وَٱتَّقُواْ يَوۡمٗا لَّا تَجۡزِي نَفۡسٌ عَن نَّفۡسٖ شَيۡـٔٗا وَلَا يُقۡبَلُ مِنۡهَا شَفَٰعَةٞ وَلَا يُؤۡخَذُ مِنۡهَا عَدۡلٞ وَلَا هُمۡ يُنصَرُونَ
Kuma ku kiyayi wata rana da babu wani (mai) rai da zai isar wa da wani (mai) rai komai a cikinta; kuma ba za a karvi wani ceto daga gare shi ba, kuma ba za a karvi wata fansa daga gare shi ba, kuma ba za a taimaka musu ba
وَٱتَّقُواْ يَوۡمٗا لَّا تَجۡزِي نَفۡسٌ عَن نَّفۡسٖ شَيۡـٔٗا وَلَا يُقۡبَلُ مِنۡهَا عَدۡلٞ وَلَا تَنفَعُهَا شَفَٰعَةٞ وَلَا هُمۡ يُنصَرُونَ
Kuma ku kiyayi wani yini da wani rai ba zai isar wa da wani rai komai ba, kuma ba za a karvi wata fansa daga gare shi ba, kuma ceto ba zai amfane shi ba, kuma su ba za a taimaka musu ba
وَٱتَّقُواْ يَوۡمٗا تُرۡجَعُونَ فِيهِ إِلَى ٱللَّهِۖ ثُمَّ تُوَفَّىٰ كُلُّ نَفۡسٖ مَّا كَسَبَتۡ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ
Kuma ku kiyayi wani yini da za a mayar da ku zuwa ga Allah a cikinsa, sannan kowane rai za a cika masa abin da ya aiwatar na aiki, kuma su ba za a zalunce su ba
لِّلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ وَإِن تُبۡدُواْ مَا فِيٓ أَنفُسِكُمۡ أَوۡ تُخۡفُوهُ يُحَاسِبۡكُم بِهِ ٱللَّهُۖ فَيَغۡفِرُ لِمَن يَشَآءُ وَيُعَذِّبُ مَن يَشَآءُۗ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ
Duk abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qasa na Allah ne. Kuma in har kuka bayyana abin da yake cikin zukatanku ko kuka voye shi, Allah zai yi muku hisabi a kansa, sai Ya yi gafara ga wanda Ya ga dama, Ya kuma yi azaba ga wanda Ya ga dama. Kuma Allah Mai iko ne a kan komai
لَا يُكَلِّفُ ٱللَّهُ نَفۡسًا إِلَّا وُسۡعَهَاۚ لَهَا مَا كَسَبَتۡ وَعَلَيۡهَا مَا ٱكۡتَسَبَتۡۗ رَبَّنَا لَا تُؤَاخِذۡنَآ إِن نَّسِينَآ أَوۡ أَخۡطَأۡنَاۚ رَبَّنَا وَلَا تَحۡمِلۡ عَلَيۡنَآ إِصۡرٗا كَمَا حَمَلۡتَهُۥ عَلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِنَاۚ رَبَّنَا وَلَا تُحَمِّلۡنَا مَا لَا طَاقَةَ لَنَا بِهِۦۖ وَٱعۡفُ عَنَّا وَٱغۡفِرۡ لَنَا وَٱرۡحَمۡنَآۚ أَنتَ مَوۡلَىٰنَا فَٱنصُرۡنَا عَلَى ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡكَٰفِرِينَ
Allah ba Ya kallafa wa rai sai abin da zai iya. Abin da ya aikata (na alheri) nasa ne, hakanan sakamakon abin da ya aikata (na sharri) shi ma nasa ne. Ya Ubangijinmu, kada Ka riqe mu da laifi idan mun yi mantuwa ko mun yi kuskure. Ya Ubangijinmu, kada kuma Ka xora mana wani nauyi irin wanda ka xora wa waxanda suke gabaninmu. Ya Ubangijinmu, kada kuma Ka xora mana abin da ba mu da iko a kansa, kuma Ka yi mana afuwa, kuma Ka yi mana gafara, kuma Ka ji qan mu; Kai ne Majivincin lamarinmu, don haka Ka taimake mu a kan mutane kafirai
فَكَيۡفَ إِذَا جَمَعۡنَٰهُمۡ لِيَوۡمٖ لَّا رَيۡبَ فِيهِ وَوُفِّيَتۡ كُلُّ نَفۡسٖ مَّا كَسَبَتۡ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ
To yaya halinsu zai kasance idan Muka tara su a wani yini da babu shakka game da shi, kuma kowane rai za a saka masa da abin da ya aikata, kuma su ba za a zalunce su ba?
