وَإِلَٰهُكُمۡ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۖ لَّآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلرَّحۡمَٰنُ ٱلرَّحِيمُ
Kuma abin bautarku abin bauta ne Guda Xaya, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi. Shi ne Mai rahama, Mai jin qai
ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡحَيُّ ٱلۡقَيُّومُۚ لَا تَأۡخُذُهُۥ سِنَةٞ وَلَا نَوۡمٞۚ لَّهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ مَن ذَا ٱلَّذِي يَشۡفَعُ عِندَهُۥٓ إِلَّا بِإِذۡنِهِۦۚ يَعۡلَمُ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡۖ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَيۡءٖ مِّنۡ عِلۡمِهِۦٓ إِلَّا بِمَا شَآءَۚ وَسِعَ كُرۡسِيُّهُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَۖ وَلَا يَـُٔودُهُۥ حِفۡظُهُمَاۚ وَهُوَ ٱلۡعَلِيُّ ٱلۡعَظِيمُ
Allah, babu wani abin bauta wa da cancanta sai Shi, Rayayye, Tsayayye da Zatinsa; gyangyaxi ba ya kama shi, ballantana barci. Abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qasa nasa ne shi kaxai. Wane ne ya isa ya yi ceto a wurinsa in ba da izininsa ba? Ya san abin da yake tare da su a yanzu da kuma abin da zai biyo bayansu; kuma ba sa iya sanin wani abu cikin iliminsa sai abin da Ya ga dama. Kursiyyunsa ya yalwaci sammai da qasa, kuma kiyaye su ba zai nauyaye Shi ba, kuma Shi ne Maxaukaki Mai girma
ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡحَيُّ ٱلۡقَيُّومُ
Allah, babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi, Shi Rayayye ne, Tsayayye da Zatinsa
شَهِدَ ٱللَّهُ أَنَّهُۥ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ وَٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ وَأُوْلُواْ ٱلۡعِلۡمِ قَآئِمَۢا بِٱلۡقِسۡطِۚ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ
Allah Ya shaida cewa, babu abin bauta wa da gaskiya sai Shi, haka mala’iku ma da ma’abota ilimi, Tsayayye ne da adalci. Babu abin bauta wa da gaskiya sai Shi, Mabuwayi, Mai hikima
إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ ٱلۡقَصَصُ ٱلۡحَقُّۚ وَمَا مِنۡ إِلَٰهٍ إِلَّا ٱللَّهُۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ
Lalle wannan shi ne ba da labari na gaskiya. Kuma babu abin bauta wa da gaskiya sai Allah. Kuma lalle Allah Shi ne Mabuwayi, Mai hikima
ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۚ لَيَجۡمَعَنَّكُمۡ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ لَا رَيۡبَ فِيهِۗ وَمَنۡ أَصۡدَقُ مِنَ ٱللَّهِ حَدِيثٗا
Allah, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi. Lalle zai tattara ku a ranar alqiyama, wadda babu kokwanto a cikinsa. Kuma wane ne ya fi Allah gaskiyar zance?
يَـٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ لَا تَغۡلُواْ فِي دِينِكُمۡ وَلَا تَقُولُواْ عَلَى ٱللَّهِ إِلَّا ٱلۡحَقَّۚ إِنَّمَا ٱلۡمَسِيحُ عِيسَى ٱبۡنُ مَرۡيَمَ رَسُولُ ٱللَّهِ وَكَلِمَتُهُۥٓ أَلۡقَىٰهَآ إِلَىٰ مَرۡيَمَ وَرُوحٞ مِّنۡهُۖ فَـَٔامِنُواْ بِٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦۖ وَلَا تَقُولُواْ ثَلَٰثَةٌۚ ٱنتَهُواْ خَيۡرٗا لَّكُمۡۚ إِنَّمَا ٱللَّهُ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۖ سُبۡحَٰنَهُۥٓ أَن يَكُونَ لَهُۥ وَلَدٞۘ لَّهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ وَكِيلٗا
Ya ku Ma’abota Littafi, kada ku wuce iyaka cikin addininku[1], kuma kada ku faxi wata magana game da Allah sai ta gaskiya. Almasihu Isa xan Maryamu Manzon Allah ne, kuma kalmarsa ce da ya jefa wa Maryamu, kuma Ruhi ne daga gare Shi; don haka ku yi imani da Allah da manzanninsa, kuma kada ku riqa cewa su uku ne. Ku daina shi ya fi alheri a gare ku. Allah Shi ne kaxai abin bauta da gaskiya, Xaya ne; Ya tsarkaka a ce Yana da xa. Kuma abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qasa nasa ne, kuma Allah Ya isa Abin dogaro
1- Watau kada su wuce iyaka wajen kuzuzuta lamarin Annabi Isa () har ta kai su ga cewa xan Allah ne.
