Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 80

وَقَالُواْ لَن تَمَسَّنَا ٱلنَّارُ إِلَّآ أَيَّامٗا مَّعۡدُودَةٗۚ قُلۡ أَتَّخَذۡتُمۡ عِندَ ٱللَّهِ عَهۡدٗا فَلَن يُخۡلِفَ ٱللَّهُ عَهۡدَهُۥٓۖ أَمۡ تَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ مَا لَا تَعۡلَمُونَ

Kuma suka ce: “Wuta ba za ta shafe mu ba sai cikin wasu ‘yan kwanaki qididdigaggu.” Ka ce: “Shin kun yi wani alqawari ne da Allah, don haka Allah ba zai sava alqawarinsa ba? Ko kuma kuna faxar abin da ba ku da ilimi ne kuna jingina wa Allah?”



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 113

وَقَالَتِ ٱلۡيَهُودُ لَيۡسَتِ ٱلنَّصَٰرَىٰ عَلَىٰ شَيۡءٖ وَقَالَتِ ٱلنَّصَٰرَىٰ لَيۡسَتِ ٱلۡيَهُودُ عَلَىٰ شَيۡءٖ وَهُمۡ يَتۡلُونَ ٱلۡكِتَٰبَۗ كَذَٰلِكَ قَالَ ٱلَّذِينَ لَا يَعۡلَمُونَ مِثۡلَ قَوۡلِهِمۡۚ فَٱللَّهُ يَحۡكُمُ بَيۡنَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ فِيمَا كَانُواْ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَ

Yahudawa suka ce: “Nasara ba a kan komai suke ba”, su ma Nasara suka ce: “Yahudawa ba a kan komai suke ba”, alhalin dukkansu suna karanta Littafi. Kamar haka ne waxanda ba su da ilimi suka yi irin maganarsu. Kuma Allah zai yi hukunci a tsakaninsu ranar Alqiyama a kan abin da suka kasance suna savani a cikinsa



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 1

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱتَّقُواْ رَبَّكُمُ ٱلَّذِي خَلَقَكُم مِّن نَّفۡسٖ وَٰحِدَةٖ وَخَلَقَ مِنۡهَا زَوۡجَهَا وَبَثَّ مِنۡهُمَا رِجَالٗا كَثِيرٗا وَنِسَآءٗۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ ٱلَّذِي تَسَآءَلُونَ بِهِۦ وَٱلۡأَرۡحَامَۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلَيۡكُمۡ رَقِيبٗا

Ya ku mutane, ku kiyaye dokokin Ubangijinku Wanda Ya halicce ku daga rai guda xaya, kuma Ya halicci matarsa daga shi, kuma Ya yaxa maza da mata masu yawa daga gare su. Kuma ku kiyaye dokokin Allah Wanda kuke yi wa juna magiya da Shi, kuma ku kiyaye (yanke) zumunci. Lalle Allah Mai kula da ku ne



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 49

أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ يُزَكُّونَ أَنفُسَهُمۚ بَلِ ٱللَّهُ يُزَكِّي مَن يَشَآءُ وَلَا يُظۡلَمُونَ فَتِيلًا

Shin ba ka ganin waxannan da suke tsarkake kawunansu? Ba haka ba ne, Allah ne Yake tsarkake wanda Ya ga dama, kuma ba za a zalunce su ba ko da gwargwadon zaren qwallon dabino ne



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 50

ٱنظُرۡ كَيۡفَ يَفۡتَرُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَۖ وَكَفَىٰ بِهِۦٓ إِثۡمٗا مُّبِينًا

Duba ka ga yadda suke qirqirar qarya su jingina wa Allah; kuma yin haka kaxai ya isa zama wani zunubi mabayyani



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 18

وَقَالَتِ ٱلۡيَهُودُ وَٱلنَّصَٰرَىٰ نَحۡنُ أَبۡنَـٰٓؤُاْ ٱللَّهِ وَأَحِبَّـٰٓؤُهُۥۚ قُلۡ فَلِمَ يُعَذِّبُكُم بِذُنُوبِكُمۖ بَلۡ أَنتُم بَشَرٞ مِّمَّنۡ خَلَقَۚ يَغۡفِرُ لِمَن يَشَآءُ وَيُعَذِّبُ مَن يَشَآءُۚ وَلِلَّهِ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَاۖ وَإِلَيۡهِ ٱلۡمَصِيرُ

