Capítulo: Suratu Maryam

Verso : 65

رَّبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَا فَٱعۡبُدۡهُ وَٱصۡطَبِرۡ لِعِبَٰدَتِهِۦۚ هَلۡ تَعۡلَمُ لَهُۥ سَمِيّٗا

“(Shi ne) Ubangijin sammai da qasa da kuma abin da yake tsakaninsu, sai ka bauta masa kuma ka yi haquri ga bautarsa. Shin ka san wani tamkarsa?”



Capítulo: Suratu Xa Ha

Verso : 14

إِنَّنِيٓ أَنَا ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنَا۠ فَٱعۡبُدۡنِي وَأَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ لِذِكۡرِيٓ

“Lalle Ni, Ni ne Allah, babu wani abin bauta sai Ni, to ka bauta mini, kuma ka tsai da salla don tuna Ni



Capítulo: Suratul Anbiya

Verso : 25

وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ مِن رَّسُولٍ إِلَّا نُوحِيٓ إِلَيۡهِ أَنَّهُۥ لَآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنَا۠ فَٱعۡبُدُونِ

Kuma ba wani manzo da Muka aiko gabaninka face sai Mun yi masa wahayi cewa, babu wani abin bauta da gaskiya sai Ni; to sai ku bauta min[1]


1- Duk manzannin da Allah ya aiko sun zo ne da saqon a bauta wa Allah shi kaxai ba tare da shirka ba.


Capítulo: Suratul Anbiya

Verso : 92

إِنَّ هَٰذِهِۦٓ أُمَّتُكُمۡ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ وَأَنَا۠ رَبُّكُمۡ فَٱعۡبُدُونِ

Lallai wannan addini naku guda xaya ne (wato Musulunci), kuma Ni ne Ubangijinku, to ku bauta min



Capítulo: Suratul Hajji

Verso : 77

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱرۡكَعُواْ وَٱسۡجُدُواْۤ وَٱعۡبُدُواْ رَبَّكُمۡ وَٱفۡعَلُواْ ٱلۡخَيۡرَ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ۩

Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi ruku’i kuma ku yi sujjada, ku kuma bauta wa Ubangijinku, kuma ku aikata alheri don ku rabauta



Capítulo: Suratul Mu’uminun

Verso : 23

وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوۡمِهِۦ فَقَالَ يَٰقَوۡمِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرُهُۥٓۚ أَفَلَا تَتَّقُونَ

Haqiqa kuma Mun aiko Nuhu zuwa ga mutanensa, sai ya ce: “Ya ku mutanena, ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bauta in ba Shi ba; me ya sa ne ba za ku yi taqawa ba.”



Capítulo: Suratul Mu’uminun

Verso : 32

فَأَرۡسَلۡنَا فِيهِمۡ رَسُولٗا مِّنۡهُمۡ أَنِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرُهُۥٓۚ أَفَلَا تَتَّقُونَ

Sai Muka aiko musu wani manzon daga cikinsu da cewa: “Ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bauta in ba Shi ba; me ya sa ne ba za ku yi taqawa ba?”



Capítulo: Suratun Nur

Verso : 55

وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مِنكُمۡ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ لَيَسۡتَخۡلِفَنَّهُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ كَمَا ٱسۡتَخۡلَفَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ وَلَيُمَكِّنَنَّ لَهُمۡ دِينَهُمُ ٱلَّذِي ٱرۡتَضَىٰ لَهُمۡ وَلَيُبَدِّلَنَّهُم مِّنۢ بَعۡدِ خَوۡفِهِمۡ أَمۡنٗاۚ يَعۡبُدُونَنِي لَا يُشۡرِكُونَ بِي شَيۡـٔٗاۚ وَمَن كَفَرَ بَعۡدَ ذَٰلِكَ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡفَٰسِقُونَ

Allah kuwa Ya yi wa waxanda suka yi imani daga cikinku suka kuma yi aiki na gari alqawarin lalle zai sanya su halifofi a bayan qasa kamar yadda Ya sanya waxanda suke gabaninsu halifofi, kuma lalle zai tabbatar musu da addininsu wanda Ya yardar musu, tabbas kuma zai dawo musu da zaman lafiya bayan zamantowarsu cikin tsoro. Su bauta mini, ba sa yin shirkar komai da Ni. Wanda kuwa ya kafirta bayan wannan, to waxannan su ne fasiqai



Capítulo: Suratun Namli

Verso : 45

وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَآ إِلَىٰ ثَمُودَ أَخَاهُمۡ صَٰلِحًا أَنِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ فَإِذَا هُمۡ فَرِيقَانِ يَخۡتَصِمُونَ

Haqiqa kuma Mun aiko wa Samudawa xan’uwansu Salihu da cewa: “Ku bauta wa Allah,” sai ga su sun rabu qungiyoyi biyu[1] suna jayayya


1- Watau qungiya ta farko su ne waxanda suka yi imani da Annabi Salihu, qungiya ta biyu su ne waxanda suka kafirce masa.


