فَتَلَقَّىٰٓ ءَادَمُ مِن رَّبِّهِۦ كَلِمَٰتٖ فَتَابَ عَلَيۡهِۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلتَّوَّابُ ٱلرَّحِيمُ
Sai Adamu ya karvi wasu kalmomi daga Ubangijinsa (na neman gafara), sai Ya yafe masa; lalle Shi ne Mai yawan karvar tuba kuma Mai yawan jin qai
إِلَّا ٱلَّذِينَ تَابُواْ وَأَصۡلَحُواْ وَبَيَّنُواْ فَأُوْلَـٰٓئِكَ أَتُوبُ عَلَيۡهِمۡ وَأَنَا ٱلتَّوَّابُ ٱلرَّحِيمُ
Sai dai waxanda suka tuba kuma suka gyara kuma suka bayyana, to waxannan zan karvi tubansu, kuma lalle Ni Mai karvar tuba ne, Mai jin qai
إِلَّا ٱلَّذِينَ تَابُواْ مِنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ وَأَصۡلَحُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٌ
Sai fa waxanda suka sake tuba bayan haka, kuma suka gyara (ayyukansu), to lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai
أُوْلَـٰٓئِكَ جَزَآؤُهُم مَّغۡفِرَةٞ مِّن رَّبِّهِمۡ وَجَنَّـٰتٞ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ وَنِعۡمَ أَجۡرُ ٱلۡعَٰمِلِينَ
Waxannan sakamakonsu shi ne gafara ta musamman daga Ubangijinsu, da gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, suna masu dawwama a cikinsu. Kuma madalla da sakamakon masu aiki
إِنَّمَا ٱلتَّوۡبَةُ عَلَى ٱللَّهِ لِلَّذِينَ يَعۡمَلُونَ ٱلسُّوٓءَ بِجَهَٰلَةٖ ثُمَّ يَتُوبُونَ مِن قَرِيبٖ فَأُوْلَـٰٓئِكَ يَتُوبُ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمۡۗ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمٗا
Tuban da Allah Yake karva kawai (ita ce) na waxanda suke aikata mummunan aiki da jahilci, sannan su gaggauta tuba, to waxannan Allah zai karvi tubansu. Allah kuma Ya kasance Mai yawan sani ne, Mai hikima
وَلَيۡسَتِ ٱلتَّوۡبَةُ لِلَّذِينَ يَعۡمَلُونَ ٱلسَّيِّـَٔاتِ حَتَّىٰٓ إِذَا حَضَرَ أَحَدَهُمُ ٱلۡمَوۡتُ قَالَ إِنِّي تُبۡتُ ٱلۡـَٰٔنَ وَلَا ٱلَّذِينَ يَمُوتُونَ وَهُمۡ كُفَّارٌۚ أُوْلَـٰٓئِكَ أَعۡتَدۡنَا لَهُمۡ عَذَابًا أَلِيمٗا
Kuma ba a karvar tuba daga waxanda suke aikata munanan ayyuka har sai lokacin da mutuwa ta zo wa xayansu, sai ya ce: “Ni kam na tuba yanzu;” kuma ba a karvar tuban waxanda suke mutuwa alhalin suna kafirai. Waxannan Mun yi musu tanadin azaba mai raxaxi
إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَغۡفِرُ أَن يُشۡرَكَ بِهِۦ وَيَغۡفِرُ مَا دُونَ ذَٰلِكَ لِمَن يَشَآءُۚ وَمَن يُشۡرِكۡ بِٱللَّهِ فَقَدِ ٱفۡتَرَىٰٓ إِثۡمًا عَظِيمًا
Lalle Allah ba Ya gafarta a yi shirka da Shi, amma Yana gafarta abin da bai kai shirka ba ga wanda Ya ga dama. Kuma duk wanda ya yi shirka da Allah, to haqiqa ya qirqiri wani gagarumin laifi
وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن رَّسُولٍ إِلَّا لِيُطَاعَ بِإِذۡنِ ٱللَّهِۚ وَلَوۡ أَنَّهُمۡ إِذ ظَّلَمُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ جَآءُوكَ فَٱسۡتَغۡفَرُواْ ٱللَّهَ وَٱسۡتَغۡفَرَ لَهُمُ ٱلرَّسُولُ لَوَجَدُواْ ٱللَّهَ تَوَّابٗا رَّحِيمٗا
