Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 83

وَإِذۡ أَخَذۡنَا مِيثَٰقَ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ لَا تَعۡبُدُونَ إِلَّا ٱللَّهَ وَبِٱلۡوَٰلِدَيۡنِ إِحۡسَانٗا وَذِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينِ وَقُولُواْ لِلنَّاسِ حُسۡنٗا وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ ثُمَّ تَوَلَّيۡتُمۡ إِلَّا قَلِيلٗا مِّنكُمۡ وَأَنتُم مُّعۡرِضُونَ

Kuma ka tuna lokacin da Muka xauki alqwari daga Banu Isra’ila cewa, ba za ku bauta wa kowa ba sai Allah, kuma za ku kyautata wa iyaye da makusanta da marayu da miskinai, kuma ku riqa yi wa mutane kyakkyawar magana, kuma ku tsai da salla, kuma ku ba da zakka, sannan sai kuka ba da baya sai ‘yan kaxan daga cikinku, alhalin kuna masu bijirewa



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 220

فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِۗ وَيَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡيَتَٰمَىٰۖ قُلۡ إِصۡلَاحٞ لَّهُمۡ خَيۡرٞۖ وَإِن تُخَالِطُوهُمۡ فَإِخۡوَٰنُكُمۡۚ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ ٱلۡمُفۡسِدَ مِنَ ٱلۡمُصۡلِحِۚ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ لَأَعۡنَتَكُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٞ

Game da lamarin duniya da lahira. Kuma suna tambayar ka game da marayu. Ka ce : “Inganta musu dukiyarsu shi ne mafi alheri, kuma in kuka haxa cimakarku da tasu, to ai ‘yan’uwanku ne. Amma fa Allah Ya san mai son yin varna daga wanda yake son yin gyara. Kuma da Allah Ya ga dama da Ya quntata muku. Lalle Allah Mabuwayi ne, Mai hikima.”



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 233

۞وَٱلۡوَٰلِدَٰتُ يُرۡضِعۡنَ أَوۡلَٰدَهُنَّ حَوۡلَيۡنِ كَامِلَيۡنِۖ لِمَنۡ أَرَادَ أَن يُتِمَّ ٱلرَّضَاعَةَۚ وَعَلَى ٱلۡمَوۡلُودِ لَهُۥ رِزۡقُهُنَّ وَكِسۡوَتُهُنَّ بِٱلۡمَعۡرُوفِۚ لَا تُكَلَّفُ نَفۡسٌ إِلَّا وُسۡعَهَاۚ لَا تُضَآرَّ وَٰلِدَةُۢ بِوَلَدِهَا وَلَا مَوۡلُودٞ لَّهُۥ بِوَلَدِهِۦۚ وَعَلَى ٱلۡوَارِثِ مِثۡلُ ذَٰلِكَۗ فَإِنۡ أَرَادَا فِصَالًا عَن تَرَاضٖ مِّنۡهُمَا وَتَشَاوُرٖ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡهِمَاۗ وَإِنۡ أَرَدتُّمۡ أَن تَسۡتَرۡضِعُوٓاْ أَوۡلَٰدَكُمۡ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ إِذَا سَلَّمۡتُم مَّآ ءَاتَيۡتُم بِٱلۡمَعۡرُوفِۗ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ

Kuma iyaye mata za su shayar da ‘ya’yansu tsawon shekara biyu cikakku, ga wanda ya yi nufin ya cika wa’adi na shayarwa. Kuma wajibi ne a kan wanda aka yi wa haihuwa ya ciyar da su (mata masu shayarwa) da yi musu tufafi ta hanyar da aka saba. Ba a xora wa wani rai sai abin da zai iya. Kar a cutar da uwa saboda xanta, haka kuma kar a cutar da uba saboda xansa. Kuma kwatankwacin irin wannan ya wajaba kan magajinsa. To idan su biyun sun yi nufin yaye bisa ga yarjejeniya da shawara da junansu, to babu laifi a kansu. Kuma idan kun yi nufin nema wa ‘ya’yanku mai shayarwa, to babu laifi a kanku idan kun bayar da abin da ya kamata ta yadda aka saba. Kuma ku kiyaye dokokin Allah, kuma ku sani cewa, lalle Allah Mai ganin abin da kuke aikatawa ne



