Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 160

إِلَّا ٱلَّذِينَ تَابُواْ وَأَصۡلَحُواْ وَبَيَّنُواْ فَأُوْلَـٰٓئِكَ أَتُوبُ عَلَيۡهِمۡ وَأَنَا ٱلتَّوَّابُ ٱلرَّحِيمُ

Sai dai waxanda suka tuba kuma suka gyara kuma suka bayyana, to waxannan zan karvi tubansu, kuma lalle Ni Mai karvar tuba ne, Mai jin qai



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 222

وَيَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡمَحِيضِۖ قُلۡ هُوَ أَذٗى فَٱعۡتَزِلُواْ ٱلنِّسَآءَ فِي ٱلۡمَحِيضِ وَلَا تَقۡرَبُوهُنَّ حَتَّىٰ يَطۡهُرۡنَۖ فَإِذَا تَطَهَّرۡنَ فَأۡتُوهُنَّ مِنۡ حَيۡثُ أَمَرَكُمُ ٱللَّهُۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلتَّوَّـٰبِينَ وَيُحِبُّ ٱلۡمُتَطَهِّرِينَ

Kuma suna tambayar ka game da jinin haila. Ka ce:  “Shi cuta ne, don haka ku qaurace wa mata a (kwanakin) haila, kuma kada ku kusance su har sai sun tsarkaka. To idan suka yi tsarki, sai ku zo musu ta inda Allah Ya umarce ku. Lalle Allah Yana son masu yawan tuba, kuma Yana son masu tsarki.”



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 133

۞وَسَارِعُوٓاْ إِلَىٰ مَغۡفِرَةٖ مِّن رَّبِّكُمۡ وَجَنَّةٍ عَرۡضُهَا ٱلسَّمَٰوَٰتُ وَٱلۡأَرۡضُ أُعِدَّتۡ لِلۡمُتَّقِينَ

Kuma ku yi gaggawa zuwa ga neman gafara ta musamman daga wajen Ubangijinku, da kuma Aljanna wadda faxinta yake daidai da sammai da qasa, an yi tanadinta domin masu taqawa



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 106

وَٱسۡتَغۡفِرِ ٱللَّهَۖ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ غَفُورٗا رَّحِيمٗا

Kuma ka roqi gafarar Allah, lalle Allah Ya kasance Mai yawan gafara ne, Mai yawan jin qai



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 74

أَفَلَا يَتُوبُونَ إِلَى ٱللَّهِ وَيَسۡتَغۡفِرُونَهُۥۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Shin yanzu ba za su tuba zuwa ga Allah ba, kuma su nemi gafararsa? Allah kuwa Mai gafara ne, Mai jin qai



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 153

وَٱلَّذِينَ عَمِلُواْ ٱلسَّيِّـَٔاتِ ثُمَّ تَابُواْ مِنۢ بَعۡدِهَا وَءَامَنُوٓاْ إِنَّ رَبَّكَ مِنۢ بَعۡدِهَا لَغَفُورٞ رَّحِيمٞ

Waxanda kuma suka aikata munanan ayyuka, sannan suka tuba daga baya, kuma suka yi imani, lalle Ubangijinka bayansa (tuban), tabbas Mai gafara ne, Mai jin qai