لَّقَدۡ كَفَرَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓاْ إِنَّ ٱللَّهَ ثَالِثُ ثَلَٰثَةٖۘ وَمَا مِنۡ إِلَٰهٍ إِلَّآ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۚ وَإِن لَّمۡ يَنتَهُواْ عَمَّا يَقُولُونَ لَيَمَسَّنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۡهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Lalle haqiqa waxannan da suka ce: “Lalle Allah Shi ne na cikon (alloli) uku,”[1] sun kafirta. Babu kuwa wani abin bautawa na gaskiya, sai abin bauta Xaya tal. Idan ba su bar abin da suke faxa xin nan ba, lalle azaba mai raxaxi za ta shafi waxanda suka kafirta daga cikinsu
1- Ana nufin aqidar Nasara da suke cewa, abu uku ne suka haxu suka zama Allah, watau Isa da mahaifiyarsa Maryamu da kuma Allah.
ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمۡۖ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ خَٰلِقُ كُلِّ شَيۡءٖ فَٱعۡبُدُوهُۚ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ وَكِيلٞ
Wannan Shi ne Allah Ubangijinku; ba wani abin bautawa da gaskiya sai Shi; Mahaliccin komai, don haka ku bauta masa. Kuma Shi Mai kiyayewa ne da komai
ٱتَّبِعۡ مَآ أُوحِيَ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَۖ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ وَأَعۡرِضۡ عَنِ ٱلۡمُشۡرِكِينَ
Ka bi abin da aka yi maka wahayi daga Ubangijinka; ba abin bautawa da gaskiya sai Shi; kuma ka kawar da kai daga mushrikai
ٱتَّخَذُوٓاْ أَحۡبَارَهُمۡ وَرُهۡبَٰنَهُمۡ أَرۡبَابٗا مِّن دُونِ ٱللَّهِ وَٱلۡمَسِيحَ ٱبۡنَ مَرۡيَمَ وَمَآ أُمِرُوٓاْ إِلَّا لِيَعۡبُدُوٓاْ إِلَٰهٗا وَٰحِدٗاۖ لَّآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۚ سُبۡحَٰنَهُۥ عَمَّا يُشۡرِكُونَ
Sun xauki malamansu da masu ibadarsu da kuma Almasihu xan Maryamu iyayen giji maimakon Allah[1], alhali kuwa ba abin da aka umarce su sai su bauta wa Abin bauta Xaya, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi. Ya tsarkaka daga abin da suke tara Shi da shi
1- Watau suna yi wa malamansu da masu bauta a cikinsu makauniyar biyayya, suna haramta musu halal, su kuma halatta musu haram. Nasara sun xauki Annabi Isa () abin bauta ba Allah ba.
فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَقُلۡ حَسۡبِيَ ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ عَلَيۡهِ تَوَكَّلۡتُۖ وَهُوَ رَبُّ ٱلۡعَرۡشِ ٱلۡعَظِيمِ
To idan sun ba da baya sai ka ce: “Allah Ya ishe ni, babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi, a gare Shi kaxai na dogara; kuma Shi ne Ubangijin Al’arshi mai girma.”
فَإِلَّمۡ يَسۡتَجِيبُواْ لَكُمۡ فَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّمَآ أُنزِلَ بِعِلۡمِ ٱللَّهِ وَأَن لَّآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ فَهَلۡ أَنتُم مُّسۡلِمُونَ
To idan ba su amsa muku ba, to ku tabbatar cewa lalle an saukar da shi ne (Alqur’ani) da sanin Allah, kuma babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi, To shin yanzu za ku miqa wuya?
