Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 34

وَإِذۡ قُلۡنَا لِلۡمَلَـٰٓئِكَةِ ٱسۡجُدُواْ لِأٓدَمَ فَسَجَدُوٓاْ إِلَّآ إِبۡلِيسَ أَبَىٰ وَٱسۡتَكۡبَرَ وَكَانَ مِنَ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Kuma ka tuna lokacin da Muka ce wa mala’iku: “Ku yi sujjada ga Adamu.” Sai duk suka yi sujjada[1], in ban da Iblis, sai shi ya qi, ya kuma yi girman kai, kuma ya tabbata cikin kafirai


1- Mala’iku sun yi wa Adamu () sujjada ne don biyayya ga umarnin Allah. Ba ya halatta a Musulunci wani ya yi wa wani sujjada ba Allah ba.


Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 36

فَأَزَلَّهُمَا ٱلشَّيۡطَٰنُ عَنۡهَا فَأَخۡرَجَهُمَا مِمَّا كَانَا فِيهِۖ وَقُلۡنَا ٱهۡبِطُواْ بَعۡضُكُمۡ لِبَعۡضٍ عَدُوّٞۖ وَلَكُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ مُسۡتَقَرّٞ وَمَتَٰعٌ إِلَىٰ حِينٖ

Sai Shaixan ya zamar da su[1] game da ita (bishiyar), sai ya fitar da su daga ni’imar da suke ciki. Sai Muka ce: “Ku sauko qasa sashinku yana mai gaba da sashi; kuma kuna da mazauni a bayan qasa da wani jin daxi zuwa wani xan lokaci.”


1- Ta hanyar yi musu waswasi, kamar yadda ya zo a Suratul A’raf, aya ta 20, da Xaha, aya ta 120.


Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 168

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ كُلُواْ مِمَّا فِي ٱلۡأَرۡضِ حَلَٰلٗا طَيِّبٗا وَلَا تَتَّبِعُواْ خُطُوَٰتِ ٱلشَّيۡطَٰنِۚ إِنَّهُۥ لَكُمۡ عَدُوّٞ مُّبِينٌ

Ya ku mutane, ku ci halal mai daxi na abin da ke bayan qasa, kada kuma ku bi hanyoyin Shaixan, lalle shi maqiyi ne mai bayyana qiyayya a gare ku



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 169

إِنَّمَا يَأۡمُرُكُم بِٱلسُّوٓءِ وَٱلۡفَحۡشَآءِ وَأَن تَقُولُواْ عَلَى ٱللَّهِ مَا لَا تَعۡلَمُونَ

Yana umartar ku ne kawai da savo da ayyukan assha da kuma faxin abin da ba ku da ilimi game da shi ku jingina wa Allah



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 208

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱدۡخُلُواْ فِي ٱلسِّلۡمِ كَآفَّةٗ وَلَا تَتَّبِعُواْ خُطُوَٰتِ ٱلشَّيۡطَٰنِۚ إِنَّهُۥ لَكُمۡ عَدُوّٞ مُّبِينٞ

Ya ku waxanda suka yi imani, ku shiga cikin addinin Musulunci gaba xaya, kuma kar ku bi hanyoyin Shaixan. Lalle shi maqiyi ne a gare ku, mai bayyana (qiyayya)



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 268

ٱلشَّيۡطَٰنُ يَعِدُكُمُ ٱلۡفَقۡرَ وَيَأۡمُرُكُم بِٱلۡفَحۡشَآءِۖ وَٱللَّهُ يَعِدُكُم مَّغۡفِرَةٗ مِّنۡهُ وَفَضۡلٗاۗ وَٱللَّهُ وَٰسِعٌ عَلِيمٞ

Shaixan ne yake tsoratar da ku da talauci, kuma yana umartar ku da alfasha; Allah kuwa Yana yi muku alqawarin gafara ta musamman daga gare Shi da kuma falala. Kuma Allah Mai yalwa ne, Masani



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 155

إِنَّ ٱلَّذِينَ تَوَلَّوۡاْ مِنكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡتَقَى ٱلۡجَمۡعَانِ إِنَّمَا ٱسۡتَزَلَّهُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ بِبَعۡضِ مَا كَسَبُواْۖ وَلَقَدۡ عَفَا ٱللَّهُ عَنۡهُمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ حَلِيمٞ

Lalle waxanda suka gudu daga cikinku yayin da runduna biyu suka haxu, Shaixan ne ya nemi ya zamar da su saboda wani laifi da suka yi; kuma tabbas haqiqa Allah Ya yi musu afuwa. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai haquri



