إِذۡ هَمَّت طَّآئِفَتَانِ مِنكُمۡ أَن تَفۡشَلَا وَٱللَّهُ وَلِيُّهُمَاۗ وَعَلَى ٱللَّهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ
Tuna lokacin da waxansu qungiyoyi guda biyu daga cikinku suka yi niyyar su ja da baya[1], amma Allah ne Majivincin lamarinsu. Sai muminai su dogara ga Allah kaxai
1- Qungiyoyin muminai biyu da suka yi nufin su janye daga wannan yaqi, su ne qabilun Banu Salima da na Banu Harisa, sai dai kuma Allah ya kafe dugadugansu.
فَبِمَا رَحۡمَةٖ مِّنَ ٱللَّهِ لِنتَ لَهُمۡۖ وَلَوۡ كُنتَ فَظًّا غَلِيظَ ٱلۡقَلۡبِ لَٱنفَضُّواْ مِنۡ حَوۡلِكَۖ فَٱعۡفُ عَنۡهُمۡ وَٱسۡتَغۡفِرۡ لَهُمۡ وَشَاوِرۡهُمۡ فِي ٱلۡأَمۡرِۖ فَإِذَا عَزَمۡتَ فَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُتَوَكِّلِينَ
To saboda rahama ta musamman daga Allah, sai ka zamo mai tausasawa gare su; in da kuwa ka kasance mai kaushin mu’amala, mai qeqasasshiyar zuciya ne, to da sun watse sun bar ka. To ka yi musu afuwa, kuma ka nema musu gafara, kuma ka nemi shawararsu cikin duk lamura; amma idan ka riga ka qulla niyya, to ka dogara ga Allah. Lalle Allah Yana son masu dogara a gare Shi
إِن يَنصُرۡكُمُ ٱللَّهُ فَلَا غَالِبَ لَكُمۡۖ وَإِن يَخۡذُلۡكُمۡ فَمَن ذَا ٱلَّذِي يَنصُرُكُم مِّنۢ بَعۡدِهِۦۗ وَعَلَى ٱللَّهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ
Idan Allah Ya ba ku nasara, to ba wanda ya isa ya rinjaye ku, amma idan Ya tavar da ku, to wane ne ya isa ya taimake ku in ba shi ba? Kuma muminai wajibi ne su dogara ga Allah Shi kaxai
ٱلَّذِينَ قَالَ لَهُمُ ٱلنَّاسُ إِنَّ ٱلنَّاسَ قَدۡ جَمَعُواْ لَكُمۡ فَٱخۡشَوۡهُمۡ فَزَادَهُمۡ إِيمَٰنٗا وَقَالُواْ حَسۡبُنَا ٱللَّهُ وَنِعۡمَ ٱلۡوَكِيلُ
Su ne waxanda mutane suka ce da su: “Lalle mutanen (Makka) fa sun tara muku runduna, to sai ku tsorace su.” Amma sai hakan ya qara musu imani, sai suka riqa cewa: “Allah Ya wadace mu, kuma madalla da abin dogara (idan har Shi ne Allah).”
وَيَقُولُونَ طَاعَةٞ فَإِذَا بَرَزُواْ مِنۡ عِندِكَ بَيَّتَ طَآئِفَةٞ مِّنۡهُمۡ غَيۡرَ ٱلَّذِي تَقُولُۖ وَٱللَّهُ يَكۡتُبُ مَا يُبَيِّتُونَۖ فَأَعۡرِضۡ عَنۡهُمۡ وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ وَكِيلًا
Kuma sukan ce: “Ai ba mu da wani abu sai biyayya.” To idan suka fita daga wajenka, sai wata qungiya daga cikinsu, su riqa qulla wani abu daban cikin dare, savanin abin da suke faxa; Allah kuwa Yana rubuta duk wani abu da suke qullawa da daddare; to ka kawar da kai daga kansu, kuma ka dogara ga Allah. Allah kuwa Ya isa abin dogaro
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱذۡكُرُواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ إِذۡ هَمَّ قَوۡمٌ أَن يَبۡسُطُوٓاْ إِلَيۡكُمۡ أَيۡدِيَهُمۡ فَكَفَّ أَيۡدِيَهُمۡ عَنكُمۡۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۚ وَعَلَى ٱللَّهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ
Ya ku waxanda suka yi imani, ku tuna ni’imar Allah da Ya yi muku, yayin da waxansu mutane suka yi niyyar shimfixa hannayensu a kanku, sai Ya kame muku hannayensu, kuma ku kiyaye dokokin Allah. To sai muminai su dogara ga Allah Shi kaxai
قَالَ رَجُلَانِ مِنَ ٱلَّذِينَ يَخَافُونَ أَنۡعَمَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمَا ٱدۡخُلُواْ عَلَيۡهِمُ ٱلۡبَابَ فَإِذَا دَخَلۡتُمُوهُ فَإِنَّكُمۡ غَٰلِبُونَۚ وَعَلَى ٱللَّهِ فَتَوَكَّلُوٓاْ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ
Waxansu mutane biyu daga cikin masu jin tsoron (Allah), waxanda Allah Ya yi musu ni’ima (ta imani), suka ce: “Ku shigar musu ta qofar (garin); idan har kun shige shi, to lalle ku masu cin nasara ne. Kuma ga Allah kaxai za ku dogara, idan kun kasance ku muminai ne.”
