Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 158

۞إِنَّ ٱلصَّفَا وَٱلۡمَرۡوَةَ مِن شَعَآئِرِ ٱللَّهِۖ فَمَنۡ حَجَّ ٱلۡبَيۡتَ أَوِ ٱعۡتَمَرَ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡهِ أَن يَطَّوَّفَ بِهِمَاۚ وَمَن تَطَوَّعَ خَيۡرٗا فَإِنَّ ٱللَّهَ شَاكِرٌ عَلِيمٌ

Lalle dutsen Safa da na Marwa suna cikin alamomin bautar Allah, don haka wanda ya je Hajji ga Xakin Allah ko ya je Umara, to babu wani laifi a gare shi ya yi xawafi tsakaninsu. Kuma wanda ya yi biyayya ta hanyar aikata alheri, to lalle Allah Mai godiya ne kuma Masani



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 196

وَأَتِمُّواْ ٱلۡحَجَّ وَٱلۡعُمۡرَةَ لِلَّهِۚ فَإِنۡ أُحۡصِرۡتُمۡ فَمَا ٱسۡتَيۡسَرَ مِنَ ٱلۡهَدۡيِۖ وَلَا تَحۡلِقُواْ رُءُوسَكُمۡ حَتَّىٰ يَبۡلُغَ ٱلۡهَدۡيُ مَحِلَّهُۥۚ فَمَن كَانَ مِنكُم مَّرِيضًا أَوۡ بِهِۦٓ أَذٗى مِّن رَّأۡسِهِۦ فَفِدۡيَةٞ مِّن صِيَامٍ أَوۡ صَدَقَةٍ أَوۡ نُسُكٖۚ فَإِذَآ أَمِنتُمۡ فَمَن تَمَتَّعَ بِٱلۡعُمۡرَةِ إِلَى ٱلۡحَجِّ فَمَا ٱسۡتَيۡسَرَ مِنَ ٱلۡهَدۡيِۚ فَمَن لَّمۡ يَجِدۡ فَصِيَامُ ثَلَٰثَةِ أَيَّامٖ فِي ٱلۡحَجِّ وَسَبۡعَةٍ إِذَا رَجَعۡتُمۡۗ تِلۡكَ عَشَرَةٞ كَامِلَةٞۗ ذَٰلِكَ لِمَن لَّمۡ يَكُنۡ أَهۡلُهُۥ حَاضِرِي ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ

Kuma ku cika aikin Hajji da umara domin Allah. To idan an tsare ku, sai ku gabatar da abin da ya sawwaqa na hadaya, kuma kada ku aske kawunanku har sai hadaya ta kai wurin yankanta. To wanda ya kasance a cikinku mara lafiya ko akwai wata cuta a kansa, (idan yayi aski) to sai ya yi fidiya ta (hanyar) yin azumi ko sadaqa ko yanka[1]. Idan kuwa kun amintu, to duk wanda ya yi tamattu’i da yin umara tare da Hajji, to sai ya yanka abin da ya sawwaqa na hadaya; amma wanda bai samu ba, sai ya yi azumin kwana uku a lokacin aikin Hajji, da kuma na kwana bakwai idan kun dawo gida. Waxannan kwana goma ke nan cikakku. Wannan hukuncin yana ga wanda iyalinsa ba sa cikin hurumin Makka ne. Kuma ku kiyaye dokokin Allah, ku sani cewa, lalle Allah Mai tsananin uquba ne


1- Watau ya yi azumi na kwana uku, ko ya ciyar da miskinai shida, kowanne ya ba shi rabin mudu ko ya yanka akuya.


Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 197

ٱلۡحَجُّ أَشۡهُرٞ مَّعۡلُومَٰتٞۚ فَمَن فَرَضَ فِيهِنَّ ٱلۡحَجَّ فَلَا رَفَثَ وَلَا فُسُوقَ وَلَا جِدَالَ فِي ٱلۡحَجِّۗ وَمَا تَفۡعَلُواْ مِنۡ خَيۡرٖ يَعۡلَمۡهُ ٱللَّهُۗ وَتَزَوَّدُواْ فَإِنَّ خَيۡرَ ٱلزَّادِ ٱلتَّقۡوَىٰۖ وَٱتَّقُونِ يَـٰٓأُوْلِي ٱلۡأَلۡبَٰبِ

(Lokacin) hajji wasu watanni ne sanannu[1]. Don haka duk wanda ya wajabta wa kansa aikin Hajji cikin waxannan (watanni), to babu maganar saduwa da mace, kuma babu fasiqanci, kuma babu jayayya a cikin aikin Hajji. Kuma duk abin da kuka aikata na alheri, Allah Yana sane da shi. Kuma ku yi guzuri, amma mafificin guzuri shi ne taqawa, kuma ku kiyaye dokokina ya ku ma’abota hankula


1- Su ne: Shawwal da Zulqi’ida da Zulhijja.


Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 198

لَيۡسَ عَلَيۡكُمۡ جُنَاحٌ أَن تَبۡتَغُواْ فَضۡلٗا مِّن رَّبِّكُمۡۚ فَإِذَآ أَفَضۡتُم مِّنۡ عَرَفَٰتٖ فَٱذۡكُرُواْ ٱللَّهَ عِندَ ٱلۡمَشۡعَرِ ٱلۡحَرَامِۖ وَٱذۡكُرُوهُ كَمَا هَدَىٰكُمۡ وَإِن كُنتُم مِّن قَبۡلِهِۦ لَمِنَ ٱلضَّآلِّينَ

Babu wani laifi gare ku ku nemi falala daga Ubangijinku, don haka idan kun gangaro daga Arfa, to ku ambaci Allah a wurin (da ake kira) Mash’arul Haraam, kuma ku ambace Shi kamar yadda Ya shiryar da ku, ko da yake a da tabbas kun kasance daga cikin vatattu



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 199

ثُمَّ أَفِيضُواْ مِنۡ حَيۡثُ أَفَاضَ ٱلنَّاسُ وَٱسۡتَغۡفِرُواْ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Sannan kuma sai ku gangaro ta inda mutane suka gangaro kuma ku nemi gafarar Allah; lalle Allah Mai yawan gafara ne, Mai yawan jin qai



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 200

فَإِذَا قَضَيۡتُم مَّنَٰسِكَكُمۡ فَٱذۡكُرُواْ ٱللَّهَ كَذِكۡرِكُمۡ ءَابَآءَكُمۡ أَوۡ أَشَدَّ ذِكۡرٗاۗ فَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَقُولُ رَبَّنَآ ءَاتِنَا فِي ٱلدُّنۡيَا وَمَا لَهُۥ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ مِنۡ خَلَٰقٖ

To idan kun gama ayyukanku na Hajji, to ku yi ta ambaton Allah kamar yadda kuke ambaton iyayenku, ko ambaton (Allah) ya fi yawa. To daga cikin mutane akwai wanda yake cewa: “Ya Ubangijimu, Ka ba mu (rabo) a nan duniya”, kuma a lahira ba shi da wani rabo



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 201

وَمِنۡهُم مَّن يَقُولُ رَبَّنَآ ءَاتِنَا فِي ٱلدُّنۡيَا حَسَنَةٗ وَفِي ٱلۡأٓخِرَةِ حَسَنَةٗ وَقِنَا عَذَابَ ٱلنَّارِ

Kuma daga cikinsu akwai wanda yake cewa: “Ya Ubangijinmu, Ka ba mu kyakkyawa a nan duniya, kuma Ka ba mu kyakkyawa a lahira, Ka kuma tsare mu daga azabar wuta.”



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 202

أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ نَصِيبٞ مِّمَّا كَسَبُواْۚ وَٱللَّهُ سَرِيعُ ٱلۡحِسَابِ

Waxannan suna da babban rabo na daga abin da suka aikata, kuma Allah Mai gaggawar hisabi ne



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 203

۞وَٱذۡكُرُواْ ٱللَّهَ فِيٓ أَيَّامٖ مَّعۡدُودَٰتٖۚ فَمَن تَعَجَّلَ فِي يَوۡمَيۡنِ فَلَآ إِثۡمَ عَلَيۡهِ وَمَن تَأَخَّرَ فَلَآ إِثۡمَ عَلَيۡهِۖ لِمَنِ ٱتَّقَىٰۗ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّكُمۡ إِلَيۡهِ تُحۡشَرُونَ

Kuma ku ambaci Allah a cikin wasu kwanaki qididdigaggu. To duk wanda ya yi gaggawar (barin Mina) cikin kwana biyu, to babu laifi a gare shi; wanda kuwa ya yi jinkiri, to babu laifi a gare shi, (amma dukkansu) ga wanda ya yi taqawa. Kuma ku kiyaye dokokin Allah, kuma ku sani cewa, zuwa gare Shi za a tattara ku



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 96

إِنَّ أَوَّلَ بَيۡتٖ وُضِعَ لِلنَّاسِ لَلَّذِي بِبَكَّةَ مُبَارَكٗا وَهُدٗى لِّلۡعَٰلَمِينَ

Lalle farkon xaki da aka tanada don mutane (su yi ibada a cikinsa) shi ne wanda yake cikin Bakka[1], (xaki ne) mai albarka, kuma shiriya ne ga talikai


1- Watau Xakin Ka’aba da yake garin Makka mai alfarma.


Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 97

فِيهِ ءَايَٰتُۢ بَيِّنَٰتٞ مَّقَامُ إِبۡرَٰهِيمَۖ وَمَن دَخَلَهُۥ كَانَ ءَامِنٗاۗ وَلِلَّهِ عَلَى ٱلنَّاسِ حِجُّ ٱلۡبَيۡتِ مَنِ ٱسۡتَطَاعَ إِلَيۡهِ سَبِيلٗاۚ وَمَن كَفَرَ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَنِيٌّ عَنِ ٱلۡعَٰلَمِينَ

A cikinsa akwai ayoyi bayyanannu, (kuma akwai) Maqamu Ibrahimu; wanda duk ya shige shi ya zama amintacce. Kuma Allah Ya wajabta wa mutane ziyarar wannan xakin ga wanda ya sami iko[1]. Wanda kuwa ya kafirce, to lalle Allah Mawadaci ne ga barin talikai


1- Allah ya farlanta ziyarar wannan Xaki domin aikin hajji sau xaya a rayuwa ga duk wanda ya sami iko na lafiya da guzuri da abin hawa da amincin hanya.


Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 1

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَوۡفُواْ بِٱلۡعُقُودِۚ أُحِلَّتۡ لَكُم بَهِيمَةُ ٱلۡأَنۡعَٰمِ إِلَّا مَا يُتۡلَىٰ عَلَيۡكُمۡ غَيۡرَ مُحِلِّي ٱلصَّيۡدِ وَأَنتُمۡ حُرُمٌۗ إِنَّ ٱللَّهَ يَحۡكُمُ مَا يُرِيدُ

Ya ku waxanda suka yi imani, ku cika alqawura. An halatta muku dabbobin ni’ima, sai dai abin da ake karanta muku (haramcinsa), ba kuna masu halatta farauta ba alhalin kuna cikin Harami, lalle Allah Yana hukunta abin da Yake nufi



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 2

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تُحِلُّواْ شَعَـٰٓئِرَ ٱللَّهِ وَلَا ٱلشَّهۡرَ ٱلۡحَرَامَ وَلَا ٱلۡهَدۡيَ وَلَا ٱلۡقَلَـٰٓئِدَ وَلَآ ءَآمِّينَ ٱلۡبَيۡتَ ٱلۡحَرَامَ يَبۡتَغُونَ فَضۡلٗا مِّن رَّبِّهِمۡ وَرِضۡوَٰنٗاۚ وَإِذَا حَلَلۡتُمۡ فَٱصۡطَادُواْۚ وَلَا يَجۡرِمَنَّكُمۡ شَنَـَٔانُ قَوۡمٍ أَن صَدُّوكُمۡ عَنِ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ أَن تَعۡتَدُواْۘ وَتَعَاوَنُواْ عَلَى ٱلۡبِرِّ وَٱلتَّقۡوَىٰۖ وَلَا تَعَاوَنُواْ عَلَى ٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡعُدۡوَٰنِۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۖ إِنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku halatta keta alfarmar alamomin addinin Allah, ko (ku wulaqanta) Wata mai alfarma[1] ko dabbobin hadaya ko dabbobin hadaya masu alama da (tare) masu nufin ziyarar Xaki mai alfarma, suna neman falala daga wurin Ubangijinsu da yardarsa. Idan kuwa kuka kwance Harami, to ku yi farauta (idan kuna so). Kuma kada qiyayyar wasu mutane da suka hana ku isa masallaci mai alfarma, ta sa ku yi ta’addanci. Kuma ku taimaki juna a kan aikin alheri da taqawa; kada kuma ku taimaka wa juna a kan ayyukan savo da ta’addanci. Kuma ku kiyaye dokokin Allah; lalle Allah Mai tsananin uquba ne


1- Watanni masu alfarma su ne: Zulqi’ida, Zulhijja, Al-Muharram da Rajab. An haramta yaqi a cikinsu.


Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 94

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَيَبۡلُوَنَّكُمُ ٱللَّهُ بِشَيۡءٖ مِّنَ ٱلصَّيۡدِ تَنَالُهُۥٓ أَيۡدِيكُمۡ وَرِمَاحُكُمۡ لِيَعۡلَمَ ٱللَّهُ مَن يَخَافُهُۥ بِٱلۡغَيۡبِۚ فَمَنِ ٱعۡتَدَىٰ بَعۡدَ ذَٰلِكَ فَلَهُۥ عَذَابٌ أَلِيمٞ

Ya ku waxanda suka yi imani, lalle Allah zai jarrabe ku da wani abu na farauta, wanda hannayenku da masunku za su kai gare shi, don Allah Ya bayyana wanda yake jin tsoron Sa alhalin bai gan Shi ba. Don haka duk wanda ya qetare iyaka bayan haka, to lalle yana da azaba mai raxaxi



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 95

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَقۡتُلُواْ ٱلصَّيۡدَ وَأَنتُمۡ حُرُمٞۚ وَمَن قَتَلَهُۥ مِنكُم مُّتَعَمِّدٗا فَجَزَآءٞ مِّثۡلُ مَا قَتَلَ مِنَ ٱلنَّعَمِ يَحۡكُمُ بِهِۦ ذَوَا عَدۡلٖ مِّنكُمۡ هَدۡيَۢا بَٰلِغَ ٱلۡكَعۡبَةِ أَوۡ كَفَّـٰرَةٞ طَعَامُ مَسَٰكِينَ أَوۡ عَدۡلُ ذَٰلِكَ صِيَامٗا لِّيَذُوقَ وَبَالَ أَمۡرِهِۦۗ عَفَا ٱللَّهُ عَمَّا سَلَفَۚ وَمَنۡ عَادَ فَيَنتَقِمُ ٱللَّهُ مِنۡهُۚ وَٱللَّهُ عَزِيزٞ ذُو ٱنتِقَامٍ

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku kashe abin farauta alhali kuna cikin Harami[1]. Duk kuwa wanda ya kashe shi daga cikinku da gangan, to sakamakonsa shi ne (ya bayar) da kwatankwacin abin da ya kashe cikin dabbobin gida; waxanda za su yi hukunci da wannan su ne mutum biyu adalai a cikinku, a matsayin hadaya wadda za ta isa Ka’aba, ko kuma ya yi kaffarar ciyar da miskinai, ko kuma ya yi azumi na kwatankwacin haka, don ya xanxani kuxar lamarinsa. Allah Ya yi afuwa dangane da abin da ya wuce. Duk kuwa wanda ya sake komawa, to Allah zai yi masa uquba. Kuma Allah Mabuwayi ne, Ma’abocin uquba


1- Watau kuna sanye da haramin hajji ko na umara.


Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 96

أُحِلَّ لَكُمۡ صَيۡدُ ٱلۡبَحۡرِ وَطَعَامُهُۥ مَتَٰعٗا لَّكُمۡ وَلِلسَّيَّارَةِۖ وَحُرِّمَ عَلَيۡكُمۡ صَيۡدُ ٱلۡبَرِّ مَا دُمۡتُمۡ حُرُمٗاۗ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ ٱلَّذِيٓ إِلَيۡهِ تُحۡشَرُونَ

An halatta muku yin farautar naman ruwa da abincin cikinsa[1], don jin daxi a gare ku da kuma matafiya; amma an haramta muku farautar naman daji matuqar kuna cikin Harami. Kuma ku kiyaye dokokin Allah Wanda zuwa gare Shi za a tattara ku


1- Watau abin da kogi ya yi ambaliyar sa an halatta wa waxanda suke cikin haramin hajji ko umara farautar sa da cin sa.


Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 97

۞جَعَلَ ٱللَّهُ ٱلۡكَعۡبَةَ ٱلۡبَيۡتَ ٱلۡحَرَامَ قِيَٰمٗا لِّلنَّاسِ وَٱلشَّهۡرَ ٱلۡحَرَامَ وَٱلۡهَدۡيَ وَٱلۡقَلَـٰٓئِدَۚ ذَٰلِكَ لِتَعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَأَنَّ ٱللَّهَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٌ

Allah Ya sanya Ka’aba xaki ne mai alfarma, wuri mai matuqar amfani ga mutane, haka watanni masu alfarma, da dabbar hadaya da dabbar hadaya mai rataye. Wannan kuwa don ku sani cewa, lalle Allah Ya san abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qasa, kuma lalle Allah Masanin komai ne



