Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 21

وَقَاسَمَهُمَآ إِنِّي لَكُمَا لَمِنَ ٱلنَّـٰصِحِينَ

Kuma ya yi musu rantsuwa cewa: “Lalle ni mai yi muku nasiha ne.”



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 22

فَدَلَّىٰهُمَا بِغُرُورٖۚ فَلَمَّا ذَاقَا ٱلشَّجَرَةَ بَدَتۡ لَهُمَا سَوۡءَٰتُهُمَا وَطَفِقَا يَخۡصِفَانِ عَلَيۡهِمَا مِن وَرَقِ ٱلۡجَنَّةِۖ وَنَادَىٰهُمَا رَبُّهُمَآ أَلَمۡ أَنۡهَكُمَا عَن تِلۡكُمَا ٱلشَّجَرَةِ وَأَقُل لَّكُمَآ إِنَّ ٱلشَّيۡطَٰنَ لَكُمَا عَدُوّٞ مُّبِينٞ

Sai ya yaudare su da ruxi. Don haka yayin da suka xanxani wannan bishiyar, sai tsiraicinsu ya bayyana a gare su, sai suka fara lulluva da ganyayen Aljanna; sai Ubangijinsu Ya kira su: “Yanzu ban hana ku cin wannan bishiyar ba, ban kuma ce da ku ba lalle Shaixan maqiyi ne a gare ku mabayyani?”



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 27

يَٰبَنِيٓ ءَادَمَ لَا يَفۡتِنَنَّكُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ كَمَآ أَخۡرَجَ أَبَوَيۡكُم مِّنَ ٱلۡجَنَّةِ يَنزِعُ عَنۡهُمَا لِبَاسَهُمَا لِيُرِيَهُمَا سَوۡءَٰتِهِمَآۚ إِنَّهُۥ يَرَىٰكُمۡ هُوَ وَقَبِيلُهُۥ مِنۡ حَيۡثُ لَا تَرَوۡنَهُمۡۗ إِنَّا جَعَلۡنَا ٱلشَّيَٰطِينَ أَوۡلِيَآءَ لِلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ

Ya ku ‘yan’adam, kada Shaixan ya fitine ku kamar yadda ya fitar da iyayenku daga cikin Aljanna, yana mai cire musu tufafinsu don ya nuna musu tsiraicin junansu. Lalle shi yana ganin ku, shi da jama’arsa ta inda ku ba kwa ganin su. Lalle Mu Mun sanya shaixanu su zamo masoya ga waxanda ba sa yin imani



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 200

وَإِمَّا يَنزَغَنَّكَ مِنَ ٱلشَّيۡطَٰنِ نَزۡغٞ فَٱسۡتَعِذۡ بِٱللَّهِۚ إِنَّهُۥ سَمِيعٌ عَلِيمٌ

Idan wani tunzuri daga Shaixan ya tunzura ka, to ka nemi tsarin Allah. Lalle Shi Mai ji ne, Masani



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 201

إِنَّ ٱلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْ إِذَا مَسَّهُمۡ طَـٰٓئِفٞ مِّنَ ٱلشَّيۡطَٰنِ تَذَكَّرُواْ فَإِذَا هُم مُّبۡصِرُونَ

Lalle waxanda suka kiyaye dokokin Allah, idan wani Shaixan mai sa waswasi ya shafe su, sai su tuna (da Allah), sai ga su suna gani tar



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 202

وَإِخۡوَٰنُهُمۡ يَمُدُّونَهُمۡ فِي ٱلۡغَيِّ ثُمَّ لَا يُقۡصِرُونَ

‘Yan’uwansu kuwa[1] suna qara kawo musu xauki na vata, sannan su ba sa taqaitawa


1- Su ne shaixanu na mutane da aljanu, suna qara ingiza kafirai cikin vata ba tare da suna gajiya ko qosawa a kan haka ba.


Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 48

وَإِذۡ زَيَّنَ لَهُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ أَعۡمَٰلَهُمۡ وَقَالَ لَا غَالِبَ لَكُمُ ٱلۡيَوۡمَ مِنَ ٱلنَّاسِ وَإِنِّي جَارٞ لَّكُمۡۖ فَلَمَّا تَرَآءَتِ ٱلۡفِئَتَانِ نَكَصَ عَلَىٰ عَقِبَيۡهِ وَقَالَ إِنِّي بَرِيٓءٞ مِّنكُمۡ إِنِّيٓ أَرَىٰ مَا لَا تَرَوۡنَ إِنِّيٓ أَخَافُ ٱللَّهَۚ وَٱللَّهُ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ

Kuma ku tuna lokacin da Shaixan ya qawata musu ayyukansu, ya kuma ce: “Babu wasu mutane a yau da za su yi galaba a kanku, lalle kuma ni maqocinku ne.” Saboda haka lokacin da qungiyoyin biyu suka haxu sai ya tsere a guje, ya kuma ce: “Lalle ni ba ruwana da ku, lalle ni ina ganin abin da ku ba kwa gani, lalle ni ina tsoron Allah. Allah kuwa Mai tsananin azaba ne.”