قَدِ ٱفۡتَرَيۡنَا عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا إِنۡ عُدۡنَا فِي مِلَّتِكُم بَعۡدَ إِذۡ نَجَّىٰنَا ٱللَّهُ مِنۡهَاۚ وَمَا يَكُونُ لَنَآ أَن نَّعُودَ فِيهَآ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُ رَبُّنَاۚ وَسِعَ رَبُّنَا كُلَّ شَيۡءٍ عِلۡمًاۚ عَلَى ٱللَّهِ تَوَكَّلۡنَاۚ رَبَّنَا ٱفۡتَحۡ بَيۡنَنَا وَبَيۡنَ قَوۡمِنَا بِٱلۡحَقِّ وَأَنتَ خَيۡرُ ٱلۡفَٰتِحِينَ
“Haqiqa mun qirqiri qarya, mun jingina wa Allah, in har muka komo cikin addininku, bayan kuwa Allah Ya tserar da mu daga gare shi. Kuma ba ma zai yiwu ba mu koma cikinsa sai dai idan Allah Ubangijinmu ne Ya ga dama. Kuma ilimin Ubangijinmu Ya yalwaci komai. Ga Allah kaxai muka dogara. Ya Ubangijinmu, Ka yi hukunci tsakaninmu da mutanenmu da gaskiya, kuma Kai ne Fiyayyen masu hukunci.”
إِنَّمَا ٱلۡمُؤۡمِنُونَ ٱلَّذِينَ إِذَا ذُكِرَ ٱللَّهُ وَجِلَتۡ قُلُوبُهُمۡ وَإِذَا تُلِيَتۡ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتُهُۥ زَادَتۡهُمۡ إِيمَٰنٗا وَعَلَىٰ رَبِّهِمۡ يَتَوَكَّلُونَ
Muminai na haqiqa (su ne) kaxai waxanda idan aka ambaci Allah, sai zukatansu su raurawa, idan kuma aka karanta musu ayoyinsa, sai su qara musu imani, kuma ga Ubangijinsu ne kawai suke dogara
إِذۡ يَقُولُ ٱلۡمُنَٰفِقُونَ وَٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٌ غَرَّ هَـٰٓؤُلَآءِ دِينُهُمۡۗ وَمَن يَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِ فَإِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٞ
Ka tuna lokacin da munafuqai da kuma waxanda suke da rauni a zukatansu suke cewa: “Waxannan addininsu ne ya ruxe su.” Duk wanda ya dogara ga Allah kuwa to lalle Allah Mabuwayi ne Mai hikima
۞وَإِن جَنَحُواْ لِلسَّلۡمِ فَٱجۡنَحۡ لَهَا وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ
Idan kuma suka karkato ga sulhu, to sai kai ma ka karkato gare shi, ka kuma dogara ga Allah. Lalle Shi Mai ji ne Masani
قُل لَّن يُصِيبَنَآ إِلَّا مَا كَتَبَ ٱللَّهُ لَنَا هُوَ مَوۡلَىٰنَاۚ وَعَلَى ٱللَّهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ
Ka ce: “Ba abin da zai same mu sai abin da Allah Ya rubuta mana, shi ne Majivincin al’amuranmu; kuma ga Allah kaxai muminai sai su dogara.”
فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَقُلۡ حَسۡبِيَ ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ عَلَيۡهِ تَوَكَّلۡتُۖ وَهُوَ رَبُّ ٱلۡعَرۡشِ ٱلۡعَظِيمِ
To idan sun ba da baya sai ka ce: “Allah Ya ishe ni, babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi, a gare Shi kaxai na dogara; kuma Shi ne Ubangijin Al’arshi mai girma.”