Capítulo: Suratun Nur

Verso : 31

وَقُل لِّلۡمُؤۡمِنَٰتِ يَغۡضُضۡنَ مِنۡ أَبۡصَٰرِهِنَّ وَيَحۡفَظۡنَ فُرُوجَهُنَّ وَلَا يُبۡدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا مَا ظَهَرَ مِنۡهَاۖ وَلۡيَضۡرِبۡنَ بِخُمُرِهِنَّ عَلَىٰ جُيُوبِهِنَّۖ وَلَا يُبۡدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا لِبُعُولَتِهِنَّ أَوۡ ءَابَآئِهِنَّ أَوۡ ءَابَآءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوۡ أَبۡنَآئِهِنَّ أَوۡ أَبۡنَآءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوۡ إِخۡوَٰنِهِنَّ أَوۡ بَنِيٓ إِخۡوَٰنِهِنَّ أَوۡ بَنِيٓ أَخَوَٰتِهِنَّ أَوۡ نِسَآئِهِنَّ أَوۡ مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُهُنَّ أَوِ ٱلتَّـٰبِعِينَ غَيۡرِ أُوْلِي ٱلۡإِرۡبَةِ مِنَ ٱلرِّجَالِ أَوِ ٱلطِّفۡلِ ٱلَّذِينَ لَمۡ يَظۡهَرُواْ عَلَىٰ عَوۡرَٰتِ ٱلنِّسَآءِۖ وَلَا يَضۡرِبۡنَ بِأَرۡجُلِهِنَّ لِيُعۡلَمَ مَا يُخۡفِينَ مِن زِينَتِهِنَّۚ وَتُوبُوٓاْ إِلَى ٱللَّهِ جَمِيعًا أَيُّهَ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ

Kuma ka ce da muminai mata su kame idanuwansu[1] kuma su kiyaye farjinsu, kada kuma su fito da adonsu sai dai abin da ya bayyana daga gare shi[2]; kuma su sanya lulluvinsu a kan wuyan rigunansu[3]; kada kuma su fitar da adonsu sai ga mazajensu ko iyayensu ko iyayen mazajensu ko ‘ya’yansu ko ‘ya’yayen mazajensu ko ‘yan’uwansu maza ko kuma ‘ya’yan ‘yan’uwansu maza ko ‘ya’yan ‘yan’uwansu mata ko kuma mata ‘yan’uwansu ko kuma bayinsu ko kuma mazaje masu bin su (don neman abinci) ba kuma masu buqatar mata ba[4], ko kuma qananan yara waxanda ba su san sha’awar al’aurar mata ba; kada kuma su buga qafafuwansu don a gane abin da suka voye na adon qafafunsu (watau mundaye). Kuma ku tuba ga Allah gaba xayanku ya ku waxannan muminai don ku rabauta


1- Watau su kawar da idanuwansu daga kallon abin da bai halatta su kalla ba.


2- Watau abin da ba za a iya voye shi ba, kamar tufafi.


3- Watau domin a daina ganin gashinsu da wuyansu da adonsu na wuya.


4- Watau tsofaffi tukub waxanda sun daina sha’awar mata gaba xaya.


Capítulo: Suratur Rum

Verso : 31

۞مُنِيبِينَ إِلَيۡهِ وَٱتَّقُوهُ وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَلَا تَكُونُواْ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ

(Kuma) kuna masu komawa zuwa gare Shi (wato Allah) kuma ku kiyaye dokokinsa ku kuma tsai da salla kuma kada ku zamanto cikin mushirikai



Capítulo: Suratuz Zumar

Verso : 53

۞قُلۡ يَٰعِبَادِيَ ٱلَّذِينَ أَسۡرَفُواْ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمۡ لَا تَقۡنَطُواْ مِن رَّحۡمَةِ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَغۡفِرُ ٱلذُّنُوبَ جَمِيعًاۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ

Ka ce[1]: “Ya ku bayina waxanda suka vata kawunansu sosai (da kafirci da savon Allah), kada ku xebe qauna daga rahamar Allah. Lalle Allah Yana gafarta zunubai baki xaya[2]. Lalle Shi Mai gafara ne, Mai rahama


1- Allah ne yake umartar Manzonsa () da ya faxa wa muminai bayin Allah.


2- Watau ga wanda ya tuba.