هَٰذَا بَلَٰغٞ لِّلنَّاسِ وَلِيُنذَرُواْ بِهِۦ وَلِيَعۡلَمُوٓاْ أَنَّمَا هُوَ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞ وَلِيَذَّكَّرَ أُوْلُواْ ٱلۡأَلۡبَٰبِ
Wannan (Alqur’ani) saqo ne ga mutane don kuma a gargaxe su da shi, kuma su san cewa Shi Allah Xaya ne, don kuma ma’abota hankali su wa’azantu
يُنَزِّلُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةَ بِٱلرُّوحِ مِنۡ أَمۡرِهِۦ عَلَىٰ مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦٓ أَنۡ أَنذِرُوٓاْ أَنَّهُۥ لَآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنَا۠ فَٱتَّقُونِ
Yana saukar da mala’iku da wahayi na umarninsa ga waxanda Ya ga dama daga bayinsa da cewa,: “Ku yi gargaxi cewa,, lalle ba wani abin bauta sai Ni, to sai ku kiyaye dokokina.”
إِلَٰهُكُمۡ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۚ فَٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ قُلُوبُهُم مُّنكِرَةٞ وَهُم مُّسۡتَكۡبِرُونَ
Abin bautarku Abin bauta ne Xaya, sai dai waxanda ba sa yin imani da ranar lahira zukatansu masu musun hakan ne, kuma su masu girman kai ne
۞وَقَالَ ٱللَّهُ لَا تَتَّخِذُوٓاْ إِلَٰهَيۡنِ ٱثۡنَيۡنِۖ إِنَّمَا هُوَ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞ فَإِيَّـٰيَ فَٱرۡهَبُونِ
Allah kuma Ya ce: “Kada ku riqi abubuwan bauta guda biyu[1]. Abin bauta Xaya Yake Tilo; to sai ku ji tsoro na Ni kaxai.”
1- Watau kamar Majusawa masu cewa, wai akwai ubangijin alheri shi ne haske, akwai kuma na sharri shi ne duhu.
لَّا تَجۡعَلۡ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ فَتَقۡعُدَ مَذۡمُومٗا مَّخۡذُولٗا
Kada ka haxa wani abin bauta daban tare da Allah, sai ka zama abin zargi tavavve
ذَٰلِكَ مِمَّآ أَوۡحَىٰٓ إِلَيۡكَ رَبُّكَ مِنَ ٱلۡحِكۡمَةِۗ وَلَا تَجۡعَلۡ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ فَتُلۡقَىٰ فِي جَهَنَّمَ مَلُومٗا مَّدۡحُورًا
Wannan yana daga cikin abin da Ubangijinka Ya yiwo maka wahayi da shi na hikima. Kada kuma ka sanya wani abin bauta tare da Allah, sai a jefa ka a cikin Jahannama kana abin zargi, korarre (daga rahama)
قُل لَّوۡ كَانَ مَعَهُۥٓ ءَالِهَةٞ كَمَا يَقُولُونَ إِذٗا لَّٱبۡتَغَوۡاْ إِلَىٰ ذِي ٱلۡعَرۡشِ سَبِيلٗا
Ka ce (da su): “Da dai akwai wasu alloli tare da shi (Allah), kamar yadda suke da’awa, to kuwa da sun nemi hanyar (yin hamayya) da Mai Al’arshi (watau Allah)[1].”
1- A wata fassarar: Da su ma sun riqa neman kusanci ne ga Allah ta hanyar yi masa xa’a da bauta masa.
قُلۡ إِنَّمَآ أَنَا۠ بَشَرٞ مِّثۡلُكُمۡ يُوحَىٰٓ إِلَيَّ أَنَّمَآ إِلَٰهُكُمۡ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۖ فَمَن كَانَ يَرۡجُواْ لِقَآءَ رَبِّهِۦ فَلۡيَعۡمَلۡ عَمَلٗا صَٰلِحٗا وَلَا يُشۡرِكۡ بِعِبَادَةِ رَبِّهِۦٓ أَحَدَۢا
Ka ce: “Ni dai mutum ne kawai kamarku da ake yi mini wahayi cewa abin bautarku abin bauta ne Xaya; don haka wanda ya kasance yana tsoron gamuwa da Ubangijinsa, to sai ya yi aiki nagari, kada kuma ya tara wani cikin bautar Ubangijinsa.”