Kuma ba Mu tava aiko wani manzo ba, face sai don a yi masa xa’a da izinin Allah. Kuma da a ce lokacin da suka zalunci kawunansu sun zo maka, sun nemi Allah Ya gafarta musu, sannan Manzo ya roqa musu gafara, to tabbas da sun sami Allah Yana Mai yawan karvar tuba, Mai jin qai
وَمَن يَعۡمَلۡ سُوٓءًا أَوۡ يَظۡلِمۡ نَفۡسَهُۥ ثُمَّ يَسۡتَغۡفِرِ ٱللَّهَ يَجِدِ ٱللَّهَ غَفُورٗا رَّحِيمٗا
Kuma duk wanda ya aikata mummunan aiki ko ya zalunci kansa, sannan ya nemi gafarar Allah, to zai sami Allah Mai yawan gafara ne, Mai yawan jin qai
إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَغۡفِرُ أَن يُشۡرَكَ بِهِۦ وَيَغۡفِرُ مَا دُونَ ذَٰلِكَ لِمَن يَشَآءُۚ وَمَن يُشۡرِكۡ بِٱللَّهِ فَقَدۡ ضَلَّ ضَلَٰلَۢا بَعِيدًا
Lalle Allah ba Ya gafartawa a yi masa shirka, Yana kuwa gafarta abin da bai kai shirka ba ga wanda Ya ga dama. Duk wanda ya yi wa Allah shirka, to haqiqa ya vata manisanciyar vata
إِلَّا ٱلَّذِينَ تَابُواْ وَأَصۡلَحُواْ وَٱعۡتَصَمُواْ بِٱللَّهِ وَأَخۡلَصُواْ دِينَهُمۡ لِلَّهِ فَأُوْلَـٰٓئِكَ مَعَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَۖ وَسَوۡفَ يُؤۡتِ ٱللَّهُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ أَجۡرًا عَظِيمٗا
Sai fa waxanda suka tuba, kuma suka gyara aikinsu, kuma suka yi riqo ga igiyar Allah; kuma suka tsantsanta addininsu don Allah; to waxannan suna tare da muminai; kuma Allah zai bai wa muminai lada mai girma
إِلَّا ٱلَّذِينَ تَابُواْ مِن قَبۡلِ أَن تَقۡدِرُواْ عَلَيۡهِمۡۖ فَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Sai dai waxanda suka tuba tun kafin ku sami damar kama su; to ku sani cewa, lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai
فَمَن تَابَ مِنۢ بَعۡدِ ظُلۡمِهِۦ وَأَصۡلَحَ فَإِنَّ ٱللَّهَ يَتُوبُ عَلَيۡهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٌ
To (amma) wanda ya tuba bayan zaluncinsa, kuma ya gyara aikinsa, to lalle Allah zai karvi tubansa. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai
وَإِذَا جَآءَكَ ٱلَّذِينَ يُؤۡمِنُونَ بِـَٔايَٰتِنَا فَقُلۡ سَلَٰمٌ عَلَيۡكُمۡۖ كَتَبَ رَبُّكُمۡ عَلَىٰ نَفۡسِهِ ٱلرَّحۡمَةَ أَنَّهُۥ مَنۡ عَمِلَ مِنكُمۡ سُوٓءَۢا بِجَهَٰلَةٖ ثُمَّ تَابَ مِنۢ بَعۡدِهِۦ وَأَصۡلَحَ فَأَنَّهُۥ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Kuma idan waxanda suke yin imani da ayoyinmu sun zo wurinka, to ka ce: “Sallama a gare ku;” Ubangijinku Ya wajabta wa kansa yin rahama cewa, lalle cikinku duk wanda ya aikata wani mummunan aiki bisa ga jahilci, sannan daga baya ya tuba kuma ya kyautata aiki, to Shi Mai gafara ne, Mai jin qai.”