Capítulo: Suratu Ibrahim

Verso : 22

وَقَالَ ٱلشَّيۡطَٰنُ لَمَّا قُضِيَ ٱلۡأَمۡرُ إِنَّ ٱللَّهَ وَعَدَكُمۡ وَعۡدَ ٱلۡحَقِّ وَوَعَدتُّكُمۡ فَأَخۡلَفۡتُكُمۡۖ وَمَا كَانَ لِيَ عَلَيۡكُم مِّن سُلۡطَٰنٍ إِلَّآ أَن دَعَوۡتُكُمۡ فَٱسۡتَجَبۡتُمۡ لِيۖ فَلَا تَلُومُونِي وَلُومُوٓاْ أَنفُسَكُمۖ مَّآ أَنَا۠ بِمُصۡرِخِكُمۡ وَمَآ أَنتُم بِمُصۡرِخِيَّ إِنِّي كَفَرۡتُ بِمَآ أَشۡرَكۡتُمُونِ مِن قَبۡلُۗ إِنَّ ٱلظَّـٰلِمِينَ لَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

Shaixan kuma lokacin da aka gama hukunci ya ce: “Lalle Allah Ya yi muku alqawari na gaskiya, ni kuma na yi muku alqawari sai na sava muku. To ba ni da wani qarfi da na nuna muku, sai dai na yi kiran ku ne sai kuka amsa mini; to kada ku zarge ni, ku zargi kanku; ni ba zan taimake ku ba, ku kuma ba za ku taimake ni ba. Lalle ni na riga na kafirta da abin da kuka yi tarayya da ni a kansa tun a da can. Lalle azzalumai suna da (sakamakon) azaba mai raxaxi.”



Capítulo: Suratul Hijr

Verso : 31

إِلَّآ إِبۡلِيسَ أَبَىٰٓ أَن يَكُونَ مَعَ ٱلسَّـٰجِدِينَ

Sai Iblis ya qi ya kasance tare da masu yin sujjadar



Capítulo: Suratul Hijr

Verso : 32

قَالَ يَـٰٓإِبۡلِيسُ مَا لَكَ أَلَّا تَكُونَ مَعَ ٱلسَّـٰجِدِينَ

(Allah) Ya ce: “Ya Iblis, me ka taka da ba za ka kasance tare da masu sujjada ba?”



Capítulo: Suratul Hijr

Verso : 33

قَالَ لَمۡ أَكُن لِّأَسۡجُدَ لِبَشَرٍ خَلَقۡتَهُۥ مِن صَلۡصَٰلٖ مِّنۡ حَمَإٖ مَّسۡنُونٖ

(Iblis) ya ce: “Ba zai yiwu ba ni in yi sujjada ga wani mutum wanda Ka halitta daga busasshen tavo mai amo na wani yumvu mai wari.”



Capítulo: Suratul Hijr

Verso : 34

قَالَ فَٱخۡرُجۡ مِنۡهَا فَإِنَّكَ رَجِيمٞ

(Allah) Ya ce: “To ka fita daga cikinta (Aljannar), lalle kai korarre ne (daga rahamar Allah)



Capítulo: Suratul Hijr

Verso : 35

وَإِنَّ عَلَيۡكَ ٱللَّعۡنَةَ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلدِّينِ

“Lalle kuma la’ana ta tabbata a kanka har zuwa ranar alqiyama.”



Capítulo: Suratul Hijr

Verso : 36

قَالَ رَبِّ فَأَنظِرۡنِيٓ إِلَىٰ يَوۡمِ يُبۡعَثُونَ

(Iblis) ya ce: “Ya Ubangijina Ka saurara min har zuwa ranar da za a tashe su (watau matattu).”



Capítulo: Suratul Hijr

Verso : 37

قَالَ فَإِنَّكَ مِنَ ٱلۡمُنظَرِينَ

(Allah) Ya ce: “To lalle kana daga cikin waxanda za a saurar musu



Capítulo: Suratul Hijr

Verso : 38

إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡوَقۡتِ ٱلۡمَعۡلُومِ

“Har zuwa rana mai sanannen lokaci.”



Capítulo: Suratul Hijr

Verso : 39

قَالَ رَبِّ بِمَآ أَغۡوَيۡتَنِي لَأُزَيِّنَنَّ لَهُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَأُغۡوِيَنَّهُمۡ أَجۡمَعِينَ

(Iblis) ya ce: “Ubangijina, saboda vatar da ni da Ka yi, to lalle kuwa zan qawata musu (varna) a bayan qasa, kuma tabbas zan vatar da su baki xaya



Capítulo: Suratul Hijr

Verso : 40

إِلَّا عِبَادَكَ مِنۡهُمُ ٱلۡمُخۡلَصِينَ

“Sai fa bayinka zavavvu daga cikinsu.”