Capítulo: Suratun Namli

Verso : 91

إِنَّمَآ أُمِرۡتُ أَنۡ أَعۡبُدَ رَبَّ هَٰذِهِ ٱلۡبَلۡدَةِ ٱلَّذِي حَرَّمَهَا وَلَهُۥ كُلُّ شَيۡءٖۖ وَأُمِرۡتُ أَنۡ أَكُونَ مِنَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ

(Ka ce da su): “Ni dai an umarce ni ne kawai da in bauta wa Ubangijin wannan garin (Makka) wanda Ya mayar da shi mai alfarma, kuma komai nasa ne; kuma an umarce ni da in zama cikin Musulmi



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 16

وَإِبۡرَٰهِيمَ إِذۡ قَالَ لِقَوۡمِهِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ وَٱتَّقُوهُۖ ذَٰلِكُمۡ خَيۡرٞ لَّكُمۡ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ

Kuma (ka tuna) Ibrahimu lokacin da ya ce da mutanensa: “Ku bauta wa Allah, kuma ku kiyaye dokokinsa, wannan shi ya fi muku alheri in kun kasance kun san (haka)



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 17

إِنَّمَا تَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَوۡثَٰنٗا وَتَخۡلُقُونَ إِفۡكًاۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ تَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ لَا يَمۡلِكُونَ لَكُمۡ رِزۡقٗا فَٱبۡتَغُواْ عِندَ ٱللَّهِ ٱلرِّزۡقَ وَٱعۡبُدُوهُ وَٱشۡكُرُواْ لَهُۥٓۖ إِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ

Lalle abin da kuke bauta wa ba Allah ba gumaka ne kawai, kuna kuma qirqirar qarya ne[1]. Lalle waxanda kuke bauta wa ba Allah ba, ba su mallaki wani arziki ba gare ku, sai ku nemi arziki a wurin Allah, kuma ku bauta masa, ku kuma gode masa; gare Shi ne kawai za a mayar da ku


1- Domin su ne suke sassaqa su da hannayensu suke kuma sanya musu sunaye sannan su bauta musu.


Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 36

وَإِلَىٰ مَدۡيَنَ أَخَاهُمۡ شُعَيۡبٗا فَقَالَ يَٰقَوۡمِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ وَٱرۡجُواْ ٱلۡيَوۡمَ ٱلۡأٓخِرَ وَلَا تَعۡثَوۡاْ فِي ٱلۡأَرۡضِ مُفۡسِدِينَ

Mun kuma (aika wa mutanen) Madyana xan’uwansu Shu’aibu, sai ya ce: “Ya ku mutanena, ku bauta wa Allah, kuma ku yi fatan (kyakkyawan samakon) ranar lahira, kada kuma ku riqa yaxa varna a bayan qasa.”



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 56

يَٰعِبَادِيَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِنَّ أَرۡضِي وَٰسِعَةٞ فَإِيَّـٰيَ فَٱعۡبُدُونِ

Ya ku bayina waxanda suka yi imani, lalle qasata yalwatacciya ce, to Ni kaxai sai ku bauta Mini



Capítulo: Suratus Sajda

Verso : 15

إِنَّمَا يُؤۡمِنُ بِـَٔايَٰتِنَا ٱلَّذِينَ إِذَا ذُكِّرُواْ بِهَا خَرُّواْۤ سُجَّدٗاۤ وَسَبَّحُواْ بِحَمۡدِ رَبِّهِمۡ وَهُمۡ لَا يَسۡتَكۡبِرُونَ۩

Lalle kawai masu imani da ayoyinmu su ne waxanda idan aka yi musu wa’azi da su za su faxi suna masu sujjada su kuma yi tasbihi tare da yabon Ubangijinsu, kuma su ba sa yin girman kai



Capítulo: Suratu Yasin

Verso : 61

وَأَنِ ٱعۡبُدُونِيۚ هَٰذَا صِرَٰطٞ مُّسۡتَقِيمٞ

Kuma ku bauta min. Wannan shi ne tafarki madaidaici



Capítulo: Suratuz Zumar

Verso : 2

إِنَّآ أَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ فَٱعۡبُدِ ٱللَّهَ مُخۡلِصٗا لَّهُ ٱلدِّينَ

Lalle Mu Muka saukar maka Littafi da gaskiya, to ka bauta wa Allah kana mai tsantsanta addini a gare Shi



Capítulo: Suratuz Zumar

Verso : 9

أَمَّنۡ هُوَ قَٰنِتٌ ءَانَآءَ ٱلَّيۡلِ سَاجِدٗا وَقَآئِمٗا يَحۡذَرُ ٱلۡأٓخِرَةَ وَيَرۡجُواْ رَحۡمَةَ رَبِّهِۦۗ قُلۡ هَلۡ يَسۡتَوِي ٱلَّذِينَ يَعۡلَمُونَ وَٱلَّذِينَ لَا يَعۡلَمُونَۗ إِنَّمَا يَتَذَكَّرُ أُوْلُواْ ٱلۡأَلۡبَٰبِ

Shin yanzu wanda yake shi mai ibada ne a cikin sa’o’in dare, yana sujjada yana kuma tsayawa, yana tsoron ranar lahira yana kuma qaunar rahamar Ubangijinsa (zai yi daidai da wanda ba haka yake ba?) Ka ce: “Yanzu waxanda suke da sani za su yi daidai da waxanda ba su da sani? Ma’abota hankula ne kawai suke wa’azantuwa