يَوۡمَ تَجِدُ كُلُّ نَفۡسٖ مَّا عَمِلَتۡ مِنۡ خَيۡرٖ مُّحۡضَرٗا وَمَا عَمِلَتۡ مِن سُوٓءٖ تَوَدُّ لَوۡ أَنَّ بَيۡنَهَا وَبَيۡنَهُۥٓ أَمَدَۢا بَعِيدٗاۗ وَيُحَذِّرُكُمُ ٱللَّهُ نَفۡسَهُۥۗ وَٱللَّهُ رَءُوفُۢ بِٱلۡعِبَادِ
Ranar da kowane rai zai sami abin da ya aikata na alheri an halarto da shi, abin da kuwa ya aikata na mummunan aiki, zai so ina ma da a ce tsakaninsa da shi akwai wata tazara mai nisa. Kuma Allah Yana tsoratar da ku kansa, kuma Allah Mai tausayi ne ga bayi
كُلُّ نَفۡسٖ ذَآئِقَةُ ٱلۡمَوۡتِۗ وَإِنَّمَا تُوَفَّوۡنَ أُجُورَكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۖ فَمَن زُحۡزِحَ عَنِ ٱلنَّارِ وَأُدۡخِلَ ٱلۡجَنَّةَ فَقَدۡ فَازَۗ وَمَا ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَآ إِلَّا مَتَٰعُ ٱلۡغُرُورِ
Kowane rai zai xanxani mutuwa. Kuma a ranar alqiyama ne za a cika muku ladan ayyukanku; to duk wanda aka nisanta shi daga wuta, kuma aka shigar da shi Aljanna, to haqiqa ya rabauta. Kuma rayuwar duniya ba komai ba ce face jin daxi mai ruxarwa
هُنَالِكَ تَبۡلُواْ كُلُّ نَفۡسٖ مَّآ أَسۡلَفَتۡۚ وَرُدُّوٓاْ إِلَى ٱللَّهِ مَوۡلَىٰهُمُ ٱلۡحَقِّۖ وَضَلَّ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَفۡتَرُونَ
A can ne kowane rai zai samu sakamakon abin da ya gabatar (a duniya). An kuma mayar da su zuwa ga Allah Majivincinsu na gaskiya; abin da kuma suka kasance suna qirqira ya vace musu
وَلَوۡ أَنَّ لِكُلِّ نَفۡسٖ ظَلَمَتۡ مَا فِي ٱلۡأَرۡضِ لَٱفۡتَدَتۡ بِهِۦۗ وَأَسَرُّواْ ٱلنَّدَامَةَ لَمَّا رَأَوُاْ ٱلۡعَذَابَۖ وَقُضِيَ بَيۡنَهُم بِٱلۡقِسۡطِ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ
Da a ce kowane rai da ya yi zalunci ya mallaki duk abin da yake bayan qasa, to lalle da ya fanshi kansa da shi. Suka kuwa voye nadama a lokacin da suka ga azaba; an kuma yi hukunci tsakaninsu na adalci; ba kuma za a zalunce su ba
يَوۡمَ يَأۡتِ لَا تَكَلَّمُ نَفۡسٌ إِلَّا بِإِذۡنِهِۦۚ فَمِنۡهُمۡ شَقِيّٞ وَسَعِيدٞ
Ranar da za ta zo ba wani mai rai da zai yi magana sai da izininsa. To daga cikinsu akwai tavavve da kuma mai rabauta
۞يَوۡمَ تَأۡتِي كُلُّ نَفۡسٖ تُجَٰدِلُ عَن نَّفۡسِهَا وَتُوَفَّىٰ كُلُّ نَفۡسٖ مَّا عَمِلَتۡ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ
Ranar da kowanne rai zai zo yana kare kansa, kuma a cika wa kowanne rai (sakamakon) abin da ya aikata, kuma su ba za a zalunce su ba
وَكُلَّ إِنسَٰنٍ أَلۡزَمۡنَٰهُ طَـٰٓئِرَهُۥ فِي عُنُقِهِۦۖ وَنُخۡرِجُ لَهُۥ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ كِتَٰبٗا يَلۡقَىٰهُ مَنشُورًا
Kuma kowane mutum Mun xaura masa littafin aikinsa a wuyansa, za kuma Mu fito masa da wani littafi a ranar alqiyama da zai same shi a buxe
ٱقۡرَأۡ كِتَٰبَكَ كَفَىٰ بِنَفۡسِكَ ٱلۡيَوۡمَ عَلَيۡكَ حَسِيبٗا
(A ce da shi): “Karanta littafinka; a yau ka isa ka yi wa kanka hukunci da kanka.”