Capítulo: Suratul Hijr

Verso : 41

قَالَ هَٰذَا صِرَٰطٌ عَلَيَّ مُسۡتَقِيمٌ

(Allah) Ya ce: “Wannan hanya ce madaidaiciya, mai kaiwa gare Ni



Capítulo: Suratul Hijr

Verso : 42

إِنَّ عِبَادِي لَيۡسَ لَكَ عَلَيۡهِمۡ سُلۡطَٰنٌ إِلَّا مَنِ ٱتَّبَعَكَ مِنَ ٱلۡغَاوِينَ

“Lalle bayina ba ka da wani iko a kansu, sai dai wanda ya bi ka daga vatattu



Capítulo: Suratul Hijr

Verso : 43

وَإِنَّ جَهَنَّمَ لَمَوۡعِدُهُمۡ أَجۡمَعِينَ

“Lalle kuma Jahannama tabbas makomarsu ce baki xaya



Capítulo: Suratul Hijr

Verso : 44

لَهَا سَبۡعَةُ أَبۡوَٰبٖ لِّكُلِّ بَابٖ مِّنۡهُمۡ جُزۡءٞ مَّقۡسُومٌ

“Tana da qofofi bakwai, kowacce qofa tana da wani kaso (na kafirai) sananne (da za su shiga ta nan).”



Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 63

تَٱللَّهِ لَقَدۡ أَرۡسَلۡنَآ إِلَىٰٓ أُمَمٖ مِّن قَبۡلِكَ فَزَيَّنَ لَهُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ أَعۡمَٰلَهُمۡ فَهُوَ وَلِيُّهُمُ ٱلۡيَوۡمَ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

Wallahi haqiqa Mun aiko (manzanni) zuwa ga al’ummun da suke gabaninka, sai Shaixan ya qawata musu ayyukansu, kuma shi ne majivincin al’amuransu a yau, kuma suna da azaba mai raxaxi



Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 98

فَإِذَا قَرَأۡتَ ٱلۡقُرۡءَانَ فَٱسۡتَعِذۡ بِٱللَّهِ مِنَ ٱلشَّيۡطَٰنِ ٱلرَّجِيمِ

To idan za ka karanta Alqur’ani sai ka nemi tsarin Allah daga Shaixan korarre (daga rahamar Allah)



Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 99

إِنَّهُۥ لَيۡسَ لَهُۥ سُلۡطَٰنٌ عَلَى ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَلَىٰ رَبِّهِمۡ يَتَوَكَّلُونَ

Lalle shi (Shaixan) ba shi da iko a kan waxanda suka yi imani kuma suke dogara da Ubangijinsu



Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 100

إِنَّمَا سُلۡطَٰنُهُۥ عَلَى ٱلَّذِينَ يَتَوَلَّوۡنَهُۥ وَٱلَّذِينَ هُم بِهِۦ مُشۡرِكُونَ

Ikonsa kawai yana kan waxanda suke jivintar sa da kuma waxanda suke yin tarayya da shi



Capítulo: Suratul Isra’i

Verso : 27

إِنَّ ٱلۡمُبَذِّرِينَ كَانُوٓاْ إِخۡوَٰنَ ٱلشَّيَٰطِينِۖ وَكَانَ ٱلشَّيۡطَٰنُ لِرَبِّهِۦ كَفُورٗا

Lalle masu almubazzaranci sun tabbata dangin shaixanu; Shaixan kuwa ya zamanto mai yawan kafirce wa Ubangijinsa ne



Capítulo: Suratul Isra’i

Verso : 53

وَقُل لِّعِبَادِي يَقُولُواْ ٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُۚ إِنَّ ٱلشَّيۡطَٰنَ يَنزَغُ بَيۡنَهُمۡۚ إِنَّ ٱلشَّيۡطَٰنَ كَانَ لِلۡإِنسَٰنِ عَدُوّٗا مُّبِينٗا

Ka kuma ce da bayina su faxi (magana) wadda ita ce ta fi kyau. Lalle Shaixan yana vata tsakaninsu. Lalle Shaixan ya tabbata maqiyi ne mai bayyana (qiyayya) ga mutum



Capítulo: Suratul Isra’i

Verso : 61

وَإِذۡ قُلۡنَا لِلۡمَلَـٰٓئِكَةِ ٱسۡجُدُواْ لِأٓدَمَ فَسَجَدُوٓاْ إِلَّآ إِبۡلِيسَ قَالَ ءَأَسۡجُدُ لِمَنۡ خَلَقۡتَ طِينٗا

Kuma (ka tuna) lokacin da Muka ce da mala’iku: “Ku yi sujjada ga Adamu.” Sai suka yi sujjadar in ban da Iblis da ya ce: “Yanzu na yi sujjada ga wanda Ka halitta da tavo?”



Capítulo: Suratul Isra’i

Verso : 62

قَالَ أَرَءَيۡتَكَ هَٰذَا ٱلَّذِي كَرَّمۡتَ عَلَيَّ لَئِنۡ أَخَّرۡتَنِ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ لَأَحۡتَنِكَنَّ ذُرِّيَّتَهُۥٓ إِلَّا قَلِيلٗا

Ya ce: “Ka gan Ka, wannan da Ka fifita shi a kaina, tabbas idan Ka jinkirta min har zuwa ranar alqiyama to lalle zan karkatar da zuriyarsa, sai dai kaxan (daga cikinsu).”