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 175

إِنَّمَا ذَٰلِكُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ يُخَوِّفُ أَوۡلِيَآءَهُۥ فَلَا تَخَافُوهُمۡ وَخَافُونِ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ

Wannan (labarin), Shaixan ne kawai yake tsoratar da ku masoyansa, don haka kar ku ji tsoron su, amma ku ji tsoro Na in dai har ku muminai ne



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 38

وَٱلَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمۡوَٰلَهُمۡ رِئَآءَ ٱلنَّاسِ وَلَا يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَلَا بِٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۗ وَمَن يَكُنِ ٱلشَّيۡطَٰنُ لَهُۥ قَرِينٗا فَسَآءَ قَرِينٗا

Waxanda kuma suke ciyar da dukiyoyinsu don mutane su gani, kuma ba sa yin imani da Allah, ba sa kuma yin imani da ranar qarshe. Duk wanda Shaixan ya kasance shi ne abokinsa, to tir da aboki irin wannan



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 60

أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ يَزۡعُمُونَ أَنَّهُمۡ ءَامَنُواْ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ وَمَآ أُنزِلَ مِن قَبۡلِكَ يُرِيدُونَ أَن يَتَحَاكَمُوٓاْ إِلَى ٱلطَّـٰغُوتِ وَقَدۡ أُمِرُوٓاْ أَن يَكۡفُرُواْ بِهِۦۖ وَيُرِيدُ ٱلشَّيۡطَٰنُ أَن يُضِلَّهُمۡ ضَلَٰلَۢا بَعِيدٗا

Shin ba ka ganin waxannan da suke riya cewa sun yi imani da abin da aka saukar maka, da abin da aka saukar gabaninka, suna nufin su kai hukunci gaban Xagutu[1] (wanin Allah), alhalin an umarce su da su kafirce masa, Shaixan kuma yana nufin ya vatar da su vata mai nisa?


1- Xagutu, shi ne duk wani abu da bawa zai qetare iyakokin Allah a sanadiyyarsa; mutum ne ko gunki ko wata doka.


Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 76

ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ يُقَٰتِلُونَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۖ وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ يُقَٰتِلُونَ فِي سَبِيلِ ٱلطَّـٰغُوتِ فَقَٰتِلُوٓاْ أَوۡلِيَآءَ ٱلشَّيۡطَٰنِۖ إِنَّ كَيۡدَ ٱلشَّيۡطَٰنِ كَانَ ضَعِيفًا

Waxanda suka yi imani suna yaqi ne don xaukaka kalmar Allah; waxanda kuma suka kafirce suna yin yaqi ne don kare Xagutu; to ku yaqi masoya Shaixan; lalle makircin Shaixan rarrauna ne



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 117

إِن يَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦٓ إِلَّآ إِنَٰثٗا وَإِن يَدۡعُونَ إِلَّا شَيۡطَٰنٗا مَّرِيدٗا

Ba waxanda suke bauta wa, baya ga Allah, sai wasu gumaka masu sunan mata, kuma babu wanda suke bauta wa sai Shaixan mai taurin kai



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 118

لَّعَنَهُ ٱللَّهُۘ وَقَالَ لَأَتَّخِذَنَّ مِنۡ عِبَادِكَ نَصِيبٗا مَّفۡرُوضٗا

Allah Ya la’ance shi. Sai kuma ya ce: “Tabbas sai na samu wani kaso qayyadajje daga bayinka



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 119

وَلَأُضِلَّنَّهُمۡ وَلَأُمَنِّيَنَّهُمۡ وَلَأٓمُرَنَّهُمۡ فَلَيُبَتِّكُنَّ ءَاذَانَ ٱلۡأَنۡعَٰمِ وَلَأٓمُرَنَّهُمۡ فَلَيُغَيِّرُنَّ خَلۡقَ ٱللَّهِۚ وَمَن يَتَّخِذِ ٱلشَّيۡطَٰنَ وَلِيّٗا مِّن دُونِ ٱللَّهِ فَقَدۡ خَسِرَ خُسۡرَانٗا مُّبِينٗا

“Kuma lalle sai na vatar da su, kuma lalle sai na sa musu dogon buri, kuma lalle zan umarce su, sai sun riqa gutsuttsure kunnuwan dabbobin gida, kuma lalle zan umarce su, sai sun canja halittar Allah.” Duk wanda kuwa ya riqi Shaixan a matsayin masoyi ba Allah ba, to haqiqa ya yi hasara bayyananniyar hasara



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 120

يَعِدُهُمۡ وَيُمَنِّيهِمۡۖ وَمَا يَعِدُهُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ إِلَّا غُرُورًا