مَّنِ ٱهۡتَدَىٰ فَإِنَّمَا يَهۡتَدِي لِنَفۡسِهِۦۖ وَمَن ضَلَّ فَإِنَّمَا يَضِلُّ عَلَيۡهَاۚ وَلَا تَزِرُ وَازِرَةٞ وِزۡرَ أُخۡرَىٰۗ وَمَا كُنَّا مُعَذِّبِينَ حَتَّىٰ نَبۡعَثَ رَسُولٗا
Wanda ya shiriya to lalle yana shiriya ne don kansa; wanda kuwa ya vata to lalle yana vata ne don kansa. Ba kuwa wanda zai xauki nauyin laifin wani. Kuma ba Mu zamanto Masu azabtarwa ba har sai Mun aiko da manzo
إِنَّ ٱلسَّاعَةَ ءَاتِيَةٌ أَكَادُ أُخۡفِيهَا لِتُجۡزَىٰ كُلُّ نَفۡسِۭ بِمَا تَسۡعَىٰ
“Lalle alqiyama za ta zo, ina nufin voye ta ne don a saka wa kowanne rai da irin abin da yake aikatawa
كُلُّ نَفۡسٖ ذَآئِقَةُ ٱلۡمَوۡتِۗ وَنَبۡلُوكُم بِٱلشَّرِّ وَٱلۡخَيۡرِ فِتۡنَةٗۖ وَإِلَيۡنَا تُرۡجَعُونَ
Kowanne rai zai xanxani mutuwa. Muna kuwa jarrabar ku da fitinar sharri da ta alheri, kuma gare Mu ne za a dawo da ku
وَنَضَعُ ٱلۡمَوَٰزِينَ ٱلۡقِسۡطَ لِيَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ فَلَا تُظۡلَمُ نَفۡسٞ شَيۡـٔٗاۖ وَإِن كَانَ مِثۡقَالَ حَبَّةٖ مِّنۡ خَرۡدَلٍ أَتَيۡنَا بِهَاۗ وَكَفَىٰ بِنَا حَٰسِبِينَ
Za Mu kuma sanya ma’aunai na adalci a ranar alqiyama, sannan ba za a zalunci kowanne rai da komai ba, ko da ya zama gwargwadon qwayar komayya ne, za Mu zo da shi. Kuma Mun isa Masu hisabi!
إِنَّ ٱلَّذِينَ سَبَقَتۡ لَهُم مِّنَّا ٱلۡحُسۡنَىٰٓ أُوْلَـٰٓئِكَ عَنۡهَا مُبۡعَدُونَ
Lalle waxanda kalmarmu mafi kyau (ta cewa su ‘yan Aljanna ne) ta riga ta tabbata gare su, waxannan waxanda ake nesantawa ne daga gare ta (wutar)
لَا يَسۡمَعُونَ حَسِيسَهَاۖ وَهُمۡ فِي مَا ٱشۡتَهَتۡ أَنفُسُهُمۡ خَٰلِدُونَ
Ba za su ji hargowarta ba, kuma su masu dawwama ne cikin abin da ransu yake so
وَلَا نُكَلِّفُ نَفۡسًا إِلَّا وُسۡعَهَاۚ وَلَدَيۡنَا كِتَٰبٞ يَنطِقُ بِٱلۡحَقِّ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ
Ba Ma kuwa xora wa kowane rai wani abu sai wanda zai iya. Kuma a wurinmu akwai littafi da yake furuci da gaskiya, kuma su ba za a zalunce su ba
فَإِذَا نُفِخَ فِي ٱلصُّورِ فَلَآ أَنسَابَ بَيۡنَهُمۡ يَوۡمَئِذٖ وَلَا يَتَسَآءَلُونَ
Sannan idan aka busa qaho to fa babu wata dangantaka (mai amfani) a tsakaninsu a wannan ranar, kuma ba za su tambayi juna ba
فَمَن ثَقُلَتۡ مَوَٰزِينُهُۥ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ
To waxanda ma’aunansu suka yi nauyi waxannan su ne masu babban rabo
وَمَنۡ خَفَّتۡ مَوَٰزِينُهُۥ فَأُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ خَسِرُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ فِي جَهَنَّمَ خَٰلِدُونَ
