Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 40

إِلَّا تَنصُرُوهُ فَقَدۡ نَصَرَهُ ٱللَّهُ إِذۡ أَخۡرَجَهُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ ثَانِيَ ٱثۡنَيۡنِ إِذۡ هُمَا فِي ٱلۡغَارِ إِذۡ يَقُولُ لِصَٰحِبِهِۦ لَا تَحۡزَنۡ إِنَّ ٱللَّهَ مَعَنَاۖ فَأَنزَلَ ٱللَّهُ سَكِينَتَهُۥ عَلَيۡهِ وَأَيَّدَهُۥ بِجُنُودٖ لَّمۡ تَرَوۡهَا وَجَعَلَ كَلِمَةَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ ٱلسُّفۡلَىٰۗ وَكَلِمَةُ ٱللَّهِ هِيَ ٱلۡعُلۡيَاۗ وَٱللَّهُ عَزِيزٌ حَكِيمٌ

Idan ba ku taimake shi ba (watau Manzon Allah) to haqiqa Allah Ya taimake shi lokacin da kafirai suka fitar da shi (daga Makka), alhalin suna su biyu, lokacin da suke a cikin kogo, yayin da yake ce wa abokinsa (Abubakar): “Kada ka damu, lalle Allah yana tare da mu,” sai Allah Ya saukar masa da nutsuwarsa Ya kuma qarfafe shi da runduna wadda ba ku gan ta ba, Ya kuma sanya kalmar waxanda suka kafirta ta zama qaskantacciya. Kalmar Allah kuwa ita ce maxaukakiya. Allah kuma Mabuwayi ne, Mai hikima



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 41

ٱنفِرُواْ خِفَافٗا وَثِقَالٗا وَجَٰهِدُواْ بِأَمۡوَٰلِكُمۡ وَأَنفُسِكُمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۚ ذَٰلِكُمۡ خَيۡرٞ لَّكُمۡ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ

Ku fita yaqi kuna da kuzari ko ba ku da shi, ku kuma yi yaqi da dukiyoyinku da kawunanku saboda Allah. Wannan ya fi alheri a gare ku, in kun kasance kun san (haka)



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 42

لَوۡ كَانَ عَرَضٗا قَرِيبٗا وَسَفَرٗا قَاصِدٗا لَّٱتَّبَعُوكَ وَلَٰكِنۢ بَعُدَتۡ عَلَيۡهِمُ ٱلشُّقَّةُۚ وَسَيَحۡلِفُونَ بِٱللَّهِ لَوِ ٱسۡتَطَعۡنَا لَخَرَجۡنَا مَعَكُمۡ يُهۡلِكُونَ أَنفُسَهُمۡ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ إِنَّهُمۡ لَكَٰذِبُونَ

Da (abin da za su samu) amfani ne na kusa, ko tafiya gajeriya, to lalle da sun bi ka, sai dai kuma tafiyar ta yi musu tsawo; kuma za su zo suna rantsuwa da Allah cewa: “Da mun sami hali da lalle mun fita tare da ku[1]”, suna hallaka kansu ne kawai, Allah kuwa Yana sane da cewa lalle su tabbas maqaryata ne


1- Watau zuwa yaqin Tabuka.


Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 43

عَفَا ٱللَّهُ عَنكَ لِمَ أَذِنتَ لَهُمۡ حَتَّىٰ يَتَبَيَّنَ لَكَ ٱلَّذِينَ صَدَقُواْ وَتَعۡلَمَ ٱلۡكَٰذِبِينَ

Allah Ya yafe maka; don me ka yi musu izini? Ai har sai ka gane musu gaskiya ka kuma san maqaryata



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 44

لَا يَسۡتَـٔۡذِنُكَ ٱلَّذِينَ يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ أَن يُجَٰهِدُواْ بِأَمۡوَٰلِهِمۡ وَأَنفُسِهِمۡۗ وَٱللَّهُ عَلِيمُۢ بِٱلۡمُتَّقِينَ