Capítulo: Suratuz Zumar

Verso : 54

وَأَنِيبُوٓاْ إِلَىٰ رَبِّكُمۡ وَأَسۡلِمُواْ لَهُۥ مِن قَبۡلِ أَن يَأۡتِيَكُمُ ٱلۡعَذَابُ ثُمَّ لَا تُنصَرُونَ

“Ku kuma koma zuwa ga Ubangijinku, ku kuma miqa wuya gare Shi tun gabanin azaba ta zo muku sannan ba za a taimake ku ba



Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 6

قُلۡ إِنَّمَآ أَنَا۠ بَشَرٞ مِّثۡلُكُمۡ يُوحَىٰٓ إِلَيَّ أَنَّمَآ إِلَٰهُكُمۡ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞ فَٱسۡتَقِيمُوٓاْ إِلَيۡهِ وَٱسۡتَغۡفِرُوهُۗ وَوَيۡلٞ لِّلۡمُشۡرِكِينَ

Ka ce: “Ni ba wani ba ne sai mutum kamarku, ana yiwo min wahayin cewa, abin bautarku abin bauta ne Guda Xaya, sai ku miqe kyam zuwa gare Shi, kuma ku nemi gafararsa. Tsananin azaba kuma ya tabbata ga mushirikai



Capítulo: Suratul Hujurat

Verso : 11

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا يَسۡخَرۡ قَوۡمٞ مِّن قَوۡمٍ عَسَىٰٓ أَن يَكُونُواْ خَيۡرٗا مِّنۡهُمۡ وَلَا نِسَآءٞ مِّن نِّسَآءٍ عَسَىٰٓ أَن يَكُنَّ خَيۡرٗا مِّنۡهُنَّۖ وَلَا تَلۡمِزُوٓاْ أَنفُسَكُمۡ وَلَا تَنَابَزُواْ بِٱلۡأَلۡقَٰبِۖ بِئۡسَ ٱلِٱسۡمُ ٱلۡفُسُوقُ بَعۡدَ ٱلۡإِيمَٰنِۚ وَمَن لَّمۡ يَتُبۡ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّـٰلِمُونَ

Ya ku waxanda suka yi imani, kada wasu mutane su yi wa wasu mutane izgili, mai yiwuwa ne su zamanto sun fi su alheri, kuma kada wasu mata (su yi wa) wasu mata (izgili), mai yiwuwa ne su zamanto sun fi su alheri; kada kuma ku riqa aibata junanku, kuma kada ku riqa jifan juna da munanan laquba (da kuke qi). Tir da sunan fasiqanci bayan imani. Wanda duk bai tuba ba, to waxannan su ne azzalumai



Capítulo: Suratut Tahrim

Verso : 8

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ تُوبُوٓاْ إِلَى ٱللَّهِ تَوۡبَةٗ نَّصُوحًا عَسَىٰ رَبُّكُمۡ أَن يُكَفِّرَ عَنكُمۡ سَيِّـَٔاتِكُمۡ وَيُدۡخِلَكُمۡ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ يَوۡمَ لَا يُخۡزِي ٱللَّهُ ٱلنَّبِيَّ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُۥۖ نُورُهُمۡ يَسۡعَىٰ بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَبِأَيۡمَٰنِهِمۡ يَقُولُونَ رَبَّنَآ أَتۡمِمۡ لَنَا نُورَنَا وَٱغۡفِرۡ لَنَآۖ إِنَّكَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Ya ku waxanda suka yi imani, ku tuba zuwa ga Allah tuba na gaskiya, tabbas Ubangijinku zai kankare muku kurakuranku Ya kuma shigar da ku gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, a ranar da Allah ba zai kunyata Manzo da waxanda suka yi imani tare da shi ba; haskensu yana tafe a gabansu da damansu suna cewa: “Ya Ubangijinmu, Ka sa haskenmu ya xore, Ka kuma gafarta mana; lalle Kai Mai iko ne a kan komai.”



Capítulo: Suratun Nasr

Verso : 3

فَسَبِّحۡ بِحَمۡدِ رَبِّكَ وَٱسۡتَغۡفِرۡهُۚ إِنَّهُۥ كَانَ تَوَّابَۢا

To ka yi tasbihi da yabon Ubangijinka, ka kuma nemi gafararsa. Lalle Shi Ya kasance Mai karvar tuba ne