وَإِن كُنتُمۡ فِي رَيۡبٖ مِّمَّا نَزَّلۡنَا عَلَىٰ عَبۡدِنَا فَأۡتُواْ بِسُورَةٖ مِّن مِّثۡلِهِۦ وَٱدۡعُواْ شُهَدَآءَكُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Kuma idan kun kasance cikin kokwanto game da abin da Muka saukar wa bawanmu, to ku zo da kwatankwacin sura xaya kamarsa, kuma ku kirawo masu taimakonku ba Allah ba in kun kasance masu gaskiya
فَإِن لَّمۡ تَفۡعَلُواْ وَلَن تَفۡعَلُواْ فَٱتَّقُواْ ٱلنَّارَ ٱلَّتِي وَقُودُهَا ٱلنَّاسُ وَٱلۡحِجَارَةُۖ أُعِدَّتۡ لِلۡكَٰفِرِينَ
To idan har ba ku aikata hakan ba, kuma ba za ku tava iyawa ba, to ku kiyayi wata wuta wadda mutane ne da duwatsu makamashinta; an kuwa tanade ta domin kafirai
أَفَلَا يَتَدَبَّرُونَ ٱلۡقُرۡءَانَۚ وَلَوۡ كَانَ مِنۡ عِندِ غَيۡرِ ٱللَّهِ لَوَجَدُواْ فِيهِ ٱخۡتِلَٰفٗا كَثِيرٗا
Shin ba za su yi zuzzurfan tunani game da (ayoyin) Alqur’ani ba ne? Kuma da a ce ya kasance daga wajen wani yake ba Allah ba, tabbas da sun sami savani mai yawa a cikinsa
وَمَا كَانَ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانُ أَن يُفۡتَرَىٰ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلَٰكِن تَصۡدِيقَ ٱلَّذِي بَيۡنَ يَدَيۡهِ وَتَفۡصِيلَ ٱلۡكِتَٰبِ لَا رَيۡبَ فِيهِ مِن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Wannan Alqur’ani bai yiwuwa a qage shi daga (tunanin) wani wanda ba Allah ba, sai dai (shi) gaskatawa ne ga abin da ya gabace shi (na littattafan da aka saukar), kuma bayani ne dalla-dalla na hukunce-hukuncen (da Allah ya saukar); babu kokwanto a cikinsa cewa daga Ubangijin talikai yake
أَمۡ يَقُولُونَ ٱفۡتَرَىٰهُۖ قُلۡ فَأۡتُواْ بِسُورَةٖ مِّثۡلِهِۦ وَٱدۡعُواْ مَنِ ٱسۡتَطَعۡتُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Ko kuma cewa suke yi: “Qagar sa ya yi ne?” Ka ce: “To ku kawo sura (xaya tal) irinsa, kuma ku kirawo wanda duk za ku iya (ya taimaka muku) wanda ba Allah ba idan kun kasance masu gaskiya!”
الٓرۚ كِتَٰبٌ أُحۡكِمَتۡ ءَايَٰتُهُۥ ثُمَّ فُصِّلَتۡ مِن لَّدُنۡ حَكِيمٍ خَبِيرٍ
ALIF LAM RA[1]. (Wannan) Littafi ne da aka kyautata ayoyinsa sannan aka bayyana su filla-filla, daga wurin Mai hikima, Masani
1- Duba Suratul Baqara aya ta 1, hashiya ta 8.
أَمۡ يَقُولُونَ ٱفۡتَرَىٰهُۖ قُلۡ فَأۡتُواْ بِعَشۡرِ سُوَرٖ مِّثۡلِهِۦ مُفۡتَرَيَٰتٖ وَٱدۡعُواْ مَنِ ٱسۡتَطَعۡتُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
A’a, ko cewa suka yi: “Ya qirqire shi ne?” Ka ce: “Ku kawo sura goma kamarsa qagaggu, kuma ku kira duk wanda za ku iya wanda ba Allah ba (ya taimake ku) in kun kasance masu gaskiya.”