Waxanda suka yi imani da Allah da ranar lahira ba sa neman izininka don kada su yi yaqi da dukiyoyinsu da kawunansu. Allah kuwa yana sane da masu taqawa



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 45

إِنَّمَا يَسۡتَـٔۡذِنُكَ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَٱرۡتَابَتۡ قُلُوبُهُمۡ فَهُمۡ فِي رَيۡبِهِمۡ يَتَرَدَّدُونَ

Waxanda kawai suke neman izininka su ne waxanda ba sa imani da Allah da ranar lahira, zukatansu kuma suka yi kokwanto, saboda haka suke ta dawurwuri a cikin kokwantonsu



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 46

۞وَلَوۡ أَرَادُواْ ٱلۡخُرُوجَ لَأَعَدُّواْ لَهُۥ عُدَّةٗ وَلَٰكِن كَرِهَ ٱللَّهُ ٱنۢبِعَاثَهُمۡ فَثَبَّطَهُمۡ وَقِيلَ ٱقۡعُدُواْ مَعَ ٱلۡقَٰعِدِينَ

Da kuwa sun yi niyyar fita to da sun yi masa tanadi, sai dai kuma Allah Ya qi zaburar da su, sai Ya dankwafar da su, aka kuma ce (da su): “Ku zauna tare da mazauna (gida)[1].”


1- Watau mata da yara da marasa lafiya da masu lalura waxanda ba za su iya fita yaqi ba.


Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 47

لَوۡ خَرَجُواْ فِيكُم مَّا زَادُوكُمۡ إِلَّا خَبَالٗا وَلَأَوۡضَعُواْ خِلَٰلَكُمۡ يَبۡغُونَكُمُ ٱلۡفِتۡنَةَ وَفِيكُمۡ سَمَّـٰعُونَ لَهُمۡۗ وَٱللَّهُ عَلِيمُۢ بِٱلظَّـٰلِمِينَ

Da sun fito cikinku xin, to ba abin da za su qare ku da shi sai tavarvarewa, kuma lalle da sun yi ta shige da fice a tsakaninku suna qoqarin haifar muku da fitina, a cikinku kuma akwai masu jiyo musu (wato abokan gaba) magana. Allah kuwa Masanin azzalumai ne



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 48

لَقَدِ ٱبۡتَغَوُاْ ٱلۡفِتۡنَةَ مِن قَبۡلُ وَقَلَّبُواْ لَكَ ٱلۡأُمُورَ حَتَّىٰ جَآءَ ٱلۡحَقُّ وَظَهَرَ أَمۡرُ ٱللَّهِ وَهُمۡ كَٰرِهُونَ

Haqiqa tun da can sun nemi yaxa fitina, suka hargitsa maka al’amura, har sai da gaskiya ta zo, al’amarin Allah kuma ya bayyana, su kuwa suna masu qin (haka)



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 49

وَمِنۡهُم مَّن يَقُولُ ٱئۡذَن لِّي وَلَا تَفۡتِنِّيٓۚ أَلَا فِي ٱلۡفِتۡنَةِ سَقَطُواْۗ وَإِنَّ جَهَنَّمَ لَمُحِيطَةُۢ بِٱلۡكَٰفِرِينَ

Daga cikinsu kuma akwai wanda yake cewa: “Ka yi mani izinin (zama), kada ka jefa ni cikin fitina.” Tabbas, ai cikin fitinar suka faxa. Lalle Jahannama kuwa mai kewaye kafirai ce



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 50

إِن تُصِبۡكَ حَسَنَةٞ تَسُؤۡهُمۡۖ وَإِن تُصِبۡكَ مُصِيبَةٞ يَقُولُواْ قَدۡ أَخَذۡنَآ أَمۡرَنَا مِن قَبۡلُ وَيَتَوَلَّواْ وَّهُمۡ فَرِحُونَ

Idan wani alheri ya same ka sai ya baqanta musu rai; idan kuwa musiba ce ta same ka sai su riqa cewa: “Haqiqa mu da ma tuni mun xauki matakin kauce mata[1],” sai kuma su juya baya suna masu farin ciki


1- Watau da suka qi fita yaqi tare da Manzon Allah ().


Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 51

قُل لَّن يُصِيبَنَآ إِلَّا مَا كَتَبَ ٱللَّهُ لَنَا هُوَ مَوۡلَىٰنَاۚ وَعَلَى ٱللَّهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ

Ka ce: “Ba abin da zai same mu sai abin da Allah Ya rubuta mana, shi ne Majivincin al’amuranmu; kuma ga Allah kaxai muminai sai su dogara.”



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 52

قُلۡ هَلۡ تَرَبَّصُونَ بِنَآ إِلَّآ إِحۡدَى ٱلۡحُسۡنَيَيۡنِۖ وَنَحۡنُ نَتَرَبَّصُ بِكُمۡ أَن يُصِيبَكُمُ ٱللَّهُ بِعَذَابٖ مِّنۡ عِندِهِۦٓ أَوۡ بِأَيۡدِينَاۖ فَتَرَبَّصُوٓاْ إِنَّا مَعَكُم مُّتَرَبِّصُونَ

Ka ce: “Shin akwai abin da kuke jira ya same mu in ban da xayan kyawawan abubuwa biyu (wato nasara ko shahada). Mu kuwa muna jiran (mu ga) Allah Ya aukar muku da wata azaba daga wurinsa ko kuwa ta hannunmu? To sai ku jira, lalle mu ma masu jira ne tare da ku.”



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 53

قُلۡ أَنفِقُواْ طَوۡعًا أَوۡ كَرۡهٗا لَّن يُتَقَبَّلَ مِنكُمۡ إِنَّكُمۡ كُنتُمۡ قَوۡمٗا فَٰسِقِينَ

Ka ce: “Ku ciyar (da dukiyarku) cikin daxin rai ko a bisa dole (duka xai suke), ba za a karva muku ba; don kuwa lalle kun kasance ku mutane ne fasiqai.”



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 54

وَمَا مَنَعَهُمۡ أَن تُقۡبَلَ مِنۡهُمۡ نَفَقَٰتُهُمۡ إِلَّآ أَنَّهُمۡ كَفَرُواْ بِٱللَّهِ وَبِرَسُولِهِۦ وَلَا يَأۡتُونَ ٱلصَّلَوٰةَ إِلَّا وَهُمۡ كُسَالَىٰ وَلَا يُنفِقُونَ إِلَّا وَهُمۡ كَٰرِهُونَ

Ba kuwa abin da yah ana a karvi ciyarwar tasu sai don sun kafirce wa Allah da Manzonsa, ba sa kuma zuwa salla sai suna cikin kasala, ba sa kuma sa ciyarwa sai aka tilas,



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 55

فَلَا تُعۡجِبۡكَ أَمۡوَٰلُهُمۡ وَلَآ أَوۡلَٰدُهُمۡۚ إِنَّمَا يُرِيدُ ٱللَّهُ لِيُعَذِّبَهُم بِهَا فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَتَزۡهَقَ أَنفُسُهُمۡ وَهُمۡ كَٰفِرُونَ

To kada dukiyoyinsu da ‘ya’yansu su qayatar da kai. Allah Yana nufin kawai Ya azabta su ne da su a rayuwar duniya, rayukansu kuma su zazzago a halin suna kafirai



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 56

وَيَحۡلِفُونَ بِٱللَّهِ إِنَّهُمۡ لَمِنكُمۡ وَمَا هُم مِّنكُمۡ وَلَٰكِنَّهُمۡ قَوۡمٞ يَفۡرَقُونَ

Sukan kuma rantse da Allah cewa lalle suna tare da ku, alhali kuwa ba sa tare da ku, kawai dai su wasu mutane ne matsorata



