Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 41

وَءَامِنُواْ بِمَآ أَنزَلۡتُ مُصَدِّقٗا لِّمَا مَعَكُمۡ وَلَا تَكُونُوٓاْ أَوَّلَ كَافِرِۭ بِهِۦۖ وَلَا تَشۡتَرُواْ بِـَٔايَٰتِي ثَمَنٗا قَلِيلٗا وَإِيَّـٰيَ فَٱتَّقُونِ

Kuma ku yi imani da abin da Na saukar yana mai gaskata abin da yake tare da ku (na wahayi), kada kuma ku zama farkon (jinsinku) da zai kafirce masa, kuma kada ku sayar da ayoyina da xan kuxi kaxan, kuma ku kiyaye dokokina



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 91

وَإِذَا قِيلَ لَهُمۡ ءَامِنُواْ بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ قَالُواْ نُؤۡمِنُ بِمَآ أُنزِلَ عَلَيۡنَا وَيَكۡفُرُونَ بِمَا وَرَآءَهُۥ وَهُوَ ٱلۡحَقُّ مُصَدِّقٗا لِّمَا مَعَهُمۡۗ قُلۡ فَلِمَ تَقۡتُلُونَ أَنۢبِيَآءَ ٱللَّهِ مِن قَبۡلُ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ

Idan aka ce da su: “Ku yi imani da abin da Allah Ya saukar”, sai su ce: “Mu muna yin imani ne da abin da aka saukar mana”. Kuma suna kafircewa da duk wani abu da ba shi ba, alhalin shi gaskiya ne, kuma mai gaskata abin da ke tare da su ne. To ka ce: “Me ya sa a da kuke kashe annabawan Allah idan kun kasance muminai?”



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 97

قُلۡ مَن كَانَ عَدُوّٗا لِّـجِبۡرِيلَ فَإِنَّهُۥ نَزَّلَهُۥ عَلَىٰ قَلۡبِكَ بِإِذۡنِ ٱللَّهِ مُصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيۡهِ وَهُدٗى وَبُشۡرَىٰ لِلۡمُؤۡمِنِينَ

Ka ce: “Duk wanda ya kasance maqiyi ne ga (Mala’ika) Jibrilu[1], to lalle shi ne ya saukar da shi (Alqur’ani) a kan zuciyarka da izinin Allah yana mai gaskata abin da ya gabace shi (na littattafai), kuma shiriya ne da bushara ga muminai.”


1- Yahudawa sun faxa wa Annabi cewa, Mala'ika Jibrilu maqiyinsu ne, wai domin shi ne yake saukowa da yaqi da kashe-kashe da azaba.


Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 3

نَزَّلَ عَلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ مُصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيۡهِ وَأَنزَلَ ٱلتَّوۡرَىٰةَ وَٱلۡإِنجِيلَ

Ya saukar maka da Littafi da gaskiya, yana mai gaskata abin da ya gabace shi, kuma Ya saukar da Attaura da Linjila



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 47

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ ءَامِنُواْ بِمَا نَزَّلۡنَا مُصَدِّقٗا لِّمَا مَعَكُم مِّن قَبۡلِ أَن نَّطۡمِسَ وُجُوهٗا فَنَرُدَّهَا عَلَىٰٓ أَدۡبَارِهَآ أَوۡ نَلۡعَنَهُمۡ كَمَا لَعَنَّآ أَصۡحَٰبَ ٱلسَّبۡتِۚ وَكَانَ أَمۡرُ ٱللَّهِ مَفۡعُولًا

Ya ku waxanda aka ba su littafi, ku yi imani da abin da Muka saukar mai gaskata abin da yake tare da ku, tun kafin Mu shafe wasu fuskoki, Mu mayar da su bayansu, ko kuma Mu la’ance su irin yadda Muka la’anci ma’abota ranar Asabar[1]. Kuma al’amarin Allah ya kasance abin zartarwa ne


1- Su ne Yahuduwa waxanda Allah ya hana su kamun kifi duk ranar Assabar, amma sai suka riqa yin dabara suna sava wa umarninsa. Duba Suratul A’araf, aya ta 163-166.


Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 15

يَـٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ قَدۡ جَآءَكُمۡ رَسُولُنَا يُبَيِّنُ لَكُمۡ كَثِيرٗا مِّمَّا كُنتُمۡ تُخۡفُونَ مِنَ ٱلۡكِتَٰبِ وَيَعۡفُواْ عَن كَثِيرٖۚ قَدۡ جَآءَكُم مِّنَ ٱللَّهِ نُورٞ وَكِتَٰبٞ مُّبِينٞ

Ya ku waxanda aka bai wa Littafi, haqiqa Manzonmu ya zo muku, yana bayyana muku da yawa daga cikin abin da kuke voyewa daga Littafin, yana kuma yin afuwa ga abubuwa da dama daga ciki. Haqiqa haske ya zo muku daga Allah, da kuma Littafi mai bayyanawa