وَٱلَّذِينَ عَمِلُواْ ٱلسَّيِّـَٔاتِ ثُمَّ تَابُواْ مِنۢ بَعۡدِهَا وَءَامَنُوٓاْ إِنَّ رَبَّكَ مِنۢ بَعۡدِهَا لَغَفُورٞ رَّحِيمٞ
Waxanda kuma suka aikata munanan ayyuka, sannan suka tuba daga baya, kuma suka yi imani, lalle Ubangijinka bayansa (tuban), tabbas Mai gafara ne, Mai jin qai
وَءَاخَرُونَ ٱعۡتَرَفُواْ بِذُنُوبِهِمۡ خَلَطُواْ عَمَلٗا صَٰلِحٗا وَءَاخَرَ سَيِّئًا عَسَى ٱللَّهُ أَن يَتُوبَ عَلَيۡهِمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٌ
Wasu kuwa sun yi iqirari da laifinsu, sun gauraya kyakkyawan aiki da wani mummuna, to tabbas Allah zai karvi tubansu. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai
أَلَمۡ يَعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ هُوَ يَقۡبَلُ ٱلتَّوۡبَةَ عَنۡ عِبَادِهِۦ وَيَأۡخُذُ ٱلصَّدَقَٰتِ وَأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلتَّوَّابُ ٱلرَّحِيمُ
Shin yanzu ba su sani ba ne cewa Allah Shi Yake karvar tuba daga bayinsa Yake kuma karvar sadakoki, kuma lalle Shi ne Mai yawan karvar tuba, Mai jin qai?
لَّقَد تَّابَ ٱللَّهُ عَلَى ٱلنَّبِيِّ وَٱلۡمُهَٰجِرِينَ وَٱلۡأَنصَارِ ٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُوهُ فِي سَاعَةِ ٱلۡعُسۡرَةِ مِنۢ بَعۡدِ مَا كَادَ يَزِيغُ قُلُوبُ فَرِيقٖ مِّنۡهُمۡ ثُمَّ تَابَ عَلَيۡهِمۡۚ إِنَّهُۥ بِهِمۡ رَءُوفٞ رَّحِيمٞ
Tabbas haqiqa Allah Ya yafe wa Annabi da masu hijira da kuma Ansaru waxanda suka bi shi a lokacin tsanani bayan har zukatan wasu qungiyoyi daga cikinsu sun kusa su karkace, sannan (Allah) Ya karvi tubansu. Lalle Shi Mai tausasawa ne, Mai jin qai a gare su
وَعَلَى ٱلثَّلَٰثَةِ ٱلَّذِينَ خُلِّفُواْ حَتَّىٰٓ إِذَا ضَاقَتۡ عَلَيۡهِمُ ٱلۡأَرۡضُ بِمَا رَحُبَتۡ وَضَاقَتۡ عَلَيۡهِمۡ أَنفُسُهُمۡ وَظَنُّوٓاْ أَن لَّا مَلۡجَأَ مِنَ ٱللَّهِ إِلَّآ إِلَيۡهِ ثُمَّ تَابَ عَلَيۡهِمۡ لِيَتُوبُوٓاْۚ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلتَّوَّابُ ٱلرَّحِيمُ
Kuma (Ya yafe wa) mutanen nan guda uku waxanda aka dakatar da karvar tubansu[1], har sai yayin da duniya ta yi musu qunci duk da yalwarta, kuma zukatansu suka quntata, suka tabbatar da cewa dai babu wata mafaka daga Allah sai dai a wajensa. Sannan sai Ya yi musu muwafaqar tuba don su tuba. Lalle Allah Shi ne Mai yawan karvar tuba, Mai jin qai
1- Su ne sahabban nan uku, watau Ka’abu xan Maliku da Muraratu xan Rabi’atu da Hilal xan Umayyatu Al-Waqifi. Sun qi fita yaqin Tabuka tare da Annabi () ba tare da wani uzuri ba.