Waxanda kuwa ma’aunansu suka yi sakayau waxannan su ne waxanda suka yi asarar kawunansu, suna masu dawwama a cikin (wutar) Jahannama
وَلَا تَزِرُ وَازِرَةٞ وِزۡرَ أُخۡرَىٰۚ وَإِن تَدۡعُ مُثۡقَلَةٌ إِلَىٰ حِمۡلِهَا لَا يُحۡمَلۡ مِنۡهُ شَيۡءٞ وَلَوۡ كَانَ ذَا قُرۡبَىٰٓۗ إِنَّمَا تُنذِرُ ٱلَّذِينَ يَخۡشَوۡنَ رَبَّهُم بِٱلۡغَيۡبِ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَۚ وَمَن تَزَكَّىٰ فَإِنَّمَا يَتَزَكَّىٰ لِنَفۡسِهِۦۚ وَإِلَى ٱللَّهِ ٱلۡمَصِيرُ
Kuma wani mai xaukar nauyi ba ya xaukan laifin wani. Idan kuma wani mai nannauyan zunubi ya yi kira zuwa xauke nauyin nasa, ba za a xauke masa komai daga nauyin ba, ko da kuwa xan’uwa ne makusanci. Kai dai kana mai gargaxi ne kawai ga waxanda suke tsoron Ubangijinsu ba tare da ganin Sa ba, suka kuma tsai da salla. Wanda kuwa ya tsarkaka, to ya tsarkaka ne don kansa. Makoma kuma na ga Allah Shi kaxai
فَٱلۡيَوۡمَ لَا تُظۡلَمُ نَفۡسٞ شَيۡـٔٗا وَلَا تُجۡزَوۡنَ إِلَّا مَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
To a yau fa ba za a zalunci wani rai da komai ba, ba kuma za a saka muku ba sai da irin abin da kuka zamanto kuna aikatawa
وَوُفِّيَتۡ كُلُّ نَفۡسٖ مَّا عَمِلَتۡ وَهُوَ أَعۡلَمُ بِمَا يَفۡعَلُونَ
Aka kuma yi wa kowane rai cikakken sakamakon abin da ya aikata, Shi ko (Allah) Yana sane da abin da suke aikatawa
ٱلۡيَوۡمَ تُجۡزَىٰ كُلُّ نَفۡسِۭ بِمَا كَسَبَتۡۚ لَا ظُلۡمَ ٱلۡيَوۡمَۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَرِيعُ ٱلۡحِسَابِ
A wannan ranar za a saka wa kowane rai da irin abin da ya aikata. Babu zalunci a wannan ranar. Lalle Allah Mai gaggawar yin hisabi ne
إِنَّ ٱلَّذِينَ قَالُواْ رَبُّنَا ٱللَّهُ ثُمَّ ٱسۡتَقَٰمُواْ تَتَنَزَّلُ عَلَيۡهِمُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ أَلَّا تَخَافُواْ وَلَا تَحۡزَنُواْ وَأَبۡشِرُواْ بِٱلۡجَنَّةِ ٱلَّتِي كُنتُمۡ تُوعَدُونَ
Lalle waxanda suka ce: “Allah ne Ubangijinmu”, sannan suka tsaya kyam, to mala’iku za su sauko musu (lokacin mutuwa suna cewa): “Kada ku tsorata, kuma kada ku yi baqin ciki, kuma ku yi farin ciki da Aljanna wadda kuka kasance ana yi muku alqawarinta
نَحۡنُ أَوۡلِيَآؤُكُمۡ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَفِي ٱلۡأٓخِرَةِۖ وَلَكُمۡ فِيهَا مَا تَشۡتَهِيٓ أَنفُسُكُمۡ وَلَكُمۡ فِيهَا مَا تَدَّعُونَ
“Mu masoyanku ne a rayuwar duniya da kuma ta lahira; kuma a cikinta (Aljanna) za ku sami duk abin da rayukanku suke marmari, za kuma ku sami duk abin da kuke nema a cikinta