۞قُلۡ أَؤُنَبِّئُكُم بِخَيۡرٖ مِّن ذَٰلِكُمۡۖ لِلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْ عِندَ رَبِّهِمۡ جَنَّـٰتٞ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَا وَأَزۡوَٰجٞ مُّطَهَّرَةٞ وَرِضۡوَٰنٞ مِّنَ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ بَصِيرُۢ بِٱلۡعِبَادِ
Ka ce: “Shin in ba ku labarin da abin da ya fi waxancan alheri? Waxanda suka yi taqawa, suna da wasu gidajen aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, a wurin Ubangijinsu, suna masu zama a cikinsu dindindin da mata na aure tsarkaka da kuma yarda daga Allah. Kuma Allah Mai ganin bayinsa ne.”
ٱلَّذِينَ يَقُولُونَ رَبَّنَآ إِنَّنَآ ءَامَنَّا فَٱغۡفِرۡ لَنَا ذُنُوبَنَا وَقِنَا عَذَابَ ٱلنَّارِ
(Su ne) waxanda suke cewa: “Ya Ubangijinmu, lalle mu mun yi imani, don haka Ka gafarta mana zunubanmu, kuma Ka tserar da mu daga azabar wuta.”
ٱلصَّـٰبِرِينَ وَٱلصَّـٰدِقِينَ وَٱلۡقَٰنِتِينَ وَٱلۡمُنفِقِينَ وَٱلۡمُسۡتَغۡفِرِينَ بِٱلۡأَسۡحَارِ
(Su ne) masu haquri, masu gaskiya, kuma masu xa’a, kuma masu ciyarwa, kuma masu neman gafara a qarshen dare
۞وَسَارِعُوٓاْ إِلَىٰ مَغۡفِرَةٖ مِّن رَّبِّكُمۡ وَجَنَّةٍ عَرۡضُهَا ٱلسَّمَٰوَٰتُ وَٱلۡأَرۡضُ أُعِدَّتۡ لِلۡمُتَّقِينَ
Kuma ku yi gaggawa zuwa ga neman gafara ta musamman daga wajen Ubangijinku, da kuma Aljanna wadda faxinta yake daidai da sammai da qasa, an yi tanadinta domin masu taqawa
ٱلَّذِينَ يُنفِقُونَ فِي ٱلسَّرَّآءِ وَٱلضَّرَّآءِ وَٱلۡكَٰظِمِينَ ٱلۡغَيۡظَ وَٱلۡعَافِينَ عَنِ ٱلنَّاسِۗ وَٱللَّهُ يُحِبُّ ٱلۡمُحۡسِنِينَ
(Su ne) waxanda suke ciyarwa a cikin halin yalwa da halin qunci, kuma masu voye fushi kuma masu yin afuwa ga mutane. Allah kuwa Yana son masu kyautatawa
وَٱلَّذِينَ إِذَا فَعَلُواْ فَٰحِشَةً أَوۡ ظَلَمُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ ذَكَرُواْ ٱللَّهَ فَٱسۡتَغۡفَرُواْ لِذُنُوبِهِمۡ وَمَن يَغۡفِرُ ٱلذُّنُوبَ إِلَّا ٱللَّهُ وَلَمۡ يُصِرُّواْ عَلَىٰ مَا فَعَلُواْ وَهُمۡ يَعۡلَمُونَ
(Su ne) kuma waxanda idan sun aikata mummunan aiki, ko suka zalunci kansu, nan take sai su tuna da Allah, sai su nemi gafarar zunubansu. Wane ne kuwa mai gafarta zunubbai in ba Allah ba? Kuma ba sa zarcewa a kan abin da suka yi, alhali suna sane
أُوْلَـٰٓئِكَ جَزَآؤُهُم مَّغۡفِرَةٞ مِّن رَّبِّهِمۡ وَجَنَّـٰتٞ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ وَنِعۡمَ أَجۡرُ ٱلۡعَٰمِلِينَ
Waxannan sakamakonsu shi ne gafara ta musamman daga Ubangijinsu, da gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, suna masu dawwama a cikinsu. Kuma madalla da sakamakon masu aiki
وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَٱلرَّسُولَ فَأُوْلَـٰٓئِكَ مَعَ ٱلَّذِينَ أَنۡعَمَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِم مِّنَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ وَٱلصِّدِّيقِينَ وَٱلشُّهَدَآءِ وَٱلصَّـٰلِحِينَۚ وَحَسُنَ أُوْلَـٰٓئِكَ رَفِيقٗا
Kuma duk waxanda suka yi wa Allah xa’a da wannan Manzon, to waxannan suna tare da waxanda Allah Ya yi musu ni’ima, su ne annabawa da siddiqai da shahidai da salihan bayi. Kuma madalla da waxannan abokai
قَالَ مُوسَىٰ لِقَوۡمِهِ ٱسۡتَعِينُواْ بِٱللَّهِ وَٱصۡبِرُوٓاْۖ إِنَّ ٱلۡأَرۡضَ لِلَّهِ يُورِثُهَا مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦۖ وَٱلۡعَٰقِبَةُ لِلۡمُتَّقِينَ
Sai Musa ya ce da mutanensa: “Ku nemi taimakon Allah, kuma ku yi haquri; lalle qasa mulkin Allah ce, Yana gadar da ita ga wanda Ya ga dama daga cikin bayinsa; kuma kyakkyawan qarshe yana tabbata ne ga masu taqawa.”