۞وَٱتۡلُ عَلَيۡهِمۡ نَبَأَ نُوحٍ إِذۡ قَالَ لِقَوۡمِهِۦ يَٰقَوۡمِ إِن كَانَ كَبُرَ عَلَيۡكُم مَّقَامِي وَتَذۡكِيرِي بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ فَعَلَى ٱللَّهِ تَوَكَّلۡتُ فَأَجۡمِعُوٓاْ أَمۡرَكُمۡ وَشُرَكَآءَكُمۡ ثُمَّ لَا يَكُنۡ أَمۡرُكُمۡ عَلَيۡكُمۡ غُمَّةٗ ثُمَّ ٱقۡضُوٓاْ إِلَيَّ وَلَا تُنظِرُونِ
Ka kuma karanta musu labarin (Annabi) Nuhu, a lokacin da ya ce da mutanensa: “Ya ku mutanena, idan zamana a cikinku da kuma wa’azin da nake muku da ayoyin Allah sun dame ku, to ni fa ga Allah ne kawai na dogara, sai ku tattara al’amarinku ku kuma (ku kira) abokan tarayyarku, sannan kada al’amarin naku ya zama a voye, sannan ku zartar (da shi) a gare ni, kada kuma ku saurara mini
وَقَالَ مُوسَىٰ يَٰقَوۡمِ إِن كُنتُمۡ ءَامَنتُم بِٱللَّهِ فَعَلَيۡهِ تَوَكَّلُوٓاْ إِن كُنتُم مُّسۡلِمِينَ
Musa kuma ya ce: “Ya ku mutanena, idan har kun yi imani da Allah, to a gare Shi kawai za ku dogara in kun kasance Musulmai
فَقَالُواْ عَلَى ٱللَّهِ تَوَكَّلۡنَا رَبَّنَا لَا تَجۡعَلۡنَا فِتۡنَةٗ لِّلۡقَوۡمِ ٱلظَّـٰلِمِينَ
Sai suka ce: “Ga Allah kaxai muka dogara. Ya Ubangijinmu, kada ka sanya mu zama fitina ga mutane azzalumai
إِنِّي تَوَكَّلۡتُ عَلَى ٱللَّهِ رَبِّي وَرَبِّكُمۚ مَّا مِن دَآبَّةٍ إِلَّا هُوَ ءَاخِذُۢ بِنَاصِيَتِهَآۚ إِنَّ رَبِّي عَلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ
“Lalle ni na dogara ga Allah, Ubangijina kuma Ubangijinku. Babu wata dabba face Shi ne Yake riqe da makwarkwaxarta. Lalle Ubangijina a kan tafarki madaidaici Yake
قَالَ يَٰقَوۡمِ أَرَءَيۡتُمۡ إِن كُنتُ عَلَىٰ بَيِّنَةٖ مِّن رَّبِّي وَرَزَقَنِي مِنۡهُ رِزۡقًا حَسَنٗاۚ وَمَآ أُرِيدُ أَنۡ أُخَالِفَكُمۡ إِلَىٰ مَآ أَنۡهَىٰكُمۡ عَنۡهُۚ إِنۡ أُرِيدُ إِلَّا ٱلۡإِصۡلَٰحَ مَا ٱسۡتَطَعۡتُۚ وَمَا تَوۡفِيقِيٓ إِلَّا بِٱللَّهِۚ عَلَيۡهِ تَوَكَّلۡتُ وَإِلَيۡهِ أُنِيبُ
Ya ce: “Ya ku mutanena, me kuke gani ne, idan na kasance a kan bayyananniyar hujja daga Ubangijina, Ya kuma arzuta ni da kyakkyawan arziki daga gare Shi. Ba na kuma nufin in aikata abin da nake hana ku aikata shi. Ba komai nake nufi ba sai gyara iyakacin ikona. Kuma dacewata daga Allah kaxai take. A gare Shi na dogara, kuma zuwa gare Shi ne zan koma
وَلِلَّهِ غَيۡبُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَإِلَيۡهِ يُرۡجَعُ ٱلۡأَمۡرُ كُلُّهُۥ فَٱعۡبُدۡهُ وَتَوَكَّلۡ عَلَيۡهِۚ وَمَا رَبُّكَ بِغَٰفِلٍ عَمَّا تَعۡمَلُونَ
Kuma (sanin) gaibu na sammai da na qasa na Allah ne, kuma gare Shi ake komar da dukkanin al’amari. To ka bauta masa kuma ka dogara gare Shi. Ubangijinka kuwa ba gafalalle ba ne ga abin da kuke aikatawa
وَقَالَ يَٰبَنِيَّ لَا تَدۡخُلُواْ مِنۢ بَابٖ وَٰحِدٖ وَٱدۡخُلُواْ مِنۡ أَبۡوَٰبٖ مُّتَفَرِّقَةٖۖ وَمَآ أُغۡنِي عَنكُم مِّنَ ٱللَّهِ مِن شَيۡءٍۖ إِنِ ٱلۡحُكۡمُ إِلَّا لِلَّهِۖ عَلَيۡهِ تَوَكَّلۡتُۖ وَعَلَيۡهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُتَوَكِّلُونَ
Ya kuma ce: “Ya ‘ya’yana, kada ku shiga (Masar) ta qofa guda; ku shiga ta qofofi daban-daban[1]. Ba zan kare muku komai daga Allah ba; ba wani hukunci sai na Allah; a gare Shi na dogara, kuma a gare Shi ne masu dogaro ya wajaba su dogara.”