Yana yi musu alqawari kuma yana sa musu dogon buri; kuma babu abin da Shaixan yake yi musu alqawari da shi sai ruxi kawai



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 90

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِنَّمَا ٱلۡخَمۡرُ وَٱلۡمَيۡسِرُ وَٱلۡأَنصَابُ وَٱلۡأَزۡلَٰمُ رِجۡسٞ مِّنۡ عَمَلِ ٱلشَّيۡطَٰنِ فَٱجۡتَنِبُوهُ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ

Ya ku waxanda suka yi imani, ita dai giya da caca da gumaka da kibau na neman sa’a[1], ba komai ba ne face qazanta daga aikin Shaixan, don haka ku nisance su domin ku sami rabauta.[2]


1- A jahiliyya balarabe idan zai yi tafiya ko zai yi wani aiki, sai ya xauko wasu kibiyoyi uku, xaya an rubuta ‘aikata’, xaya kuma ‘kada ka aikata’, ta uku kuma ba a rubuta komai a kanta ba, sai ya karkaxa su sannan ya zavi xaya don ya gane sa’arsa ko rashinta.


2- Da wannan ayar Allah () ya haramta wa Musulmi shan giya da kasuwancinta.


Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 91

إِنَّمَا يُرِيدُ ٱلشَّيۡطَٰنُ أَن يُوقِعَ بَيۡنَكُمُ ٱلۡعَدَٰوَةَ وَٱلۡبَغۡضَآءَ فِي ٱلۡخَمۡرِ وَٱلۡمَيۡسِرِ وَيَصُدَّكُمۡ عَن ذِكۡرِ ٱللَّهِ وَعَنِ ٱلصَّلَوٰةِۖ فَهَلۡ أَنتُم مُّنتَهُونَ

Abin da kawai Shaixan yake nufi shi ne, ya jefa gaba da qiyayya a tsakankaninku, ta hanyar giya da caca, kuma ya hana muku ambaton Allah da yin salla. Shin ko kun hanu?



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 43

فَلَوۡلَآ إِذۡ جَآءَهُم بَأۡسُنَا تَضَرَّعُواْ وَلَٰكِن قَسَتۡ قُلُوبُهُمۡ وَزَيَّنَ لَهُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

To me ya hana lokacin da musibarmu ta zo musu, su qasqantar da kai? Sai dai kuma zukatansu ne suka qeqashe, Shaixan kuma ya qawata musu abin da suka kasance suna aikatawa



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 68

وَإِذَا رَأَيۡتَ ٱلَّذِينَ يَخُوضُونَ فِيٓ ءَايَٰتِنَا فَأَعۡرِضۡ عَنۡهُمۡ حَتَّىٰ يَخُوضُواْ فِي حَدِيثٍ غَيۡرِهِۦۚ وَإِمَّا يُنسِيَنَّكَ ٱلشَّيۡطَٰنُ فَلَا تَقۡعُدۡ بَعۡدَ ٱلذِّكۡرَىٰ مَعَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Kuma idan ka ga waxanda suke kutsawa cikin ayoyinmu (suna izgili), to ka rabu da su, har sai sun canja wani zancen da ba wancan ba. Amma in da Shaixan zai mantar da kai kuwa, to bayan ka tuna kar ka sake zama tare da azzalumai



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 142

وَمِنَ ٱلۡأَنۡعَٰمِ حَمُولَةٗ وَفَرۡشٗاۚ كُلُواْ مِمَّا رَزَقَكُمُ ٱللَّهُ وَلَا تَتَّبِعُواْ خُطُوَٰتِ ٱلشَّيۡطَٰنِۚ إِنَّهُۥ لَكُمۡ عَدُوّٞ مُّبِينٞ

Daga cikin dabbobin gida kuma akwai masu xaukan kaya da kuma qanana. Ku ci daga abin da Allah Ya arzuta ku da shi, kuma kada ku bi hanyoyin Shaixan. Lalle shi maqiyi ne mai bayyana qiyayya a gare ku



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 11

وَلَقَدۡ خَلَقۡنَٰكُمۡ ثُمَّ صَوَّرۡنَٰكُمۡ ثُمَّ قُلۡنَا لِلۡمَلَـٰٓئِكَةِ ٱسۡجُدُواْ لِأٓدَمَ فَسَجَدُوٓاْ إِلَّآ إِبۡلِيسَ لَمۡ يَكُن مِّنَ ٱلسَّـٰجِدِينَ

Kuma lalle haqiqa Mun halicce ku, sannan kuma Muka suranta ku; sannan Muka ce wa mala’iku: “Ku yi sujjada ga Adamu,” sai suka yi sujjada, sai Iblis ne kaxai bai kasance cikin masu sujjada ba



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 12

قَالَ مَا مَنَعَكَ أَلَّا تَسۡجُدَ إِذۡ أَمَرۡتُكَۖ قَالَ أَنَا۠ خَيۡرٞ مِّنۡهُ خَلَقۡتَنِي مِن نَّارٖ وَخَلَقۡتَهُۥ مِن طِينٖ

(Allah) Ya ce: “Me ya hana ka yin sujada lokacin da Na umarce ka?” Sai ya ce: “Ai ni na fi shi alheri; Ka halicce ni da wuta, shi kuwa Ka halicce shi da tavo.”