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 48

وَأَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ مُصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيۡهِ مِنَ ٱلۡكِتَٰبِ وَمُهَيۡمِنًا عَلَيۡهِۖ فَٱحۡكُم بَيۡنَهُم بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُۖ وَلَا تَتَّبِعۡ أَهۡوَآءَهُمۡ عَمَّا جَآءَكَ مِنَ ٱلۡحَقِّۚ لِكُلّٖ جَعَلۡنَا مِنكُمۡ شِرۡعَةٗ وَمِنۡهَاجٗاۚ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ لَجَعَلَكُمۡ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ وَلَٰكِن لِّيَبۡلُوَكُمۡ فِي مَآ ءَاتَىٰكُمۡۖ فَٱسۡتَبِقُواْ ٱلۡخَيۡرَٰتِۚ إِلَى ٱللَّهِ مَرۡجِعُكُمۡ جَمِيعٗا فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ فِيهِ تَخۡتَلِفُونَ

Kuma Mun saukar maka da Littafin (Alqur’ani) da gaskiya, yana mai gaskata abin da ya gabace shi na sauran littattafai, kuma mai xaukaka a kansu; don haka ka yi hukunci a tsakaninsu da abin da Allah Ya saukar; kuma kada ka bi soye-soyen zukatansu ka bar abin da ya zo maka na gaskiya don bin son zuciyarsu. Kowanne daga cikinku Mun sanya musu tsari na shari’a da tsari na rayuwa. Kuma in da Allah Ya ga dama, da sai Ya sanya ku ku zamo al’umma xaya, sai dai kuma don Ya jarrabe ku cikin abin da Ya ba ku; don haka sai ku yi gaggawar aikata ayyuka na alheri. Gaba xaya makomarku zuwa ga Allah take, kuma zai ba ku labarin abin da kuka kasance kuna savani a kansa



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 92

وَهَٰذَا كِتَٰبٌ أَنزَلۡنَٰهُ مُبَارَكٞ مُّصَدِّقُ ٱلَّذِي بَيۡنَ يَدَيۡهِ وَلِتُنذِرَ أُمَّ ٱلۡقُرَىٰ وَمَنۡ حَوۡلَهَاۚ وَٱلَّذِينَ يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ يُؤۡمِنُونَ بِهِۦۖ وَهُمۡ عَلَىٰ صَلَاتِهِمۡ يُحَافِظُونَ

Kuma wannan (Alqur’ani) littafi ne mai albarka, wanda Muka saukar da shi mai gaskata abin da ya gabace shi (na littattafai), kuma don ka gargaxi uwar alqaryu (mutanen Makka) da waxanda suke kewaye da ita. Waxanda kuwa suke yin imani da ranar lahira, suna yin imani da shi ne (Alqur’ani), kuma su suna kiyaye sallolinsu



Capítulo: Suratu Yunus

Verso : 37

وَمَا كَانَ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانُ أَن يُفۡتَرَىٰ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلَٰكِن تَصۡدِيقَ ٱلَّذِي بَيۡنَ يَدَيۡهِ وَتَفۡصِيلَ ٱلۡكِتَٰبِ لَا رَيۡبَ فِيهِ مِن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Wannan Alqur’ani bai yiwuwa a qage shi daga (tunanin) wani wanda ba Allah ba, sai dai (shi) gaskatawa ne ga abin da ya gabace shi (na littattafan da aka saukar), kuma bayani ne dalla-dalla na hukunce-hukuncen (da Allah ya saukar); babu kokwanto a cikinsa cewa daga Ubangijin talikai yake



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 111

لَقَدۡ كَانَ فِي قَصَصِهِمۡ عِبۡرَةٞ لِّأُوْلِي ٱلۡأَلۡبَٰبِۗ مَا كَانَ حَدِيثٗا يُفۡتَرَىٰ وَلَٰكِن تَصۡدِيقَ ٱلَّذِي بَيۡنَ يَدَيۡهِ وَتَفۡصِيلَ كُلِّ شَيۡءٖ وَهُدٗى وَرَحۡمَةٗ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ

Haqiqa akwai izina a cikin labaransu (annabawa) ga ma’abota hankali. (Alqur’ani) bai zamanto zance ne da ake qirqirar sa ba, sai dai zance ne da yake gaskata abin da ya rigaye shi (na littattafai), da kuma bayanin komai; shiriya ne kuma da rahama ga mutanen da suke yin imani



Capítulo: Suratul Ahqaf 

Verso : 12

وَمِن قَبۡلِهِۦ كِتَٰبُ مُوسَىٰٓ إِمَامٗا وَرَحۡمَةٗۚ وَهَٰذَا كِتَٰبٞ مُّصَدِّقٞ لِّسَانًا عَرَبِيّٗا لِّيُنذِرَ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ وَبُشۡرَىٰ لِلۡمُحۡسِنِينَ

A gabaninsa kuwa akwai littafin Musa wanda yake jagora ne da rahama. Wannan littafin kuma mai gaskata (na gabaninsa) ne a harshen Larabci, don ya gargaxi waxanda suka kafirta da kuma yin albishir ga masu kyautatawa



Capítulo: Suratul Ahqaf 

Verso : 30

قَالُواْ يَٰقَوۡمَنَآ إِنَّا سَمِعۡنَا كِتَٰبًا أُنزِلَ مِنۢ بَعۡدِ مُوسَىٰ مُصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيۡهِ يَهۡدِيٓ إِلَى ٱلۡحَقِّ وَإِلَىٰ طَرِيقٖ مُّسۡتَقِيمٖ

Suka ce: “Ya ku mutanenmu, haqiqa mu mun jiwo wani littafi da aka saukar bayan Musa, mai gaskata abin da yake gabaninsa, yana shiryarwa zuwa gaskiya da kuma zuwa tafarki madaidaici