Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 43

وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ وَٱرۡكَعُواْ مَعَ ٱلرَّـٰكِعِينَ

Kuma ku tsayar da salla, ku kuma ba da zakka, kuma ku yi ruku’i tare da masu ruku’i



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 83

وَإِذۡ أَخَذۡنَا مِيثَٰقَ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ لَا تَعۡبُدُونَ إِلَّا ٱللَّهَ وَبِٱلۡوَٰلِدَيۡنِ إِحۡسَانٗا وَذِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينِ وَقُولُواْ لِلنَّاسِ حُسۡنٗا وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ ثُمَّ تَوَلَّيۡتُمۡ إِلَّا قَلِيلٗا مِّنكُمۡ وَأَنتُم مُّعۡرِضُونَ

Kuma ka tuna lokacin da Muka xauki alqwari daga Banu Isra’ila cewa, ba za ku bauta wa kowa ba sai Allah, kuma za ku kyautata wa iyaye da makusanta da marayu da miskinai, kuma ku riqa yi wa mutane kyakkyawar magana, kuma ku tsai da salla, kuma ku ba da zakka, sannan sai kuka ba da baya sai ‘yan kaxan daga cikinku, alhalin kuna masu bijirewa



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 110

وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَۚ وَمَا تُقَدِّمُواْ لِأَنفُسِكُم مِّنۡ خَيۡرٖ تَجِدُوهُ عِندَ ٱللَّهِۗ إِنَّ ٱللَّهَ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ

Kuma ku tsayar da salla ku kuma ba da zakka; kuma duk abin da kuka aikata na alheri domin kawunanku za ku same shi a wajen Allah. Lalle Allah Mai ganin abin da kuke aikatawa ne



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 12

۞وَلَقَدۡ أَخَذَ ٱللَّهُ مِيثَٰقَ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ وَبَعَثۡنَا مِنۡهُمُ ٱثۡنَيۡ عَشَرَ نَقِيبٗاۖ وَقَالَ ٱللَّهُ إِنِّي مَعَكُمۡۖ لَئِنۡ أَقَمۡتُمُ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَيۡتُمُ ٱلزَّكَوٰةَ وَءَامَنتُم بِرُسُلِي وَعَزَّرۡتُمُوهُمۡ وَأَقۡرَضۡتُمُ ٱللَّهَ قَرۡضًا حَسَنٗا لَّأُكَفِّرَنَّ عَنكُمۡ سَيِّـَٔاتِكُمۡ وَلَأُدۡخِلَنَّكُمۡ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۚ فَمَن كَفَرَ بَعۡدَ ذَٰلِكَ مِنكُمۡ فَقَدۡ ضَلَّ سَوَآءَ ٱلسَّبِيلِ

Kuma lalle haqiqa Allah Ya xauki alqawari (daga) Banu-Isra’ila, kuma Mun aiko musu wakilai goma sha biyu daga cikinsu; kuma Allah Ya ce: “Lalle Ni Ina tare da ku; tabbas idan har kuka tsayar da salla, kuma kuka bayar da zakka, kuma kuka yi imani da manzannina, kuma kuka qarfafe su, kuma kuka bai wa Allah kyakkyawan rance, to lalle zan kankare muku kurakuranku, kuma zan shigar da ku gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu. To duk wanda ya kafirce daga cikinku bayan haka, to haqiqa ya vace wa tafarki madaidaici.”



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 156

۞وَٱكۡتُبۡ لَنَا فِي هَٰذِهِ ٱلدُّنۡيَا حَسَنَةٗ وَفِي ٱلۡأٓخِرَةِ إِنَّا هُدۡنَآ إِلَيۡكَۚ قَالَ عَذَابِيٓ أُصِيبُ بِهِۦ مَنۡ أَشَآءُۖ وَرَحۡمَتِي وَسِعَتۡ كُلَّ شَيۡءٖۚ فَسَأَكۡتُبُهَا لِلَّذِينَ يَتَّقُونَ وَيُؤۡتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَٱلَّذِينَ هُم بِـَٔايَٰتِنَا يُؤۡمِنُونَ

“Kuma Ka rubuta mana kyakkyawan abu a cikin wannan duniyar, haka ma a lahira, lalle mu mun tuba zuwa gare Ka.” (Allah) Ya ce: “Ina saukar da azabata a kan wanda Na ga dama; rahamata kuwa ta yalwaci komai. Don haka da sannu zan rubuta ta ga waxanda suke kiyaye dokokin Allah, kuma suke bayar da zakka da kuma waxanda suke yin imani da ayoyinmu



