قُل لِّلۡمُؤۡمِنِينَ يَغُضُّواْ مِنۡ أَبۡصَٰرِهِمۡ وَيَحۡفَظُواْ فُرُوجَهُمۡۚ ذَٰلِكَ أَزۡكَىٰ لَهُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ خَبِيرُۢ بِمَا يَصۡنَعُونَ
Ka ce da muminai maza su kame idanuwansu[1] kuma su kiyaye farjinsu. Wannan shi ya fi tsarki a gare su. Lalle Allah Masanin abin da suke aikatawa ne
1- Watau su kawar da idanuwansu daga kallon matan da bai halatta su kalle su ba, hakanan da kallon al’aurarsu.
وَقُل لِّلۡمُؤۡمِنَٰتِ يَغۡضُضۡنَ مِنۡ أَبۡصَٰرِهِنَّ وَيَحۡفَظۡنَ فُرُوجَهُنَّ وَلَا يُبۡدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا مَا ظَهَرَ مِنۡهَاۖ وَلۡيَضۡرِبۡنَ بِخُمُرِهِنَّ عَلَىٰ جُيُوبِهِنَّۖ وَلَا يُبۡدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا لِبُعُولَتِهِنَّ أَوۡ ءَابَآئِهِنَّ أَوۡ ءَابَآءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوۡ أَبۡنَآئِهِنَّ أَوۡ أَبۡنَآءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوۡ إِخۡوَٰنِهِنَّ أَوۡ بَنِيٓ إِخۡوَٰنِهِنَّ أَوۡ بَنِيٓ أَخَوَٰتِهِنَّ أَوۡ نِسَآئِهِنَّ أَوۡ مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُهُنَّ أَوِ ٱلتَّـٰبِعِينَ غَيۡرِ أُوْلِي ٱلۡإِرۡبَةِ مِنَ ٱلرِّجَالِ أَوِ ٱلطِّفۡلِ ٱلَّذِينَ لَمۡ يَظۡهَرُواْ عَلَىٰ عَوۡرَٰتِ ٱلنِّسَآءِۖ وَلَا يَضۡرِبۡنَ بِأَرۡجُلِهِنَّ لِيُعۡلَمَ مَا يُخۡفِينَ مِن زِينَتِهِنَّۚ وَتُوبُوٓاْ إِلَى ٱللَّهِ جَمِيعًا أَيُّهَ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ
Kuma ka ce da muminai mata su kame idanuwansu[1] kuma su kiyaye farjinsu, kada kuma su fito da adonsu sai dai abin da ya bayyana daga gare shi[2]; kuma su sanya lulluvinsu a kan wuyan rigunansu[3]; kada kuma su fitar da adonsu sai ga mazajensu ko iyayensu ko iyayen mazajensu ko ‘ya’yansu ko ‘ya’yayen mazajensu ko ‘yan’uwansu maza ko kuma ‘ya’yan ‘yan’uwansu maza ko ‘ya’yan ‘yan’uwansu mata ko kuma mata ‘yan’uwansu ko kuma bayinsu ko kuma mazaje masu bin su (don neman abinci) ba kuma masu buqatar mata ba[4], ko kuma qananan yara waxanda ba su san sha’awar al’aurar mata ba; kada kuma su buga qafafuwansu don a gane abin da suka voye na adon qafafunsu (watau mundaye). Kuma ku tuba ga Allah gaba xayanku ya ku waxannan muminai don ku rabauta
1- Watau su kawar da idanuwansu daga kallon abin da bai halatta su kalla ba.
2- Watau abin da ba za a iya voye shi ba, kamar tufafi.
3- Watau domin a daina ganin gashinsu da wuyansu da adonsu na wuya.
4- Watau tsofaffi tukub waxanda sun daina sha’awar mata gaba xaya.