فَإِلَّمۡ يَسۡتَجِيبُواْ لَكُمۡ فَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّمَآ أُنزِلَ بِعِلۡمِ ٱللَّهِ وَأَن لَّآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ فَهَلۡ أَنتُم مُّسۡلِمُونَ
To idan ba su amsa muku ba, to ku tabbatar cewa lalle an saukar da shi ne (Alqur’ani) da sanin Allah, kuma babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi, To shin yanzu za ku miqa wuya?
إِنَّا نَحۡنُ نَزَّلۡنَا ٱلذِّكۡرَ وَإِنَّا لَهُۥ لَحَٰفِظُونَ
Lalle Mu Muka saukar da Alqur’ani, lalle kuma tabbas Mu za Mu kiyaye shi
قُل لَّئِنِ ٱجۡتَمَعَتِ ٱلۡإِنسُ وَٱلۡجِنُّ عَلَىٰٓ أَن يَأۡتُواْ بِمِثۡلِ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانِ لَا يَأۡتُونَ بِمِثۡلِهِۦ وَلَوۡ كَانَ بَعۡضُهُمۡ لِبَعۡضٖ ظَهِيرٗا
Ka ce da su: “Lalle da mutane da aljannu sun haxu kan su kawo irin wannan Alqur’anin, to ba za su zo da irinsa ba, ko da kuwa wasu sun zamanto suna taimaka wa wasu.”
وَمَا كُنتَ تَتۡلُواْ مِن قَبۡلِهِۦ مِن كِتَٰبٖ وَلَا تَخُطُّهُۥ بِيَمِينِكَۖ إِذٗا لَّٱرۡتَابَ ٱلۡمُبۡطِلُونَ
Ba ka zamanto kuma kana karanta wani littafi kafinsa ba (wato Alkur’ani), kuma ba ka rubuta shi da hannun damanka; da kuwa haka ya faru, to da sai masu qaryatawa su shiga kokwanto
بَلۡ هُوَ ءَايَٰتُۢ بَيِّنَٰتٞ فِي صُدُورِ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَۚ وَمَا يَجۡحَدُ بِـَٔايَٰتِنَآ إِلَّا ٱلظَّـٰلِمُونَ
A’a, shi dai (Alqur’ani) ayoyi ne bayyanannu (da suke) cikin zukatan waxanda aka bai wa ilimi. Ba kuwa mai yin musun ayoyinmu sai azzalumai
إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِٱلذِّكۡرِ لَمَّا جَآءَهُمۡۖ وَإِنَّهُۥ لَكِتَٰبٌ عَزِيزٞ
Lalle waxanda suka kafirce wa Alqur’ani lokacin da ya zo musu (tabbas Allah zai saka musu). Lalle kuma shi littafi ne mabuwayi
لَّا يَأۡتِيهِ ٱلۡبَٰطِلُ مِنۢ بَيۡنِ يَدَيۡهِ وَلَا مِنۡ خَلۡفِهِۦۖ تَنزِيلٞ مِّنۡ حَكِيمٍ حَمِيدٖ
Varna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa; saukakke ne daga Mai hikima, Sha-yabo
لَوۡ أَنزَلۡنَا هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانَ عَلَىٰ جَبَلٖ لَّرَأَيۡتَهُۥ خَٰشِعٗا مُّتَصَدِّعٗا مِّنۡ خَشۡيَةِ ٱللَّهِۚ وَتِلۡكَ ٱلۡأَمۡثَٰلُ نَضۡرِبُهَا لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمۡ يَتَفَكَّرُونَ
Da za Mu saukar da wannan Alqur’ani ga wani dutse, da lalle ka gan shi yana mai qasqantar da kai mai tsattsagewa don tsoron Allah. Waxannan misalan Muna buga wa mutane su ne don su yi tunani