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 2

وَءَاتُواْ ٱلۡيَتَٰمَىٰٓ أَمۡوَٰلَهُمۡۖ وَلَا تَتَبَدَّلُواْ ٱلۡخَبِيثَ بِٱلطَّيِّبِۖ وَلَا تَأۡكُلُوٓاْ أَمۡوَٰلَهُمۡ إِلَىٰٓ أَمۡوَٰلِكُمۡۚ إِنَّهُۥ كَانَ حُوبٗا كَبِيرٗا

Kuma ku bai wa marayu dukiyoyinsu; kuma kada ku musanya kyakkyawa da mummuna; kuma kada ku ci dukiyoyinsu haxe da dukiyoyinku. Lalle yin hakan ya tabbata zunubi ne mai girma



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 6

وَٱبۡتَلُواْ ٱلۡيَتَٰمَىٰ حَتَّىٰٓ إِذَا بَلَغُواْ ٱلنِّكَاحَ فَإِنۡ ءَانَسۡتُم مِّنۡهُمۡ رُشۡدٗا فَٱدۡفَعُوٓاْ إِلَيۡهِمۡ أَمۡوَٰلَهُمۡۖ وَلَا تَأۡكُلُوهَآ إِسۡرَافٗا وَبِدَارًا أَن يَكۡبَرُواْۚ وَمَن كَانَ غَنِيّٗا فَلۡيَسۡتَعۡفِفۡۖ وَمَن كَانَ فَقِيرٗا فَلۡيَأۡكُلۡ بِٱلۡمَعۡرُوفِۚ فَإِذَا دَفَعۡتُمۡ إِلَيۡهِمۡ أَمۡوَٰلَهُمۡ فَأَشۡهِدُواْ عَلَيۡهِمۡۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ حَسِيبٗا

Kuma ku jarraba hankulan marayu, har lokacin da suka isa aure, to idan kun ga alamar hankali tare da su, sai ku ba su dukiyoyinsu; kuma kada ku ci dukiyarsu ta hanyar almubazzaranci da kuma gaggawa don gudun kada su girma. Duk kuma wanda ya kasance mawadaci ne, to ya kame kansa; wanda kuma ya kasance mabuqaci ne, to ya ci ta hanyar da ta dace. To idan za ku miqa musu dukiyoyinsu, sai ku kafa musu shaidu. Kuma Allah Ya isa Mai hisabi



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 8

وَإِذَا حَضَرَ ٱلۡقِسۡمَةَ أُوْلُواْ ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينُ فَٱرۡزُقُوهُم مِّنۡهُ وَقُولُواْ لَهُمۡ قَوۡلٗا مَّعۡرُوفٗا

Kuma idan dangi makusanta da marayu da mabuqata suka halarci rabon gado, to ku arzurta su daga cikin wannan dukiya, kuma ku faxa musu magana mai daxi



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 10

إِنَّ ٱلَّذِينَ يَأۡكُلُونَ أَمۡوَٰلَ ٱلۡيَتَٰمَىٰ ظُلۡمًا إِنَّمَا يَأۡكُلُونَ فِي بُطُونِهِمۡ نَارٗاۖ وَسَيَصۡلَوۡنَ سَعِيرٗا

Lalle waxanda suke cin dukiyar marayu bisa zalunci, wuta ce kawai suke ci a cikkunansu; kuma da sannu za su shiga wuta mai tsananin quna



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 26

يُرِيدُ ٱللَّهُ لِيُبَيِّنَ لَكُمۡ وَيَهۡدِيَكُمۡ سُنَنَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكُمۡ وَيَتُوبَ عَلَيۡكُمۡۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٞ

Allah Yana nufin yi muku bayani ne, kuma Ya shiryar da ku hanyoyin waxanda suka gabace ku, kuma Ya karvi tubanku. Kuma Allah Mai yawan sani ne, Mai hikima



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 127

وَيَسۡتَفۡتُونَكَ فِي ٱلنِّسَآءِۖ قُلِ ٱللَّهُ يُفۡتِيكُمۡ فِيهِنَّ وَمَا يُتۡلَىٰ عَلَيۡكُمۡ فِي ٱلۡكِتَٰبِ فِي يَتَٰمَى ٱلنِّسَآءِ ٱلَّـٰتِي لَا تُؤۡتُونَهُنَّ مَا كُتِبَ لَهُنَّ وَتَرۡغَبُونَ أَن تَنكِحُوهُنَّ وَٱلۡمُسۡتَضۡعَفِينَ مِنَ ٱلۡوِلۡدَٰنِ وَأَن تَقُومُواْ لِلۡيَتَٰمَىٰ بِٱلۡقِسۡطِۚ وَمَا تَفۡعَلُواْ مِنۡ خَيۡرٖ فَإِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِهِۦ عَلِيمٗا