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 57

لَوۡ يَجِدُونَ مَلۡجَـًٔا أَوۡ مَغَٰرَٰتٍ أَوۡ مُدَّخَلٗا لَّوَلَّوۡاْ إِلَيۡهِ وَهُمۡ يَجۡمَحُونَ

Da za su sami wata mafaka ko wani kogo ko wata mashiga, to da sun juya zuwa gare shi suna gaggawar (shiga)



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 58

وَمِنۡهُم مَّن يَلۡمِزُكَ فِي ٱلصَّدَقَٰتِ فَإِنۡ أُعۡطُواْ مِنۡهَا رَضُواْ وَإِن لَّمۡ يُعۡطَوۡاْ مِنۡهَآ إِذَا هُمۡ يَسۡخَطُونَ

Daga cikinsu kuma akwai waxanda suke aibata ka game da rabon sadaka; idan an ba su wani abu daga cikinta to sai su gamsu, idan kuwa ba a ba su daga cikinta ba sai ka gan su suna fushi



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 59

وَلَوۡ أَنَّهُمۡ رَضُواْ مَآ ءَاتَىٰهُمُ ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥ وَقَالُواْ حَسۡبُنَا ٱللَّهُ سَيُؤۡتِينَا ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦ وَرَسُولُهُۥٓ إِنَّآ إِلَى ٱللَّهِ رَٰغِبُونَ

Da kuwa za su yarda da abin da Allah da Manzonsa suka ba su, su kuma ce: “Allah ya ishe mu, kuma Allah zai ba mu daga falalarsa Manzonsa ma (zai ba mu), lalle mu masu kwaxayi ne a wurin Allah kaxai.”



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 81

فَرِحَ ٱلۡمُخَلَّفُونَ بِمَقۡعَدِهِمۡ خِلَٰفَ رَسُولِ ٱللَّهِ وَكَرِهُوٓاْ أَن يُجَٰهِدُواْ بِأَمۡوَٰلِهِمۡ وَأَنفُسِهِمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَقَالُواْ لَا تَنفِرُواْ فِي ٱلۡحَرِّۗ قُلۡ نَارُ جَهَنَّمَ أَشَدُّ حَرّٗاۚ لَّوۡ كَانُواْ يَفۡقَهُونَ

(Munafukai) waxanda suka qi fita (yaqi) sun yi farin ciki da zamansu (a gida) suna masu sava wa Manzon Allah, suka kuma qi su yi yaqi da dukiyoyinsu da kawunansu saboda Allah, suka kuma ce (da junansu): “Kada ku fita yaqi cikin zafin nan.” Ka ce da su: “Wutar Jahannama ta fi tsananin zafi.” Da sun zamanto suna ganewa



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 82

فَلۡيَضۡحَكُواْ قَلِيلٗا وَلۡيَبۡكُواْ كَثِيرٗا جَزَآءَۢ بِمَا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ

Sai su yi dariya kaxan su kuma yi kuka mai yawa a sakamakon abin da suka kasance suna aikatawa



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 83

فَإِن رَّجَعَكَ ٱللَّهُ إِلَىٰ طَآئِفَةٖ مِّنۡهُمۡ فَٱسۡتَـٔۡذَنُوكَ لِلۡخُرُوجِ فَقُل لَّن تَخۡرُجُواْ مَعِيَ أَبَدٗا وَلَن تُقَٰتِلُواْ مَعِيَ عَدُوًّاۖ إِنَّكُمۡ رَضِيتُم بِٱلۡقُعُودِ أَوَّلَ مَرَّةٖ فَٱقۡعُدُواْ مَعَ ٱلۡخَٰلِفِينَ

To idan Allah Ya dawo da kai zuwa ga wata jama’a daga cikinsu sai suka nemi izinin fita a wajenka, to sai ka ce (da su): “Ba za ku fita tare da ni ba har abada, kuma ba za ku yaqi wani abokin gaba ba tare da ni ba har abada. Lalle kun yarda da zama tun farko, to sai ku zauna tare da masu zama.” (wato mata da yara)