Kuma Yahudawa da Nasara suka ce: “Mu ‘ya’yan Allah ne, kuma masoyansa.” Ka ce: “To don me Yake muku azaba a sanadiyyar zunubanku? Ba haka ne ba, ku mutane ne daga cikin waxanda Ya halitta. Yana yin gafara ga wanda Ya ga dama, kuma Yana yin azaba ga wanda Ya ga dama. Kuma mulkin sammai da qasa da abin da yake tsakaninsu na Allah ne, kuma zuwa gare Shi ne makoma take.”



Capítulo: Suratul Mu’uminun

Verso : 101

فَإِذَا نُفِخَ فِي ٱلصُّورِ فَلَآ أَنسَابَ بَيۡنَهُمۡ يَوۡمَئِذٖ وَلَا يَتَسَآءَلُونَ

Sannan idan aka busa qaho to fa babu wata dangantaka (mai amfani) a tsakaninsu a wannan ranar, kuma ba za su tambayi juna ba



Capítulo: Suratul Qasas

Verso : 4

إِنَّ فِرۡعَوۡنَ عَلَا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَجَعَلَ أَهۡلَهَا شِيَعٗا يَسۡتَضۡعِفُ طَآئِفَةٗ مِّنۡهُمۡ يُذَبِّحُ أَبۡنَآءَهُمۡ وَيَسۡتَحۡيِۦ نِسَآءَهُمۡۚ إِنَّهُۥ كَانَ مِنَ ٱلۡمُفۡسِدِينَ

Lalle Fir’auna ya yi xagawa a cikin qasar (Masar) ya kuma mayar da mutanenta qungiyoyi daban-daban, yana bautar da wata qungiyar daga cikinsu, yana yanka ‘ya’yayensu maza, yana kuma qyale matansu da rai. Lalle shi ya kasance cikin mavarnata



Capítulo: Suratul Qasas

Verso : 15

وَدَخَلَ ٱلۡمَدِينَةَ عَلَىٰ حِينِ غَفۡلَةٖ مِّنۡ أَهۡلِهَا فَوَجَدَ فِيهَا رَجُلَيۡنِ يَقۡتَتِلَانِ هَٰذَا مِن شِيعَتِهِۦ وَهَٰذَا مِنۡ عَدُوِّهِۦۖ فَٱسۡتَغَٰثَهُ ٱلَّذِي مِن شِيعَتِهِۦ عَلَى ٱلَّذِي مِنۡ عَدُوِّهِۦ فَوَكَزَهُۥ مُوسَىٰ فَقَضَىٰ عَلَيۡهِۖ قَالَ هَٰذَا مِنۡ عَمَلِ ٱلشَّيۡطَٰنِۖ إِنَّهُۥ عَدُوّٞ مُّضِلّٞ مُّبِينٞ

Sai ya shiga cikin birnin a lokacin hutawar mutanensa, sai ya sami mutum biyu a cikinsa suna faxa; wannan xan qabilarsa ne, wannan kuma daga maqiyansa, sai xan qabilar tasa ya nemi taimakonsa a kan wanda yake daga maqiyansa; to sai Musa ya naushe shi, sai kuwa ya kashe shi; (da ya ga haka sai) ya ce: “Wannan yana daga aikin Shaixan, lalle shi kuwa maqiyi ne mai vatarwa na fili.”



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 22

وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦ خَلۡقُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَٱخۡتِلَٰفُ أَلۡسِنَتِكُمۡ وَأَلۡوَٰنِكُمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّلۡعَٰلِمِينَ

Yana kuma daga cikin ayoyinsa halittar sammai da qasa da kuma sassavawar harsunanku da launukanku. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga ma’abota ilimi



Capítulo: Suratu Sad

Verso : 28

أَمۡ نَجۡعَلُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ كَٱلۡمُفۡسِدِينَ فِي ٱلۡأَرۡضِ أَمۡ نَجۡعَلُ ٱلۡمُتَّقِينَ كَٱلۡفُجَّارِ

Shin za Mu mayar da waxanda suka yi imani suka yi ayyuka nagari kamar masu varna a bayan qasa, ko kuma za Mu mayar da masu taqawa kamar lalatattu?