Kuma suna neman fatawarka game da lamarin mata. Ka ce: “Allah ne Yake ba ku fatawa game da lamarinsu da kuma abin da ake karanta muku a cikin Littafi dangane da marayu mata waxanda ba kwa iya ba su sadakinsu cikakke, ga shi kuma kuna kwaxayin ku aure su; hakanan da kuma (dukiyar) yara masu rauni. Kuma ku tsaya wajen kula da (dukiyar) marayu ta hanyar adalci. Kuma duk abin da kuka aikata na alheri, to lalle Allah Yana sane da shi.”



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 139

وَقَالُواْ مَا فِي بُطُونِ هَٰذِهِ ٱلۡأَنۡعَٰمِ خَالِصَةٞ لِّذُكُورِنَا وَمُحَرَّمٌ عَلَىٰٓ أَزۡوَٰجِنَاۖ وَإِن يَكُن مَّيۡتَةٗ فَهُمۡ فِيهِ شُرَكَآءُۚ سَيَجۡزِيهِمۡ وَصۡفَهُمۡۚ إِنَّهُۥ حَكِيمٌ عَلِيمٞ

Kuma suka ce: “Abin da yake cikin waxannan dabbobi, a kevance yake ga mazajenmu, amma haramun ne ga matayenmu.” Idan kuma ya zamo mushe, to su duka sai su yi tarayya a kansa. Da sannu (Allah) zai yi musu sakayyar wannan abin da suka siffanta. Lalle Shi Mai hikima ne, Mai yawan sani



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 41

۞وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّمَا غَنِمۡتُم مِّن شَيۡءٖ فَأَنَّ لِلَّهِ خُمُسَهُۥ وَلِلرَّسُولِ وَلِذِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينِ وَٱبۡنِ ٱلسَّبِيلِ إِن كُنتُمۡ ءَامَنتُم بِٱللَّهِ وَمَآ أَنزَلۡنَا عَلَىٰ عَبۡدِنَا يَوۡمَ ٱلۡفُرۡقَانِ يَوۡمَ ٱلۡتَقَى ٱلۡجَمۡعَانِۗ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ

Kuma ku sani cewa duk abin da kuka samu na ganima to lalle xaya bisa biyar na Allah ne da Manzo da kuma makusantan (Annabi)[1], da marayu da kuma miskinai da kuma matafiya[2], idan kun kasance kun yi imani da Allah da kuma abin da Muka saukar wa bawanmu ranar rabewa (ranar yaqin Badar) ranar da qungiyoyin nan biyu suka haxu. Allah kuwa Mai iko ne a kan komai


1- Su ne Banu Hashim da Banu Muxxalib waxanda aka haramta musu cin zakka.


2- Suran kashi huxun kuwa na mayaqa ne.


Capítulo: Suratul Isra’i

Verso : 24

وَٱخۡفِضۡ لَهُمَا جَنَاحَ ٱلذُّلِّ مِنَ ٱلرَّحۡمَةِ وَقُل رَّبِّ ٱرۡحَمۡهُمَا كَمَا رَبَّيَانِي صَغِيرٗا

Ka kuma qasqantar da kai gare su don tausayawa, ka kuma ce: “Ubangijina Ka ji qan su kamar yadda suka raine ni ina xan qarami.”



Capítulo: Suratul Isra’i

Verso : 31

وَلَا تَقۡتُلُوٓاْ أَوۡلَٰدَكُمۡ خَشۡيَةَ إِمۡلَٰقٖۖ نَّحۡنُ نَرۡزُقُهُمۡ وَإِيَّاكُمۡۚ إِنَّ قَتۡلَهُمۡ كَانَ خِطۡـٔٗا كَبِيرٗا

Kada kuma ku kashe ‘ya’yayenku don tsoron talauci: Mu ne Muke arzuta su har ma da ku. Lalle kashe su kuskure ne babba