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 13

قَالَ فَٱهۡبِطۡ مِنۡهَا فَمَا يَكُونُ لَكَ أَن تَتَكَبَّرَ فِيهَا فَٱخۡرُجۡ إِنَّكَ مِنَ ٱلصَّـٰغِرِينَ

Sai Ya ce: “To ka sauka daga cikinta, bai dace gare ka ka yi girman kai a cikinta ba, don haka sai ka fita, lalle kai kana cikin qasqantattu.”



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 14

قَالَ أَنظِرۡنِيٓ إِلَىٰ يَوۡمِ يُبۡعَثُونَ

Sai ya ce: “Ka yi min jinkiri zuwa ranar da za a tashe su (mutane).”



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 15

قَالَ إِنَّكَ مِنَ ٱلۡمُنظَرِينَ

Sai Ya ce: “Lalle kai kana cikin waxanda za a yi wa jinkiri.”



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 16

قَالَ فَبِمَآ أَغۡوَيۡتَنِي لَأَقۡعُدَنَّ لَهُمۡ صِرَٰطَكَ ٱلۡمُسۡتَقِيمَ

Ya ce: “Saboda vatar da ni da Ka yi, lalle sai na zaune musu tafarkinka madaidaici



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 17

ثُمَّ لَأٓتِيَنَّهُم مِّنۢ بَيۡنِ أَيۡدِيهِمۡ وَمِنۡ خَلۡفِهِمۡ وَعَنۡ أَيۡمَٰنِهِمۡ وَعَن شَمَآئِلِهِمۡۖ وَلَا تَجِدُ أَكۡثَرَهُمۡ شَٰكِرِينَ

“Sannan lalle zan zo musu ta gabansu da kuma ta bayansu da kuma ta damansu, da kuma ta hagunsu; kuma ba za Ka samu yawancinsu masu godiya ba.”



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 18

قَالَ ٱخۡرُجۡ مِنۡهَا مَذۡءُومٗا مَّدۡحُورٗاۖ لَّمَن تَبِعَكَ مِنۡهُمۡ لَأَمۡلَأَنَّ جَهَنَّمَ مِنكُمۡ أَجۡمَعِينَ

Ya ce: “Ka fita daga cikinta kana abin aibatawa, korarre (daga rahama); Na rantse duk wanda ya bi ka daga cikinsu, lalle zan cika Jahannama da ku gaba xaya.”



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 19

وَيَـٰٓـَٔادَمُ ٱسۡكُنۡ أَنتَ وَزَوۡجُكَ ٱلۡجَنَّةَ فَكُلَا مِنۡ حَيۡثُ شِئۡتُمَا وَلَا تَقۡرَبَا هَٰذِهِ ٱلشَّجَرَةَ فَتَكُونَا مِنَ ٱلظَّـٰلِمِينَ

“Kuma ya kai Adam, ka zauna cikin Aljanna, da kai da matarka, kuma ku ci duk abin da kuka ga dama, amma kada ku kusanci wannan bishiyar, sai ku kasance cikin azzalumai.”



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 20

فَوَسۡوَسَ لَهُمَا ٱلشَّيۡطَٰنُ لِيُبۡدِيَ لَهُمَا مَا وُۥرِيَ عَنۡهُمَا مِن سَوۡءَٰتِهِمَا وَقَالَ مَا نَهَىٰكُمَا رَبُّكُمَا عَنۡ هَٰذِهِ ٱلشَّجَرَةِ إِلَّآ أَن تَكُونَا مَلَكَيۡنِ أَوۡ تَكُونَا مِنَ ٱلۡخَٰلِدِينَ

Sai Shaixan ya yi musu waswasi, domin ya bayyana musu abin da aka voye musu na tsiraicinsu, kuma ya ce: “Ba abin da ya sa Ubangijinku Ya hane ku daga wannan bishiyar, sai don kawai kada ku zama mala’iku ko kuma ku zama daga cikin dawwamammu.”