فَتَقَبَّلَهَا رَبُّهَا بِقَبُولٍ حَسَنٖ وَأَنۢبَتَهَا نَبَاتًا حَسَنٗا وَكَفَّلَهَا زَكَرِيَّاۖ كُلَّمَا دَخَلَ عَلَيۡهَا زَكَرِيَّا ٱلۡمِحۡرَابَ وَجَدَ عِندَهَا رِزۡقٗاۖ قَالَ يَٰمَرۡيَمُ أَنَّىٰ لَكِ هَٰذَاۖ قَالَتۡ هُوَ مِنۡ عِندِ ٱللَّهِۖ إِنَّ ٱللَّهَ يَرۡزُقُ مَن يَشَآءُ بِغَيۡرِ حِسَابٍ
Sai Ubangijinta Ya karve ta da kyakkyawar karva, kuma Ya yi mata kyakkyawar tarbiyya, kuma Ya danqa renonta a hannun Zakariyya; duk lokacin da Zakariyya ya shiga wurinta a xakin ibada, sai ya sami abinci a wurinta, sai ya ce: “Ya ke Maryamu, wannan daga ina kika samu?” Sai ta ce: “Wannan daga Allah ne; lalle Allah Yana arzurta wanda Ya ga dama ba tare da lissafi ba.”
هُنَالِكَ دَعَا زَكَرِيَّا رَبَّهُۥۖ قَالَ رَبِّ هَبۡ لِي مِن لَّدُنكَ ذُرِّيَّةٗ طَيِّبَةًۖ إِنَّكَ سَمِيعُ ٱلدُّعَآءِ
A wannan lokacin sai Zakariyya ya roqi Ubangijinsa, ya ce: “Ya Ubangijina, Ka ba ni zurriyya ta gari daga gare Ka, lalle Kai Mai amsa roqo ne.”
فَنَادَتۡهُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ وَهُوَ قَآئِمٞ يُصَلِّي فِي ٱلۡمِحۡرَابِ أَنَّ ٱللَّهَ يُبَشِّرُكَ بِيَحۡيَىٰ مُصَدِّقَۢا بِكَلِمَةٖ مِّنَ ٱللَّهِ وَسَيِّدٗا وَحَصُورٗا وَنَبِيّٗا مِّنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ
Sai mala’iku suka kira shi, lokacin yana tsaye yana salla a cikin xakin ibada, (suka ce): “Lalle Allah Yana yi maka albishir da Yahya, wanda yake mai gaskatawa da wata kalma daga Allah, kuma zai zama shugaba, kuma mai tsare kansa daga mata, kuma Annabi daga cikin salihan bayi.”
قَالَ رَبِّ أَنَّىٰ يَكُونُ لِي غُلَٰمٞ وَقَدۡ بَلَغَنِيَ ٱلۡكِبَرُ وَٱمۡرَأَتِي عَاقِرٞۖ قَالَ كَذَٰلِكَ ٱللَّهُ يَفۡعَلُ مَا يَشَآءُ
Ya ce: “Ya Ubangijina, ta yaya zan sami xa, ga shi tsufa ya riga ya cim mini, kuma ga shi matata juya ce?” Sai ya ce: “Kamar haka ne Allah Yake aikata abin da Ya ga dama.”
قَالَ رَبِّ ٱجۡعَل لِّيٓ ءَايَةٗۖ قَالَ ءَايَتُكَ أَلَّا تُكَلِّمَ ٱلنَّاسَ ثَلَٰثَةَ أَيَّامٍ إِلَّا رَمۡزٗاۗ وَٱذۡكُر رَّبَّكَ كَثِيرٗا وَسَبِّحۡ بِٱلۡعَشِيِّ وَٱلۡإِبۡكَٰرِ
Ya ce: “Ya Ubangijina, Ka sanya mini wata alama.” Ya ce: “Alamarka ita ce ka kasa yi wa mutane magana yini uku sai dai da nuni. Kuma ka ambaci Ubangijinka ambato mai yawa, kuma ka yi tasbihi yammaci da safiya.”
وَزَكَرِيَّا وَيَحۡيَىٰ وَعِيسَىٰ وَإِلۡيَاسَۖ كُلّٞ مِّنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ
Da Zakariyya da Yahaya da Isa da Iliyasu; kowanne daga cikinsu yana cikin salihan bayi
ذِكۡرُ رَحۡمَتِ رَبِّكَ عَبۡدَهُۥ زَكَرِيَّآ
(Wannan) ambaton rahamar Ubangijinka ne (da Ya yi wa) Bawansa Zakariyya
إِذۡ نَادَىٰ رَبَّهُۥ نِدَآءً خَفِيّٗا
Lokacin da ya kira Ubangijinsa (ya roqe Shi) cikin asiri
قَالَ رَبِّ إِنِّي وَهَنَ ٱلۡعَظۡمُ مِنِّي وَٱشۡتَعَلَ ٱلرَّأۡسُ شَيۡبٗا وَلَمۡ أَكُنۢ بِدُعَآئِكَ رَبِّ شَقِيّٗا
Ya ce: “Ya Ubangiji lalle qasusuwana sun yi rauni, kaina kuma ya yi fari fat da furfura, Ubangijina ban kuma zama mai tavewa ba game da roqon Ka
وَإِنِّي خِفۡتُ ٱلۡمَوَٰلِيَ مِن وَرَآءِي وَكَانَتِ ٱمۡرَأَتِي عَاقِرٗا فَهَبۡ لِي مِن لَّدُنكَ وَلِيّٗا
“Kuma lalle ni na ji tsoron dangina a bayana[1], matata kuma ga ta bakarara ce, saboda haka Ka yi mini baiwa daga gare Ka ta (xa) majivinci
1- Watau kada su watsar da kulawa da addini, su shagala da neman abincinsu.