Capítulo: Suratul Kahf 

Verso : 82

وَأَمَّا ٱلۡجِدَارُ فَكَانَ لِغُلَٰمَيۡنِ يَتِيمَيۡنِ فِي ٱلۡمَدِينَةِ وَكَانَ تَحۡتَهُۥ كَنزٞ لَّهُمَا وَكَانَ أَبُوهُمَا صَٰلِحٗا فَأَرَادَ رَبُّكَ أَن يَبۡلُغَآ أَشُدَّهُمَا وَيَسۡتَخۡرِجَا كَنزَهُمَا رَحۡمَةٗ مِّن رَّبِّكَۚ وَمَا فَعَلۡتُهُۥ عَنۡ أَمۡرِيۚ ذَٰلِكَ تَأۡوِيلُ مَا لَمۡ تَسۡطِع عَّلَيۡهِ صَبۡرٗا

“To game da shi garun nan kuwa ya kasance na wasu yara ne marayu a cikin wannan birnin, a qarqashinsa kuwa da akwai wata taska tasu, mahaifinsu kuma ya kasance mutumin kirki ne, to sai Ubangijinka Ya nufi su girma su cika hankalinsu su, kuma fito da taskarsu, don rahama daga Ubangijinka. Ban aikata haka ba ne da raxin kaina. Wannan shi ne fassarar abin da ka kasa haquri a kansa.”



Capítulo: Suratu Maryam

Verso : 7

يَٰزَكَرِيَّآ إِنَّا نُبَشِّرُكَ بِغُلَٰمٍ ٱسۡمُهُۥ يَحۡيَىٰ لَمۡ نَجۡعَل لَّهُۥ مِن قَبۡلُ سَمِيّٗا

(Aka ce): Ya Zakariyya, lalle Muna yi maka albishir da samun xa, sunansa Yahya, ba Mu kuwa sanya wa wani sunan ba gabaninsa



Capítulo: Suratu Luqman

Verso : 19

وَٱقۡصِدۡ فِي مَشۡيِكَ وَٱغۡضُضۡ مِن صَوۡتِكَۚ إِنَّ أَنكَرَ ٱلۡأَصۡوَٰتِ لَصَوۡتُ ٱلۡحَمِيرِ

“Kuma ka tsakaita tafiyarka, kuma ka yi qasa-qasa da muryarka. Lalle mafi munin muryoyi ita ce muryar jakai.”



Capítulo: Suratux Xur

Verso : 26

قَالُوٓاْ إِنَّا كُنَّا قَبۡلُ فِيٓ أَهۡلِنَا مُشۡفِقِينَ

Suka ce: “Lalle sanda muke cikin iyalinmu (a duniya) kafin wannan, mun kasance masu tsoron azabar Allah



Capítulo: Suratul Hashr

Verso : 7

مَّآ أَفَآءَ ٱللَّهُ عَلَىٰ رَسُولِهِۦ مِنۡ أَهۡلِ ٱلۡقُرَىٰ فَلِلَّهِ وَلِلرَّسُولِ وَلِذِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينِ وَٱبۡنِ ٱلسَّبِيلِ كَيۡ لَا يَكُونَ دُولَةَۢ بَيۡنَ ٱلۡأَغۡنِيَآءِ مِنكُمۡۚ وَمَآ ءَاتَىٰكُمُ ٱلرَّسُولُ فَخُذُوهُ وَمَا نَهَىٰكُمۡ عَنۡهُ فَٱنتَهُواْۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۖ إِنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ

Abin da Allah ya bai wa Manzonsa na wata dukiya daga mutanen alqaryu, to na Allah ne da Manzonsa da kuma danginsa na kusa[1] da marayu da miskinai da matafiyin (da guzuri ya yanke wa), don kada ya zama mai juyawa tsakanin mawadata daga cikinku. Kuma abin da Manzo ya ba ku sai ku karve shi, abin kuma da ya hana ku sai ku hanu. Ku kuma kiyaye dokokin Allah; lalle Allah Mai tsananin uquba ne


1- Watau Banu Hashim da Banul Muxxalib, waxanda aka haramta musu karvar sadaka ko zakka.


Capítulo: Suratul Insan

Verso : 8

وَيُطۡعِمُونَ ٱلطَّعَامَ عَلَىٰ حُبِّهِۦ مِسۡكِينٗا وَيَتِيمٗا وَأَسِيرًا

Suna kuma ciyar da abinci tare da suna son sa ga miskini da maraya da kuma ribataccen yaqi



Capítulo: Suratud Dhuha

Verso : 9

فَأَمَّا ٱلۡيَتِيمَ فَلَا تَقۡهَرۡ

Don haka maraya fa kada ka yi masa fin qarfi