1- Domi kauce wa wata cutarwa da za ta iya fuskantar su, don kada ta same su gaba xayansu a lokaci guda.
كَذَٰلِكَ أَرۡسَلۡنَٰكَ فِيٓ أُمَّةٖ قَدۡ خَلَتۡ مِن قَبۡلِهَآ أُمَمٞ لِّتَتۡلُوَاْ عَلَيۡهِمُ ٱلَّذِيٓ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ وَهُمۡ يَكۡفُرُونَ بِٱلرَّحۡمَٰنِۚ قُلۡ هُوَ رَبِّي لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ عَلَيۡهِ تَوَكَّلۡتُ وَإِلَيۡهِ مَتَابِ
Kamar haka Muka aiko ka cikin al’umma wadda tuni wasu al’ummun sun wuce kafinta, don ka karanta musu abin da Muka yi maka wahayinsa, alhali kuwa su suna kafirce wa Arrahamanu[1]. Ka ce: “Shi ne Ubangijina, babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi, gare Shi kawai na dogara, kuma gare Shi kawai tubata take.”
1- Kafiran Quraishawa suna qyamar su siffanta Allah da suna Arrahman, watau Mai rahma, kamar yadda ya zo a cikin Suratul Furqan aya ta 60.
قَالَتۡ لَهُمۡ رُسُلُهُمۡ إِن نَّحۡنُ إِلَّا بَشَرٞ مِّثۡلُكُمۡ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يَمُنُّ عَلَىٰ مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦۖ وَمَا كَانَ لَنَآ أَن نَّأۡتِيَكُم بِسُلۡطَٰنٍ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۚ وَعَلَى ٱللَّهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ
Manzanninsu suka ce: “Mu ba kowa ba ne in ban da mutane kamarku, sai dai Allah Yana yin baiwa ga wanda Ya ga dama ne daga bayinsa, kuma ba zai yiwu ba a gare mu mu zo muku da wata hujja sai dai da izinin Allah. Muminai kuwa lalle su dogara ga Allah kawai
وَمَا لَنَآ أَلَّا نَتَوَكَّلَ عَلَى ٱللَّهِ وَقَدۡ هَدَىٰنَا سُبُلَنَاۚ وَلَنَصۡبِرَنَّ عَلَىٰ مَآ ءَاذَيۡتُمُونَاۚ وَعَلَى ٱللَّهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُتَوَكِّلُونَ
“Kuma me zai hana mu mu dogara ga Allah, alhali kuwa haqiqa Ya shiryar da mu hanyoyinmu? Lalle kuwa tabbas za mu yi haquri bisa irin cutar mu da kuka yi. Masu dogaro kuma sai su dogara ga Allah kaxai.”
ٱلَّذِينَ صَبَرُواْ وَعَلَىٰ رَبِّهِمۡ يَتَوَكَّلُونَ
Waxanda suka yi haquri kuma ga Ubangijinsu kawai suke dogaro
إِنَّهُۥ لَيۡسَ لَهُۥ سُلۡطَٰنٌ عَلَى ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَلَىٰ رَبِّهِمۡ يَتَوَكَّلُونَ
Lalle shi (Shaixan) ba shi da iko a kan waxanda suka yi imani kuma suke dogara da Ubangijinsu
وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱلۡحَيِّ ٱلَّذِي لَا يَمُوتُ وَسَبِّحۡ بِحَمۡدِهِۦۚ وَكَفَىٰ بِهِۦ بِذُنُوبِ عِبَادِهِۦ خَبِيرًا
Kuma ka dogara ga (Allah) Rayayye Wanda ba zai mutu ba, kuma ka yi tasbihi da godiyar sa, kuma Ya isa Masani ga zunuban bayinsa
وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱلۡعَزِيزِ ٱلرَّحِيمِ
Ka kuma dogara ga Mabuwayi, Mai rahama
ٱلَّذِي يَرَىٰكَ حِينَ تَقُومُ
Wanda Yake ganin ka yayin da kake tashi (don yin salla)
وَتَقَلُّبَكَ فِي ٱلسَّـٰجِدِينَ
Da kuma (yayin) jujjuyawarka cikin masu sujjada[1]
1- Watau masallata a sallar jam’i.
إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ
Haqiqa Shi Mai ji ne, Masani