ٱلتَّـٰٓئِبُونَ ٱلۡعَٰبِدُونَ ٱلۡحَٰمِدُونَ ٱلسَّـٰٓئِحُونَ ٱلرَّـٰكِعُونَ ٱلسَّـٰجِدُونَ ٱلۡأٓمِرُونَ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَٱلنَّاهُونَ عَنِ ٱلۡمُنكَرِ وَٱلۡحَٰفِظُونَ لِحُدُودِ ٱللَّهِۗ وَبَشِّرِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Masu tuba, masu bauta, masu godiya, masu azumi, masu ruku’i, masu sujjada, masu yin umarni da aikin alheri masu kuma hani ga mummunan aiki, da masu kiyaye iyakokin Allah. To sai ka yi wa muminai (masu irin waxannan siffofin) albishir
إِنَّ ٱللَّهَ مَعَ ٱلَّذِينَ ٱتَّقَواْ وَّٱلَّذِينَ هُم مُّحۡسِنُونَ
Lalle Allah Yana tare da waxanda suka yi taqawa da kuma waxanda suke masu kyautatawa ne
رَّبُّكُمۡ أَعۡلَمُ بِمَا فِي نُفُوسِكُمۡۚ إِن تَكُونُواْ صَٰلِحِينَ فَإِنَّهُۥ كَانَ لِلۡأَوَّـٰبِينَ غَفُورٗا
Ubangijinku ne Mafi sanin abin da yake zukatanku. Idan kuka zamanto nagari, to lalle Shi Ya tabbata Mai gafara ne ga masu komawa gare Shi da tuba
وَلَقَدۡ كَتَبۡنَا فِي ٱلزَّبُورِ مِنۢ بَعۡدِ ٱلذِّكۡرِ أَنَّ ٱلۡأَرۡضَ يَرِثُهَا عِبَادِيَ ٱلصَّـٰلِحُونَ
Kuma haqiqa Mun rubuta cikin saukakkun littattafai bayan (an rubuta a Lauhul-Mahfuzu) cewa, ita qasa bayina na gari ne za su gaje ta
إِنَّهُۥ كَانَ فَرِيقٞ مِّنۡ عِبَادِي يَقُولُونَ رَبَّنَآ ءَامَنَّا فَٱغۡفِرۡ لَنَا وَٱرۡحَمۡنَا وَأَنتَ خَيۡرُ ٱلرَّـٰحِمِينَ
“Lalle yadda lamarin yake, wata qungiya daga bayina sun kasance suna cewa: “Ya Ubangijinmu, mun yi imani, sai Ka gafarta mana, kuma Ka ji qan mu, Kai ne kuwa Fiyayyen masu jin qai
وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَيَخۡشَ ٱللَّهَ وَيَتَّقۡهِ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡفَآئِزُونَ
Duk kuwa wanda ya bi Allah da Manzonsa kuma yake tsoron Allah kuma yake kiyaye dokokinsa, to waxannan su ne masu rabauta
وَعِبَادُ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلَّذِينَ يَمۡشُونَ عَلَى ٱلۡأَرۡضِ هَوۡنٗا وَإِذَا خَاطَبَهُمُ ٱلۡجَٰهِلُونَ قَالُواْ سَلَٰمٗا
Bayin (Allah) Mai rahama kuwa (su ne) waxanda suke tafiya a bayan qasa a natse; idan kuma wawaye sun yi musu magana (sai) su faxa (musu) magana ta aminci
وَٱلَّذِينَ يَبِيتُونَ لِرَبِّهِمۡ سُجَّدٗا وَقِيَٰمٗا
(Su ne) kuma waxanda suke kwana suna masu sujjada da tsayuwa ga Ubangijinsu
وَٱلَّذِينَ يَقُولُونَ رَبَّنَا ٱصۡرِفۡ عَنَّا عَذَابَ جَهَنَّمَۖ إِنَّ عَذَابَهَا كَانَ غَرَامًا
(Su ne) kuma waxanda suke cewa: “Ya Ubangijinmu, Ka kawar mana da azabar Jahannama; lalle azabarta ta kasance halaka ce mai xorewa
إِنَّهَا سَآءَتۡ مُسۡتَقَرّٗا وَمُقَامٗا
“Lalle ita (Jahannama) ta kasance mummunar matabbata kuma mazauna (ga kafirai).”
