وَإِلَىٰ ثَمُودَ أَخَاهُمۡ صَٰلِحٗاۚ قَالَ يَٰقَوۡمِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرُهُۥۖ قَدۡ جَآءَتۡكُم بَيِّنَةٞ مِّن رَّبِّكُمۡۖ هَٰذِهِۦ نَاقَةُ ٱللَّهِ لَكُمۡ ءَايَةٗۖ فَذَرُوهَا تَأۡكُلۡ فِيٓ أَرۡضِ ٱللَّهِۖ وَلَا تَمَسُّوهَا بِسُوٓءٖ فَيَأۡخُذَكُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ
Zuwa ga Samudawa kuwa Mun aika xan’uwansu Salihu. Ya ce: “Ya ku mutanena, ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi; haqiqa hujja ta zo muku daga Ubangijinku. Wannan kuma taguwar Allah aya ce a gare ku; don haka ku qyale ta ta ci a bayan qasar Allah; kuma kar ku tava ta da wani mugun abu, sai wata azaba mai raxaxi ta shafe ku
وَٱذۡكُرُوٓاْ إِذۡ جَعَلَكُمۡ خُلَفَآءَ مِنۢ بَعۡدِ عَادٖ وَبَوَّأَكُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ تَتَّخِذُونَ مِن سُهُولِهَا قُصُورٗا وَتَنۡحِتُونَ ٱلۡجِبَالَ بُيُوتٗاۖ فَٱذۡكُرُوٓاْ ءَالَآءَ ٱللَّهِ وَلَا تَعۡثَوۡاْ فِي ٱلۡأَرۡضِ مُفۡسِدِينَ
“Kuma ku tuna lokacin da Ya sanya ku kuka zama masu maye gurbi bayan Adawa, kuma Ya zaunar da ku a bayan qasa, kuna yin benaye a wurarenta masu taushi, kuma kuna sassaqa gidaje a duwatsu; don haka ku tuna ni’imomin Allah, kada kuma ku yi varna a bayan qasa.”
قَالَ ٱلۡمَلَأُ ٱلَّذِينَ ٱسۡتَكۡبَرُواْ مِن قَوۡمِهِۦ لِلَّذِينَ ٱسۡتُضۡعِفُواْ لِمَنۡ ءَامَنَ مِنۡهُمۡ أَتَعۡلَمُونَ أَنَّ صَٰلِحٗا مُّرۡسَلٞ مِّن رَّبِّهِۦۚ قَالُوٓاْ إِنَّا بِمَآ أُرۡسِلَ بِهِۦ مُؤۡمِنُونَ
Manyan gari waxanda suka yi girman kai daga mutanensa, suka ce wa waxanda suke raunana waxanda suka yi imani daga cikinsu: “Yanzu kun san cewa Salihu Manzo ne daga wajen Ubangijinsa?” Sai suka ce; “Lalle mu dai mun yi imani da abin da aka aiko shi da shi.”
قَالَ ٱلَّذِينَ ٱسۡتَكۡبَرُوٓاْ إِنَّا بِٱلَّذِيٓ ءَامَنتُم بِهِۦ كَٰفِرُونَ
Waxanda suka yi girman kai suka ce: “Lalle mu kuma mun kafirce wa abin da kuka yi imani da shi.”
فَعَقَرُواْ ٱلنَّاقَةَ وَعَتَوۡاْ عَنۡ أَمۡرِ رَبِّهِمۡ وَقَالُواْ يَٰصَٰلِحُ ٱئۡتِنَا بِمَا تَعِدُنَآ إِن كُنتَ مِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Sai suka soke taguwar, suka kuma yi tsaurin kai game da umarnin Ubangijinsu, kuma suka ce: “Ya Salihu, ka zo mana da abin da kake mana alqawarin zai same mu (na azaba) in ka kasance cikin manzanni.”
فَأَخَذَتۡهُمُ ٱلرَّجۡفَةُ فَأَصۡبَحُواْ فِي دَارِهِمۡ جَٰثِمِينَ
Sai wata girgizar qasa mai tsanani ta auka musu, sai suka wayi gari a gurfane kan gwiwoyinsu, (matattu) a cikin gidajensu
فَتَوَلَّىٰ عَنۡهُمۡ وَقَالَ يَٰقَوۡمِ لَقَدۡ أَبۡلَغۡتُكُمۡ رِسَالَةَ رَبِّي وَنَصَحۡتُ لَكُمۡ وَلَٰكِن لَّا تُحِبُّونَ ٱلنَّـٰصِحِينَ
Sai ya juya ya rabu da su, kuma ya ce: “Ya ku mutanena, lalle haqiqa na isar muku da saqon Ubangijina, kuma na yi muku nasiha, sai dai ku ba kwa son masu nasiha.”
