وَبَشِّرِ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ أَنَّ لَهُمۡ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۖ كُلَّمَا رُزِقُواْ مِنۡهَا مِن ثَمَرَةٖ رِّزۡقٗا قَالُواْ هَٰذَا ٱلَّذِي رُزِقۡنَا مِن قَبۡلُۖ وَأُتُواْ بِهِۦ مُتَشَٰبِهٗاۖ وَلَهُمۡ فِيهَآ أَزۡوَٰجٞ مُّطَهَّرَةٞۖ وَهُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ
Kuma ka yi albishir ga waxanda suka yi imani kuma suka aikata ayyuka na qwarai cewa suna da wasu gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu. Duk sa’adda aka arzuta su da ’ya’yan itatuwa daga gare su sai su ce: “Wannan shi ne irin abin da aka arzuta mu da shi xazu.” An kawo musu shi yana mai kama da juna, kuma suna da wasu mata tsarkaka a cikinsu, kuma su masu zama ne a cikinsu dindindin
۞قُلۡ أَؤُنَبِّئُكُم بِخَيۡرٖ مِّن ذَٰلِكُمۡۖ لِلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْ عِندَ رَبِّهِمۡ جَنَّـٰتٞ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَا وَأَزۡوَٰجٞ مُّطَهَّرَةٞ وَرِضۡوَٰنٞ مِّنَ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ بَصِيرُۢ بِٱلۡعِبَادِ
Ka ce: “Shin in ba ku labarin da abin da ya fi waxancan alheri? Waxanda suka yi taqawa, suna da wasu gidajen aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, a wurin Ubangijinsu, suna masu zama a cikinsu dindindin da mata na aure tsarkaka da kuma yarda daga Allah. Kuma Allah Mai ganin bayinsa ne.”
ٱلَّذِينَ يَقُولُونَ رَبَّنَآ إِنَّنَآ ءَامَنَّا فَٱغۡفِرۡ لَنَا ذُنُوبَنَا وَقِنَا عَذَابَ ٱلنَّارِ
(Su ne) waxanda suke cewa: “Ya Ubangijinmu, lalle mu mun yi imani, don haka Ka gafarta mana zunubanmu, kuma Ka tserar da mu daga azabar wuta.”
ٱلصَّـٰبِرِينَ وَٱلصَّـٰدِقِينَ وَٱلۡقَٰنِتِينَ وَٱلۡمُنفِقِينَ وَٱلۡمُسۡتَغۡفِرِينَ بِٱلۡأَسۡحَارِ
(Su ne) masu haquri, masu gaskiya, kuma masu xa’a, kuma masu ciyarwa, kuma masu neman gafara a qarshen dare
۞وَسَارِعُوٓاْ إِلَىٰ مَغۡفِرَةٖ مِّن رَّبِّكُمۡ وَجَنَّةٍ عَرۡضُهَا ٱلسَّمَٰوَٰتُ وَٱلۡأَرۡضُ أُعِدَّتۡ لِلۡمُتَّقِينَ
Kuma ku yi gaggawa zuwa ga neman gafara ta musamman daga wajen Ubangijinku, da kuma Aljanna wadda faxinta yake daidai da sammai da qasa, an yi tanadinta domin masu taqawa
وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ سَنُدۡخِلُهُمۡ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدٗاۖ لَّهُمۡ فِيهَآ أَزۡوَٰجٞ مُّطَهَّرَةٞۖ وَنُدۡخِلُهُمۡ ظِلّٗا ظَلِيلًا
Waxanda suka yi imani kuwa, kuma suka yi aiki nagari, to za Mu shigar da su gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, suna masu dawwama a cikinsu har abada; suna da mata tsarkaka a cikinsu; kuma za Mu shigar da su cikin wata inuwa, inuwa mayalwaciya marar gushewa
وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَا وَمَسَٰكِنَ طَيِّبَةٗ فِي جَنَّـٰتِ عَدۡنٖۚ وَرِضۡوَٰنٞ مِّنَ ٱللَّهِ أَكۡبَرُۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ
Allah Ya yi wa muninai maza da muminai mata alqawarin gidajen Aljanna da qoramu suke gudana ta qarqashinsu suna masu dawwama a cikinsu, da kuma wuraren zama masu kyau a cikin gidajen Aljanna na dawwama. Yardar Allah kuwa ita ce fiye da komai. Wannan shi ne rabo mai girma
۞مَّثَلُ ٱلۡجَنَّةِ ٱلَّتِي وُعِدَ ٱلۡمُتَّقُونَۖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۖ أُكُلُهَا دَآئِمٞ وَظِلُّهَاۚ تِلۡكَ عُقۡبَى ٱلَّذِينَ ٱتَّقَواْۚ وَّعُقۡبَى ٱلۡكَٰفِرِينَ ٱلنَّارُ
Misalin Aljannar nan da aka yi wa masu taqawa alqawari da ita; qoramu ne suke gudana ta qarqashinta; abincinta kuma mai dawwama ne da kuma inuwarta. Wannan shi ne makomar waxanda suka kiyaye dokokin Allah; makomar kafirai kuma ita ce wuta
إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي جَنَّـٰتٖ وَعُيُونٍ
Lalle masu kiyaye dokokin Allah suna cikin gidajen Aljanna da idanuwan (ruwa)
ٱدۡخُلُوهَا بِسَلَٰمٍ ءَامِنِينَ
(A ce da su): “Ku shige ta lafiya lau kuna amintattu.”
وَنَزَعۡنَا مَا فِي صُدُورِهِم مِّنۡ غِلٍّ إِخۡوَٰنًا عَلَىٰ سُرُرٖ مُّتَقَٰبِلِينَ
Muka kuma cire abin da ke cikin zukatansu na qullata (suka zama) ‘yan’uwa a kan gadaje suna fuskantar juna
لَا يَمَسُّهُمۡ فِيهَا نَصَبٞ وَمَا هُم مِّنۡهَا بِمُخۡرَجِينَ
Wata gajiya ba za ta shafe su ba, kuma su ba waxanda za a fitar ba ne
أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ جَنَّـٰتُ عَدۡنٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهِمُ ٱلۡأَنۡهَٰرُ يُحَلَّوۡنَ فِيهَا مِنۡ أَسَاوِرَ مِن ذَهَبٖ وَيَلۡبَسُونَ ثِيَابًا خُضۡرٗا مِّن سُندُسٖ وَإِسۡتَبۡرَقٖ مُّتَّكِـِٔينَ فِيهَا عَلَى ٱلۡأَرَآئِكِۚ نِعۡمَ ٱلثَّوَابُ وَحَسُنَتۡ مُرۡتَفَقٗا
Waxannan suna da gidajen Aljanna na dawwama waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, ana yi musu ado a cikinsu (watau gidajen) da awarwaro na zinare, suna kuma sanya tufafi koraye na alharini mai shara-shara da mai kauri, suna kwance a kan gadaje. Madalla (da wannan) lada, wurin hutu kuma ya kyautata
جَنَّـٰتِ عَدۡنٍ ٱلَّتِي وَعَدَ ٱلرَّحۡمَٰنُ عِبَادَهُۥ بِٱلۡغَيۡبِۚ إِنَّهُۥ كَانَ وَعۡدُهُۥ مَأۡتِيّٗا
(Watau) gidajen Aljanna na dindindin waxanda (Allah) Mai rahama Ya yi wa bayinsa alqawari da su alhali ba su gan su ba. Lalle alqawarinsa kuwa ya tabbata mai zuwa ne
لَّا يَسۡمَعُونَ فِيهَا لَغۡوًا إِلَّا سَلَٰمٗاۖ وَلَهُمۡ رِزۡقُهُمۡ فِيهَا بُكۡرَةٗ وَعَشِيّٗا
