِي وَعَدۡنَٰهُمۡ فَإِنَّا عَلَيۡهِم مُّقۡتَدِرُونَ

Ko kuma Muka nuna maka irin abin da muka yi musu alqawarin narko da shi, to lalle Mu Masu iko ne a kansu



Capítulo: Suratul Hashr

Verso : 6

وَمَآ أَفَآءَ ٱللَّهُ عَلَىٰ رَسُولِهِۦ مِنۡهُمۡ فَمَآ أَوۡجَفۡتُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ خَيۡلٖ وَلَا رِكَابٖ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يُسَلِّطُ رُسُلَهُۥ عَلَىٰ مَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Kuma duk abin da Allah Ya bai wa Manzonsa na wata dukiya tasu (don falalarsa), to ba wani hari kuka kai na dawaki ko raquma[1] ba saboda shi, sai dai kuma Allah Shi ne Yake xora manzanninsa a kan wanda Ya ga dama. Allah kuwa Mai iko ne a kan komai


1- Watau ku sami dukiya ba tare da yaqi ba.


Capítulo: Suratul Mulk

Verso : 1

تَبَٰرَكَ ٱلَّذِي بِيَدِهِ ٱلۡمُلۡكُ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ

Wanda mulki yake a hannunsa alhairansa sun yawaita, kuma Shi Mai iko ne a kan komai



Capítulo: Suratul Ma’arij

Verso : 40

فَلَآ أُقۡسِمُ بِرَبِّ ٱلۡمَشَٰرِقِ وَٱلۡمَغَٰرِبِ إِنَّا لَقَٰدِرُونَ

To, ina yin rantsuwa da Ubangijin wuraren hudowar rana da wuraren faxuwarta, lalle Mu Masu iko ne



Capítulo: Suratul Ma’arij

Verso : 41

عَلَىٰٓ أَن نُّبَدِّلَ خَيۡرٗا مِّنۡهُمۡ وَمَا نَحۡنُ بِمَسۡبُوقِينَ

A kan Mu musanya wasu fiye da su, kuma Mu ba Masu kasawa ba ne