Capítulo: Suratuz Zumar

Verso : 11

قُلۡ إِنِّيٓ أُمِرۡتُ أَنۡ أَعۡبُدَ ٱللَّهَ مُخۡلِصٗا لَّهُ ٱلدِّينَ

Ka ce: “Lalle ni an umarce ni da in bauta wa Allah ina mai tsantsanta addini gare Shi



Capítulo: Suratuz Zumar

Verso : 14

قُلِ ٱللَّهَ أَعۡبُدُ مُخۡلِصٗا لَّهُۥ دِينِي

Ka ce: “Allah kawai nake bauta wa, ina mai tsantsanta addinina gare Shi



Capítulo: Suratuz Zumar

Verso : 64

قُلۡ أَفَغَيۡرَ ٱللَّهِ تَأۡمُرُوٓنِّيٓ أَعۡبُدُ أَيُّهَا ٱلۡجَٰهِلُونَ

Ka ce: “Yanzu wanin Allah kuke umarta ta da in bauta wa, ya ku waxannan wawaye?”



Capítulo: Suratuz Zumar

Verso : 65

وَلَقَدۡ أُوحِيَ إِلَيۡكَ وَإِلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكَ لَئِنۡ أَشۡرَكۡتَ لَيَحۡبَطَنَّ عَمَلُكَ وَلَتَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ

Haqiqa kuma an yi maka wahayi kai da waxanda suka gabace ka cewa: “Tabbas idan ka yi shirka lallai aikinka zai vaci, kuma tabbas za ka kasance daga asararru.”



Capítulo: Suratuz Zumar

Verso : 66

بَلِ ٱللَّهَ فَٱعۡبُدۡ وَكُن مِّنَ ٱلشَّـٰكِرِينَ

A’a, Allah kaxai za ka bauta wa, ka kuma kasance daga masu godiya



Capítulo: Suratu Ghafir

Verso : 66

۞قُلۡ إِنِّي نُهِيتُ أَنۡ أَعۡبُدَ ٱلَّذِينَ تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ لَمَّا جَآءَنِيَ ٱلۡبَيِّنَٰتُ مِن رَّبِّي وَأُمِرۡتُ أَنۡ أُسۡلِمَ لِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Ka ce: “Lalle ni an hana ni in bauta wa waxanda kuke bauta wa ba Allah ba a yayin da (ayoyi) bayyanannu suka zo min daga Ubangijina, an kuma umarce ni da in miqa wuya ga Ubangijin talikai



Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 37

وَمِنۡ ءَايَٰتِهِ ٱلَّيۡلُ وَٱلنَّهَارُ وَٱلشَّمۡسُ وَٱلۡقَمَرُۚ لَا تَسۡجُدُواْ لِلشَّمۡسِ وَلَا لِلۡقَمَرِ وَٱسۡجُدُواْۤ لِلَّهِۤ ٱلَّذِي خَلَقَهُنَّ إِن كُنتُمۡ إِيَّاهُ تَعۡبُدُونَ

Kuma dare da wuni da rana da wata suna daga ayoyinsa. Kada ku yi sujjada ga rana ko ga wata, ku yi sujjada ga Allah Wanda Ya halicce su idan har kun kasance Shi kaxai kuke bauta wa



Capítulo: Suratuz Zukhruf 

Verso : 64

إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ رَبِّي وَرَبُّكُمۡ فَٱعۡبُدُوهُۚ هَٰذَا صِرَٰطٞ مُّسۡتَقِيمٞ

“Lalle Allah Shi ne Ubangijina kuma Ubangijinku, sai ku bauta masa. Wannan ita ce hanya madaidaiciya.”



Capítulo: Suratu Qaf 

Verso : 39

فَٱصۡبِرۡ عَلَىٰ مَا يَقُولُونَ وَسَبِّحۡ بِحَمۡدِ رَبِّكَ قَبۡلَ طُلُوعِ ٱلشَّمۡسِ وَقَبۡلَ ٱلۡغُرُوبِ

To ka yi haquri a kan abin da suke faxa, ka kuma yi tasbihi da yabon Ubangijinka kafin fudowar rana da kuma kafin faxuwarta



Capítulo: Suratu Qaf 

Verso : 40

وَمِنَ ٱلَّيۡلِ فَسَبِّحۡهُ وَأَدۡبَٰرَ ٱلسُّجُودِ

Da daddare kuma sai ka tsarkake shi, da kuma bayan salloli



Capítulo: Suratuz Zariyat

Verso : 56

وَمَا خَلَقۡتُ ٱلۡجِنَّ وَٱلۡإِنسَ إِلَّا لِيَعۡبُدُونِ

Ban halicci aljanu da mutane ba sai don su bauta min



Capítulo: Suratun Najm

Verso : 62

فَٱسۡجُدُواْۤ لِلَّهِۤ وَٱعۡبُدُواْ۩

To ku yi sujjada ga Allah ku kuma bauta (masa)