Ba za su ji wani zancen banza ba a cikinsu sai sallama (daga mala’iku); kuma arzikinsu na nan tare da su a cikinsu safe da yamma
تِلۡكَ ٱلۡجَنَّةُ ٱلَّتِي نُورِثُ مِنۡ عِبَادِنَا مَن كَانَ تَقِيّٗا
Waccan ita ce Aljannar da za Mu gadar da ita ga wanda ya zamo mai taqawa daga cikin bayinmu
إِنَّ ٱللَّهَ يُدۡخِلُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ يُحَلَّوۡنَ فِيهَا مِنۡ أَسَاوِرَ مِن ذَهَبٖ وَلُؤۡلُؤٗاۖ وَلِبَاسُهُمۡ فِيهَا حَرِيرٞ
Lalle Allah Yana shigar da waxanda suka yi imani kuma suka yi ayyuka na gari gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, ana yi musu ado a cikinsu da awarwaro na zinare da kuma lu’ulu’u; tufafinsu kuwa a cikinsu alharini ne
وَهُدُوٓاْ إِلَى ٱلطَّيِّبِ مِنَ ٱلۡقَوۡلِ وَهُدُوٓاْ إِلَىٰ صِرَٰطِ ٱلۡحَمِيدِ
Kuma an shiryar da su zuwa ga magana mai daxi (a duniya, wato Kalmar Shahada), an kuma shiryar da su zuwa ga tafarkin (Allah) Sha-yabo
جَنَّـٰتُ عَدۡنٖ يَدۡخُلُونَهَا يُحَلَّوۡنَ فِيهَا مِنۡ أَسَاوِرَ مِن ذَهَبٖ وَلُؤۡلُؤٗاۖ وَلِبَاسُهُمۡ فِيهَا حَرِيرٞ
(Watau) gidajen Aljanna na dawwama da za su shige su, za a yi musu ado a cikinsu na awarwaron zinare da kuma lu’ulu’u; tufafinsu a cikinsu (gidajen Aljanna) alharini ne
وَقَالُواْ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِيٓ أَذۡهَبَ عَنَّا ٱلۡحَزَنَۖ إِنَّ رَبَّنَا لَغَفُورٞ شَكُورٌ
Kuma Su ce: “Yabo ya tabbata ga Allah Wanda Ya yaye mana baqin ciki; lalle Ubangijinmu Mai gafara ne, Mai godiya
ٱلَّذِيٓ أَحَلَّنَا دَارَ ٱلۡمُقَامَةِ مِن فَضۡلِهِۦ لَا يَمَسُّنَا فِيهَا نَصَبٞ وَلَا يَمَسُّنَا فِيهَا لُغُوبٞ
“Wanda Ya saukar da mu a gidan dawwama don falalarsa, ba wata wahala da za ta shafe mu a cikinsa, kuma ba wata gajiya da za ta shafe mu a cikinsa.”
إِنَّ أَصۡحَٰبَ ٱلۡجَنَّةِ ٱلۡيَوۡمَ فِي شُغُلٖ فَٰكِهُونَ
Lalle ‘yan Aljanna a yau suna cikin shagali, suna masu farin ciki
هُمۡ وَأَزۡوَٰجُهُمۡ فِي ظِلَٰلٍ عَلَى ٱلۡأَرَآئِكِ مُتَّكِـُٔونَ
Su da matansu suna cikin inuwoyi kishingixe a kan gadaje
لَهُمۡ فِيهَا فَٰكِهَةٞ وَلَهُم مَّا يَدَّعُونَ
Suna da kayan marmari a cikinta, suna kuma da duk irin abin da suke nema
سَلَٰمٞ قَوۡلٗا مِّن رَّبّٖ رَّحِيمٖ
Sallama (za a riqa yi musu), magana ce daga Ubangiji Mai rahama
أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ رِزۡقٞ مَّعۡلُومٞ
Waxannan suna da arziki sananne
فَوَٰكِهُ وَهُم مُّكۡرَمُونَ
(Shi ne) kayan marmari; su kuma ababen karramawa ne
فِي جَنَّـٰتِ ٱلنَّعِيمِ
A cikin gidajen Aljanna na ni’ima
عَلَىٰ سُرُرٖ مُّتَقَٰبِلِينَ
A kan gadaje suna fuskantar juna
يُطَافُ عَلَيۡهِم بِكَأۡسٖ مِّن مَّعِينِۭ
Ana zagaya su da kofuna na giya