وَمَا ذَرَأَ لَكُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ مُخۡتَلِفًا أَلۡوَٰنُهُۥٓۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّقَوۡمٖ يَذَّكَّرُونَ
Da kuma abubuwan da Ya halitta muku a qasa masu launi iri daban-daban. Lalle a game da wannan tabbas akwai aya ga mutanen da suke wa’azantuwa
وَٱللَّهُ أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَحۡيَا بِهِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَآۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّقَوۡمٖ يَسۡمَعُونَ
Allah kuma Ya saukar da ruwa daga sama, sai Ya raya qasa da shi bayan mutuwarta. Lalle a game da wannan akwai aya ga mutanen da suke ji
وَإِنَّ لَكُمۡ فِي ٱلۡأَنۡعَٰمِ لَعِبۡرَةٗۖ نُّسۡقِيكُم مِّمَّا فِي بُطُونِهِۦ مِنۢ بَيۡنِ فَرۡثٖ وَدَمٖ لَّبَنًا خَالِصٗا سَآئِغٗا لِّلشَّـٰرِبِينَ
Lalle kuma kuna da wata izina a game da dabbobin ni’ima; Muna shayar da ku da abin da yake cikin cikkunansu (mai fitowa) ta tsakankanin uwar hanji da jinni; nono tatacce mai daxin kwankwaxa ga masu sha
وَمِن ثَمَرَٰتِ ٱلنَّخِيلِ وَٱلۡأَعۡنَٰبِ تَتَّخِذُونَ مِنۡهُ سَكَرٗا وَرِزۡقًا حَسَنًاۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّقَوۡمٖ يَعۡقِلُونَ
Daga kuma ‘ya’yan dabinai da na inabai kuna yin giya da shi[1], da kuma arziki mai kyau. Lalle a game da wannan akwai aya ga mutanen da suke hankalta
1- Wannan ayar ta sauka kafin a haramta shan giya. Daga baya Allah () ya haramta duk wani abu mai gusar da hankali.
وَأَوۡحَىٰ رَبُّكَ إِلَى ٱلنَّحۡلِ أَنِ ٱتَّخِذِي مِنَ ٱلۡجِبَالِ بُيُوتٗا وَمِنَ ٱلشَّجَرِ وَمِمَّا يَعۡرِشُونَ
Ubangijinka kuma Ya kimsa wa qudan zuma cewa,: “Ki gina gidaje a duwatsu da kan bishiyoyi da kuma rufin da (mutane) suke yi”
ثُمَّ كُلِي مِن كُلِّ ٱلثَّمَرَٰتِ فَٱسۡلُكِي سُبُلَ رَبِّكِ ذُلُلٗاۚ يَخۡرُجُ مِنۢ بُطُونِهَا شَرَابٞ مُّخۡتَلِفٌ أَلۡوَٰنُهُۥ فِيهِ شِفَآءٞ لِّلنَّاسِۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّقَوۡمٖ يَتَفَكَّرُونَ
“Sannan kuma ki ci daga kowanne ‘ya’yan itace, kuma ki shiga hanyoyin Ubangijinki horarru (gare ki).” Abin sha mai launi daban-daban yana fitowa daga cikin cikinta; a cikinsa (kuma) da akwai waraka ga mutane. Lalle a game da wannan akwai aya ga mutane masu tunani
أَلَمۡ يَرَوۡاْ إِلَى ٱلطَّيۡرِ مُسَخَّرَٰتٖ فِي جَوِّ ٱلسَّمَآءِ مَا يُمۡسِكُهُنَّ إِلَّا ٱللَّهُۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ
Yanzu ba sa ganin tsuntsaye da aka lamunce wa (tashi) a sararin sama, ba mai riqe su sai Allah? Lalle a game da wannan akwai ayoyi ga mutane masu yin imani
وَجَعَلۡنَا ٱلَّيۡلَ وَٱلنَّهَارَ ءَايَتَيۡنِۖ فَمَحَوۡنَآ ءَايَةَ ٱلَّيۡلِ وَجَعَلۡنَآ ءَايَةَ ٱلنَّهَارِ مُبۡصِرَةٗ لِّتَبۡتَغُواْ فَضۡلٗا مِّن رَّبِّكُمۡ وَلِتَعۡلَمُواْ عَدَدَ ٱلسِّنِينَ وَٱلۡحِسَابَۚ وَكُلَّ شَيۡءٖ فَصَّلۡنَٰهُ تَفۡصِيلٗا
Muka kuma sanya dare da rana su zama ayoyi guda biyu; sai Muka shafe ayar dare (ta zama duhu) Muka kuma sanya ayar rana ta zama mai haskakawa, don ku nemi falala daga Ubangijinku, don kuma ku san yawan shekaru da lissafi. Kowane abu kuwa Mun rarrabe shi filla-filla
وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَىٰ تِسۡعَ ءَايَٰتِۭ بَيِّنَٰتٖۖ فَسۡـَٔلۡ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ إِذۡ جَآءَهُمۡ فَقَالَ لَهُۥ فِرۡعَوۡنُ إِنِّي لَأَظُنُّكَ يَٰمُوسَىٰ مَسۡحُورٗا
Kuma haqiqa Mun bai wa Musa ayoyi tara bayyanannu; to ka tambayi Banu Isra’ila lokacin da ya zo musu, sai Fir’auna ya ce da shi: “Lalle ni fa ina tsammanin kai Musa sihirtacce ne!”