Capítulo: Suratul Hujurat

Verso : 13

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنَّا خَلَقۡنَٰكُم مِّن ذَكَرٖ وَأُنثَىٰ وَجَعَلۡنَٰكُمۡ شُعُوبٗا وَقَبَآئِلَ لِتَعَارَفُوٓاْۚ إِنَّ أَكۡرَمَكُمۡ عِندَ ٱللَّهِ أَتۡقَىٰكُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمٌ خَبِيرٞ

Ya ku mutane, lalle Mu Muka halicce ku daga namiji da mace, Muka kuma sanya ku al’ummu da qabilu don ku san juna. Lalle mafi girmanku a wurin Allah shi ne wanda ya fi ku taqawa. Lalle Allah Masanin sarari ne, Masanin voye



Capítulo: Suratun Najm

Verso : 32

ٱلَّذِينَ يَجۡتَنِبُونَ كَبَـٰٓئِرَ ٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡفَوَٰحِشَ إِلَّا ٱللَّمَمَۚ إِنَّ رَبَّكَ وَٰسِعُ ٱلۡمَغۡفِرَةِۚ هُوَ أَعۡلَمُ بِكُمۡ إِذۡ أَنشَأَكُم مِّنَ ٱلۡأَرۡضِ وَإِذۡ أَنتُمۡ أَجِنَّةٞ فِي بُطُونِ أُمَّهَٰتِكُمۡۖ فَلَا تُزَكُّوٓاْ أَنفُسَكُمۡۖ هُوَ أَعۡلَمُ بِمَنِ ٱتَّقَىٰٓ

(Su ne) waxanda suke nisantar manya-manyan zunubai da munanan ayyukan savo, sai dai ‘yan qananan zunubai. Lalle Ubangijinka Mayalwacin gafara ne. Shi ne Ya fi sanin ku, tun sanda Ya halicce ku daga qasa, sai ga ku kun zama ‘yan tayi a cikin cikin iyayenku mata; to kada ku tsarkake kanku; Shi ne Ya fi sanin wanda ya fi taqawa



Capítulo: Suratul Qamar

Verso : 43

أَكُفَّارُكُمۡ خَيۡرٞ مِّنۡ أُوْلَـٰٓئِكُمۡ أَمۡ لَكُم بَرَآءَةٞ فِي ٱلزُّبُرِ

Yanzu kafiranku (ku mutanen Makka) su ne suka fi waxancan alheri, ko kuwa kuna da wata hanya ta kuvuta ne a cikin littattafan da aka saukar?



Capítulo: Suratul Jumu’a

Verso : 6

قُلۡ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ هَادُوٓاْ إِن زَعَمۡتُمۡ أَنَّكُمۡ أَوۡلِيَآءُ لِلَّهِ مِن دُونِ ٱلنَّاسِ فَتَمَنَّوُاْ ٱلۡمَوۡتَ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

Ka ce: “Ya ku waxanda suka zama Yahudawa, idan kun riya cewa ku ne masoyan Allah ban da sauran mutane, to ku yi burin mutuwa, idan kun kasance masu gaskiya ne.”



Capítulo: Suratul Munafiqun

Verso : 8

يَقُولُونَ لَئِن رَّجَعۡنَآ إِلَى ٱلۡمَدِينَةِ لَيُخۡرِجَنَّ ٱلۡأَعَزُّ مِنۡهَا ٱلۡأَذَلَّۚ وَلِلَّهِ ٱلۡعِزَّةُ وَلِرَسُولِهِۦ وَلِلۡمُؤۡمِنِينَ وَلَٰكِنَّ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ لَا يَعۡلَمُونَ

Suna cewa: “Tabbas idan muka koma Madina, lalle mafi daraja zai fitar da mafi wulaqanci daga cikinta[1]”. Alhali kuwa girma na Allah ne da Manzonsa da kuma muminai, sai dai kuma munafukai ba sa sanin (haka)


1- Watau shugaban munafukai na Madina Abdullahi xan Ubayyu xan Salul shi ne yake faxa wa Annabi () wannan mummunar maganar.