Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 65

وَلَقَدۡ عَلِمۡتُمُ ٱلَّذِينَ ٱعۡتَدَوۡاْ مِنكُمۡ فِي ٱلسَّبۡتِ فَقُلۡنَا لَهُمۡ كُونُواْ قِرَدَةً خَٰسِـِٔينَ

Kuma haqiqa kun san waxanda suka yi shisshigi daga cikinku game da ranar Assabar, sai Muka ce da su: “Ku zama birrai kuna qasqantattu.”



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 154

وَرَفَعۡنَا فَوۡقَهُمُ ٱلطُّورَ بِمِيثَٰقِهِمۡ وَقُلۡنَا لَهُمُ ٱدۡخُلُواْ ٱلۡبَابَ سُجَّدٗا وَقُلۡنَا لَهُمۡ لَا تَعۡدُواْ فِي ٱلسَّبۡتِ وَأَخَذۡنَا مِنۡهُم مِّيثَٰقًا غَلِيظٗا

Kuma Muka xaga dutsen Xuri a kansu don su karvi alqawarinsu, kuma Muka ce da su: “Ku shiga qofar (garin) a sunkuye.” Kuma Muka ce da su: “Kada ku qetare iyaka (ta kamun kifi) a ranar Asabar,” kuma Muka yi alqawari mai qarfi da su



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 163

وَسۡـَٔلۡهُمۡ عَنِ ٱلۡقَرۡيَةِ ٱلَّتِي كَانَتۡ حَاضِرَةَ ٱلۡبَحۡرِ إِذۡ يَعۡدُونَ فِي ٱلسَّبۡتِ إِذۡ تَأۡتِيهِمۡ حِيتَانُهُمۡ يَوۡمَ سَبۡتِهِمۡ شُرَّعٗا وَيَوۡمَ لَا يَسۡبِتُونَ لَا تَأۡتِيهِمۡۚ كَذَٰلِكَ نَبۡلُوهُم بِمَا كَانُواْ يَفۡسُقُونَ

Kuma ka tambaye su game da (mutanen) alqaryar nan wadda take dab da gavar teku, yayin da suke qetare iyaka a ranar Asabar, yayin da kifayensu suke zuwa a ranar Asabar baja-baja, amma ranar da ba Asabar ba kuwa ba sa zuwa. Kamar haka ne muka jarrabe su saboda abin da suka kasance suna yi na fasiqanci



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 164

وَإِذۡ قَالَتۡ أُمَّةٞ مِّنۡهُمۡ لِمَ تَعِظُونَ قَوۡمًا ٱللَّهُ مُهۡلِكُهُمۡ أَوۡ مُعَذِّبُهُمۡ عَذَابٗا شَدِيدٗاۖ قَالُواْ مَعۡذِرَةً إِلَىٰ رَبِّكُمۡ وَلَعَلَّهُمۡ يَتَّقُونَ

Kuma ka tuna lokacin da wata jama’a cikinsu suka ce: “Don me za ku riqa wa’azi ga waxansu mutanen da idan Allah Ya ga dama sai Ya hallakar da su ko Ya yi musu azaba mai tsanani?” Sai suka ce: “Don yanke hanzari ne a wurin Ubangijinku ko watakila kuma sa kiyaye dokokin Allah.”



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 165

فَلَمَّا نَسُواْ مَا ذُكِّرُواْ بِهِۦٓ أَنجَيۡنَا ٱلَّذِينَ يَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلسُّوٓءِ وَأَخَذۡنَا ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ بِعَذَابِۭ بَـِٔيسِۭ بِمَا كَانُواْ يَفۡسُقُونَ

To yayin da suka yi watsi da abin da aka yi musu wa’azi da shi, sai Muka tserar da waxanda suke hana mummunan aiki, Muka kuma kama waxanda suka yi zalunci, da wata mummunar azaba, saboda abin da suka riqa yi na fasiqanci



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 166

فَلَمَّا عَتَوۡاْ عَن مَّا نُهُواْ عَنۡهُ قُلۡنَا لَهُمۡ كُونُواْ قِرَدَةً خَٰسِـِٔينَ

To yayin da suka yi tsaurin kai a kan abin da aka hana su, sai Muka ce da su: “Ku zama birrai, qasqantattu.”



Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 124

إِنَّمَا جُعِلَ ٱلسَّبۡتُ عَلَى ٱلَّذِينَ ٱخۡتَلَفُواْ فِيهِۚ وَإِنَّ رَبَّكَ لَيَحۡكُمُ بَيۡنَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ فِيمَا كَانُواْ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَ

An farlanta (girmama ranar) Asabar kawai a kan waxanda suka yi savani game da ita. kuma lalle Ubangijinka tabbas zai yi hukunci tsakaninsu ranar alqiyama game da abin da suka kasance suna savani a game da shi