أَلَمۡ يَأۡتِهِمۡ نَبَأُ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ قَوۡمِ نُوحٖ وَعَادٖ وَثَمُودَ وَقَوۡمِ إِبۡرَٰهِيمَ وَأَصۡحَٰبِ مَدۡيَنَ وَٱلۡمُؤۡتَفِكَٰتِۚ أَتَتۡهُمۡ رُسُلُهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِۖ فَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيَظۡلِمَهُمۡ وَلَٰكِن كَانُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ يَظۡلِمُونَ
Yanzu labarin waxanda suke gabaninsu bai zo musu ba: Mutanen (Annabi) Nuhu da Adawa da Samudawa, da mutanen (Annabi) Ibrahimu da kuma mutanen Madyana da waxanda aka kifar (watau mutanen Annabi Luxu)? Manzanninsu sun zo musu da (ayoyi) mabayyana; ba kuma zai zamana Allah Ya zalunce su ba sai dai kawunansu ne kawai suke zalunta
۞وَإِلَىٰ ثَمُودَ أَخَاهُمۡ صَٰلِحٗاۚ قَالَ يَٰقَوۡمِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرُهُۥۖ هُوَ أَنشَأَكُم مِّنَ ٱلۡأَرۡضِ وَٱسۡتَعۡمَرَكُمۡ فِيهَا فَٱسۡتَغۡفِرُوهُ ثُمَّ تُوبُوٓاْ إِلَيۡهِۚ إِنَّ رَبِّي قَرِيبٞ مُّجِيبٞ
Haka kuma Muka aiko wa Samudawa xan’uwansu Salihu. Ya ce: “Ya ku mutanena, ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bauta ba shi ba; Shi ne Ya halicce ku daga qasa, Ya kuma ba ku damar ku raya ta; to ku nemi gafararsa sannan ku tuba gare Shi. Lalle Ubangijina Makusanci ne, Mai amsawa.”
قَالُواْ يَٰصَٰلِحُ قَدۡ كُنتَ فِينَا مَرۡجُوّٗا قَبۡلَ هَٰذَآۖ أَتَنۡهَىٰنَآ أَن نَّعۡبُدَ مَا يَعۡبُدُ ءَابَآؤُنَا وَإِنَّنَا لَفِي شَكّٖ مِّمَّا تَدۡعُونَآ إِلَيۡهِ مُرِيبٖ
Suka ce: “Ya Salihu, haqiqa a da ka kasance a cikinmu abin yi wa (kyakkyawan) fata kafin (ka zo mana da) wannan; yanzu ka riqa hana mu mu bauta wa abin da iyayenmu suke bauta wa? Lalle mu kam tabbas muna matuqar shakka game da abin da kake kiran mu gare shi.”
قَالَ يَٰقَوۡمِ أَرَءَيۡتُمۡ إِن كُنتُ عَلَىٰ بَيِّنَةٖ مِّن رَّبِّي وَءَاتَىٰنِي مِنۡهُ رَحۡمَةٗ فَمَن يَنصُرُنِي مِنَ ٱللَّهِ إِنۡ عَصَيۡتُهُۥۖ فَمَا تَزِيدُونَنِي غَيۡرَ تَخۡسِيرٖ
Ya ce: “Ya ku mutanena, ku ba ni labari, yanzu idan na kasance a kan bayyananniyar hujja daga Ubangijina, Ya kuma ba ni rahama (ta annabci) to wa zai kare ni daga (azabar) Allah idan na sava masa? Don haka babu abin da za ku qare ni da shi in ban da tavewa.”
وَيَٰقَوۡمِ هَٰذِهِۦ نَاقَةُ ٱللَّهِ لَكُمۡ ءَايَةٗۖ فَذَرُوهَا تَأۡكُلۡ فِيٓ أَرۡضِ ٱللَّهِۖ وَلَا تَمَسُّوهَا بِسُوٓءٖ فَيَأۡخُذَكُمۡ عَذَابٞ قَرِيبٞ
“Kuma ya ku mutanena, wannan fa taguwar Allah ce a gare ku, sai ku bar ta ta ci a qasar Allah, kada ku cutar da ita, sai azaba ta kusa-kusa ta afka muku.”
فَعَقَرُوهَا فَقَالَ تَمَتَّعُواْ فِي دَارِكُمۡ ثَلَٰثَةَ أَيَّامٖۖ ذَٰلِكَ وَعۡدٌ غَيۡرُ مَكۡذُوبٖ
Amma sai suka soke ta, sai ya ce (da su): “Ku ji daxi cikin gidajenku kwana uku (rak). Wannan alqawari ne ba abin qaryatawa ba.”