يَرِثُنِي وَيَرِثُ مِنۡ ءَالِ يَعۡقُوبَۖ وَٱجۡعَلۡهُ رَبِّ رَضِيّٗا
“(Wanda) zai gaje ni[1] ya kuma gaji iyalan Ya’aqub; Ubangijina kuma Ka sanya shi yardajje (a wurinka).”
1- Watau ya gaji ilimi da annabta da shugabantar gudanar da harkokin addini.
يَٰزَكَرِيَّآ إِنَّا نُبَشِّرُكَ بِغُلَٰمٍ ٱسۡمُهُۥ يَحۡيَىٰ لَمۡ نَجۡعَل لَّهُۥ مِن قَبۡلُ سَمِيّٗا
(Aka ce): Ya Zakariyya, lalle Muna yi maka albishir da samun xa, sunansa Yahya, ba Mu kuwa sanya wa wani sunan ba gabaninsa
قَالَ رَبِّ أَنَّىٰ يَكُونُ لِي غُلَٰمٞ وَكَانَتِ ٱمۡرَأَتِي عَاقِرٗا وَقَدۡ بَلَغۡتُ مِنَ ٱلۡكِبَرِ عِتِيّٗا
Ya ce: “Ubangijina ta qaqa zan samu xa, alhali kuwa matata ta zamanto bakarara ce, ni kuma ga shi na tsufa tukuf”
قَالَ كَذَٰلِكَ قَالَ رَبُّكَ هُوَ عَلَيَّ هَيِّنٞ وَقَدۡ خَلَقۡتُكَ مِن قَبۡلُ وَلَمۡ تَكُ شَيۡـٔٗا
Ya ce: “Kamar haka Ubangijinka Ya faxa (cewa): ‘Shi (wannan) mai sauqi ne a wurina, don kuwa haqiqa Na halicce ka alhalin ba ka zama komai ba.’”
قَالَ رَبِّ ٱجۡعَل لِّيٓ ءَايَةٗۖ قَالَ ءَايَتُكَ أَلَّا تُكَلِّمَ ٱلنَّاسَ ثَلَٰثَ لَيَالٖ سَوِيّٗا
Ya ce: “Ubangijina Ka sanya mini wata alama.” Sai (Allah) Ya ce: “Alamarka ita ce ka kasa yi wa mutane magana (tsawon) kwana uku daidai.”
فَخَرَجَ عَلَىٰ قَوۡمِهِۦ مِنَ ٱلۡمِحۡرَابِ فَأَوۡحَىٰٓ إِلَيۡهِمۡ أَن سَبِّحُواْ بُكۡرَةٗ وَعَشِيّٗا
Sannan (Zakariyya) ya fito wa mutanensa daga wurin ibada ya yi musu ishara cewa: “Ku yi tasbihi safe da maraice.”
وَزَكَرِيَّآ إِذۡ نَادَىٰ رَبَّهُۥ رَبِّ لَا تَذَرۡنِي فَرۡدٗا وَأَنتَ خَيۡرُ ٱلۡوَٰرِثِينَ
(Ka tuna) kuma Zakariya’u lokacin da ya roqi Ubangijinsa (cewa): “Ya Ubangijina, kada Ka bar ni ni kaxai (ba magaji), Kai ne kuwa Fiyayyen magada.”
فَٱسۡتَجَبۡنَا لَهُۥ وَوَهَبۡنَا لَهُۥ يَحۡيَىٰ وَأَصۡلَحۡنَا لَهُۥ زَوۡجَهُۥٓۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ يُسَٰرِعُونَ فِي ٱلۡخَيۡرَٰتِ وَيَدۡعُونَنَا رَغَبٗا وَرَهَبٗاۖ وَكَانُواْ لَنَا خَٰشِعِينَ
Sai Muka amsa masa Muka ba shi Yahya, Muka kuma gyara masa (mahaifar) matarsa. Lallai su sun kasance suna gaggawa wajen yin alherai, suna kuma roqon Mu suna masu kwaxayin (rahamarmu) masu kuma tsoron (azabarmu), sun kuma zamanto masu qasqantar da kai gare Mu