مَا كَانَ لِلَّهِ أَن يَتَّخِذَ مِن وَلَدٖۖ سُبۡحَٰنَهُۥٓۚ إِذَا قَضَىٰٓ أَمۡرٗا فَإِنَّمَا يَقُولُ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ
Ba zai yiwu a ce Allah yana da xa ba; tsarki ya tabbata a gare Shi. Idan Ya nufi zartar da wani lamari sai kawai Ya ce masa: “Kasance”, sai ko ya kasance
ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ لَهُ ٱلۡأَسۡمَآءُ ٱلۡحُسۡنَىٰ
Allah (Shi ne wanda) babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi; Yana da sunaye mafiya kyau
إِنَّنِيٓ أَنَا ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنَا۠ فَٱعۡبُدۡنِي وَأَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ لِذِكۡرِيٓ
“Lalle Ni, Ni ne Allah, babu wani abin bauta sai Ni, to ka bauta mini, kuma ka tsai da salla don tuna Ni
إِنَّمَآ إِلَٰهُكُمُ ٱللَّهُ ٱلَّذِي لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۚ وَسِعَ كُلَّ شَيۡءٍ عِلۡمٗا
Abin bautarku kawai shi ne Allah wanda babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi. Ya yalwaci komai da iliminsa
لَوۡ كَانَ فِيهِمَآ ءَالِهَةٌ إِلَّا ٱللَّهُ لَفَسَدَتَاۚ فَسُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ رَبِّ ٱلۡعَرۡشِ عَمَّا يَصِفُونَ
Da ya zamana akwai wasu ababen bauta ba Allah ba a cikinsu (wato sammai da qasa), to da sun lalace. Sai dai tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin Al’arshi game da abin da suke siffata (Shi da shi)
أَمِ ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِهِۦٓ ءَالِهَةٗۖ قُلۡ هَاتُواْ بُرۡهَٰنَكُمۡۖ هَٰذَا ذِكۡرُ مَن مَّعِيَ وَذِكۡرُ مَن قَبۡلِيۚ بَلۡ أَكۡثَرُهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ ٱلۡحَقَّۖ فَهُم مُّعۡرِضُونَ
Ko kuma sun riqi wasu ababen bauta ne ba Shi ba? Ka ce (da su): “To ku kawo dalilinku (a kan haka). Ga wa’azin waxanda suke tare dani (watau Alqur’ani), ga kuma wa’azin waxanda suka gabace ni (watau littattafan annabawa sai ku duba).” A’a, yawancinsu dai ba sa sanin gaskiya sannan kuma masu bijire (mata) ne
وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ مِن رَّسُولٍ إِلَّا نُوحِيٓ إِلَيۡهِ أَنَّهُۥ لَآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنَا۠ فَٱعۡبُدُونِ
Kuma ba wani manzo da Muka aiko gabaninka face sai Mun yi masa wahayi cewa, babu wani abin bauta da gaskiya sai Ni; to sai ku bauta min[1]
1- Duk manzannin da Allah ya aiko sun zo ne da saqon a bauta wa Allah shi kaxai ba tare da shirka ba.
۞وَمَن يَقُلۡ مِنۡهُمۡ إِنِّيٓ إِلَٰهٞ مِّن دُونِهِۦ فَذَٰلِكَ نَجۡزِيهِ جَهَنَّمَۚ كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلظَّـٰلِمِينَ
Daga cikinsu kuwa duk wanda ya ce: “Ni abin bauta ne ba shi (Allah) ba,” to wannan za Mu saka masa da (wutar) Jahannama. Kamar haka kuwa Muke saka wa azzalumai
قُلۡ إِنَّمَا يُوحَىٰٓ إِلَيَّ أَنَّمَآ إِلَٰهُكُمۡ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۖ فَهَلۡ أَنتُم مُّسۡلِمُونَ
Ka ce (da su): “Abin da kawai ake yiwo min wahayinsa (shi ne) lallai abin bautar ku Allah ne Guda Xaya; to shin ko za ku miqa wuya?”