فَلَمَّا جَآءَ أَمۡرُنَا نَجَّيۡنَا صَٰلِحٗا وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُۥ بِرَحۡمَةٖ مِّنَّا وَمِنۡ خِزۡيِ يَوۡمِئِذٍۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ ٱلۡقَوِيُّ ٱلۡعَزِيزُ
To lokacin da umarninmu ya zo sai Muka tserar da Salihu shi da waxanda suka yi imani tare da shi saboda wata rahama daga gare mu, kuma (Muka tserar da su) daga kunyatar wannan rana. Lalle Ubangijinka Shi ne Mai qarfi Mabuwayi
وَأَخَذَ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ ٱلصَّيۡحَةُ فَأَصۡبَحُواْ فِي دِيَٰرِهِمۡ جَٰثِمِينَ
Kuma tsawa ta kama waxanda suka yi zalunci, sai suka wayi gari cikin gidajensu a duddurqushe (babu rai)
كَأَن لَّمۡ يَغۡنَوۡاْ فِيهَآۗ أَلَآ إِنَّ ثَمُودَاْ كَفَرُواْ رَبَّهُمۡۗ أَلَا بُعۡدٗا لِّثَمُودَ
Kamar daxai ba su tava zama a cikinsu ba (gidajen). Ku saurara! Lalle Samudawa kam sun kafirce wa Ubangijinsu. Ku saurara! Halaka ta tabbata ga Samudawa
كَأَن لَّمۡ يَغۡنَوۡاْ فِيهَآۗ أَلَا بُعۡدٗا لِّمَدۡيَنَ كَمَا بَعِدَتۡ ثَمُودُ
Kamar daxai ba su tava zama ba a cikinsu (gidajen) ba. Ku saurara; halaka ta tabbata ga (mutanen) Madyana kamar yadda Samudawa suka halaka
وَلَقَدۡ كَذَّبَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡحِجۡرِ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Haqiqa kuma mutanen Hijiru (Samudawa) sun qaryata manzanni
وَءَاتَيۡنَٰهُمۡ ءَايَٰتِنَا فَكَانُواْ عَنۡهَا مُعۡرِضِينَ
Muka kuma kawo musu ayoyinmu, sai suka zamanto masu bijirewa daga gare su
وَكَانُواْ يَنۡحِتُونَ مِنَ ٱلۡجِبَالِ بُيُوتًا ءَامِنِينَ
Sun zamanto suna fafe duwatsu suna yin gidaje su zama cikin aminci
فَأَخَذَتۡهُمُ ٱلصَّيۡحَةُ مُصۡبِحِينَ
Sai tsawa ta auka musu da asuba
فَمَآ أَغۡنَىٰ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ
Sai abin da suka zamanto suna aikatawa bai amfane su ba
وَمَا مَنَعَنَآ أَن نُّرۡسِلَ بِٱلۡأٓيَٰتِ إِلَّآ أَن كَذَّبَ بِهَا ٱلۡأَوَّلُونَۚ وَءَاتَيۡنَا ثَمُودَ ٱلنَّاقَةَ مُبۡصِرَةٗ فَظَلَمُواْ بِهَاۚ وَمَا نُرۡسِلُ بِٱلۡأٓيَٰتِ إِلَّا تَخۡوِيفٗا
Kuma ba abin da ya hana Mu aiko da ayoyi sai don (al’ummu) na farko sun qaryata su; Muka kuma bai wa Samudawa taguwa (don ta zama aya) bayyananniya, sai suka butulce mata. Ba Ma kuwa aiko da ayoyi sai don tsoratarwa
وَإِن يُكَذِّبُوكَ فَقَدۡ كَذَّبَتۡ قَبۡلَهُمۡ قَوۡمُ نُوحٖ وَعَادٞ وَثَمُودُ
Idan kuwa suka qaryata ka, to haqiqa mutanen Nuhu da Adawa da Samudawa sun qaryata (manzanni) kafin su
وَعَادٗا وَثَمُودَاْ وَأَصۡحَٰبَ ٱلرَّسِّ وَقُرُونَۢا بَيۡنَ ذَٰلِكَ كَثِيرٗا
Kuma (Muka hallakar da) Adawa da Samudawa da kuma mutanen (rijiyar) Rassu, da kuma wasu al’ummu masu yawa tsakanin hakan
كَذَّبَتۡ ثَمُودُ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Samudawa sun qaryata manzanni[1]
1- Domin qaryata Annabi Salihu () daidai yake da qaryata duk manzannin Allah, saboda saqo iri xaya suke xauke da shi.
إِذۡ قَالَ لَهُمۡ أَخُوهُمۡ صَٰلِحٌ أَلَا تَتَّقُونَ
Lokacin da xan’uwansu Salihu ya ce da su: “Yanzu ba kwa yi taqawa ba?
إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٞ
“Lalle ni Manzo ne amintacce gare ku
فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
“To ku kiyaye dokokin Allah kuma ku bi ni
وَمَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
“Kuma ba na tambayar ku wani lada game da shi (isar da manzancin); ladana yana wajen Ubangijin talikai kawai