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 11

فَإِن تَابُواْ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَوُاْ ٱلزَّكَوٰةَ فَإِخۡوَٰنُكُمۡ فِي ٱلدِّينِۗ وَنُفَصِّلُ ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يَعۡلَمُونَ

To idan sun tuba, suka kuma tsayar da salla kuma suka ba da zakka, to sun zama ‘yan’uwanku a cikin addini. Muna kuwa bayanin ayoyi ne filla-filla ga mutane da suke da sani



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 60

۞إِنَّمَا ٱلصَّدَقَٰتُ لِلۡفُقَرَآءِ وَٱلۡمَسَٰكِينِ وَٱلۡعَٰمِلِينَ عَلَيۡهَا وَٱلۡمُؤَلَّفَةِ قُلُوبُهُمۡ وَفِي ٱلرِّقَابِ وَٱلۡغَٰرِمِينَ وَفِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَٱبۡنِ ٱلسَّبِيلِۖ فَرِيضَةٗ مِّنَ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٞ

Dukiyoyin zakka na matalauta ne kaxai da miskinai da ma’aikatanta[1] da waxanda ake lallashin zukatansu da kuma game da ‘yanta bayi da waxanda ake bi bashi da kuma wajen jihadi saboda Allah da matafiyi. Farilla ce daga Allah. Allah kuwa Masani ne, Mai hikima


1- Su ne waxanda aka wakilta wajen karvo ta da kula da ita da rarraba wa mabuqata.


Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 103

خُذۡ مِنۡ أَمۡوَٰلِهِمۡ صَدَقَةٗ تُطَهِّرُهُمۡ وَتُزَكِّيهِم بِهَا وَصَلِّ عَلَيۡهِمۡۖ إِنَّ صَلَوٰتَكَ سَكَنٞ لَّهُمۡۗ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ

Ka karvi sadaka daga dukiyoyinsu da za ka tsarkake su kuma ka gyara musu halaye da ita, ka kuma yi musu addu’a. Lalle addu’arka nutsuwa ce a gare su. Allah kuwa Mai ji ne, Masani



Capítulo: Suratul Hajji

Verso : 78

وَجَٰهِدُواْ فِي ٱللَّهِ حَقَّ جِهَادِهِۦۚ هُوَ ٱجۡتَبَىٰكُمۡ وَمَا جَعَلَ عَلَيۡكُمۡ فِي ٱلدِّينِ مِنۡ حَرَجٖۚ مِّلَّةَ أَبِيكُمۡ إِبۡرَٰهِيمَۚ هُوَ سَمَّىٰكُمُ ٱلۡمُسۡلِمِينَ مِن قَبۡلُ وَفِي هَٰذَا لِيَكُونَ ٱلرَّسُولُ شَهِيدًا عَلَيۡكُمۡ وَتَكُونُواْ شُهَدَآءَ عَلَى ٱلنَّاسِۚ فَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ وَٱعۡتَصِمُواْ بِٱللَّهِ هُوَ مَوۡلَىٰكُمۡۖ فَنِعۡمَ ٱلۡمَوۡلَىٰ وَنِعۡمَ ٱلنَّصِيرُ

Kuma ku yi jihadi wajen (xaukaka addinin) Allah iyakar iyawarku. Shi ne Ya zave ku, bai kuma sanya muku wani qunci ba cikin addini. Addinin Babanku ne Ibrahimu. (Allah) Shi ne Ya kira ku Musulmi tuntuni, da kuma cikin wannan (Alqur’ani) don Manzo ya zama shaida a gare ku, ku kuma ku zama shaida ga (sauran) mutane. To sai ku tsai da salla kuma ku ba da zakka, ku kuma yi riqo da (addinin) Allah, Shi ne Majivincin al’amarinku; to madalla da Majivinci, kuma madalla da Mataimaki



Capítulo: Suratul Mu’uminun

Verso : 4

وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِلزَّكَوٰةِ فَٰعِلُونَ

Kuma waxanda suke masu aiwatar da zakka



Capítulo: Suratun Nur

Verso : 56

وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَ لَعَلَّكُمۡ تُرۡحَمُونَ

Kuma ku tsai da salla ku kuma ba da zakka kuma ku bi Manzo don a ji qan ku



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 39

وَمَآ ءَاتَيۡتُم مِّن رِّبٗا لِّيَرۡبُوَاْ فِيٓ أَمۡوَٰلِ ٱلنَّاسِ فَلَا يَرۡبُواْ عِندَ ٱللَّهِۖ وَمَآ ءَاتَيۡتُم مِّن زَكَوٰةٖ تُرِيدُونَ وَجۡهَ ٱللَّهِ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُضۡعِفُونَ

Kuma abin da kuka bayar na riba don ya qaru a cikin dukiyoyin mutane, to ba ya qaruwa a wurin Allah[1]; abin kuma da kuka bayar na zakka kuna masu nufin Fuskar Allah, to waxannan su ne masu ninninka (ladansu)


1- Da yawa daga cikin malamai sun fassara wannan gavar da cewa, ana nufin wanda zai bayar da kyauta yana nufin a mayar masa da fiye da abin da ya bayar, to ba shi da lada a wurin Allah.


Capítulo: Suratul Muzzammil

Verso : 20

۞إِنَّ رَبَّكَ يَعۡلَمُ أَنَّكَ تَقُومُ أَدۡنَىٰ مِن ثُلُثَيِ ٱلَّيۡلِ وَنِصۡفَهُۥ وَثُلُثَهُۥ وَطَآئِفَةٞ مِّنَ ٱلَّذِينَ مَعَكَۚ وَٱللَّهُ يُقَدِّرُ ٱلَّيۡلَ وَٱلنَّهَارَۚ عَلِمَ أَن لَّن تُحۡصُوهُ فَتَابَ عَلَيۡكُمۡۖ فَٱقۡرَءُواْ مَا تَيَسَّرَ مِنَ ٱلۡقُرۡءَانِۚ عَلِمَ أَن سَيَكُونُ مِنكُم مَّرۡضَىٰ وَءَاخَرُونَ يَضۡرِبُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ يَبۡتَغُونَ مِن فَضۡلِ ٱللَّهِ وَءَاخَرُونَ يُقَٰتِلُونَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۖ فَٱقۡرَءُواْ مَا تَيَسَّرَ مِنۡهُۚ وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ وَأَقۡرِضُواْ ٱللَّهَ قَرۡضًا حَسَنٗاۚ وَمَا تُقَدِّمُواْ لِأَنفُسِكُم مِّنۡ خَيۡرٖ تَجِدُوهُ عِندَ ٱللَّهِ هُوَ خَيۡرٗا وَأَعۡظَمَ أَجۡرٗاۚ وَٱسۡتَغۡفِرُواْ ٱللَّهَۖ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمُۢ

Lalle Ubangijinka Yana sane da cewa kai kana tsayawa qasa da kashi biyu cikin uku na dare, da kuma rabinsa, da kuma xaya bisa ukunsa, kai da wata jama’ar da take tare da kai. Allah ne kuma Yake qaddara dare da rana. Ya san kuma cewa, ba za ku iya qididdige (sa’o’insa) ba, don haka sai Ya yafe muku; to sai ku karanta abin da ya sauqaqa daga Alqur’ani. Ya san cewa daga cikinku akwai waxanda za su kasance marasa lafiya, waxansu kuma suna tafiya a bayan qasa don fatauci suna neman falala daga Allah, waxansu kuma suna yin yaqi saboda Allah; to sai ku karanta abin da ya sauqaqa daga gare shi (Alqur’ani). Ku kuma tsayar da salla, ku kuma ba da zakka, kuma ku bai wa Allah rance kyakkyawa[1]. Kuma abin da kuka gabatar wa kanku na wani alheri, to za ku same shi wurin Allah, shi ya fi alheri ya kuma fi girman lada. Ku kuma nemi gafarar Allah; lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai


1- Watau su ciyar da dukiyoyinsu don Allah wuraren da suka dace.


Capítulo: Suratul Bayyina

Verso : 5

وَمَآ أُمِرُوٓاْ إِلَّا لِيَعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ حُنَفَآءَ وَيُقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُؤۡتُواْ ٱلزَّكَوٰةَۚ وَذَٰلِكَ دِينُ ٱلۡقَيِّمَةِ

Ba a kuma umarce su ba sai don su bauta wa Allah suna masu tsantsanta addini gare Shi, suna masu kauce wa varna, suna kuma tsayar da salla, kuma suna ba da zakka. Wannan kuwa shi ne addinin miqaqqiyar hanya