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 84

وَلَا تُصَلِّ عَلَىٰٓ أَحَدٖ مِّنۡهُم مَّاتَ أَبَدٗا وَلَا تَقُمۡ عَلَىٰ قَبۡرِهِۦٓۖ إِنَّهُمۡ كَفَرُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَمَاتُواْ وَهُمۡ فَٰسِقُونَ

Kada ka qara yi wa xaya daga cikinsu da ya mutu salla har abada, kada kuma ka tsaya a kan qabarinsa (don addu’a). Lalle su sun kafirce wa Allah da Manzonsa, suka kuma mutu suna fasiqai



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 85

وَلَا تُعۡجِبۡكَ أَمۡوَٰلُهُمۡ وَأَوۡلَٰدُهُمۡۚ إِنَّمَا يُرِيدُ ٱللَّهُ أَن يُعَذِّبَهُم بِهَا فِي ٱلدُّنۡيَا وَتَزۡهَقَ أَنفُسُهُمۡ وَهُمۡ كَٰفِرُونَ

Kada kuma dukiyoyinsu da ‘ya’yansu su qayatar da kai. Lalle kawai Allah Yana nufin azabtar da su ne da su (dukiyoyin da ‘ya’yan), rayukansu kuma su zazzago suna kafirai



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 86

وَإِذَآ أُنزِلَتۡ سُورَةٌ أَنۡ ءَامِنُواْ بِٱللَّهِ وَجَٰهِدُواْ مَعَ رَسُولِهِ ٱسۡتَـٔۡذَنَكَ أُوْلُواْ ٱلطَّوۡلِ مِنۡهُمۡ وَقَالُواْ ذَرۡنَا نَكُن مَّعَ ٱلۡقَٰعِدِينَ

Idan kuma aka saukar da wata sura mai cewa: “Ku yi imani da Allah kuma ku yi yaqi tare da Manzonsa,” sai masu wadata daga cikinsu su nemi izininka su ce: “Qyale mu mu kasance tare da masu zama (a gida, wato mata da yara).”



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 87

رَضُواْ بِأَن يَكُونُواْ مَعَ ٱلۡخَوَالِفِ وَطُبِعَ عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ فَهُمۡ لَا يَفۡقَهُونَ

Sun yarda da su kasance tare da mata masu zaman gida, an kuma doxe zukatansu, saboda haka ba sa ganewa



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 88

لَٰكِنِ ٱلرَّسُولُ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُۥ جَٰهَدُواْ بِأَمۡوَٰلِهِمۡ وَأَنفُسِهِمۡۚ وَأُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمُ ٱلۡخَيۡرَٰتُۖ وَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ

Sai dai shi Manzo da waxanda suka yi imani tare da shi sun yi yaqi da dukiyoyinsu da kuma kawunansu. Waxannan kuwa suna da alherai; kuma waxannan su ne marabauta



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 89

أَعَدَّ ٱللَّهُ لَهُمۡ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ ذَٰلِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ

Allah Ya tanadar musu da gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, suna masu dawwama a cikinsu. Wannan shi ne rabo mai girma



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 90

وَجَآءَ ٱلۡمُعَذِّرُونَ مِنَ ٱلۡأَعۡرَابِ لِيُؤۡذَنَ لَهُمۡ وَقَعَدَ ٱلَّذِينَ كَذَبُواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥۚ سَيُصِيبُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۡهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

Masu kawo uzurin qarya daga mutanen qauye kuma suka zo don a yi musu izini, sai kuma waxanda suka yi wa Allah da Manzonsa qarya suka yi zamansu (ba tare da kawo hanzari ba). To azaba mai raxaxi za ta samu waxanda suka kafirta daga cikinsu