۞نَبِّئۡ عِبَادِيٓ أَنِّيٓ أَنَا ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ
Ka bai wa bayina labarin cewa lalle Ni, Ni ne Mai gafara, Mai jin qai
ثُمَّ إِنَّ رَبَّكَ لِلَّذِينَ هَاجَرُواْ مِنۢ بَعۡدِ مَا فُتِنُواْ ثُمَّ جَٰهَدُواْ وَصَبَرُوٓاْ إِنَّ رَبَّكَ مِنۢ بَعۡدِهَا لَغَفُورٞ رَّحِيمٞ
Sannan lalle Ubangjinka (Mai gafara ne da jin qai) ga waxanda suka yi hijira bayan an fitine su, sannan suka yi jihadi suka kuma yi haquri, lalle Ubangijinka, bayansu (waxannan ayyuka) Mai gafara ne, Mai jin qai
ثُمَّ إِنَّ رَبَّكَ لِلَّذِينَ عَمِلُواْ ٱلسُّوٓءَ بِجَهَٰلَةٖ ثُمَّ تَابُواْ مِنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ وَأَصۡلَحُوٓاْ إِنَّ رَبَّكَ مِنۢ بَعۡدِهَا لَغَفُورٞ رَّحِيمٌ
Sannan lalle Ubangijinka (Mai gafara ne) ga waxanda suka aikata mummuna a cikin jahilci sannan suka tuba bayan haka suka kuma gyara, lalle Ubagijinka Mai gafara ne, Mai jin qai
وَإِنِّي لَغَفَّارٞ لِّمَن تَابَ وَءَامَنَ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا ثُمَّ ٱهۡتَدَىٰ
Lalle Ni kuma Mai yawan gafara ne ga wanda ya tuba kuma ya yi aiki na gari sannan ya (tabbata bisa) shiriya
إِلَّا ٱلَّذِينَ تَابُواْ مِنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ وَأَصۡلَحُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Sai dai waxanda suka tuba bayan wannan suka kuma gyara, to haqiqa Allah Mai gafara ne, Mai jin qai ne
إِلَّا مَن تَابَ وَءَامَنَ وَعَمِلَ عَمَلٗا صَٰلِحٗا فَأُوْلَـٰٓئِكَ يُبَدِّلُ ٱللَّهُ سَيِّـَٔاتِهِمۡ حَسَنَٰتٖۗ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمٗا
Sai dai wanda ya tuba ya kuma yi imani, kuma ya yi aiki na gari, to waxannan Allah zai musanya munanan ayyukansu da kyawawa. Allah kuwa ya kasance Mai gafara ne, Mai jin qai
وَمَن تَابَ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا فَإِنَّهُۥ يَتُوبُ إِلَى ٱللَّهِ مَتَابٗا
Wanda kuwa ya tuba ya kuma yi aiki na gari, to lalle shi ne wanda yake tuba na gaskiya zuwa ga Allah
قَالَ رَبِّ إِنِّي ظَلَمۡتُ نَفۡسِي فَٱغۡفِرۡ لِي فَغَفَرَ لَهُۥٓۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ
Ya ce: “Ya Ubangijina, lalle ni na zalunci kaina, sai Ka yi min gafara,” sai ko Ya yi masa gafara. Lalle Shi kuwa Mai gafara ne, Mai jin qai
فَأَمَّا مَن تَابَ وَءَامَنَ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا فَعَسَىٰٓ أَن يَكُونَ مِنَ ٱلۡمُفۡلِحِينَ
To amma wanda ya tuba ya kuma yi imani ya kuma yi aiki nagari, to ana fatan ya zama cikin masu samun babban rabo
لِّيُعَذِّبَ ٱللَّهُ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ وَٱلۡمُنَٰفِقَٰتِ وَٱلۡمُشۡرِكِينَ وَٱلۡمُشۡرِكَٰتِ وَيَتُوبَ ٱللَّهُ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِۗ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمَۢا
Don Allah Ya azabtar da munafukai maza da munafukai mata, da mushirikai maza da mushirikai mata, Ya kuma karvi tubar muminai maza da muminai mata. Allah kuwa Ya kasance Mai gafara ne, Mai jin qai
وَهُوَ ٱلَّذِي يَقۡبَلُ ٱلتَّوۡبَةَ عَنۡ عِبَادِهِۦ وَيَعۡفُواْ عَنِ ٱلسَّيِّـَٔاتِ وَيَعۡلَمُ مَا تَفۡعَلُونَ
Shi ne kuma wanda Yake karvar tuba daga bayinsa, Yake kuma yin afuwa game da munanan (ayyuka), Yana kuma sane da abin da kuke aikatawa