وَٱلۡقَوَٰعِدُ مِنَ ٱلنِّسَآءِ ٱلَّـٰتِي لَا يَرۡجُونَ نِكَاحٗا فَلَيۡسَ عَلَيۡهِنَّ جُنَاحٌ أَن يَضَعۡنَ ثِيَابَهُنَّ غَيۡرَ مُتَبَرِّجَٰتِۭ بِزِينَةٖۖ وَأَن يَسۡتَعۡفِفۡنَ خَيۡرٞ لَّهُنَّۗ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٞ
Tsofaffin mata kuwa waxanda ba sa tsammanin yin aure to babu laifi a kansu su sauke lulluvinsu, amma ba masu fitar da adonsu ba; amma kuma su yi lulluvi shi ya fi zama alheri a gare su. Allah kuwa Mai ji ne, Masani
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَدۡخُلُواْ بُيُوتَ ٱلنَّبِيِّ إِلَّآ أَن يُؤۡذَنَ لَكُمۡ إِلَىٰ طَعَامٍ غَيۡرَ نَٰظِرِينَ إِنَىٰهُ وَلَٰكِنۡ إِذَا دُعِيتُمۡ فَٱدۡخُلُواْ فَإِذَا طَعِمۡتُمۡ فَٱنتَشِرُواْ وَلَا مُسۡتَـٔۡنِسِينَ لِحَدِيثٍۚ إِنَّ ذَٰلِكُمۡ كَانَ يُؤۡذِي ٱلنَّبِيَّ فَيَسۡتَحۡيِۦ مِنكُمۡۖ وَٱللَّهُ لَا يَسۡتَحۡيِۦ مِنَ ٱلۡحَقِّۚ وَإِذَا سَأَلۡتُمُوهُنَّ مَتَٰعٗا فَسۡـَٔلُوهُنَّ مِن وَرَآءِ حِجَابٖۚ ذَٰلِكُمۡ أَطۡهَرُ لِقُلُوبِكُمۡ وَقُلُوبِهِنَّۚ وَمَا كَانَ لَكُمۡ أَن تُؤۡذُواْ رَسُولَ ٱللَّهِ وَلَآ أَن تَنكِحُوٓاْ أَزۡوَٰجَهُۥ مِنۢ بَعۡدِهِۦٓ أَبَدًاۚ إِنَّ ذَٰلِكُمۡ كَانَ عِندَ ٱللَّهِ عَظِيمًا
Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku shiga gidajen Annabi sai idan an yi muku izini zuwa (cin) abinci, alhali ba tare da kuna jiran dahuwarsa ba, sai dai kuma idan aka kira ku, to ku shiga, sannan idan kuka ci sai ku fice, ba tare da yin wata hira ta xebe kewa ba. Lalle wannan ya kasance yana cutar Annabi, sai yakan ji kunyar ku; Allah kuwa ba Ya jin kunyar (faxar) gaskiya. Idan kuma za ku tambaye su (wato matan Annabi) wani abu na amfani, sai ku tambaye su ta bayan shamaki. Yin wannan shi ya fi tsarki ga zukatanku da kuma zukatansu. Kuma bai kamace ku ba ku cuci Manzon Allah ko kuma ku auri matansa a bayansa har abada. Lalle (yin) wannan ya kasance abu mai girma a wurin Allah
لَّا جُنَاحَ عَلَيۡهِنَّ فِيٓ ءَابَآئِهِنَّ وَلَآ أَبۡنَآئِهِنَّ وَلَآ إِخۡوَٰنِهِنَّ وَلَآ أَبۡنَآءِ إِخۡوَٰنِهِنَّ وَلَآ أَبۡنَآءِ أَخَوَٰتِهِنَّ وَلَا نِسَآئِهِنَّ وَلَا مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُهُنَّۗ وَٱتَّقِينَ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ شَهِيدًا
Babu laifi a kansu (matan) game da iyayensu maza (su gan su kuma su yi magana da su ba tare da shamaki ba) da kuma ‘ya’yansu maza da ‘ya’uwansu da ‘ya’yan ‘yan’uwansu maza da ‘ya’yan ‘yan’uwansu mata, da kuma matansu da bayinsu. Ku kiyaye dokokin Allah. Lalle Allah Ya kasance Mai ganin komai ne
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ قُل لِّأَزۡوَٰجِكَ وَبَنَاتِكَ وَنِسَآءِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ يُدۡنِينَ عَلَيۡهِنَّ مِن جَلَٰبِيبِهِنَّۚ ذَٰلِكَ أَدۡنَىٰٓ أَن يُعۡرَفۡنَ فَلَا يُؤۡذَيۡنَۗ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمٗا
Ya kai wannan Annabi, faxa wa matanka da ‘ya’yanka mata da kuma matan muminai (cewa) su sanya lulluvinsu. Wannan shi ya fi sanya wa a gane su[1], don kada a cuce su. Allah kuma Ya kasance Mai gafara ne, Mai rahama
1- Watau a tantance tsakaninsu da mata marasa kamun kai.