قَالَ لَقَدۡ عَلِمۡتَ مَآ أَنزَلَ هَـٰٓؤُلَآءِ إِلَّا رَبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ بَصَآئِرَ وَإِنِّي لَأَظُنُّكَ يَٰفِرۡعَوۡنُ مَثۡبُورٗا
(Musa) ya ce: “Haqiqa ka sani ba wanda ya saukar da waxannan (ayoyin) sai Ubangijin sammai da qasa don su zama hujjoji, kuma lalle ina tsammanin kai Fir’auna halakakke ne.”
۞وَتَرَى ٱلشَّمۡسَ إِذَا طَلَعَت تَّزَٰوَرُ عَن كَهۡفِهِمۡ ذَاتَ ٱلۡيَمِينِ وَإِذَا غَرَبَت تَّقۡرِضُهُمۡ ذَاتَ ٱلشِّمَالِ وَهُمۡ فِي فَجۡوَةٖ مِّنۡهُۚ ذَٰلِكَ مِنۡ ءَايَٰتِ ٱللَّهِۗ مَن يَهۡدِ ٱللَّهُ فَهُوَ ٱلۡمُهۡتَدِۖ وَمَن يُضۡلِلۡ فَلَن تَجِدَ لَهُۥ وَلِيّٗا مُّرۡشِدٗا
(Sai) kuma ka ga rana idan za ta vullo tana kauce wa kogonsu ta vangaren dama, idan kuma za ta faxi sai ta riqa kauce musu ta vangaren hagu, su kuwa suna tsakiyarsa. Wannan yana daga ayoyin Allah. Wanda Allah Ya shiryar to shi ne shiryayye, wanda kuwa Ya vatar to ba za ka sami wani majivinci da zai shirye shi ba
قَالَ رَبِّ ٱجۡعَل لِّيٓ ءَايَةٗۖ قَالَ ءَايَتُكَ أَلَّا تُكَلِّمَ ٱلنَّاسَ ثَلَٰثَ لَيَالٖ سَوِيّٗا
Ya ce: “Ubangijina Ka sanya mini wata alama.” Sai (Allah) Ya ce: “Alamarka ita ce ka kasa yi wa mutane magana (tsawon) kwana uku daidai.”
قَالَتۡ أَنَّىٰ يَكُونُ لِي غُلَٰمٞ وَلَمۡ يَمۡسَسۡنِي بَشَرٞ وَلَمۡ أَكُ بَغِيّٗا
Ta ce: “Ta qaqa zan samu xa, alhalin kuwa wani namiji bai tava shafa ta ba, kuma ni ban zamanto mazinaciya ba?”
قَالَ كَذَٰلِكِ قَالَ رَبُّكِ هُوَ عَلَيَّ هَيِّنٞۖ وَلِنَجۡعَلَهُۥٓ ءَايَةٗ لِّلنَّاسِ وَرَحۡمَةٗ مِّنَّاۚ وَكَانَ أَمۡرٗا مَّقۡضِيّٗا
(Mala’ika) ya ce: “Kamar haka ne Ubangijinki Ya faxa (cewa): “Shi (wannan) mai sauqi ne a wurina, kuma don Mu mayar da shi aya ga mutane da kuma rahama daga gare Mu, kuma (yin haka) ya zamanto al’amari ne tabbatacce (rubuce a Lauhul-Mahafuzu).”
ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلۡأَرۡضَ مَهۡدٗا وَسَلَكَ لَكُمۡ فِيهَا سُبُلٗا وَأَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَخۡرَجۡنَا بِهِۦٓ أَزۡوَٰجٗا مِّن نَّبَاتٖ شَتَّىٰ
“(Shi ne) Wanda Ya sanya muku qasa a shimfixe, Ya kuma sanya muku hanyoyi na tafiya cikinta, kuma Ya saukar da ruwa daga sama”, sannan Muka fitar da dangogin shuke-shuke iri-iri da shi (ruwa)
كُلُواْ وَٱرۡعَوۡاْ أَنۡعَٰمَكُمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّأُوْلِي ٱلنُّهَىٰ
Ku ci (daga tsirran) kuma ku yi kiwon dabbobinku. Lalle a game da wannan akwai ayoyi ga ma’abota hankula
أَفَلَمۡ يَهۡدِ لَهُمۡ كَمۡ أَهۡلَكۡنَا قَبۡلَهُم مِّنَ ٱلۡقُرُونِ يَمۡشُونَ فِي مَسَٰكِنِهِمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّأُوْلِي ٱلنُّهَىٰ
Yanzu (mutanen Makka) ba su gane cewa al’ummu nawa muka hallaka a gabaninsu ba waxanda suna wucewa ta gidajensu? Lalle a game da wannan akwai ayoyi ga ma’abota hankali
وَٱلَّتِيٓ أَحۡصَنَتۡ فَرۡجَهَا فَنَفَخۡنَا فِيهَا مِن رُّوحِنَا وَجَعَلۡنَٰهَا وَٱبۡنَهَآ ءَايَةٗ لِّلۡعَٰلَمِينَ
(Ka tuna) kuma wadda ta tsare matancinta, sai Muka yi busa a cikinta daga Ruhinmu, Muka kuma sanya ta ita da xanta aya ga talikai
فَأَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡهِ أَنِ ٱصۡنَعِ ٱلۡفُلۡكَ بِأَعۡيُنِنَا وَوَحۡيِنَا فَإِذَا جَآءَ أَمۡرُنَا وَفَارَ ٱلتَّنُّورُ فَٱسۡلُكۡ فِيهَا مِن كُلّٖ زَوۡجَيۡنِ ٱثۡنَيۡنِ وَأَهۡلَكَ إِلَّا مَن سَبَقَ عَلَيۡهِ ٱلۡقَوۡلُ مِنۡهُمۡۖ وَلَا تُخَٰطِبۡنِي فِي ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓاْ إِنَّهُم مُّغۡرَقُونَ
Sai Muka yiwo masa wahayi cewa: “Ka sassaqa jirgin ruwa a qarqashin kulawarmu da umarninmu, sannan idan umarninmu (na hallaka su) ya zo, kuma tanderu ya vuvvugo da ruwa, sai ka saka ma’aurata guda biyu daga kowane jinsi a cikinsa, da kuma iyalanka, sai wanda kalmar (halaka) ta rigaya a kansa daga cikinsu; kuma kada ka ce min komai game da waxanda suka kafirta; lalle su waxanda za a nutsar ne
فَإِذَا ٱسۡتَوَيۡتَ أَنتَ وَمَن مَّعَكَ عَلَى ٱلۡفُلۡكِ فَقُلِ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِي نَجَّىٰنَا مِنَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلظَّـٰلِمِينَ
“To idan kai da waxanda suke tare da kai kuka daidaita a kan jirgin, sai ka ce: “Na gode wa Allah wanda Ya tserar da mu daga mutane azzalumai.”
وَقُل رَّبِّ أَنزِلۡنِي مُنزَلٗا مُّبَارَكٗا وَأَنتَ خَيۡرُ ٱلۡمُنزِلِينَ
Kuma ka ce: “Ubangijina Ka saukar da ni masauki mai albarka, Kai ne kuwa Fiyayyen masu saukarwa.”
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ وَإِن كُنَّا لَمُبۡتَلِينَ
Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi, Mu kuma haqiqa Mun kasance Masu jarrabawa ne
وَجَعَلۡنَا ٱبۡنَ مَرۡيَمَ وَأُمَّهُۥٓ ءَايَةٗ وَءَاوَيۡنَٰهُمَآ إِلَىٰ رَبۡوَةٖ ذَاتِ قَرَارٖ وَمَعِينٖ
Muka kuma sanya Xan Maryamu da mahaifiyarsa (don su zama) aya, Muka kuma zaunar da su a wata jigawa ta hutawa da kuma ruwa mai gudana
إِن نَّشَأۡ نُنَزِّلۡ عَلَيۡهِم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ ءَايَةٗ فَظَلَّتۡ أَعۡنَٰقُهُمۡ لَهَا خَٰضِعِينَ
Da Mun ga dama da sai Mu saukar musu da aya daga sama sai wuyoyinsu su zamo masu qanqan da kai gare ta[1]
1- Watau mu’ujizar da za ta tilasta musu su miqa wuya ko ba sa so.
أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ إِلَى ٱلۡأَرۡضِ كَمۡ أَنۢبَتۡنَا فِيهَا مِن كُلِّ زَوۡجٖ كَرِيمٍ
Shin ba su yi duba zuwa ga qasa ba, (su ga) dangogin tsirrai masu kyau nawa ne Muka tsirar daga cikinta?
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ
Lalle a game da wannan tabbas akwai aya (mai nuna cikar ikon Allah); kuma yawancinsu ba su zamanto masu imani ba
فَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنِ ٱضۡرِب بِّعَصَاكَ ٱلۡبَحۡرَۖ فَٱنفَلَقَ فَكَانَ كُلُّ فِرۡقٖ كَٱلطَّوۡدِ ٱلۡعَظِيمِ
Sai Muka yi wahayi ga Musa cewa: “Ka bugi kogin da sandarka;” (da ya buge shi) sai ya dare, kowanne yanki sai ya zama kamar qaton dutse
وَأَزۡلَفۡنَا ثَمَّ ٱلۡأٓخَرِينَ
Muka kuma kusantar da waxancan (watau mutanen Fir’auna) zuwa can (kusa da kogin)
وَأَنجَيۡنَا مُوسَىٰ وَمَن مَّعَهُۥٓ أَجۡمَعِينَ
Muka kuma tserar da Musa da waxanda suke tare da shi gaba xaya
ثُمَّ أَغۡرَقۡنَا ٱلۡأٓخَرِينَ
Sannan Muka nutsar da sauran mutanen (watau Fir’auna da mutanensa)