وَٱلَّذِينَ إِذَآ أَنفَقُواْ لَمۡ يُسۡرِفُواْ وَلَمۡ يَقۡتُرُواْ وَكَانَ بَيۡنَ ذَٰلِكَ قَوَامٗا
(Su ne) kuma waxanda idan suka ciyar ba sa almubazzaranci kuma ba sa yin qwauro, (ciyarwarsu) kuwa ta kasance tsaka-tsaki ce
وَٱلَّذِينَ لَا يَدۡعُونَ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ وَلَا يَقۡتُلُونَ ٱلنَّفۡسَ ٱلَّتِي حَرَّمَ ٱللَّهُ إِلَّا بِٱلۡحَقِّ وَلَا يَزۡنُونَۚ وَمَن يَفۡعَلۡ ذَٰلِكَ يَلۡقَ أَثَامٗا
(Su ne) kuma waxanda ba sa bauta wa wani tare da Allah, kuma ba sa kashe ran da Allah Ya hana kashewa sai da haqqi, kuma ba sa yin zina. Wanda kuwa ya aikata hakan to zai haxu da (uqubar) laifinsa
يُضَٰعَفۡ لَهُ ٱلۡعَذَابُ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَيَخۡلُدۡ فِيهِۦ مُهَانًا
Za a ninninka masa azaba ranar alqiyama, kuma ya dawwama a cikinta a wulaqance
إِلَّا مَن تَابَ وَءَامَنَ وَعَمِلَ عَمَلٗا صَٰلِحٗا فَأُوْلَـٰٓئِكَ يُبَدِّلُ ٱللَّهُ سَيِّـَٔاتِهِمۡ حَسَنَٰتٖۗ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمٗا
Sai dai wanda ya tuba ya kuma yi imani, kuma ya yi aiki na gari, to waxannan Allah zai musanya munanan ayyukansu da kyawawa. Allah kuwa ya kasance Mai gafara ne, Mai jin qai
وَمَن تَابَ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا فَإِنَّهُۥ يَتُوبُ إِلَى ٱللَّهِ مَتَابٗا
Wanda kuwa ya tuba ya kuma yi aiki na gari, to lalle shi ne wanda yake tuba na gaskiya zuwa ga Allah
وَٱلَّذِينَ لَا يَشۡهَدُونَ ٱلزُّورَ وَإِذَا مَرُّواْ بِٱللَّغۡوِ مَرُّواْ كِرَامٗا
(Su ne) kuma waxanda ba sa halartar wuraren baxala, idan kuma suka wuce ta wurin aikin assha to sai su wuce suna masu mutunta kansu
وَٱلَّذِينَ إِذَا ذُكِّرُواْ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِمۡ لَمۡ يَخِرُّواْ عَلَيۡهَا صُمّٗا وَعُمۡيَانٗا
(Su ne) kuma waxanda idan aka yi musu wa’azi da ayoyin Ubangijinsu ba sa fuskantar su suna kurame kuma makafi
وَٱلَّذِينَ يَقُولُونَ رَبَّنَا هَبۡ لَنَا مِنۡ أَزۡوَٰجِنَا وَذُرِّيَّـٰتِنَا قُرَّةَ أَعۡيُنٖ وَٱجۡعَلۡنَا لِلۡمُتَّقِينَ إِمَامًا
(Su ne) kuma waxanda suke cewa: “Ya Ubangijinmu, Ka ba mu masu sanyaya mana zukata daga matayenmu da zuri’armu, kuma Ka sanya mu abin koyi ga masu taqawa
أُوْلَـٰٓئِكَ يُجۡزَوۡنَ ٱلۡغُرۡفَةَ بِمَا صَبَرُواْ وَيُلَقَّوۡنَ فِيهَا تَحِيَّةٗ وَسَلَٰمًا
Waxannan su ne ake saka wa da xakuna na Aljanna saboda haqurin da suka yi, za kuma a tare su a cikinta da gaisuwa da sallama
خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ حَسُنَتۡ مُسۡتَقَرّٗا وَمُقَامٗا
Suna madawwama a cikinta. Matabbata da mazauni sun kyautata
تِلۡكَ ٱلدَّارُ ٱلۡأٓخِرَةُ نَجۡعَلُهَا لِلَّذِينَ لَا يُرِيدُونَ عُلُوّٗا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَا فَسَادٗاۚ وَٱلۡعَٰقِبَةُ لِلۡمُتَّقِينَ
Wancan gida na lahira Muna ba da shi ga waxanda ba sa nufin girman kai da varna a bayan qasa. Kyakkyawan qarshe kuma yana ga masu kiyaye dokokin Allah ne