Capítulo: Suratul Hajji

Verso : 27

وَأَذِّن فِي ٱلنَّاسِ بِٱلۡحَجِّ يَأۡتُوكَ رِجَالٗا وَعَلَىٰ كُلِّ ضَامِرٖ يَأۡتِينَ مِن كُلِّ فَجٍّ عَمِيقٖ

Kuma ka yi shela cikin mutane saboda yin Hajji, za su zo maka matafiya a qasa da kuma kan kowanne raqumi mai xamammen ciki, za su zo maka daga kowane wuri mai nisa



Capítulo: Suratul Hajji

Verso : 28

لِّيَشۡهَدُواْ مَنَٰفِعَ لَهُمۡ وَيَذۡكُرُواْ ٱسۡمَ ٱللَّهِ فِيٓ أَيَّامٖ مَّعۡلُومَٰتٍ عَلَىٰ مَا رَزَقَهُم مِّنۢ بَهِيمَةِ ٱلۡأَنۡعَٰمِۖ فَكُلُواْ مِنۡهَا وَأَطۡعِمُواْ ٱلۡبَآئِسَ ٱلۡفَقِيرَ

Don su halarci amfanin da za su samu, kuma su ambaci sunan Allah cikin kwanaki sanannu a kan abin da Ya arzuta su da shi na dabbobin ni’ima (watau raquma da tumaki da awakai da shanu); sai ku ci daga gare su kuma ku ciyar da galavaitaccen matalauci



Capítulo: Suratul Hajji

Verso : 29

ثُمَّ لۡيَقۡضُواْ تَفَثَهُمۡ وَلۡيُوفُواْ نُذُورَهُمۡ وَلۡيَطَّوَّفُواْ بِٱلۡبَيۡتِ ٱلۡعَتِيقِ

Sannan su kammala ayyukan hajjinsu (kamar yin aski da yanke farce), kuma su cika alqawuransu (na yin hadaya da layya), kuma su yi xawafi a ‘yantaccen Xaki (na Ka’aba)



Capítulo: Suratul Hajji

Verso : 33

لَكُمۡ فِيهَا مَنَٰفِعُ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗى ثُمَّ مَحِلُّهَآ إِلَى ٱلۡبَيۡتِ ٱلۡعَتِيقِ

Kuna da wata moriya game da su (dabbobin)[1] har zuwa wani lokaci qayyadajje (shi ne lokacin yanka su), sannan kuma wurin yankansu zuwa ga Xaki ne ‘yantacce (wato Harami baki xayansa)


1- Watau za su amfana da su wajen hawansu da amfani da gashinsu da nononsu da sauransu.


Capítulo: Suratul Hajji

Verso : 36

وَٱلۡبُدۡنَ جَعَلۡنَٰهَا لَكُم مِّن شَعَـٰٓئِرِ ٱللَّهِ لَكُمۡ فِيهَا خَيۡرٞۖ فَٱذۡكُرُواْ ٱسۡمَ ٱللَّهِ عَلَيۡهَا صَوَآفَّۖ فَإِذَا وَجَبَتۡ جُنُوبُهَا فَكُلُواْ مِنۡهَا وَأَطۡعِمُواْ ٱلۡقَانِعَ وَٱلۡمُعۡتَرَّۚ كَذَٰلِكَ سَخَّرۡنَٰهَا لَكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ

(Raquma) kuma masu qiba Mun sanya muku su alamomi ne na bautar Allah; kuna da amfani game da su (na rayuwarku). To sai ku ambaci sunan Allah a kansu suna tsaye a kan qafa uku (lokacin soke su). To idan ransu ya fita bayan sun faxi, sai ku ci daga gare su kuma ku ciyar da mai wadatar zuci da kuma mai bara. Kamar haka Muka hore muku su don ku yi godiya



Capítulo: Suratul Hajji

Verso : 37

لَن يَنَالَ ٱللَّهَ لُحُومُهَا وَلَا دِمَآؤُهَا وَلَٰكِن يَنَالُهُ ٱلتَّقۡوَىٰ مِنكُمۡۚ كَذَٰلِكَ سَخَّرَهَا لَكُمۡ لِتُكَبِّرُواْ ٱللَّهَ عَلَىٰ مَا هَدَىٰكُمۡۗ وَبَشِّرِ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Namansu da jininsu ba sa zuwa wajen Allah, sai dai taqawarku ce za ta isa gare Shi. Kamar haka Ya hore muku su don ku girmama Allah bisa shiryarwar da Ya yi muku (da addininsa). Kuma ka yi albishir ga masu kyautatawa